← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 112

Sashe 47

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga gida direct ta wuce ɗakinta,  ko mayafinta bata cire ba, ta zauna haɗe da soma yaye ledan da akayimawa kwalinnan ado dashi,   tana buɗe kwalin tayi arba da wani ƙatuwar ta karda wanda aka naɗeta,  cikin sauri ta ɗago takardan haɗe da soma warwareta, amatuƙar razane tayi wurgi da takardan sakamakon idanunta da sukayi mata tozali da zanen hoton dake jikin takardan.

(🤔Ga Zaid ga Sadeeq ko waye cikinsu zai mallaki Zahrah🤷‍♀)

*17/December/2019*

*Follow me ...*
*Wattpad user name* *@fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *SHU'UMIN NAMIJI!!*

     
        *Written By*
  *PHATYMASARDAUNA*
   _(Shalelen Kainuwa)_

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
      @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

     *CHAPTER 61 to 62*

Idanu ta ƙara zarowa domin tabbatar mawa kanta cewa abun da tagani gaskiya ne, ko kuwa, gizo idanunta keyi mata.

Tabbas dagaske ne bawai gizo bane, hoton zanen fuskarta ne raɗau ajikin takardan. Hanunta na rawa haka ta durƙusa ƙasa, haɗe da sanya hanu ta sake ware takardan, tabbas itaɗince babu ko kokonto, zanen fuskarta ce kwance ajikin takardan, amma saboda tsananin kyawun da zanen yayi tamkar azahiri haka zaka gani,   hanu tasanya ta shafi zanen, cike da fargaba haɗe da ɗaurewar kai.

Lallai yazama dole a gareta tanemo wanda yake aikata mata waƴan nan abubuwan,  kusan kwana uku yanzu kenan ana turo mata da saƙonni, bata kuma san daga waye bane.

Bata damu da ta duba sauran kayan dake cikin kwalin ba, ta tattara shi ta ɓoye acikin kayanta.

Zama tayi dirshan akan katifa tana mai da numfashi akai akai, sosai abun yabata mamaki, tabbas ko ma waye ne wanda yake bibiyarta ta tabbata yayi mata farin sani, amma kuma rainin hankalin yayi yawa, dole zataimawa tufkar hanci. Abun da ta ƙudurta kenan acikin zuciyarta domin iskancin yasoma isarta.

Ƙarfe 6:30 na yammaci Dr Sadeeq yayi wa gidansu Zahrah tsinke, bayan yasha adon sa cikin riga da wando na shadda ƴar bugu mai kyau. Zama yayi acikin motarsa yana mai jiran fitowar Zahrah, domin kuwa yamata waya yasanar da'ita cewa gashi nan, a ƙofar gidansu.

Kafeta da idanu yayi domin kuwa bakaɗan ba tayi masa kyau, cikin shigar doguwar rigan dake jikinta, lallai Zahrah ƙarshe ce wajen haɗuwa dakuma kyau.

Fuskarta ɗauke da murmushi Zahrah ta ƙaraso wajen da motar tasa take fake.  Tsayawa tayi ajikin motar, batare da ta buɗe tashiga ba. Ganin haka yasa Dr Sadeeq buɗe murfin motar yafito.

"Yau kuma aji ake jamin  ne?" ya tambayeta cikin yanayin tsokana.

Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da juya idanunta.    "Eh mana, ko bankai naja aji bane?" itama ta tambayesa cikin yanayi na shauƙi.

"Murmushi yayi haÉ—e da É—age giransa sama "Kin isa har kinma wuce, ko bakisan cewa keÉ—in tamusamman bace?"

Hararan wasa Zahrah ta wurgamai haÉ—e da kawar da kanta gefe, batare da tace dashi komai ba. Haka take al'adar ta ne, bakoda wani lokaci take bada amsar tambaya ba, domin a cewarta shiru ma magana ne.

"Kona zagayo na buɗe miki murfin motar ne gimbiyata, saboda  naga kamar bazaki iya ba ?" yafaɗi hakan cike da kulawa.

"A'a ba buƙatar hakan, ni dakaina ma zan iya" taƙare maganar tana mai buɗe murfin motar, haɗe da shiga tayi mawa kanta mazauni.

Shima komawa yayi cikin motar ya zauna. Bayan ya É—aura duka idanunsa a kanta.

"Kinyi kyau sosai, fiye da ko yaushe" yafaÉ—i haka yanamai kashe idanunsa.

Ɗanguntun murmushi Zahrah tayi "Nagode" tace dashi ataƙaice

Jinjina kansa yayi azuciyarsa kuwa cewa yayi "Lallai Zahrah tana da aji, duk da ta rasa Virginity ɗinta hakan baisanya ta zama wata sakaka da'ita ba, yanason mace wacce ta'iya takunta, wacce bata sakar baki tayita dariya like mental problem, wasu matan da zaran kace dasu sunyi kyau tofa take zasu wage baki suita ƙyaƙyata dariya,  babu wani ɗan jan aji ba komai.  nima shaida ce irin su Sister Munubiya idan kace dasu sunyi kyau ae har kyautan kuɗi zasu baka tsabar daɗi🤣"

Sake gyara zamansa yayi haÉ—e da dawo da nutsuwarsa zuwa gareta.

"Zaki'iya zama dani a ko wani irin hali Zahrah?"
Ya jefomata tambayar da bata tsammaci jinsa ba.

Cikin yanayin mamaki Zahrah ta dawo da kallonta garesa, haÉ—e da cewa "Banfahimci maikake nufi ba"

"Inanufin zaki iya rayuwa dani ako wani irin hali na tsinci kaina? sannan zaki iya yarda na haÉ—aku ku biyu na aura?" yakuma maimaita tambayar tasa.

Dummm haka Zahrah taji ƙirjinta ya buga, idan da badon kada yace ta rainasa ba, to tabbas da zatace dashi yasake maimaita maganar da yayi. Domin idan kunnuwanta sunjiye mata dai dai, to kuwa bata da amsar da zata basa, domin koda ta basa amsa zata iya faɗuwa, saboda balallai ta bashi amsa dai dai da abun da ya tambaya ba.

Idanunsa duka ya tsura mata,  amsa kawai yakeson ji daga bakinta.

Kasa ce dashi komai tayi, domin kuwa haryanzu bata gama haÉ—a amsar da zata basa ba.

"Nasani dama ba lallaine ki amince ba, Hajiya na ta amince da aurena dake, amma kuma kamar yanda nafaɗamiki a baya, tun tuni akwai zaɓin da tayimin, takuma umarceni da na aureku duka biyu, shin zaki iya aurena a haka, zaki iya zama da wata a matsayin kishiyar ki?"  yafaɗi hakan cike da zaƙuwan son jin amsa daga gareta.

Jikinta ne gaba ɗaya yayi sanyi, take taji zuciyarta ta karaya, batasan ya'ake zama da kishiya ba,  haryanzu ita yarinyace, bakomai tasani  na game da al'amarin duniya ba, tanaji a labarai irin illan da kishiyoyi suke mawa junansu saboda kishi, amma ita yanzu ba wannan bane a gabanta,  makomarta na gaba take tunawa, shinya zata kasance?" ta tambayi zuciyarta...

"Kinyi shiru kice wani abu  mana zahrah ko zuciyata zata daina bugawan da takeyi" Dr yafaɗi hakan cikin yanayin damuwa.

"Bazan taɓa ƙin aurenka ba, sai dai idan har kaine kace kafasa aurena, sai dai kuma inajin tsoro, bansan mene zai kasance dani gaba ba, dan Allah kada soyayyar matarka ta ruɗeka, ka wulaƙantani, banda wani madogari sai ALLAH sai kuma kai" taƙare maganar cikin rawar murya, yayinda idanunta sukayi rau rau dasu, alamar zasu zubda ƙwalla.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe, haɗe da sakin ɗan taƙaitaccen murmushi.   "Har abada kada kitaɓa tunanin zan wulaƙantaki Zahrah, inasonki da gaske bada wasa ba,  namiki alƙwari zan kamanta adalci a tsakaninku, bazan juya miki bayaba insha Allah!" Doctor Sadeeq ya faɗi haka cike da lallashi.

Tuni idanun Zahrah suncika da ƙwalla, amma idan ta tuno cewa bata da zaɓi sai taji gwamma kawai ta daure zuciyarta, haka ta ta ƙaddaran take.

"Kada kiyi kuka kinji My Princess, ina tare dake ako wani lokaci,  zankuma share miki dukkanin hawayenki nan bada jimawa ba namiki alƙawari"

Saurin maida hawayenta tayi haɗe da ƙaƙalo murmushin dole ta'aza akan fuskarta, wan nan damuwarta ne ita kaɗai, baikamata ace tabari Dr Sadeeq yagane ba, lallai tun yanzu yakamata ta zama mai juriya.

"Baffa yana gida kuwa?" Dr. Sadeeq ya tambaya.

Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haÉ—e da kaÉ—a masa kai alamar "Eh"

Kai yajinjina haɗi  da cewa "Yanaga duk jikinki yayi sanyi? banace kada kisa damuwa a ranki ba" cikin kulawa yayi maganar.

Cike da shagwaɓa Zahrah ta langwaɓar  da kanta gefe haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba,  "Nibansa damuwa a raina ba"  tace haka cikin sanyayewar jiki.

Wani irin kallo maiɗauke da ma'anoni masu yawa Dr.Sadeeq yashiga yi mata, ji yake tamkar yajawota jikinsa ya rungumeta tsam acikin ƙirjinsa,   saboda ako da yaushe idan yana tare da'ita wani irin feeling yakeji a jikinsa.

"Kije kimin sallama da Baffa inaso zamuyi magana" 

"To" kawai tace dashi haɗi da buɗe murfin motar tafita. Dakallo kawai ya bita harta shige  gida.

Tana shiga cikin gida ta iske Baffa yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakinsa.

"Zahrah har kindawo? badai likitan yatafi ba?" Baffa yajeromata tambayoyi alokaci É—aya.

"A'a baitafi ba Baffa, shine ma yace nace ma yana son magana dakai" Zahrah tafaÉ—i haka ga Baffa cikin girmamawa.

"To Allah yasa lafiya, yanzu kuwa zanje na sa mesa"   ya faɗi  maganar yana mai nufar hanyar fita daga gidan.

Zahrah kuwa É—akinta takoma.
Sosai maganar Dr.Sadeeq yataɓa mata zuciya,  bakomai take hangomawa kanta ba, sai yanda makomarta zai kasance acikin gidansa, tabbas ta tabbatar wacce zai aura, ba irin ta bane, tasan tana da galihu, saɓanin ita da take ko oho, sannan kuma dole zata ga banbanci daga ƴan uwansa,  haka ma Dr.Sadeeq ɗin dole zai banbantasu, saboda waccar zai sameta a budurwa, saɓanin ita da zai sameta ba'a budurwa ba,  kukane yaƙwace mata  mai sauti,  cusa kanta cikin cinyoyinta tayi tashiga rera kukanta,  har abada cutar da Zaid yayi mata bazai  taɓa gushewa ba.....

"Alhmdlh masha Allah! haƙiƙa naji daɗin wannan magana taka Likita, lallai kacika mutumin kirki kuma mutumin ƙwarai, Allah yasaka ma da gidan Aljanna, kuma idan dai Zahrah ce kada kaji komai natabbatar itama tana ƙaunarka, saboda haka nabaka izini ka turo magabatanka, don mu tsaida magana,kuma maganar bayarwa nabaka Zahrah!" Baffa yafaɗi haka cikin farinciki, duk da kuwa  cewa dama tun abaya yasan cewa Dr.Sadeeq yanason Zahrah, amma sake tabbatar masa da Dr. ɗin yayi yanzu, yasanyashi jin daɗi, domin shima yanzu burinsa shine ya inganta farincikin marainiyar Allah wato Zahrah..

Farinciki ne sosai yakama Dr.Sadeeq, yaji daÉ—in aminta dashi da Baffa yayi.

"Nagode da wannan dama da kabani Baffa, Allah yajiƙan magabata" Dr Sadeeq yafaɗa cike da girmamawa.

"Mune da godiya Likita, ai mu ba'abun da zamuce maka saidai fatan alkhairi" Baffa yafaɗa shima cikin jin daɗi, domin yasan Zahrah na auren Dr.Sadeeq wahalanta yaƙare da yardan Allah,saboda yana da tabbacin cewa Dr.Sadeeq zai bata kyakkyawan kulawa, duk da kuwa cewa Dr.Sadeeq ɗin yasanar dashi cewa ba Zahrah ita kaɗai zai auraba, yasanar dashi komai, kuma Baffa yayi na'am da hakan, saboda shi baimaga wani aibu acikin hakan ba, ai namiji mijin mace huɗu ne.
(Nima nace wannan gaskia ne, sbd haka duk me mace ɗaya ya ƙara😜😂)

Cike da farinciki Baffa da Likita sukayi sallama, yayinda Baffa yakoma cikin gida, ya kumace da Dr.Sadeeq zai turo masa Zahrah suyi sallama.
Chapter 47 · 0% Book details