Sashe 43
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"ZAHRAH!" yaƙira sunanta a bayyane, duk da kuwa yasan cewa bazata ji sa ba. dai dai lokacin daya soma yunƙurin buɗe murfin motarsa don yaƙarasa gareta, dai dai lokacin itakuma ta shige cikin mota tare da Husnah.
*13/December/2019*
 Â
 *Voted, Comment, and Share please.... Follow me on Wattpad @fatymasardauna
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
        *SHU'UMIN NAMIJI !!*
   *Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated to My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
       *WATTPAD*
    @fatymasardauna
     ___________________
*Editing is not allowed📵*
  *CHAPTER 57 to 58*
Cikin Hanzari ya buɗe murfin motar tasa ya fito, sai dai baikai ga ƙarasawa garesu ba, motar su ta gangara kan titi haɗe da ɗaukar hanya.
Hannayensa duka biyu yasanya ya kama ƙugunsa, haɗe da furzar da iskan numfashi ta bakinsa, sam baiso haka ba, amma babu yanda ya'iya dole binsu zaiyi.
Kallonsa yamaida ga sauran cincirindon É—aliban da suke tsaye a bakin gate É—in makarantar.
Gani yayi gaba ɗaya sun saki baki da hanci suna kallonsa, sai kace wanda suka ga baƙon halitta, bama kamar ƴan matan dake tsaye a wajen.
Tsuka mai sauti yayi haÉ—e da komawa cikin motarsa, da gudun gaske ya cilla motar tasa kan titi, haÉ—e da rufa mawa motar su Zahrah baya.
"Yadai, naga lokaci ɗaya duk kinyi wata iri dake?" Husnah tatambayi Zahrah wacce tazama silently lokaci ɗaya.
A jiyar zuciya ta sauƙe haɗe da maida kallonta ga Husnah " Faɗuwar gaba nakeji Husnah, ban kuma san dalilin hakan ba" Zahrah ta faɗi haka cikin damuwa.
"To fa, Allah dai ya tsare, amma ki yawanta addu'a, domin hakanne zaisa koma mene ne yazo da sauƙi" inji cewar Husnah.
"Insha Allah!" Zahrah tafaɗi hakan tana mai kwantar da kanta a jikin kujeran motar, tanajin Husnah tace da Driver'n ya karkata akalar motar, ta sanja shawara shoprite kawai zasuje, bamusu kuwa ya sanja hanya zuwa Shoprite ɗin. Itadai Zahrah batace dasu komai ba.
Basu wani jima suna tafiya ba, suka iso tangamemen Shoprite ɗin.  "Muje ko" Husnah tace da Zahrah tana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar.
Cikin sanyin jiki Zahrah, tafito daga cikin motar suka nufi cikin shoprite É—in.Â
Basket biyu Husnah ta ɗauka nata ɗaya na Zahrah ma ɗaya, acewarta Zahrah ta zaɓi duk wani abun da take so, sam bahaka Zahrah tasoba amma babu yanda ta'iya, domin kuwa Husnah kafiya gareta, idan tace kayi abu tofa wai dole sai kayi.
Kayan shafa suka soma ɗauka, kafun suka garzaya zuwa kan su jaka da takalma ƴan yayi, basu tsaya anan ba hadda kayan ciye ciye sai da suka ɗauka.
Cike da gajiyawa Zahrah ke tura Basket ɗin da kayanta ke ciki, ita mamaki ma take yanda Husnah tasa suka jidi kaya mai yawa har haka, amma idan tayi la'akari da irin gata da kuma kuɗin da mahaifin Husnah ke dashi, to sai tagama ba wani abun mamaki bane, kuma kuɗin kayan bazai mawa Husnah wahalar biya ba, domin kuwa anshagwaɓata sosai agida.
Daki daki aka lissafa kayan nasu, inda Zahrah ta ɗauki kayan dubu ishirin Husnah kuwa na dubu ishirin da biyar ta eba, ƙoƙarin miƙa wa Cashier ATM card ɗin dake hanunta Husnah ta soma yi. Amma sai Cashier'n yayi murmushi haɗe da cewa
"Ai Hajiya ba'a buƙatar kuɗin ku, domin kuwa an riga da an biya muku, tunkafun ku kammala sayayyan, sannan wanda yabiya muku yace idan ma kuna da buƙatar ƙari, to kukoma ku ƙara, duk shi zai biya kuɗin"
Cike da mamaki Zahrah da Husnah suka shiga kallon juna.
"Anbiyamana fa kace Cashier? shin ka kosan me kake cewa?" Husnah tatambayeshi cike da mamaki.
"Ƙwarai kuwa nasan me nake cewa, kudai ku ɗau kayanku kawai kuje, sannan ku gode mawa Allah, don shi yaje fo muku tsuntsu daga sama gasashshe " Cashier'n nan yafaɗi haka yana mai washe baki, kasan cewar shima anbarmasa kyautan ragowan canjin su.
Mamakine ya lulluɓe su Zahrah domin su a iyaka sanin su basu da wani wanda zai biya musu kuɗin siyayyan da sukayi, domin kuwa basu zo da kowa ba banda driver, inakuwa driver zaisamu maƙudan kuɗaɗe irin haka har ya biya musu kuɗin siyayya alhali shima yana fama da kansa.
"Kozaka iya faÉ—amana wanda ya biya mana kuÉ—in ?" Husnah ta tambaya.
"A gaskia bansan saba, sai dai da duk kan alamu irin larabawan nan ne da suke zuwa Nigeria lokaci zuwa lokaci" Cashier É—in nan yafaÉ—a musu haka, domin shi a yanda yafahimta, da dukkan alamu wanda.yabiya musu kuÉ—in baiyi zubi da Æ´an nan gida Nigeria ba, duk da kuwa cewa muma muna da kyawawan maza amma kuma kyawun wani ya É—are na wani.
Idanu Zahrah da Husnah suka zaro atare, sakamakon jin abun da Cashier yace.
"Balarabe fa kace?" Husnah ta sake tambaya cike da mamaki.
"Eh Balarabe, kece Zahrah ko?" Cashier'n nan ya tambaya yana mai nuna Zahrah da hanunsa.
"Ya'akayi kasan sunana ?" Zahrah ta tambayesa cike da mamaki.
Murmushi kawai yayi haɗe da miƙa mata wata farar takarda.
"Ungo yace inbaki"
Cikin tsoro Zahrah ta karɓi takardan da Cashier ke miƙo mata, haɗe da buɗewa.
_"Kiɗauki duk wani abun da kikeso MY ZAHRAH! ban damuba koda duka Shoprite ɗin zaki ce kinaso, zan iya mallaka miki kome kikeso a duniyar nan, ko da kuwa dukiyata zata ƙare"_ abun da aka rubuta a jikin takardan kenan.
Wani irin bugawa Zahrah taji ƙirjinta yayi, "To waye?" tatambayi kanta a fili.
"Yadai me aka rubuta acikin takarda'n?" Husnah ta tambayi Zahrah cike da zaƙuwa.
Bata takarda'n Zahrah tayi domin batasan me zatace da'ita ba.
Husnah tana gama karanta takarda'n tasaki murmushi haɗe da kallon Cashier'n nan daya zura musu idanu... "Mungode sosai, idan ka haɗu da wanda yabiyamana kuɗin, ka isar mana da saƙon godiya" daga haka ta kama hanun Zahrah suka fice daga cikin Shoprite ɗin, bayan sun ɗau ledodin siyayyarsu.
"Saida sukazo bakin mota kafun Husnah ta saki hanun Zahrah, still fuskarta ɗauke da murmushi tace "Mekika fahimta game da wannan takardan, da kuma biya mana kuɗin sayayya da akayi?"
Cikin ɗaurewar kai Zahrah tace "Ni ban fahimci komai ba, sai ma tsananin mamaki da nake, taya haka zata kasance, anya kuwa ba wata maƙarƙashiyan ake shirin ƙulla mana ba Husnah?"
Dariya sosai Husnah ta kwashe dashi,  domin kuwa maganar Zahrah takai a dara.
"Maƙarƙashiyan soyayya ba, babu wani aljanu, kawai dai inaga wani ne yaganki kuma ya yaba, shine kawai" Husnah tafaɗa tana mai danne dariyanta.
"Bangane ba me kike nufi?" Zahrah ta tambaya cike da ruÉ—u, domin ita kwata kwata ma bata fahimci inda kalaman Husnah suka dosa ba.
"Kada ki damu zaki gane mushiga mota"
Jiki a sanyaye Zahrah tabuɗe murfin motar tashiga, a gidan baya sukai mawa kansu masauƙi ita da Husnah..
Suna shiga driver yayi mawa motar key suka É—auki hanyar Suleja unguwar su Zahrah.
(yauwa kuyi haƙuri jiya nayi mistake sunan unguwar su Zahrah ba Maraba bane, sunan unguwarsu Zahrah Suleja ne, kainane ya ɗau charge shiyasa)
Yanaganin tafiyarsu yasaki ƙawataccen murmushinsa, "Haryanzu tananan da halinta na tsoro, yayi imani Zahrah bazata taɓa sanjawa ba"
" komai naki yana burgeni Zahrah, inason komai naki!" Zaid dake cikin motarsa yafaɗi haka cike da shauƙi.
"Nifa gaba ɗaya kaina ya kulle, kimin bayani mana Husnah, me takardan nan take nufi ne?" Zahrah tafaɗi haka cikin zaƙuwa.
"Ki kwantar da hankalinki ƙawata, kawai dai bazai wuce irin mutanen nan masu alkhairi bane suka aikata hakan, wayasani ma ko Dr Sadeeq ne" Husnah tafaɗi hakan tana mai kallon Zahrah.
"Mene? kinanufin wai Doctor ne zaiyi haka? gaskiya banjin cewa shi ne, domin idan da shi ne, dole zai bayyana kansa na gansa, kodai ke akeso amawa wannan hidiman akayi mistake aka ambaceni" Zahrah tafaÉ—i haka cikin kokonto.Â
Dariya Husnah takuma sawa, haɗe da dafa kafaɗan Zahrah..
"Wai lafiyanki kuwa Zahrah? kinga yanda kika firgice lokaci ɗaya sai kace wacce ta aikata aikin rashin gaskiya, to ni miye ma abun damuwa ne don wani yabiyamana kuɗin sayayya? kinga bafa mu muka sa sa ba, ko ma waye shi yasanya kansa, kishare kawai ƙawata" Husnah taƙare maganar ta ta bayan ta ɓare sweet ta jefa acikin bakinta.
"Hmmm" kawai Zahrah ta'iya cewa, haɗe da mai da kanta jikin kujera, itakam gaba ɗaya kanta ya kulle, taya za'ace bakasan mutum ba, amma kuma ya biyamaka kuɗin siyayyan da kayi, irin haka ne mutum sai yaje ya jefa kansa a matsala.
Tafiya suke amma Zahrah ta kasa cewa komai, sai ma Husnah ce keta ƙoƙarin janta da hira, amma jefi jefi take amsa mata, domin kuwa wannan faɗuwar gaban da takeji har yanzu baidaina ba.
A haka har suka iso ƙofar gidan su Zahrah'n... Har cikin gida Husnah tayimawa Zahrah rakiya, kana ta fito tashiga mota suka tafi.
Zama tayi akan katifarta haɗe da zubawa kayan siyayya da sukayi ido, sam zuciyarta bata kwanta da wanda yabiya musu kuɗin kayan ba, zuwa yanzu ya kamata ace tayi hankali, domin sarai yanzu tasan salon yaudaran maza baida ƙarshe, suna iya yimaka komai don su samu biyan buƙatarsu, wannan yana ɗaya daga cikin babban dalilin da yasanya ta amince da auren Dr Sadeeq, ko ba komai idan ya aureta ta tsallake wani babban siraɗi na daga yaudaran da Maza sukeyi mawa ƴan mata a wannan zamanin.
Ƙaran wayartane yakatseta daga tunanin da takeyi, cikin sanyin jiki ta ɗaga ƙiran nasa, haɗe da kara wayar akan kunnen ta.
"Barkanki da hutawa My Princess!"
Dr Sadeeq yafaÉ—a cike da tsantsar kulawa.
ÆŠan guntun murmushi tayi haÉ—e da cewa "Kaima barkanka dai ya aiki?"
Æata fuska yayi tamkar dai tana ganinsa haÉ—e da cewa "Aiki ba daÉ—i kokaÉ—an, ya kundawo a super market É—in kenan?"
"Eh" tabashi amsa a taƙaice. Domin tsabar gajiyan da ta kwaso har wani bacci bacci takeji.
"Naga kamar kingaji da yawa, ki samu ki ɗan huta, zuwa anjima zanzo gida, inaso na samu Baffa, idan yabani dama zanturo magabata na ayi maganar auren mu, domin banso akai nanda wata ɗaya ban mallakeki ba!" yaƙare maganar cikin yanayin shauƙi.