← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 112

Sashe 105

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanciya yayi luf abayanta bayan yacire rigar dake jikinsa,  hanunsa yasanya ya ɓalle mata aninayen dake jere a gaban rigarta,  lumshe kyawawan idanunsa yayi haɗe da sanya hanu ya shafi breast ɗinta.  Saida ya sauƙe ajiyar zuciya me ƙarfi, kana ya sake rungumeta ajikinsa, kansa ya ɗaura akan wuyanta, haɗe da sanya harshensa, yashiga lasan fatar wuyanta, yayinda hanunsa ke kan breast ɗinta, yana murzawa a hankali. Kamar acikin mafarki takejin abun da yakeyi mata,ahankali ta buɗe idanunta, batakai ga kallonsa ba, daddaɗan ƙamshin turarensa, ya sanar da ita cewa shine, sake narke jikinta tayi acikin nasa,  jin alamun cewa tafarka ne, yasanyasa juyo da ita suka zama suna fuskantar juna.  Kallonsa tayi da idanunta, da suke cike da magagin bacci, murmushi tasakarmasa haɗe da sanya hanu ta shafi lallausan sajen fuskarsa.   Idanunsa da suke cike da  tarin sha'awarta ya watsa mata haɗe da matso da fuskarsa daf da tata, har numfashinsu na gauraya dana juna,  yanayin irin yanda yake kallonta ne, yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, wani irin ƙaunarsa me sanyi taji tana shiga cikin jikinta.  Ranƙofowa yayi haɗe da yi mata rumfa da ƙirjinsa,  baikai gayin romancing ɗinta ba, amma gaba ɗaya kallon daya keyi mata, ya gama kashe mata jiki,  ahankali ta lumshe idanunta, sosai ƙamshinsa keyi mata daɗi.   Kansa ya cusa acikin ƙirjinta dake tashin ƙamshi, ahankali yake goga mata lallausan sajensa akan breast ɗinta.  Sake lumshe idanunta tayi, haɗe da sanya hanunta, a bayansa ahankali take shafawa, tana fidda wani irin numfashi.  Slowly yake kissing ɗinta, tundaga ƙirjinta har zuwa kan bakinta, da kaɗan kaɗan yake tsotson pink lips ɗinta, yana me lumshe idanunsa, da suka koma kalar ja,     baitaɓa mata irin wannan kissing ɗin me rikita tunani ba sai yau, sosai takejinta cikin wani irin yanayi na musamman,  ajiyar zuciya me ƙarfi ta sauƙe, haɗe da buɗe bakinta,  kamar zatace dashi wani abu, amma kuma babu wata kalma da zata iya fitowa daga bakinta, saboda gaba ɗaya ya shiɗar da ita. Ya ruɗata da salonsa,   harshensa ya tura acikin bakinta, haɗe da soma kaɗa mata shi acikin bakin nata.  Hanunsa yasanya ya zare ƴar rigan dake jikinta.  ƙasa yayi da kansa yana sucking ɗinta,  kamar kullum daya fara sucking ɗinta take saka masa kuka ta kuma shiɗe masa, yau ma hakance takasance, ganin numfashinta nashirin ƙwace mata ne, yasa ta janye kansa, haɗe da mirginawa gefe tana sauƙe wani irin numfashi,  ji take kanta na juya mata,  ga wani irin sha'awarsa dake fusgarta. Sake kwanciya yayi a bayanta, haɗe da cusa kansa cikin tulin gashin kanta.   Numfashi shima yake fitarwa akai akai, burinsa ɗaya shine yaji wannan ɗumin nata, me zautar masa da tunani.
Juyowa tayi gareshi haɗe da hayewa saman ƙirjinsa, hanu tasanya tana shafa gashin kansa, yayinda taɗaura bakinta akan ƙirjinsa, tana sakar masa wasu irin kiss dake tada masa da tsikar jiki,    lumshe idanunsa yayi yana me karɓan saƙonta, dama akunne yake matuƙa, gashi yanzu tana ƙara kunnasa.   Ganin da yayi cewa zata haukatasa da yawa ne, yasanya sa dawo da ita ƙasansa yazamana shine a samanta.   Kallon da yayi mata ne ya ƙara kashe mata jiki,  haɗe bakinsu yayi waje ɗaya,  lokacin da ɗumin jikinta ya ratsashi saida ya sauƙe wata ajiyar zuciya me ƙarfin gaske, take kuma ya fara manta awacce duniya yake, atare suke kissing ɗin juna, cike da wani irin so,   sun matuƙar zautuwa, kowannensu yatafi wata duniyar ta daban, amma duk da haka bakinsu yana cikin na juna..........

*** *** ***
Bayan Wata Biyu.😜

Yanzu cikinta yana wata tara harda sati biyu, amma haihuwa shiru, zuwa yanzu ko tashi bata iyawa sai antaimaka mata, cikinta yayi wani irin girma, hakannema yasa Hajiya da kanta taje ta ɗaukota, ta dawo gidanta da zama, bahaka Dr.Sadeeq yasoba amma babu yanda ya iya, dolensa ya haƙura, kuma sosae yake kewar matartasa, wai donma yanasamu suna keɓewa, idan dare tayi, har hotel suke zuwa.

Kwance take akan doguwar kujeran dake falon Hajiya, green Apple ne riƙe a hanunta, ita bata ciba ita bata ajiye ba.  Tun daran jiya take fama da wani irin ciwon mara dana baya,  amma babu wanda ta faɗawa, gudun kada su tashi hankalinsu,  yanzu kam abun yasoma fin ƙarfinta, don ciwon kamar zai zautar da ita haka takeji, zamowa tayi ƙasa daga kan kujeran da take, haɗe da durƙushewa aƙasan tiles, hanu tasanya takama gefe da gefen cikinta, tare da sakin wani ƙaran azaba, lokaci guda taji wani irin ciwo yataso mata gadan gadan.  Fitowar Hajiya daga ɗaki, yayi daidai da shigowan Doctor Sadeeq cikin falon.  Dukansu da sauri sukayi kanta. 
"Innalillahi Hajiya, dama bata da lafiya ne?" Dr. Yatambayi Hajiya a matuƙar ruɗe.  Kafun Hajiya takai ga cewa wani abu Zahrah ta fashe da kuka haɗe da faɗawa jikin Doctor ta ƙanƙameshi ƙam,  gaba ɗaya ya ruɗe yarasa inda zai tsoma kansa, shima rungumeta yayi tuni idanunsa sun kawo ƙwalla.
Hajiya ce tafito daga ɗakin Zahrah'n hanunta ɗauke da Hijab, ita tasawa Zahrah'n hijab ɗin, kana tace doctor Sadeeq ɗin ya ɗauki Zahrah su wuce asibiti.  Jikinsa na rawa haka ya ɗaga ta ca ɗak yasata a mota, Hajiya tashiga motar ta riƙeta, shikuma yaja suka nufi asibiti, gudu yake dasu kamar zaitashi sama, kanaganinsa kaga wanda baya cikin hayyacinsa,  bayaso wani abu na wahala yasamu matarsa ko kaɗan, da ace zai yiwu to daya karɓa mata naƙudan, don baya ƙaunar ganinta cikin wahala da azaba har haka.

Suna shiga cikin asibitin direct aka wuce da Zahrah labour room.  Wasu likitoti ne guda uku mata akanta,  babu abun da take sai salati da cije baki, ita kaɗai tasan me takeji,  ganin bazai iya jurewa ba, yasanya sa faɗawa cikin labour room ɗin, dayake dama asibitinsu ya kawota, yanazuwa gaban gadon, ya kama hanunta,  buɗe wahalallun idanunta tayi ta kalleshi,  atare wasu hawaye masu zafi suka fito daga cikin idanunsu,  matsanancin tausayinta yakeji, fiye da tunanin me tunani,  Hanunsa dake saman nata, takama ta matse, haɗe da girgiza masa kanta, cikin wata irin murya me ɗauke da tsananin ciwo tace.
"Kayafemin idan na mutu dan Allah!"

Kai ya girgiza mata da sauri haɗe da cewa. "Bazaki mutu ba Zahrah, zamu rayudake acikin duniyarnan insha Allah, zaki raini abun da zaki haifa ɗa hanunki, insha Allah!!" cike da tsananin rauni ya faɗi haka, sosai zuciyarsa ta karye,  bata sake ce dashi komaiba, kawai ta ɗauke idanunta akansa, cigaba tayi da nishi haɗe da karanto addu'a, Doctor na riƙe da hanunta, yana tofa mata addu'a, haɗe da shafa kanta, ƙwalla ne kawai suke fita daga idanunsa. Wani irin yunƙuri haɗe da nishi tayi sai ga kukan jariri ya cika ɗakin.  Laƙwas haka tayi akan gadon, lokaci guda komai nata ya tsaya, motsi da numfashinta, duk suka ɗauke, kumatunta yasoma bubbugawa yana ƙiran sunanta, hawaye kuwa akan fuskarsa wani na koran wani kamar an buɗe famfo.
Wata daga cikin likitoti matanne ta É—auki yaron, takaishi wajen da ake aje jariri, kallon Dr.Sadeeq da yake hawaye tayi, tace
"Haba Sir, wannan fa ba wani abun damuwa bane kasani, yanzu zata farfaÉ—o insha Allah"
Hankalinsa ma baya wajenta balle yaji me take cewa, shigaba ɗaya ma basirarsa toshewa tayi, amaimakon yabata taimakon dayasan zai dawo da ita hayyacinta, saiya tsaya yana ƙiran sunanta, yana kuma jijjigata.   Likitance tashiga bata taimako,  wani ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe,  alaman ta farfaɗo, bayan kamar mintuna uku ta shiga buɗe idanunta a hankali,  dashi tafara tozali ya tusata a gaba, sai kuka yake, hanunta ta miƙa masa, da sauri yataho yakama hanun,  kissing ɗinta yayi akan goshinta, haɗe da  rungumeta, atare suka shiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, sun kusan 8 minute ahaka, kafun taɗan janye jikinta daga nasa, murya a sanyaye tace "Ina Hajiya?"  "Tana waje" yabata amasa a taƙaice, yana me binta da kallo me ɗauke da tsananin ƙauna, haɗe da tausayi me ruguza zuciya.  

Wata daga cikin likitotinne tace "Sir yakamata a kimtsata, sai mukaita É—akin hutu"
Juyowa yayi ya kalli likitan haɗe da cewa. "Babu buƙatar ɗaya daga cikinku sai ta kimtsata, nida kaina zan kimtsa abata"

"Sir tana buƙatar ɗinkifa, saboda ta ƙaru" likitan takuma faɗan haka.

Da sauri ya kalli Zahrah, take hawayen dake cike acikin idanunsa, suka gangaro kan ƙuncinsa, wani sabon tausayinta ne yasake kamasa, "Ina sam bazai iya mata ɗinki ba, bazai taɓa koda kwatantawa bane ma, dakansa da hanunsa ya huda Zahrah'nsa? wannan abun bamai yiwuwa bane" yafaɗi haka acikin ransa. Baice da likitotin komai ba, sai matsawa dayayi kusa da Zahrah, yasake sumbatarta akaro na biyu, wata allura ya ɗauko yayi mata a hanunta, tayanda yasan bazataji zafiba,   kallonta yayi still hawaye yake, daƙyar ya iya jan ƙafansa yafice daga cikin ɗakin, abun mamaki kota kan jaririn baibiba, tun dama yafaɗo dunia bai kulasaba, yanata rabin ransa Zahrah. 

Likitotinnan ne suka ɗinke ta tsab, saidai bata wani ji zafi sosai ba, domin alluran da Doctor yayi mata, allurace me ƙarfi dake hana jin zafi, suna gama ɗinketa, wata acikin likitotin takamata suka wuce bathroom,  likitance ta haɗa mata ruwa tayi wanka, tana fitowa likitan tabata wata riga wacce takarɓo awajen Hajiya tasanya, miƙo mata jaririn likitan tayi, hanunta na rawa haka ta karɓi jaririn ɗan nata, tana karɓansa taji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, fuskar Dr.Sadeeq ta kalla sak akan fuskar yaron nata, lokaci ɗaya taji wani irin so da ƙaunarsa sun cika mata zuciya, tana fitowa acikin labour room ɗin, Hajiya da Dr.Sadeeq sukayo kanta, daga ita har jaririn Hajiya ta haɗasu ta rungume, sai ga ƙwallan farinciki na zuba daga idon Hajiya, amsar yaron tayi daga hanun Zahrah haɗe da sanya sa acikin ƙirjinsa ta rungumesa, sosai takejin ƙaunar jikan nata, musamman dataga yana kama da ubansa, sai dai duk da haka akwai kamannin Zahrah a tattare dashi. Dr.Sadeeq kuwa ko kunyan Hajiya dake tsaye baiyiba yaje ya rungume matarsa, kyakkyawan kiss ya sauƙe mata akan ƙuncinta, haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗanta.

Saurin tureshi tayi daga jikinta, ta haye gado ta kwanta, tana sauƙe numfashi, kawar da kanta gefe tayi, wasu irin siraran hawayene suka gangaro daga cikin idanunta, ita kaɗai tasan menene yasata wannan hawayen. Mintuna kaɗan bacci ɓarawo ya ɗauketa, dagani kuma kasan tanajin daɗin baccin.
Chapter 105 · 0% Book details