← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 112

Sashe 40

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka Zahrah ta fashe dashi, wanda batasan dalilin yinsaba, ita ta amincewa kanta cewa zata auri Dr Sadeeq amma saitakeji tamkar dole tayimawa kanta.

Batayi zato ba saiji tayi Dr Sadeeq yajawota jikinsa haɗe da sanya hannayensa duka biyu ya rungumeta.  "Inasonki Zahrah, kuma nayi maki alƙawarin bazantaɓa wulaƙanta ki ba har'abada, kidaina kuka kinji princess ɗina!" yaƙare maganar tasa cikin sigar lallashi.

Daddaɗan ƙamshinsa shiyaso birkita mata tunani don haka tayi saurin janyewa daga jikinsa, tana mai yin ƙasa da kanta.

Sam shikam ma yamanta da cewa hakan da yayi ba'abu bane mai kyau, gaba ɗaya murna yacika masa zuciya.  

"Uh sorry baby, gaba ɗaya kece kikamantar dani komai!!"  Dr Sadeeq yafaɗi hakan yana mai dafe goshinsa.

Ƙasa ƙasa Zahrah tayi murmushi haɗe da kawar da kanta gefe, hakanan taji wani irin nauyin Dr Sadeeq ɗin yaƙaru acikin zuciyarta, haka kuma yaƙara girma acikin idanunta.

Wani irin kallo Dr Sadeeq yashiga yimawa Zahrah duk dacewa takau da kanta gefe,   sai yanzu nema yake ƙara ganin haɗuwarta fiye da  da, tabbas da Zahrah bata amince dashi ba to da ya tabka babban rashi, domin kuwa Zahrah tahaɗu, macece ita da kowanni Namiji zaiyi fatan mallaka.

Sam batayi tunanin kallonta yake ba, don haka taɗan juyo dan itama ta saci kallonsa,  aikuwa karab idanunsu suka sauƙa akan najuna, da sauri Zahrah tayi ƙasa da kanta haɗe da cusa fuskarta tsakan kanun  cinyoyinta.

Dariya Dr Sadeeq yayi cike da shauƙi haɗe da shafa sajen dake kwance akan fuskarsa. "Yaushe kika farajin kunyana? lallai zamu ɓata idan harkinajin kunyana!" ya faɗi hakan cike da zolaya.

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba, haɗe da marairaice fuska cike da shagwaɓa tace "To bakaine kaketa kallo na ba, saikace baka sanni ba!"

Lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu a lokaci guda, irin wannan salon shagwaɓan ai saita sashi bacci batare da yashiryawa hakan ba,lol.

"Ki faɗamin laifi ne don nakalli abar sona? saidai kiyi haƙuri amma kallonki yanzuma na fara, tunda kinamin kyau, kina kuma burgeni!" yanayin yanda yayi maganar abun burgewa ne, ga macen da tasan daɗin soyayya.

"Nidai kada ka wani ce inada kyau, daɗin bakine kawai nasan kakemin!" still da yanayin shagwaɓa tayi maganan.

Lumshe idanunsa yayi haɗe da fitar da iskan numfashi daga bakinsa,  yanayin shagwaɓan  Zahrah yafi komai burgesa a tattare da'ita, haka kuma sosai yake sauƙar masa da kasala.    "Princess!!" yaƙira sunanta dawani irin murya mai taɓa zuciya.

A hankali ta ɗago idanunta ta kallesa, batare da ta amsa masa ba,    ganin idanunsa a rufe, yasanya taɗan tsaya ƙaremawa fuskarsa kallo.     "Duk kallona  ɗaya da zaki yi bazai tafi a banza ba, sai kin biya kuɗi, gwamma ma kisani!" Dr Sadeeq yafaɗi haka batare da ya buɗe idanunsa ba.
Saurin ɗauke kanta tayi daga kallonsa haɗe da cewa "Niba kallonka nake ba"   

"Zaki iya rantsewa cewa bani kike kallo ba?" yaje fo mata tambayar da batayi zato ba.

kanta tashiga girgizawa haÉ—e da cewa "Ai bankalleka sosai ba, kaÉ—an nakalleka!"

Dariya Dr Sadeeq yasanya wanda harsaida dimple ɗinsa suka bayyana,  yanzu yayarda cewa Zahrah yarinyace ƙarama, kuma zakayi saurin kamata idan tamaka laifi.

Ƙoƙarin buɗe murfin motar Zahrah tasomayi, cikin mamaki Dr yace "ina zaki?"

"Zankoma gida ne, dama magana zan faɗa ma, shiyasa  na ƙiraka, kuma nafaɗa ma, inada karatu, gobe muna da test a makaranta" Zahrah tafaɗi hakan dai dai lokacin da ta gama sanya ƙafafunta waje.

"Shikenan to My Princess kikulamin da kanki kinji, inasonki sosai!" Dr Sadeeq yafaÉ—a cike da kulawa.

Wani irin muguwar kunyarsace takama Zahrah, bashiri ta wuce cikin gida tana mai rufe fuskanta da tafukan hanunta.

Shima Dr ɗin murmushi yayi cike da jindaɗi,  lallai idan ya auri Zahrah yakasance mutum mai sa'a,   acikin satinnan insha Allah, zai sanarda ƙanin mahaifinsa azo a nemamasa auren Zahrah, a wajen Baffa.

"Aurenka da Salima fa?" Wata zuciyar ta jefo masa wannan tambayar, wani irin bugawa yaji ƙirjinsa yayi,  gaba ɗaya amincewa dashi da Zahrah tayi yasanyashi manta halin da yake ciki na batun auren sa da Salima. Jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, tabbas akwai ƙalubale a gabansa, domin kuwa yanada tabbacin cewa Hajiyarsa bazata taɓa sanja maganarta ba, gashi har ansoma shirye shiryen bikinsa da Salima, kuma shi a tsarinsa bai sha'awar auren mata biyu, Zahrah ita kaɗai ta'ishesa rayuwa, amma kuma tabbas yasan zai fuskanci matsaloli da yawa daga ƴan uwansa, matuƙar ya jajirce akan cewa Zahrah yakeso ba Salima ba, to amma dole zai jarraba sa'ansa, domin a gaskiya baijin cewa zai'iya haƙura da Zahrah.
Cike da sanyin jiki yayimawa motar tasa key, haÉ—e da nausawa kan titi.

Suna isa katafaren gidannasu, adai dai parking space motar tasu ta tsaya.

Bawani jinkiri Zaid yabuɗe murfin motar yafito,    batare da yatsaya sauraran   Mahaifinnasa ba, yanufi ɓangarensa kai tsaye.

Komai dake cikin ɓangaren nasa a gyare yake tsab, tamkar akwai wani wanda ke rayuwa a cikinsa,  hakan kuma yasamo asaline da yawan gyara part ɗin da akeyi duk bayan kwana biyu, kasancewar Zaid mutum ne da bayason ƙazanta.

Direct bedroom ɗinsa yanufa,  yanashiga yasoma rage kayan dake jikinsa,   rigan wanka irin na maza mai gashi gashi a jiki yasanya,  haɗe da sanya badroom slippers a ƙafafunsa, kai tsaye wajen fridge ɗin dake aje  cikin ɗakin yanufa,  maltina can  yaciro haɗe da ɓalle ɗan ƙarfen da aka rufe  bakin can ɗin dashi,  yakai bakinsa, tunda yakai  maltina can ɗin nan bakinsa bai ɗauke ba harsaida yatabbatar da cewa  bakomai ciki ya shanye,  cikin dustbin ɗin dake aje a ɗakin ya jefa can ɗin.  Bathroom ya wuce haɗe da sakarmawa kansa shower.   Wanka yakeyi amma gaba ɗaya tunaninsa baya garesa, yanaga shugar baby'nsa,  amatuƙar matse yake da sha'awarta, haryanajin bazai iya daurewa yakai zuwa wani ɗan lokaci mai tsawo batare da'ita ba.

Bayan yafito a wanka yashiga shirya kansa  cikin, haɗaɗɗun riga da wando masu kyau da tsadar gaske, gaskia komai na Zaid me kyau ne, domin kuwa kowani kaya yasanya saiya yi kyau, bakuma kayanne yake masa kyauba, shi ɗin kansa ne yake  mawa kayan kyau,lol.

Haɗaɗɗen takalminsa  sau ciki ƙiran kamfanin Gucci yasanya, aƙafansa, bayan ya ɗaura tsadadden agogon nan na  Rolex a hanunsa mai kyau da burgewa. Daddaɗan ƙamshi ne kawai ke fita daga jikin shi, ƙamshine mai wahalar mantawa.

Black facing cap, yasanya akansa, domin kuwa yanayin garin ana É—an busa sanyi, duk dakuwa cewa daga cikin sanyin yafito.
Wayarsa yaɗauka haɗe da car key ɗinsa, kai tsaye yafice daga cikin ɗakinnasa.   Ɓangaren Mom ɗinsa yanufa.   Hajiya Safara'u ne tsaye a gaban ƙatoton teburin cin abinci, yayinda Alhaji Ma'aruf ke zaune tana serving ɗinsa,    batasan da shigowarsa ba saiji tayi ya rungumeta ta baya haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗarta, cike da soyayyar mahaifiyarta sa yace "Barka da gida Momy!"

Cike da tsananin farinciki itama ta rungumesa haɗe da basa sumba a kan kumatunsa, "Barkanka da dawowa my son, ya gajiyar hanyar?" 

"Alhmdlh!" Zaid yafaɗa a taƙaice, bayan ya janye jikinsa daga na mahaifiyartasa.    Ƙoƙarin juyawa yakeyi, Mom tace "Inakuma zaka my son ba abinci kazo ciba?" cike da kulawa ta tambayesa.

Ɗan ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa "Banajin yunwa Mom, idan nadawo zanci!"  baijira jin maizasu ceba yasakai yafice daga cikin falon.

Da kallo kawai Mom tabisa har yafice, fuskarta É—auke da damuwa, itakam ta rasa wani irin haline da Zaid, sam ba'a iya gane gabansa da bayansa.

"Miye abun shiga damuwa  Hajiya Safara'u? zuwa yanzu yakamata ace duk wani hali na yaronnan Zaid kin gama saninsa!"  Alhaji Ma'aruf yafaɗi hakan cike da nuna kulawa ga matar tasa.

"Nasan halinsa Alhaji, amma kuma ace mutum shi baya taɓa sanjawa, ko da yaushe fa Zaid bayason zama a cikin mu, sannan kuma sam baya sakewa damu!" Mom tafaɗi hakan cike da damuwa.

"Zauna muci abincin mu, aishi ba ƙaramin yaro bane, yasan me yakeyi!" Alhaji Ma'aruf yafaɗi hakan yana mai kama hanun Mom yazaunar da'ita a kusa dashi.

Zaid kuwa yana fita daga ɓangaren mahaifiyartasa, kai tsaye wajen motarsa yanufa,   koda driver yanemi da yabarsa ya tuƙasa, ɗaga masa hanu yayi alamar baya buƙata,  shida kansa yayimawa motar key, ya harbata zuwa kan titi.

Tafiya yake cikin nutsuwa yayinda airpiece ke saƙale a kunnuwansa,   wayarsa ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira,   ganin cewa babban manager'n company'nsa dake nan gida Nigeria ne ke ƙiransa yasanya shi ɗaga ƙiran.   Banji mai Manager'n nasa yace masa ba, sai gani nayi ya'aje wayan, haɗe da buga dogon tsaki,   lokaci ɗaya yakarkata akalar motar tasa  zuwa wata hanya daban saɓanin hanayar daya nufa, wanda zai sadasa da unguwar su Zahrah.

Dr Sadeeq kuwa yana barin unguwar su Zahrah kaitsaye gidansu yanufa, acewarsa gwamma yayi maganin matsalarsa tunkafun tayi nisa.

Usaina mai aikin ɓangaren Hajiyarsa yasanya tane ma masa iso awajen Hajiyar tasa, domin kuwa bai isketa a falo ba.

Da sallama yashiga cikin ɗakin Hajiyar tasa,  fuskarta ɗauke da fari'a ta amsa masa sallaman da yakeyi. Zaune take akan gado, yayinda  take duba wasu kayayyaki dake zube a gabanta.

"Barka da huwatawa Hajiya!" yafaÉ—a cike da ladabi.

"Yauwa  barkanka, kamar kuwa kasan ina nemanka, wai me kake nufi da auren nan ne Sadeeq? har yanzufa banga kana wani cuku cuku ba, kayan lefe ma saini kabarmawa ɗawainiyar haɗasu, gashi kuma Salima tacemin tunda kaje sau ɗaya baka sake zuwa ba, mai ke damunka ne wai?" Hajiya tatambayesa cike da kulawa.

Kansa yashiga sosawa haɗe da sake yin ƙasa da kansa,   "Am...dama Am...." "Dakata banson wani kwana kwana, kafaɗi abunda zaka faɗa kai tsaye kawai" Hajiya ta katsesa daga kame kamen maganan dayake ƙoƙarin yi mata.

"Hajiya kamar dai yanda na faɗamiki ne,  wallahi Hajiya dagaske nake, yanzu nasamu wacce nakeso kuma idan harkin yarda aurenmu bazai wuce nan da Sati uku ba, kamar yanda kikeso!" yafaɗi hakan cike da ladabi.

Sororo haka Hajiya ta tsaya tana kallonsa,  "anya kuwa Sadeeq yana lafiya? " tatambayi kanta.
Chapter 40 · 0% Book details