Sashe 59
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni kaina inaso naganni cikin farinciki Husnah, amma nasan hakan bazai samu ba matuƙar Zaid yana raye a doron ƙasa, koda ma ace baya raye nasan bazanyi farinciki ba Husnah saboda yariga daya gama lalatamin rayuwa, bana tunanin cewa akwai wani namiji da zaiyi ɗokina idan ya aureni? Shifa budurci wani abune me matuƙar mahaimmanci a rayuwar ƴa mace Husnah, babu wani mutumci dakuma karamci wanda ya wuce mace takai budurcinta ɗakin mijinta, mafi ganganci da kuskure da mace zata aikata kafun aurenta shine ta yarda ta bawa wani kyautar budurcinta,  mata irina suna da yawa Husnah wa ƴanda aka mawa fyaɗe aka ƙwaci budurcinsu da ƙarfin tsiya, san nan kuma akwai waƴanda maza suke ruɗansu da kuɗi ko kuma da soyayya harsu yi nasaran rabasu da budurcinsu, san nan akwai kuma wanda dan kansu suke bada kyautar nasu budurcin ga wani daban,  rasa budurci abune me matuƙar ciwo Husnah musamman ma ga iri na wanda aka mawa fyaɗe, Yawancin maza suna fatan idan sunyi aure su samu matansu da cikekken mutumcinsu, inde kuwa har a matsayin budurwa suka aureta, haƙiƙa akwai wata soyayya dakuma girmamawa dake shiga tsakanin mace da mijinta matuƙar takawomasa budurcinta ɗakinsa, saɓanin haka kuwa shike hargitsa tunanin namiji, shike jagulawa mace zaman aure'nta, koda ace ya yarda ƙaddarane hakan amma tabbas wani lokaci abun zaina masa ciwo, duk da nasan cewa Dr.Sadeeq yasan komai daya faru dani, amma duk da haka tabbas nasan duk randa yakusanceni saiyaji ciwo acikin ransa, saikuma yaji wani abu saɓanin tunaninsa, shi a yanzu yana ganin cewa hakan bakomai bane, amma kuma hakan komai ne bakuma ze gane hakan ba sai randa ya aureni yakuma nemi dana basa haƙƙinsa na aure,,  wan nan ranan nake gujewa kaina Husnah bansan ina zan tsoma kai da zuciyata ba amma nabarwa Allah komai!!" gaba ɗaya hawaye sungama wankewa Zahrah da Husnah fuska, lalle kuwa wan nan itace mummunar ƙaddara wand ba'a taɓa mantawa da'ita,, rungume Zahrah Husnah tayi cike da tsananin tausayin ƙawarta ta,,, tabbas duk abun da Zahrah tafaɗa gaskiya ne kai budurci ɗakin miji yafi komai daɗi a rayuwa saboda ko ba komai zaiƙara muku danƙon soyayya dakuma mutunta juna, duk da cewa Zahrah ba'asonta tarasa budurcinta ba amma kuma tabbas kamar yanda Zahrah ta faɗa hakan yake dolene Dr.Sadeeq zaiji zafin abun sosai aduk ranarda kusantar farko tashiga tsakaninsu, amma kuma babu wanda ya isa ya tsallakewa ƙaddararsa.....
Hawayenta tasanya hanu tashare kafun tashiga sharewa Zahrah ma nata hawayen,,,, Â
"Ki kwantar da hankalinki Zahrah komai zai zo cikin sauƙi insha Allah taso muje musamu ruwa muwanke fuskarmu ko"
Ba musu Zahrah ta tashi tsaye Husnah takama hanunta suka nufi wajen da sukasan zasu samu ruwa......
***********
Jigum haka su Dad dake tsaye agefen gadon Zaid sukayi, yanzu awa 5 kenan suna irgawa batare daya buɗe idanunsa ba, gashi kuma 4 hours likita yace musu zaiyi....
Babban yatsar ƙafansane tasoma motsawa kafun idanunsa da sukayi nauyi suka soma buɗewa a hankali,, da sauri Dad ɗinsa yaƙaraso jikin gadon yanayi masa sannu...
Ƙoƙarin tashi zaune yasomayi da sauri Dad ɗinsa yamaidasa ya kwanta "Ba sai ka tashi ba Zaid yakamata kabari kaɗan wastsake tukunna kafun kasoma yunƙurin tashi"
ÆŠan yamutsa fuska Zaid yayi haÉ—e dabin ledar ruwan da aka É—aura masa da kallo.
Dai de lokacin Labisat suka shigo ita da Dr.Bilal domin dama Mom naganin Zaid ɗin yabuɗe ido tace da Labisat tayi mata ƙiran Doctor...
Ƴan gwaje gwaje Dr.Bilal yayi masa haɗe dayi masa wasu ƴan tambayoyi, ko motsawa bakin Zaid beyiba balle Dr.Bilal yasa ran samun amsa, ganin haka yasa Dr.Bilal yin murmushi batun yauba yasan Zaid ɗin saboda haka shirun da Zaid ɗin  yayi masa bawani abu bane daya kamata ace yadamu ba,, kallon Dad Dr.Bilal yayi haɗe da cewa
"Ko yanzu idan kuna buƙatar sallama se a baku saboda babu wata damuwa, se daifa a kiyaye kamar yanda na faɗa"
Kai Dad yajinjina haɗe da cewa "Shikenan Doctor insha Allah za'a kiyaye, muje sai nakarɓi takardan sallaman ko"  Dad da Dr.Bilal suna fita Zaid yatattaro duka wani kuzarinsa dayayi masa saura yamiƙe tsaye, kafaɗun Labisat dake tsaye kusa dashi ya kamo haɗe da ɗaura hanunsa akan kafaɗan nata suka nufi hanyar fita daga ɗakin, domin kuwa koda Dr.Bilal be basu sallama ba tabbas bazai ƙara 1 hour a cikin asibitin ba...
Yana riƙe da kafaɗan Labisat harzuwa cikin mota, shida Labisat mota ɗaya suka shiga, yayinda su Dad da Mom suka shiga wata motar wanda duk su sukazo da ita... Direct gida suka nufa
Idanunsa gaba É—aya suna a lumshe yayinda yajingina bayansa a jikin kujeran motar wanda yake zaune akai.
Ɗan satan kallonsa Labisat tayi hakanan taji wani irin mugun tausayin ɗan uwan nata ya kamata, tabbas basuyi wani shaƙuwa da yayan nata ba amma tafuskanci cewa yanacikin damuwa, takuma tabbatar da cewa sanadin damuwarne ma har ya kaisa ga kwanciya a asibiti, to wan nan wace irin damuwace yayanta yake ciki haka? tabbas zataso sanin damuwar dake damunsa saboda tana matuƙar son ɗan uwan nata bandashi batada wani ɗan uwa dasuke uwa ɗaya uba ɗaya shikaɗaine yayanta kuma garkuwanta......
Koda suka isa gidama Labisat ce tarakasa har ɓangarensa,, zama yayi akan kujera haɗe da jawo wani ɗan ƙaramin table ɗin dake tsakiyar falon yaɗaura ƙafafunsa akai..
"Yaya mezan kawo maka, yakamata kasa wani abu acikin ka!"Â cike da É—ar É—ar Labisar tafaÉ—i maganar saboda tasansa sarai ba'a iyarmasa yanzu saiya saceka..
"Friedrice" yafaɗa a taƙaice batare kuma daya buɗe kyawawan idanunsa dasuke a lumshe ba..
Jiki na mazari haka Labisat ta tafi kawo masa friedrice É—in dayace, domin kuwa dama agidan nasu ba a rasa friedrice..
Mintuna kaɗan tadawo hanunta ɗauke da ƙaton tire hadda plate ɗin yankakkun kayan marmari akan tire ɗin,, adede gabansa ta ajiye tire ɗin haɗe da ɗaukan plate ta buɗe kulan da friedrice ɗin ke ciki ta zuba masa.
"Yaya gashinan na kawo" tafaÉ—a tana me tura masa plate É—in friedrice É—in gabansa.
Ganin da tayi bece da ita komai ba yasanyata miƙewa sumu sumu tafice daga falon nasa...
Jawo plate ɗin yayi gabansa yasoma tsakuran abincin yanaci kaɗan kaɗan duk da kuwa bawai buƙatar abincin yakeyi ba adole kawai yakeci...  Lomansa huɗu ya aje spoon ɗin dake hanunsa haɗe da jawo plate ɗin yankakkun kayan marmarin dake gabansa yasoma sha, sai alokacin yasoma jin daɗin bakinsa, amma da kwata kwata bayajin ɗanɗanon komai,, fruits ɗinma baiwani sha me yawaba haka yature yakuma maidakansa yajingina da kujera,, idan akwai abun dayake ƙauna dakuma muradin gani yanzu arayuwarsa baiwuce Zahrah ba, dole yaje gidansu ayau ɗin koda kuwa idan yaje zata ɗauki wuƙa ne taluma masa a cikinsa.....
Yauma de kamar kullum Zaune take a tsakar gidan nasu, kwanon abincine aje agabanta tana tsakura da kaɗan kaɗan tana kaiwa bakinta domin kuwa haryanzu bata wani jin daɗin jikinta..
Inna ce zaune daga gefenta tana ta ƙoƙari wajen ganin ta seta tashan radion ta..
Wani yarone yayi sallama yace wai ana ƙiran Zahrah,,  "Jekace tanazuwa" Inna tahanzarta faɗa, har yaron yakama hanyar fita daga gidan, Zahrah ta tsaidasa haɗe da cewa "Kace bazata zo ba"
Hangame baki Inna tayi tana kallon Zahrah "Bazakijeba fa kikace?"
"Eh Inna dan Allah kuma kada kitambayeni dalili" tayi maganar tana me langwaɓar da kanta gefe.
Harara Inna ta watsa mata haɗe dayin tsuka baƙin ciki kawai Zahrah'n takeyi mata wayasani ma ko wanda ke ƙiran nata da alkhairi yazo...
"Wai Bazata zoba" yaron nan yafaÉ—awa wanda ya aikosa.
Waro idanu Zaid yayi maganar ma shi dariya taso basa, amma a irin wan nan yanayin dayake ciki bayatunanin zai iyayin dariya...
"Wayene yacema bazata zo ba?" Zaid yatambayi yaron.
"Ita da kanta" yaron yabasa amsa domin kuwa shiɗin ɗan maƙotansu ne saboda haka yasan Zahrah'n.
Kai Zaid yajinjina haɗe da cije laɓɓansa,, Allah sarki rayuwa babu yanda bata juyawa mutum, amma in banda haka wai yau shine a wata ƙasƙantacciyar unguwa kuma ƙofar gidan su mace yakuma aika tace bazata zo ba, shine fa Zaid ɗin da har gobe ƴan mata suke rushing akan sa, to amma meyasa haka takasance dashi?"  ganin da yayi yaron nashirin tafiya ne yasanya yace "Kaje kace injini nace tayi haƙuri tafito"  bamusu yaron yakoma yakuma faɗi saƙon da akabasa umarnin yafaɗa..
Tsuka Zahrah taja haɗe da tashi tsaye "Kaje kace wai inji Zahrah kozai mutu a tsaye baza ta zoba" tanakaiwa nan azancenta tayi wucewarta ɗaki..
Abunda Zahrah tafaɗa shi yaron nan yazo ya sanarwa Zaid,  kuɗi Zaid yaciro a aljihunsa 1k yabawa yaron dafari yaron yatsorita yaƙi amsa, amma Zaid yatilasta masa saida ya amsa, haka yaron yatafi yana murna...
Motarsa yabuɗe yashiga yayinda yakifa kansa a steering motar meyasa soyayya zata masa haka, idanunsa Zahrah kawai suke son gane masa tabbas yau bazai taɓa iya runtsawaba matuƙar baiga Zahrah ba, yana mawa Zahrah wani irin mugun so me tsananin zafi..   Jan motarsa yayi yakoma ƙarƙashin wata bishiya tayanda bakowa zai lura da cewa yana wajen ba, yaƙudurta aransa cewa koda zai kwana a wajen ne bazai gusa ba harsai idanunsa sun mai tozali da Zahrah....
Bayan awa É—aya
Zahrah ce tafito daga cikin gidan nasu sanye da wani siririn mayafi wayarta ce riƙe a hanunta se kuma wani littafi.   Zaid dake zaune cikin motarsa yana ganinta ya sake waro idanu haɗe da sauƙe ajiyar zuciya me ƙarfi,  jiyakeyi tamkar yaje ya ɗauƙota can caɗak yatafi da ita... Yana kallonta tayi shigewarta wani gida dake kusa da nasu gidan.. Bayan kamar mintuna 8 da shiganta gidan yaga takuma fitowa da sauri yabuɗe murfin motarsa daniyar ƙarasawa gareta sai de kuma ko taku biyu baiyiba tashige cikin gida ko ganinsa ma ita batayi ba, haushine yasanyashi buga tayar motarsa da ƙafarsa,   haka yakoma yayiwa motarsa key haɗe dayin reverse yabar unguwar tasu cike da ƙuncin rashin samun daman yi mata magana da be yiba, amma de yaji sanyi sosai a zuciyarsa daya ganta...
*********