← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 112

Sashe 75

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sarai ya fuskanci halin da take ciki,     "Zoki kwanta" yafaɗi haka yana meyi mata nuni da kan gadon dayake zaune,,  kamar wacce ƙwai yafashewa haka Zahrah ta zo ta kwanta akan gadon, gaba ɗaya ta takure kanta waje ɗaya,,,   miƙewa yayi daga zaunen dayake haɗe da  kashe  wutan ɗakin ya kunna na bacci, Zahrah najin takusan alamar yakusa zuwa kan gadon taji bugun zuciyarta ya tsananta, yayinda ƙirjinta yashiga wani irin luguden duka,,  kwanciyarsa akan gadon yayi dai dai da kusan ɗaukewar numfashinta,,,,   da ƙyar ta'iya ƙwato numfashinta, haɗi sa soma  sauƙe ajiyar zuciya  a ɓoye, kusan minti goma da hawansa kan gadon amma kuma taji baiyi mata wani abu ba, hakan yasa taɗanji zuciyarta tayi sanyi.    Shiru tayi tana me jin sauƙar numfashinsa ahankali, wani irin mugun tausayinsa ne taji yaɗarsu acikin zuciyarta amma kuma ita bata da yanda zatayi, tunaninta ne ya katse alokacin da taji sauƙar hanunsa  a bayanta,,   ahankali ya juyota tadawo tana fuskantarsa,, kallon fuskarta yashigayi batare dayace da ita komai ba, kusan mintuna 4 yayi yana kallonta, cikin wata irin murya wanda batasanshi da ita ba yace
"kicire hijabin nan saboda kiji daɗin baccinki ko"   
babu musu ta cire hijabin daga jikinta sai dai kuma bahaka ranta yaso ba, bargo yaja ya rufa musu  hanunta yakamo ta cikin bargon yariƙe acikin nasa,  "Ki kwantar da hankalinki, nasan kingaji, kiyi addu'a, kiyi bacci me daɗi" yafaɗi haka cikin muryar raɗa,  hanunta yasake damƙewa acikin nasa hanun haɗe da lumshe idanunsa,  zai bartane kawai saboda tausayinta dayake ji, amma bawai don baya sha'awarta ba, hasalima baita ɓa jin matsanancin sha'awarta irin nayau ba,  hakan yafarune kuma saboda baitaɓa samun kusanci me tsanani da ita irin na yau ɗin ba, da wannan tunanin bacci ya ɗaukesa,,,,   Zahrah ma dai baccin ne yaɗauketa batare data shiryawa hakan ba,,    ƙarfe ɗaya na dare wani irin zazzafan zazzaɓi yarufe jikin Zahrah take tasoma karkarwa haƙwaranta har haɗewa suke, suna ba da wani sauti, hakan yafaru ne kuma sakamakon  sanyin AC wanda yayi mata yawa,   acikin baccinsa yakejin hucin numfashinta nafita da sauri,  a hankali ya buɗe idanunsa ya sauƙesu akanta, da sauri yatashi ya zauna haɗe da kamo kafaɗunta,,  "Zahrah!" yaƙira sunanta a hankali,,   tanajinsa amma bazata iya amsa masa ba domin kuwa ba iya zazzaɓi ba hatta kanta jinsa take tamkar anɗaura mata gungumen ice, yamata nauyi   Da sauri ya sauƙa akan gadon, AC'n yafara kashewa, kana ya buɗe wata ƴar drower  maganin ciwon kai da zazzaɓi ya ɗauko haɗe da goran ruwa,, yana zuwa ya ta data zaune, ɓalle maganin yayi yasa mata abaki haɗi da kafa mata goran ruwa, babu musu ta haɗiye maganin, ajiye goran yayi  haɗe da hawa kan gadon, hanunsa yasanya akan wuyanta, zafi yaji zau kamar wuta,  ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da cire rigan dake jikinsa, cikin  bargon yakoma, haɗe da jawota kusa dashi,  ahankali yasanya hanunsa a bayanta yayi ƙasa da zip ɗin  doguwar rigan dake jikinta,,  cike da nutsuwa ya cire mata rigan,, Zahrah tana jinsa amma kuma ayanzu babu wani abu da zata iyayi wanda zata kare kanta,, bashi kaɗaiba har ita kanta saida ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi alokacin da  zallan fatar jikinsu suka samu haɗewa waje guda.    lokaci ɗaya yaji tunaninsa yasoma sauyawa, nutsuwarsa tafara gushewa, haka kuma idanunsa sun soma rufewa,,  haɗewar jikin Zahrah danasa jikin baƙaramin feeling me girman gaske ya sauƙar masa ba, tunda yake aduniyarsa yau shine karo na farko, da ya fara haɗa jikinsa dana mace haka, yasan yataɓa rungumar   Zahrah amma ba runguma irin wannan ba,,,,  Zahrah  kuwa baƙaramin jin daɗin jikin nasa tayi ba, jitayi gaba ɗaya nutsuwa yasoma sauƙar mata, sake maƙalewa ajikinsa tayi haɗe da cusa kanta acikin faffaɗan ƙirjinsa har yazamana laɓɓan ta suna gogan  fatar wuyansa,, jin yanda take ƙara shigewa jikinsa shiya ƙara taimakawa wajen ƙara masa wutar sha'awarta, hannayensa duka yasanya a bayanta yasake riƙeta gam,  numfashi kawai yake fitarwa akai akai shi kaɗai yasan meyakeji acikin jikinsa,,  yana cikin wannan irin yanayin yaji sauƙar numfashin Zahrah ahankali yana fita da'alama baccine yakuma ɗaukarta,,,   haka yarungumeta ƙam acikin jikinsa yayinda yacusa kansa acikin gashin kanta yana shaƙan daddaɗan ƙamshinta dake ƙara rikitasa,, bakaɗan ba ya yi jarumta wajen ganin ya ƙyaleta baiyi mata komai ba,  haƙiƙa bakowani irin namiji bane zai haɗa jiki da mace ace ya iya daure zuciyarsa baiyi mata komai ba, balle ma mace irin Zahrah wanda irinsu basu da yawa acikin mata,,  da ƙyar bacci ya'iya ɗaukarsa.......

*(Kuyi Haƙuri idan kunga typing error ina busy ne)*
   
        

*18/January/2020*

          *Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

       *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
     @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

       *CHAPTER 92 to 93*

Ƙiran sallan asuban fari akan kunnensa,, a hankali ya ware idanunsa akanta, baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali da'alama zazzaɓi da ciwon kan dake damunta sun jima da kama gabansu,,  baisan lokacin da murmushi ya ƙwace masa ba, komai na Zahrah me kyau ne, har idan tana bacci kyawunta baya ɓuya, kallon zara zaran eye lashes ɗinta daya kwanto aɗan ƙasan idanunta yayi,,  ahankali ya zare jikinsa daga nata jikin, cikin sanɗa yatura ƙofar bathroom yashige, gudun kada motsinsa ya tashe ta daga daddaɗan baccin da take,,  saida yafarayin wanka kafun ya ɗauro alwala,,  tsayawa yayi yana kallon yanda taketa fidda numfashi a hankali,  badon sallah yazama dole akanta ba, to tabbas da babu abun da zai sanya ya tasheta a dai-dai wannan lokacin, zai bartane tasha baccinta ta ƙoshi,, ahankali yashiga girgiza ƙafanta haɗe da ɗan ƙiran sunanta, cikin murya ƙasa ƙasa... Da yake bata da nauyin bacci, ƙira biyu yayi mata ta buɗe idanunta,, da sauri ta sake jawo bargo ta rufe jikinta, kana tasoma raba idanu,   murmushi yakumayi mata haɗe da sanya hanu ya shafi gefen kumatunta.

"Kitashi kiyi sallah, ni na wuce masallaci"

Bata iya amsa masa ba haryafice daga cikin ɗakin,,    kallon kanta tashiga yi gaba ɗaya gashinta ya watse yayi buji buji dashi, da'alama dai tasha juyi acikin bacci,,,    tana shiga bathroom ta haɗawa kanta ruwa me ɗan ɗumi, wanka tayi itama kana ta ɗauro alwala (🤔Yadai dukanku wanka sai kace 🙊)....

Tana fitowa daga bathroom ɗin ta zura wata jan doguwar riga marar nauyi, haɗe da zura hijab ajikinta,  kan sallaya tahau  haɗe da dai-dai ta tsayuwarta......      Koda ta'idar da sallan saida tayi azkar kafun ta miƙe daga kan sallayan,,   harta zauna akan gado, maganganun Hajiya Shuwa suka faɗo mata arai inda take ce mata  _"Kada ta sake ƙamshi yabar jikinta, sannan kuma idan tayi sallan asuba kullum tana shafa turare aduk wani lungu da saƙo na jikinta"_ batasan mene manufar hakan ba, amma dai ta ɗau maganar kuma zatayi aiki dashi.   Gaban mirror tanufa haɗe da ɗaukan ƴar ƙaramar hand bag ɗinta dake aje kan mirror'n  wani ɗan kwalban body spray ta ciro daga cikin jakar, haɗe da fesawa ajikinta, daga kan wuyanta har zuwa bayan kunnenta, sosai turaren yake da ƙamshi, take ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren,, tana shirin maida turaren cikin jakarta, Dr.Sadeeq yaturo ƙofar yashigo bakinsa ɗauke da sallama,, cikin murya me sanyi ta amsa masa sallaman nasa,,    direct inda take tsaye ya nufo, batayi tsammani ba saiji tayi ya buɗe hannuwansa ya rungumeta ta baya haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta,,,, idanunsa ya lumshe haɗe da buɗe hanci ya shaƙi daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta cikin wata irin murya yace
"Good morning madam!"

Kunyan sane yakamata,  saikawai tayi ƙasa da kanta haɗe da cewa

"Ina kwana"

"Lafiya ƙalau, yajikinki?" ya amsa mata yana me cusa kansa acikin wuyanta..

"Da sauƙi"

Ta mayarmai da amsa cikin ƙasa da murya...

"Ƙamshinki yamin daɗi sosai, kinyi sallah ne?"

Kanta ta ƙaɗa masa alamar "Eh" hanunta yakama yajata zuwa kan gado... Zama yayi kana ya jawota jikinsa,,    ɗago fuskarta yayi haɗe da jefa idanunsa cikin nata.     Sunanta yaƙira cikin wata irin murya me ɗauke da nutsuwa..

Kanta ta ɗago ta kallesa, ganin idanunsa tsaye cak akanta yasanya tayi saurin meda kanta ƙasa..    

"Meyasa kikejin kunya na sosai ne?"

Yayi mata tambayar da bata tsammata ba,, jijjiga kanta tayi alaman 
"babu"

Sake matseta acikin jikinsa yayi haÉ—e da kwantar da kansa akan kafaÉ—anta.

"Mallakarki danayi wata babban nasara ce dana samu acikin rayuwata Zahrah, inasonki ne da duka zuciyata,  dakuma iya gaskiyata, banda niyar cutar dake acikin rayuwar zaman aurenmu,   abu ɗaya nakeso kiyi mini shine, ki rage yawan tunani da kuma kukan nan dakikeyi, inajin tsoro kada su haifarmiki da wata cuta, yanzu nasan kina da buƙatar hutu ko, ki kwanta ki huta, kafun anjima sai kiyi break fast"   
Chapter 75 · 0% Book details