Sashe 33
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dagaske kike, saboda ni kike wannan nishaɗin? " Dr ya tambayeta cike da zaƙuwa, duk da kuwa cewa yasan sabo da shiɗinne take nishaɗin.
"Eh mana, saboda kaine, kasan kaban dariya sosai, kuma nasan bama ni kaÉ—aiba, duk wacce takalleka a irin wannan yanayin dole zatayi dariya"
Ajiyar zuciya Dr ya sauÆ™e haÉ—e da murza key É—in motar, suka É—au hanyar da zata sadasu da titi. Â
"Idan kina dariya kinfi ko yaushe kyau Æ´an mata na!" Dr yafaÉ—a cikin muryar nutsuwa.
Saurin maida kallonta garesa tayi, jin abun da yafaɗa tayi kamar wani almara, sai kuma taga yanayinsa tamkar bashine yayi maganar ba.
Yi tayi itama kamar bataji mai yace ba, mai da kallonta tayi ga titi, tana mai kallon yanda ababen hawa suke gudanar da hada hadansu.
"Maiyasa ki ka ƙi cin abinci? ko kinfiso ki zauna da yunwa ne?" Doctor ya jefo mata tambayar da batayi zato ba.
Kallo É—aya ta yi masa ta kau da kanta gefe, "Banjin yunwa ne, sannan kuma banaso na yi latti"
tafaɗi maganar a taƙaice.
Baice da'ita komaiba, saima buɗe ɗan ƙaramin drowern dake jikin motar yayi, wani haɗaɗɗen cake dake cikin wani ɗan ƙaramin kwali ya ciro, haɗe da ɗaura mata akan cinyarta, " Kici, kuma banson musu" yanayin yanda yayi maganar zai tabbatar ma da cewa, ba wasa yake ba.
"Nagode, amma zanci idan muka fito a lecture" itama ta faÉ—a kai tsaye.
"Yanzu nakeso kici, umarnine bawai shawara ba" yakuma faɗi maganar cikin yanayi mai nuni da cewa da gaske yake maganar.
Batason yi masa musu, domin koba komai yayi mata halacci a cikin rayuwarta, a hankali take gutsuran cake É—in tana kaiwa bakinta, duk da cewa cake É—in yayi mata daÉ—i.Â
Duk abun da takeyi yana lure da'ita, yanayin yanda take tauna abincin shiyafi komai burgesa.
Saida taci cake ɗin fiye da rabi, kafun ta dawo da kallonta garesa, "Naƙoshi" tafaɗa tana mai yatsine fuska.
"Dole sai kin cinye, domin kuwa ni idan nabawa mutum abuna, bai isa yacemin ya ƙoshi ba, dole sai yacinye koda kuwa ya ƙoshin"
Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa "Dagaske nake naƙoshi, amma da alama dole kakeson min"
"Dolen dole ma kuwa" yafaɗa dai dai lokacin da yagama parking motar tasa, domin kuwa harsun kawo cikin makarantar tasu, hanu ta ɗaura akan murfin motar da niyar buɗewa ta fita, tuni ya dannawa ƙofofin luck, saurin kallonsa tayi domin bata fahimci hakan da yayi me yake nufi ba.
"Babu inda zakije, matuƙar baki cinye cake ɗin nan ba" yafaɗi hakan yana me jingina bayansa a jikin kujeran da yake kai.
Ƙwaɓe fuska Zahrah tayi cikin sigar lallashi, tace "Kayi haƙuri, naƙoshi, idan naci da yawa, bazan iya karatu yanda ya kamata ba!"
"Um,Um, naƙi wayon, saura kaɗanne fa please kicinye shi mana Zahrah!" Doctor Sadeeq yaƙare maganar cikin lallashi.
"Um, Um, na ƙoshi, gaskiya idan naci zai cutar dani, zanyi ƙatuwa da yawa, ni kuma banaso nayi ƙatuwa!" cikin zallan shagwaɓa Zahrah tayi maganan.
Dariya sosai Dr Sadeeq ya sanya, domin kuwa maganar Zahrah ta bashi dariya, wai ita bataso tayi ƙatuwa hmm.
"To ai yaune kawai, kuma kinga bazakiyi ƙatuwa ba, nima banso kiyi ƙatuwa da yawa, amma inaso kiyi ƙatuwa kaɗan!" yanayin yanda yayi maganar kaɗai ya isa sanyawa mutum mutuwar jiki.
Batace dashi komaiba, domin bata fahimci inda maganar tasa ta dosa ba, É—aukan ragowan cake É—in tayi, tashiga turawa acikin bakinta, tamkar wacce aka bawa guba.Â
Dariya Doctor Sadeeq yashiga yi mata ƙasa ƙasa, domin kuwa yanda takecin cake ɗin, dagani kasan dole a kayi mata bawai a son ranta bane. tana cinyewa ya miƙomata goran ruwa, ai kuwa ba musu ta karɓa ta shiga sha, domin dama duk cake ɗin ya shaƙeta.
Cikin yanayi na shagwaÉ“a da É“ata fuska tace " Na cinye yanzu zan iya tafiya!"Â
Dariya Dr yayi haɗe da cire luck ɗin da yasanyawa ƙofofin motar "Zaki iya tafiya, amma kikula da kanki sosai, sannan idan kun fito a lecture wani zai kawo miki saƙo daga nine ki amsa"
"Wani saƙo?" Zahrah ta tambaya cike da ɗaurewar kai.
"Zakiyi latti,kiyi sauri kije" Dr yafaÉ—i hakan don kawar da tambayar da tayi masa.
Bata sake cewa komai ba tabuÉ—e murfin motar tafice, yauma dai sai da yaga shiganta cikin hall É—in kafun yatada motarsa yabar cikin makarantar, direct shima asibiti ya nufa, domin yau yanada aiki sosai.
Sosai yau ta gane Lecture ɗin da akayi musu, saɓanin sauran ranakun da suka wuce wanda ba komai take fahimta daga cikin abun da ake koyar musu ba.
Fitowarsu kenan daga lecture, tafe suke su biyu, yayinda Husnah keta mita, wai jimawan da sukayi suna lecture, yasanya tanemi gaba É—aya abincin cikinta ta rasa.
Dariya Zahrah tayi haÉ—e da cewa "Nikuwa kinga É—igo na yunwa banaji, domin kuwa yau É—ure, a kamin dan dole na"
"É—ure kuma bestie? Amma badai Inna da Baffa bane sukaimiki É—uren bako?"
"Doctor Sadeeq ne!" Zahrah tafaɗa a taƙaice.
"Doctor Sadeeq kuma? lallai kuwa Doctor yayi babban ƙoƙari, shiyasa na ganki yau kina cikin farinciki" Husnah tafaɗa tana mai ƙoƙarin gimtse dariyar da take ƙoƙarin taso ma ta, domin ita kam ta hango wani babban al'amari dangane da Doctor dakuma Zahrah.
"Maikike nufi?" Zahrah ta tambayi Husnah cikin tsare gida.
Husnah batakai ga bata amsa ba, wani mutumi ya ƙaraso garesu, hanunsa ɗauke da wata leda, sallama yayi musu suka amsa masa.
Kaitsaye ya miƙomawa Zahrah ledar dake hanunsa, haɗe da cewa "Gashi inji oga"
Take maganar da Dr yafaɗa mata ɗazu a cikin mota, cewar wani zai kawo mata saƙo, ya faɗo mata, cikin sanyin jiki ta amshi ledan, haɗe da ce masa ta gode.
"Saurin karɓe ledan Husnah tayi daga hanun Zahrah, haɗe da cewa "Allah yasa abun daɗi ne, domin yawuna haryafara tsinkewa, kinsanni ba baya bace wajen kwaɗayi"
"Wow special gift!!" Husnah tafaÉ—a sanda idanunta suka gane mata abun da ke cikin ledar,
"Amma ba haka naso ba, ƙawata naso ace wani abun ci ne kinga da sai na morewa bakina!" Husnah ta ƙare maganar tana mai ɓata fuska.
Dariya Zahrah tayi haɗe da sanya hannayenta ta dafa kafaɗun Husnah, cike da nishaɗi tace " Allah ƙawata, ki rage kwaɗayi, yanzu idan abun ci ne, yazuba mana wani abu a ciki, mukazo mukaci, ya cutar da mu,kuma fa? kinga kwaɗayi ya jawo mana kenan,kuma bai mana rana ba"
"Dan Allah malama sakeni, nayarda da Dr nasan babu abun da zai ɓamu wanda zai cutar da mu, kedai kawai mugunta ne irin naki, bayan kinsan inajin yunwa, muje cafeteria muci abinci please!" Husnah tafaɗa tana mai daɗa kwaɓe fuska.
"Yi haƙuri ƙawata bani nakar zomonba, muje sai kici abincin ko" Zahrah tafaɗa cike da kulawa.
"Ungo kayan shafanki, domin kuwa cigaba da riƙesu ma, ƙaramin yunwa zaiyi" Husnah ta ƙare maganar tana mai miƙomawa Zahrah ledar dake hanunta.
Dariya kawai Zahrah tayi haɗe da amsar kayan, sarai tasan Husnah bata da haƙurin yunwa ko kaɗan.
Ice cream kawai Zahrah tasha, yayinda Husnah kuwa ta cika cikinta da shinkafa.  Yau darasi biyu garesu kacal, don haka suna fitowa kowa ya yi ƙoƙarin kama gabansa.
Waige waige tashiga yi ko zata hangosa, amma babu alamar komai irin motarsa, wayarta ce ta soma ƙara alamar shigowar ƙira,  Number ne ke yawo a kan screen ɗin wayar babu suna, dama kuma batayi tunanin Numbern zai fito da suna ba, domin batayi saving numbern kowa ba, wama ta sani da zatayi saving number'nsa.
Har saida wayar ta kusa katsayewa kafun Zahrah ta ɗaga ƙiran,  "Zahrah! na gaji, da yawa, aiki yamin yawa, please ga nan driver na, zaizo ya ɗaukeki ya kaiki gida, kiyi haƙuri kinji ƙanwata!!" Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin kwantar da murya, da gajin yanda muryansa take fita slow kasan cewa a matuƙar gajiye yake.
A jiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa "Shikenan kahuta lafiya"
"Yauwa Ƴan mata na, ki kulamin da kanki" ƙit ya kashe wayar, ba tare da ya tsaya ya saurari mai zata ce ba.
Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da girgiza kanta, "Hmm wai itace ƴan mata, itakam yanzu ai ta wuce a ƙirata ƴan mata saidai sauran Zaid" tafaɗi hakan a zuciyarta, take kuma taji idanunta sun kawo ruwa. Dai dai lokacin motar Dr Sadeeq ta ƙaraso inda take tsaye,  kasan cewar yayi mata bayanin cewa driver'n sane zaizo ɗaukarta, dan haka batayi wani jinkiri ba, ta buɗe murfin motar tashiga, ko kallon inda driver'n yake batayi ba,   "ZAHRAH!" muryan Dr Sadeeq ya daki dodon kunnuwanta, saurin maida kallonta inda taji muryan tayi, ai kuwa shiɗinne kwance a jikin kujeran gidan baya, idanunsa ɗaya ya kashe mata haɗe da ɗage giransa ɗaya sama, "Surprise!" yafaɗa fuskarsa ɗauke da murmushi.
Murmushi itama tayi masa, haÉ—e dayin Æ™asa da kanta, domin yanayin yanda yayi mata maganan, yasanya taji jikinta yayi sanyi.Â
"Dawo nan muzauna, ki bar driver yayi aikinshi"
Æata fuska Zahrah tayi haÉ—e da turo baki gaba, cike da shagwaÉ“a tace "Ni dai kabarni na zauna anan É—in ma yayi!"
"Nace ki dawo nan muzauna ko!" yafaÉ—i hakan babu alamar wasa akan fuskarsa.
Cike da sakalci Zahrah ta dawo gidan baya inda yake zaune, ko kallonsa batayi ba saima langwaÉ“ewa da tayi a jikin kujera.  Har sukayi nisa a tafiyan babu wanda yace da É—an uwansa Æ™ala,  cikin shagwaÉ“a tace "Bakace min aiki yamaka yawa ba, amma mai yasa kazo?"Â
"Saboda ya cancanta nazo, ina da burin baki kyakkyawan kulawa a ko da yaushe, ko bakiyi farinciki da hakan ba?"
"Nayi farinciki sosai!" Zahrah tafaÉ—a kai tsaye, domin kuwa sam batason irin kallon da yake yawan yi mata a wasu lokutan.
Baisake ce da ita komai ba, shima sai ma komawa da yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran motar.
A haka har suka iso ƙofar gidan su Zahrah'n,  kallo ɗaya tayi masa haɗe da buɗe murfin motar tayi ficewarta, yana ganin shigewarta gida, yace driver ya ta da motar suje.
Bayan Sati Biyu....