Sashe 20
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaf yagama shirya kansa cikin wasu mayun riga da wando, masu kyau da tsadar gaske, bakaɗan ba yayi kyau sai tashin daddaɗan ƙamshi jikinsa yake, SHU'UMIN NAMIJI kenan ganinka babu alkhari acikinsa, ƴar ƙaramar trolly bag ɗinsa ya shiga ja, bayan yaɗauki wayoyinsa da kuma duk wani abu dayasan zai buƙata,, wannan karan ko ɓangaren mahaifiyarsa bai jeba, motarsa ƙirar BUGATI yashige, yayin da driver yabamawa motar wuta, kaitsaye airport suka nufa, domin dai alƙawari Zaid yaɗauka yau bazai kwana acikin Nigeria ba, yawon shaƙatawa zai tafi New York City (America).. Yana shiga cikin jirgin baiwani jimaba, jirginnasu yaɗaga zuwa sararin samaniya.....
 *((kuyi haƙuri page ɗin yau baida yawa...))*
    *12/November/2019*
   _________________________
   *MRS SARDAUNA*
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
   Â
       *SHU'UMIN NAMIJI !!*
        Â
  *Written By*
phatymasardauna
*Dedicated To My Loveƙy Brother Khabier...*
*🌈Kainuwa Writers Association*
'''{United we stand and succeed our ambition is to intertain & motivate the mind of readers}'''
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
       *WATTPAD*
    @fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*Wannan Page É—in gabaki É—ayansa kyautane a gareku.*
  Â
   *UMMIEE-ZARIA.*
   *MRS MAI LAWAL.*
   *MAMAN TEEMAH.*
   *ZEE BLACK.*
   *AYSHA HUMAIRA.*
  *SA'ADAH GALADIMA.*
  *MY ADIZATOU (Ummu Adnan.)*
  *MARIYA...â¤.*
*Chapter 27 to 28*
Tunda Zahrah tasume, bata sake sanin inda kanta yake ba, sai ƙarfe shida na yamma, alokacin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba, wannan karon sam batayi wannan iface ifacen da kuma fusge fusgen da tasaba yi ba, sai dai idanunta da ta tsayar waje ɗaya,wato kan ceiling ɗin dake saman ɗakin, hawayene kawai kefitowa daga cikin idanun ta, yana mai sauƙa a gefen fuskarta,  "Zahrah !" Inna dake gefe taƙira sunan Zahrah.
Ko gizau Zahrah ba tayi ba, balle Inna tasaran zata amsa mata, gyra tsayuwa Inna tayi haɗe da jinjina kanta, tabbas tasan koma meyafaru da Zahrah sune sanadi, domin kuwa basu riƙe amanar da iyayenta suka basu kafun su rasu ba.
Dr Saddiq ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo, bakinsa ɗauke da sallama, yayinda Baffa ke biye da shi a baya,  "Yauwa likita kazo ko? ta farka amma kwata-kwata bata magana!" Inna tafaɗa cike da damuwa.
Ɗan guntun murmushi kawai Dr Saddiq yayi,haɗe da nufar inda Zahrah'n ke kwance, kallonta yayi na ɗan wasu mintuna, kana yajuyo da kallonsa wajen su Baffa...  "Inaso Za'ayi mata gwajin ƙwaƙwalwa, domin sake tabbatar da lafiyarta, saboda haka zanturo Nurses su ɗauketa " Dr Saddiq yafaɗa.
Sosa kai Baffa yashiga yi, cike da damuwa yace "To kamar nawa ake buƙata likita? kuma naga tunda mukazo ka ke bata kulawa, amma banji anyi min maganar nakawo ko sisi ba, fatana Allah yasa gwajin ƙwaƙwalwar bashi da tsada !" Baffa yafaɗa cikin karyewar zuciya, domin kuwa idan gwajin yana da tsada tofa sai dai ahaƙura, saboda bashi da kuɗi.
Kallonsa kawai Dr S.S yayi batare da yace dashi ƙalaba, ya sa kai yayi ficewarsa daga cikin ɗakin.
Mintuna kaɗan da fitarsa, wasu nurses su biyu suka shigo, ɗaukan Zahrah sukayi, suka ɗaurata kan wani gado mai ƙafafun taya, suka fice da'ita, ba don idanunta da suke buɗeba, tabbas da idan ka ganta zakayi zaton gawace, domin kuwa babu abun dake, motsi a jikinta, sai hawaye kawai dake ambaliya a cikin idanunta...
Alhmdlh anyi mawa Zahrah gwadin ƙwaƙwalwa lafiya, saura kawai ajira fitowar result.
Babu abun dayake É—aga mawa Dr S.S hankali a yanzu, kamar yanda take yawan firgita, gashi hawaye sun kasa daina zubowa daga cikin idanunta, babban abun damuwar kuma shine bata um balle um um, ko motsawa bakinta bayayi, sannan kuma waje É—aya idanunta suke kallo, wato sama.
Result ɗin gwadin da'akayi mata yafito, kuma masha Allah, ƙwaƙwalwarta tana nan lafiya, babu abun daya sameta, kawai dai tashiga halin firgici ne, kuma dama ana yawan samun irin haka...
"Likita ya sakamakon, Allah yasa bata samu wani matsala a ƙwaƙwalwarta ta ba ? " Baffa dake zaune cikin office ɗin Dr S.S ya tambaya.
"ku kwantar da hankalinku, sakamako yayi kyau, domin kuwa brain É—inta nanan lafiya"
"Alhamdulillah, Allah mungodema !" Baffa yafaÉ—a cike da jin daÉ—i,
"Kaine Babanta mahaifi ?" Dr S.S yatambaya sanda yake ƙoƙarin cike wani file dake gabansa.
"A'a bani na haifeta ba, ƴar ɗan uwana ne da ya rasu, amanarta yabarmin, gashi yanzu bansan wani tsinannen bane ya aikata ma ta wannan abun ba !" Baffa yaƙare maganar yana matsan ƙwalla.
Kallon sa Dr S.S yayi na tsawon wasu mintuna, kafun ya kau da kansa gefe, "Dawa take mu'amala, saurayi ko aboki ?" Dr S.S ya kuma tambaya.
"Bata mu'amala da kowa sai wani yaron arziki, shine ma yace yana sonta, kuma hargida yataɓa zuwa ya gaisheni, a zahirin gaskia bana tunanin shi zai yi mata wannan aika aikan" Baffa yafaɗa da ƙwarin guiwarsa.
"Maiyasa kake tunanin shi bazai iya yi mata haka ba ?" Dr S.S yakuma jefo mawa Baffa tambaya,
"Saboda shiÉ—in yaron kirkine kuma É—an babban gida ne, mutane masu dattako"Â (readers kuji Baffa fa da sharri )
"Zaka iya tafiya, anjima zanzo na bata maganinta" Dr S.S yafaɗa a taƙaice, domin kuwa wani irin taƙuƙin takaicin Baffa ne ya cika masa zuciya,
Sumi sumi haka Baffa yafice daga cikin office ɗin, yana matsan ƙwalla.
"Wai maiyasa mutane suke wasa da amana ne ? idan har ɗan uwanka bazai iya riƙe maka ahalinka, idan baka raye ba, to waye zai iya riƙe maka su da gaskia dakuma amana? ƴar ɗan uwanka tamkar ƴa take a wajenka, idan baka nuna ma ta soyayya ba, to wazai nuna ma ta? irin su Baffa ne suke ɓatawa mutane suna, kuma suke tozarta marayu, ya Allah kabamu ƴan uwa masu amana, wanda zasu kula da namu ko bama raye Ameen." Dr S.S yafaɗa acikin zuciyarsa,
Yau kwanan Zahrah Biyu kenan bata magana, hawaye har sun gaji da fitowa daga cikin idanunta sun kafe, duk kuwa yanda su Baffa suka so ta faɗi koda kalma ɗaya ne, hakan ya gagara, domin kuwa ko kallonsu batayi balle su sa ran zatai musu magana. Sosai Dr S.S yake ƙoƙari wajen kulawa da'ita, baya wasa da lokacin shan maganinta, domin yana da yaƙinin zuwa yanzu, ɗinkin da akayi mata a ƙasanta ya warke.
Zaune yake a kan É—aya daga cikin kujerun falon mahaifiyar sa, sanye yake da riga da wando na maroon É—in bugaggiyar shadda, bakaÉ—an ba kuwa yayi kyau acikin kayan,  kallo É—aya zakai masa kafahimci cewa a kwai damuwa a tattare dashi, domin kuwa tun É—azu aka aje masa plate É—in snacks a gabansa, amma yakasa É—aukan ko da Æ™waya É—aya ne, yakai bakinsa, duk da kuwa snacks É—in abune mafi soyuwa a garesa,,Â
Hajiya ce tsaye a kansa, tayi kusan minti É—aya da zuwa amma sam baisan da zuwan nata ba,
"Saddiq!" Hajiya taƙira sunansa.
"Na'am, Hajiya sannu da fitowa!" Dr S.S yafaÉ—a cikin girmamawa.
Zama Hajiya tayi haɗe da kallonsa cike da kulawa tace " Wai meke damunka ne Saddiq ? ina lure da kai gabaki ɗaya kwana biyunnan bana gane kanka, idan kafita aiki baka dawowa da wuri, ga yawan tunani da kakeyi, meke faruwa ne ?" Hajiya ta tambaya.
Gyara zama Dr S.S yayi, domin sam baya ɓoyewa mahaifiyar tasa matsalarsa,ko ta me cece kuwa,  cike da damuwa yace "Hajiya wata yarinya aka kawo hospital ɗinmu, duka dukanta bazata wuce 18 to 19 year ba, yarinyar tana matuƙar baƙatar taimako, domin kuwa, wani ne yayi raped ɗinta, ahalin da ake ciki yanzu, ko magana batayi, narasa wace hanya zanbi nashawo kan lamarin!"  Dr S.S ƴafaɗa cike da raunin murya,
"Subanallahi fyaÉ—e kuma Saddiq ?"
"Eh Hajiya, shiyasa abun yake damuna" Dr S.S yafaÉ—a,
"Allah sarki! Allah ubangiji ya cigaba da tsare mana Æ´aÆ´anmu, amma iyayenta sun maka case É—in a kotu ne ?" Hajiya ta tambaya.
"A'a Hajiya banjin zasu kai case ɗin kotu, domin kuwa talakawa ne basu da wani ƙarfi " Dr S.S ya faɗa cike da tausayawa.
"To Allah yabata lafiya, amma miye na jefa kanka acikin damuwa haka Saddiq? irin wannan matsalolin naga dama an riga da an saba kawo muku, sai dai Allah yarufa asiri kawai, bakaci snacks É—inba mai yasa ?"
"Zanci Hajiya ko zuwa anjima ma" Dr S.S yafaɗa lokacin dayake miƙewa daga kan kujeran dayake zaune,
"A'a ina zaka kuma ?" Hajiya ta tambaya.
"Lokacin shan maganin Zahrah yayi Hajiya, zanje ne na bata" yaƙare maganar yana mai duba wrist watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.
"Zahrah! wacece kuma Zahrah ?" Hajiya ta tambaya,
"Itace yarinyar da akayi raped nata dana gaya miki"
"To to adawo lafiya"
"Ameen Hajiyana!"
Yana fita yashige cikin motarsa kaitsaye hanyar asibitinsu ya É—auka....  Â
Kamar koda yaushe zaune take akan gado, yayinda idanunta ke kafe a waje É—aya, ruwan hawayene kawai ke tsiyayowa daga cikinsu,
Da Sallama É—auke a bakinsa yaturo Æ™ofar É—akin, harya Æ™araso tsakiyar É—akin, batasan ma da zuwan sa ba,Â
Aje abubuwan dake hanunsa yayi akan ƴar ƙaraman drowern dake gefen gadon,  "Zahrah!" yaƙira sunanta cikin kwantar da murya, bata amsaba kuma bata juyo zuwa garesa ba, dama kuma yasan hakan zai iya faruwa, domin bata taɓa amsawa idan yaƙirata, bakuma ta tankamai komai zaice, duk da kuwa yasan tanajinsa.