Sashe 48
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tanajin Muryan Baffa a tsakar gida, tayi saurin share hawayenta, haɗe da miƙewa tsaye, domin har Baffa yafara ƙwaɗa mata ƙira.
Fuska cike da fari'a Baffa yace "Likita ke yake jira, zai tafi"
Sumi sumi haka Zahrah ta fice yayinda tabar Baffa yana gayamawa Inna abun da ya wakana tsakaninsa da Likita.
Tun fitowarta yake ta zabga murmushi, kallo É—aya zakai mawa fuskarsa ka gane cewa yanacikin farinciki.
"Kitayani murna My Princess saura ƴan kwanaki ƙalilan na mallake ki!" Dr Sadeeq yafaɗi haka cike da shauƙi.
Kunyane yakama Zahrah, don haka ta sanya duka hannayenta biyu ta rufe fuskarta, bayan ta ƙaƙalo murmushi ta aza akan fuskar ta..
"Baffa yabani daman naturo magabatana don asa mana ranan aure, kuma insha Allah, gobe magabatana zasu zo, za'asa ranan aurenmu nan bada jimawa ba, so sai ki shirya domin kin kusa zama amaryata!" yanayin yanda ya ƙare maganar kaɗai ya isa taɓa zuciya..
Kunyane yasake kama Zahrah, har batasan sanda murmushi mai sauti ya kufce mata ba, gaba ɗaya ta lura Dr.Sadeeq ya ƙosa da ayi aurensu bata kumasan dalilinsa nayin hakan ba..
"Kinyi shiru kodai bakya farinciki ne my princess?" yatambaya.
ÆŠan satan kallonsa tayi haÉ—e da sakarmasa murmushi mai tsayawa a zuciya.
Ƙaran wayarsane ta katsesa daga kallonta da kuma zancen zucin da yakeyi. Ajiyar zuciya ya sauƙe ganin wacce take ƙiran nasa, maida wayar tasa cikin aljihu yayi batare daya ɗaga ƙiran ba.
"Dare yayi Zahrah kishiga gida, zamuyi waya, kikulamin da kanki "  yafaɗi hakan yana me ƙoƙarin shiga cikin motarsa.
Murmushin dole Zahrah tayi haɗe da yi masa saida safe, tajuya ta nufi cikin gida, hakanan taji wani iri a zuciyarta duk da batasan me yasa baiɗaga ƙiran da ake mai ba, amma tana da yaƙinin cewa matar da zai aura tare da itane ta ƙirasa. Saurin kawar da tunanin tayi aranta, domin tuna hakan ma bashida amfani a gareta.
Washe Gari....
Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaɗa hakanne ya kasance da da dare bayan sallan magriba Baffa Amadu shida amininsa suka zo gidansu Zahrah don tambayan aurenta, balaifi Baffa yayi musu tarba mai kyau, sunkuma ji daɗin hakan, duk da sun lura cewa suɗin basuda wani ƙarfi, ma'ana arziki...
Magana ta fahimta akayi tsakanin Baffa da kuma Baffa Amadu, a taƙaice dai Baffa yabasu auren Zahrah, yayinda sukuma suka ɗau alƙawarin cewa a cikin satin za'akawo kayan tambaya dakuma na lefe, daga nan sai asa ranan aure, amma basason auren ya ɗau lokaci, saboda rana ɗaya suke so ayi dana Salima.. Da to kawai Baffa ya amsa musu domin shi baida wani abun cewa banda hakan, sai dai a ƙasan zuciyarsa tunani yake taya zai samu kuɗin da zaiyi mawa Zahrah kayan ɗaki, domin dai bayanda za'ayi ace anyi aure ba kayan ɗaki... Haka dai sukayi sallama cike da mutun ta juna...
Baffa ne Zaune akan tabarma ya yi jigum bakomai ke damunsa ba, kamar sha'anin auren Zahrah, Allah yasani ko abincin da za'aci abikin bai tanada ba, balle wata uwa uba kayan É—akin da za akaita dashi..
"Wai tunanin mekakeyine haka tun É—azu?" Inna dake zaune gefensa ta jefo masa tambaya.
"Ba dole nayi tunani ba Salame, kinga dai yau iyayen yaron nan Sadeeq suka zo, kuma da duk kan alama basa so aja auren nan yakai wani lokaci, kin kuma san halin dai da muke ciki na rashin kuÉ—i"
"Yo dama akan wannan kake ɗaga hankalinka? hmm Malam kenan to ai ni banga abun ɗaga hankali anan ba, ca nake shi Sadeeq ɗin yasan duk halin da muke ciki, kuma shi yakawo kansa yace ya na so, bawai mu makai masa dole ba, saboda haka malam ka kwantar da hankalinka, Zahrah ya nema kuma Zahrah'n zamu bashi" Inna tafaɗi haka da'iyaka gaskiyarta...
Kallon Inna kawai Baffa yayi haɗe da girgiza kansa, yasan ma koda yayi ƙoƙarin fahimtar da'ita to fa bazata fahimta ba.
***
"What? Mom cewa fa kikayi wai bani kaÉ—ai Sadeeq zai aura ba, anya kuwa Mom kinji abun da Hajiya Habiba tafaÉ—amiki da kyau?" Salima tatambayi mahaifiyarta Hajiya Furaira cike da mamakin jin abun da mahaifiyarta tace da'ita..
"Abun da na faɗa miki shi naji daga bakin Hajiya Habiba, Salima kicire Sadeeq a ranki, domin kuwa aurenki dashi bazai taɓa yiyuwa ba, da raina dakuma hankalina bazan taɓa bari ƴata taje kan kishiya ba!" Hajiya Furaira tafaɗi haka cikin ɓacin rai..
Kuka ne ya Æ™wacemawa Salima cikin muryan kuka ta soma cewa "Wani irin cin amana ne wannan mom, sai da maganar aurena dashi ta kankama sannan wata banzar magana zata É“ullo, wallahi bazan haÆ™ura da shi ba, bakuma zan taÉ“a zama da wata a matsayin kishiyata ba, dole ne Sadeeq ya aureni ni É—aya batare da wata ba, bazan iya jure rashin saba Mom, dan Allah kiyi wani abu" Salima ta Æ™are maganar cikin shaÉ“e shaÉ“e da hawaye.Â
"Mekikeso nayi Salima? so kike naje na basu haƙuri akan su sa Sadeeq ya aureki ke kaɗai? ko ko sokike na zubar miki da ƙima daƙuma ƴancinki? Hajiya Habiba ƴar uwatace kuma ƙawata, bantaɓa tunanin haka daga gareta ba, amma bakomai, zanyi maganin abun, kuma ni banzauna da kishiya ba, ƴa tama bazata zuana da kishiya ba, wannan alƙawarine na ɗaukar mawa kaina" still cikin ɓacin rai Hajiya Furaira take maganan...
Cikin matsanancin ɓacin rai Salima ta juya ta koma ɗakinta, ji takeyi zuciyarta na tafarfasa, kamar ita ace ta haɗa miji da wata, sam bazai yi wuba, lallai ko da mahaifiyarta bazatayi wani abu ba yakamata ace ita tayi, wayarta da mayafinta ta ɗauka, a fusace ta fice daga ɗakin nata, tana son Sadeeq tun ba yau ba, zata kuma iyayin komai akan sa.
Æangaren Dr Sadeeq kuwa tuni yasoma haÉ—a mawa Zahrah kayan lefe, sosai yake iya Æ™oÆ™arin sa wajen ganin yasanya duk wani abu da yasan zai burge Zahrah.
Æangaren Hajiyarsa da Aunty Raliya kuwa, sam basu wani damu da auren ba, hakanne ma yasa suka tura masa aniyarsa, su dai sunfi bada Æ™arfi wajen ganin Salima tasamu abun da take so, yayinda Hajiya Furaira ta kafe kan cewa Æ´arta bazata auri Sadeeq ba matuÆ™ar ba'a fasa aurensa da Zahrah ba, ranta bai Æ™ara É“aci ba ma, sai da taji labarin cewa Zahrah Æ´ar talakawa ne, sannan kuma bata da wani galihu, ai take ranta yaÆ™ara É“aci, tace sam bata amince ba, yayinda Salima kuwa ta kafe akan cewa lallai sai ta ruguza auren da Dr.Sadeeq yake nema bayan nata.
Gaba ɗaya Zahrah ta ruɗe, zuwa yanzu wanda yake turo mata saƙo ya uzurawa rayuwarta, a yanda ta fahimta shine duk inda tayi yana biye da'ita, wani babban tashin hankali daya kunnu mata shine, sabbin saƙonnin da yafara turo mata a cikin wayarta, tagama iya hasashenta ko zata gano a ina yasamu number'n ta amma takasa samun daman sanin inda yasamu number'nta, gaba ɗaya yanzu salon saƙonnin nasa sun sauya salo, domin kuwa yanzu saƙon kalamai yaƙe turo mata masu daɗi, wanda kuma duk rabin saƙon yaba kyawunta yake,  babban abun daya ƙara ruɗata shine irin maƙudan kuɗaɗen dayake turomata ta waya. sannan kuma idan ta gwada ƙiran number'n da yake turo mata saƙo dashi, bata samu domin da zaran taƙira wayan za'ace mata a kashe wayar take, hakan yasa tafara tunanin cewa kodai gamo tayi...
Ɗan ƙara wayarta tayi alamar shigowar saƙo, take taji gabanta yafaɗi, zuwa yanzu har tsoro take taji wayarta tayi ƙara, domin kuwa tasan idan har wayanta tayi ƙara to ko ƙiran Dr.Sadeeq ko kuma saƙon mutumin da batasan shiba...
Number'n nan ce dai, da aka saba turo mata saƙo dashi, yauma saƙonne aka kuma turowa..
_Tunaninki ya hanani sukuni My Zahrah, ina fatan dai kina lafiya, ina kuma fatan zuwa yanzu kindaina tsoro da kuma mummunan tunanin da kikeyi akaina, kina da kyau My Zahrah, komai naki me kyau da burgewa ne._
Abun da saƙon ya ƙunsa kenan.
Zahrah ta karanta saƙon nan yafi sau biyar, kwata kwata ta kasa fahimtar abun da saƙon yake nufi.
Saurin yin Deleting saƙon tayi haɗe dayin switch off ɗin wayar tata, bazata taɓa yarda wan nan mai saƙon ya haukata mata tunanin ta ba, yazama dole a gareta ta sanja layi.. Kwanciya tayi lamo tana mai addu'an Allah yasa bacci ya ɗauketa. domin bacci ne kaɗai zai kawo mata sauƙi a zuciyarta.
Zaune suke dukansu a ɗan madai dai cin tsakar gidan nasu, domin dama idan dare yayi sukan zauna a tsakar gida su ɗan taɓa hira, haka al'adarsu take..
Wani yarone yashigo cikin gidan bakinsa É—auke da sallama, haÉ—a baki sukayi wajen amsa masa sallaman.
"Wai ana sallama da mai gidan nan" yaron yafaɗa.
"To kace inazuwa" Baffa yafaɗi haka yana ƙoƙarin miƙewa tsaye.
Kusan tare suka fita shida yaron sai da Baffa yaji wani irin faɗuwar gaba sakamakon wasu irin danƙara danƙaran motoci guda biyu da yagani fake a ƙofar gidansa.
Ja Baffa yayi ya tsaya turus yana me mamakin ganin waƴan nan rantsatstsun motocin a ƙofar gidansa, "Allah yasa da alkhairi suka zo" Baffa yafaɗi haka a cikin zuciyarsa.
Buɗe murfin motar Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da sako ƙafarsa waje.
Sake waro idanu Baffa yayi haɗe da kafe Alhaji Ma'aruf dake ƙoƙarin fitowa daga cikin mota da ido.
Fuska cike da annuri Alhaji Ma'aruf ya ƙaraso wajen Baffa, haɗe da miƙa masa hanu alamar su gaisa.
Cikin ɗari ɗari Baffa ya ɗago hanunsa haɗe da miƙamawa Alhaji Ma'aruf suka gaisa.
"Inafatan kaine ma mallakin wannan gida, kuma Baffa ga Zahrah?" Alhaji Ma'aruf ya tambaya.
Saida Baffa yaji zuciyarsa tayi tsalle sakamakon jin an ambaci Zahrah, Allah yasa ba wani abun Zahrah tajawo musu ba.
"Eh nine ranka ya daÉ—e, Allah yasa lafiya?" cikin dar É—ar Baffa yafaÉ—i hakan.
Murmushi irin nasu na manya Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da kallon Baffa..."Nazo da magana mai mahimmanci, inaga zaifi kyautuwa kabiyoni cikin mota mu tattauna, don maganar bata tsaye bace"
Kallon Alhaji Ma'aruf Baffa yashiga yi, haɗe da excort ɗin da suke bayan Alhaji'n, tabbas Alhaji Ma'aruf baiyi masa kama da irin mugayen mutanen nan ba, domin daga ka gansa zaka fahimci cewa dattijon arziki ne, hakanne yasa Baffa bai musa masa ba, yabisa zuwa mota..
Acikin mota kuwa bayan sun sake gaisawa, Alhaji Ma'aruf yayi gyaran murya haɗe da cewa...