Sashe 88
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba iya miji bane ni agareki, ni ɗan uwa ne wanda baki da kamarsa, najima da sanin cewa har yanzu Zaid yana cikin rayuwarki, nasan Inasonki so me tsanani, sai dai kuma duk irin soyayyar danakeyi miki Zaid yafini sonki, da ace zan iya to da najima da mallakawa Zaid ke amma bazan taɓa iyawa ba Zahrah nima masoyinki ne na haƙiƙa kamar yanda Zaid yakejin bazai iya rayuwa ba idan babuke, haka nima nakeji ajikina, batun yauba nasan Zaid yana nan kwance aƙasan zuciyarki, bana yaudaran kaina nakan faɗi abu ne aduk yanda natsaya na fahimceshi, koda kuwa abun dana faɗa bazasuyimin daɗin ji acikin kunnuwa naba, duk da kuwa nina faɗesu, bana ɓoye gaskiya saboda biyan buƙatar kaina"
KafaÉ—unta yakama da duka hannayensa. Ci gaba yayi da cewa
"Yanzu zanyi miki magana ne a matsayina na mijinki kuma wanda yake sonki, har yanzu duk da na aureki kina aƙarƙashin ikona bazan taɓa takuramiki ba, inamatuƙar son farincikin ki, idan har kinaji ajikinki cewa bazaki iya rayuwa ba idan babu Zaid shikenan zan iya....." rumtse idanunsa yayi da ƙarfi ya kasa ƙarasa maganar, da sauri ya miƙe yafice daga cikin ɗakin.
Zahrah wanda tun fara maganarsa tayi saroro tana kallonsa, tana ganin ficewarsa ta fashe da kuka.
"Me doctor yake shirin cewa? badai zai haƙura da ita ba?" tambayar da tayiwa kanta kenan, sam haka bazai taɓa yiwuwa ba, wace irin banzace ita? taya ya zata iya jure rashin masoyi kamar doctor Sadeeq? kuka tashiga rerawa me tsuma zuciya, kaiconta tunda dai harta bari Dr.Sadeeq ya iya sanin sirrin dake cikin zuciyarta, yanzu da wani idanu zata kalleshi bayan yasan cewa akwai son wani maƙare acikin zuciyarta? lallai koda ace Zaid ubantane yakamata tayi ƙoƙarin mantawa dashi....
Dr.Sadeeq kuwa yana fita daga ɗakin falo yanufa, yanazuwa ya buɗe fridge haɗe da ɗaukan goran ruwa yakafa a bakinsa, saida yasha ruwan fiye da rabin gora kafun ya kai goran ƙasa, ajiyar zuciya kawai yake sauƙewa akai akai.
"Meyake shirin aikatawa ne haka?" yatambayi kansa. Girgiza kansa yayi haɗe da ware idanunsa, idan yace zai iya rabuwa da Zahrah to yayi ƙarya, amma kuma idan yazamana bashine zaɓin ranta ba, to fa tabbas yazama dole ne yarabu da ita, badon kowaba saidon samun ingantaccen farincikinta, yasani shima abune me wahala ya iya jure rashinta, amma kuma itama yakamata aduba zuciyarta, yakamata tasamu abun da takeso.
key ɗin motarsa dake aje kan ɗan ƙaramin stull dake falon ya ɗauka haɗe da sakai yafice gaba ɗaya daga cikin falon, motarsa yashiga ya fice daga cikin gidan, bayajin zai iya zama acikin gidan gaba ɗaya zuciyarsa a dagule take..
Zahrah kuwa tanajin alamar fitansa daga cikin gidan tasake fashewa da kuka, duk da kuwa zafin zazzaɓin dake damunta. Kuka tayi sosai amaimakon zazzaɓin nata ya ragu sai gashi ya ƙara hawa, to taƙi tabar zuciya da ƙwaƙwalwanta su huta...
****
Da ƙyar ya iya kai kansa gida, tsabar yana acikin wani irin yanayi har idanunsa soma rufewa sukayi, yazamana duhu duhu kawai yake gani, hanunsa dafe da saitin zuciyarsa yafito daga cikin motar, taku biyu yayi duhu ya mamaye duka idanunsa take wani irin juwa ta ɗebesa saigashi yashe a ƙasa bayako da numfashi, da gudu ma aikatan gidan sukayo kansa suna ƙiran sunansa
"Oga! Oga!!"
Oga baimasan sunayi ba, wani daga cikin masu bawa flowers ruwa ne ya ranta aguje yaje yasanarwa Mummy dama Dad na nan atare suka fito amatuƙar ruɗe.
Ganin da suka mawa Zaid yashe a ƙasa yafi komai ɗaga musu hankali, da taimakon ma'aikatan wajen Dad yasanyasa amota direct suka wuce asibiti Mom sai kuka take.
Emergency aka karɓesa, Lallashin duniya Dad yayimawa Mom akan tayi shiru ta daina kuka amma taƙi, duk da cewa tana fushi dashi amma bata ƙaunar taga ko taji wani abu yasameshi, yanzu idan akace ya mutu yazatayi da rayuwarta?
Sama da 1 hour likitoti suka kwashe akansa suna bashi taimakon gaggawa. ÆŠaya daga cikin likitotin ne ya kalli Dr.Bilal haÉ—e da É—aga masa kai alamar wai Zaid É—in babu rai ajikinsa. girgiza kai Dr.Bilal yayi alamar bai yarda cewa babu rai ajikin Zaid É—in ba..
Hmmm likitotin nan sunsha matuƙar wahala kafun suka samu numfashin Zaid ya dawo dai-dai. Dukansu haka suka fito suna gumi domin kuwa da fari harsun cire rai dashi, sun ɗauka dagaske ya mutu.
Da gudu gudu sauri sauri Dad yataho wajen Doctor Bilal, hanun Dad Dr.Bilal yakama suka wuce office É—insa.....
"Yajikin nasa doctor? dan Allah kafaɗamin wani hali yake ciki a yanzun?" Dad yatambayi Dr.Bilal cikin yanayi na matuƙar ruɗewa.
"Ka kwantar da hankalinka Alhaji, yau Zaid ya hau matakin ƙarshe wanda da taimakon Allah muka samu da ƙyar muka shawo kan matsalan, amma bazan taɓa ɓoye maka ba idan har yasake shiga cikin yanayi irin wannan to fa tabbas wata ƙila saidai haƙuri, ba'aja da ikon Allah amma kuma fa da matuƙar wahala idan zai sakeyin numfashi, dama wannan shine matakin ƙarshe kuma gashi yakawosa idan irin haka tasake faruwa kuma to saidai dukanmu muyi haƙuri, haka Allah dama yake abunsa, duk wani me rai mamaci ne, koda ciwo ko babu ciwo, watarana dole mutum saiya mutu idan lokacinsa yazo, haka kuma gaba ɗaya zamu zama tarihi, saidai aba da labarin mu kamar yanda aka bamu na waƴanda suka shuɗe kafun zuwanmu iyaye da kakanninmu kenan!" Dr.Bilal yafaɗi haka yana me tattara nutsuwarsa ga Dad.
Gumi kawai Alhaji Ma'aruf ke sharewa sai ambatan
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" yakeyi gaba É—aya ji yayi duniyar tayi masa nauyi.
"Doctor menene mafita?" Dad yatambayi Dr.Bilal cikin sanyayewar guiwa.
"A yanzu kam dai bamu da mafita Alhaji Ma'aruf, sai dai mujira muga me Allah zaiyi, wataƙila Zaid zai iyakaiwa kwana uku batare daya farka ba, wataƙila kuma ko nanda kwana biyu ya farka, amma yazama dole ku kula dashi, yanzu bakamar da bane, yanzu abu kaɗan na ɓata masa rai zuciyarsa zata hau zafi, sannan kuma idan ya yawaita yin tunani to fa akwai babbar matsala, yazama dole ku tsaya akansa ku lura, akwai magungunan dazan rubuta muku, idan yatsaya akansu insha Allah zasu taimaka masa sosai."
Sai alokacin Alhaji Ma'aruf ya É—anji sanyi acikin ransa.
"Nagode ƙwarai Dr.Bilal kuma Insha ALLAH zamu kiyaye sosai!" Dad yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye. Musabaha sukayi da Dr.Bilal kafun ya fice acikin office ɗin.
*****
A daddafe ta tashi tayi sallan isha. Tana kan sallayan bata tashiba yashigo cikin ɗakin, idanunta ta zuba masa, bada kayan da yafita ya dawo ba, yanzu rigane da wando na jeans ajikinsa, kallonsa takeyi kamar wani wanda bata taɓa ganinsa ba, shima kallonta yayi haɗe da yi mata murmushi, ya wuce cikin bathroom, mintuna kaɗan yafito daga cikin bathroom ɗin.
"Kizo kici abinci" yana faÉ—a mata haka yafice daga cikin É—akin.
Wani irin kunyan sa ne yaka mata, amma kuma babu yanda zatayi, abundake cikin zuciyarta ta faÉ—a.
Miƙewa tayi sumi sumi ko hijab ɗin dake jikinta bata cire ba ta fita zuwa falo.
Zama tayi akan sofa kusa da inda yake zaune, haÉ—e da takure jikinta waje É—aya, shawarma ne da gasashshen kifi (roasted fish) ya sayo musu, tura mata plate É—in yayi gabanta.
"Kici sai kisha magani" yafaÉ—i haka fuskarsa É—auke da É—an murmushi, kallonsa tayi kamar zatace dashi wani abu kuma saita fasa tasoma cin abincin da kaÉ—an kaÉ—an. Shikuwa sannu a hankali yake sipping country yoghurt É—insa yana me kuma latsa wayarsa.
Haka suka zauna shiru babu me cewa da ɗan uwansa ƙala.
Tana kammala cin abincin ya bata wasu magunguna daya shigo dasu, babu musu ta amsa tasha. Ganin yatashi yabar falonne yasanya itama ta tashi ta koma ɗaki, wanka tayi kana ta fito ta sanya wata sleeping gown wacce ta tsaya iyaka cinyarta, ko guiwa bata ƙarasa ba, sosai rigar tayi mata kyau ta kuma fito da farar fatarta fili, dogon gashinta ta kama ta tubke a tsakiyar kanta haɗe da ɗaureshi da ribbon, turarenta me daɗin ƙamshi ta shafa, tana nan tsaye a cikin ɗakin yaturo ƙofar ɗakin yashigo.
Wani irin yawu ya haɗiye a maƙoshinsa, sanda idanunsa sukayi masa tozali da ita, sosai tayi kyau acikin rigar, ga fararen cinyoyinta sun bayyana kansu a fili, da ƙyar ya iya daure zuciyarsa, murmushi kawai yayi mata haɗe da kawar da kansa gefe, shi kaɗai yasan me yakeji acikin zuciyarsa, yana tsananin kishin matarsa, kamar yanda yake tsananin sonta.
Kan gado ta koma ta kwanta, agogon hanunsa yacire haÉ—e da cire rigarsa, 3 guater jeans yasanya..
Zama yayi a gefen gadon haÉ—e da jawo laptop É—insa yasamo dannawa, dama yanada ayyukan da suka masa yawa yanaso ya É—an ragesu, bayaso ya kwanta shiru tunani ya damesa.
Hanu tasa ta share hawayen dake fitowa daga cikin idanunta.
"fushi Dr.Sadeeq yakeyi da ita kenan?" tambayar da take ta yiwa kanta tun É—azu kenan, bazata iya jure fushinsa akanta ba, duk da baifito ya nuna mata hakan afili ba, amma duk wasu alamu sun nuna hakan, bayason yi mata magana me tsawo sannan kuma baya sake mata kamar yanda ya saba, idan tabarsa haka batayi masa adalci ba, ayanzu bata da wani wanda ya wuce mata shi, shi É—inne dai komai nata, bazata iya É—aukar fushinsa akanta ba.
Aikinsa yake cikin nutsuwa amma kuma gaba É—aya tunaninsa akanta yake, ba abun dayafi damunsa kamar cutar hawanjini dake da munta, yasani sarai cutar hawan jini bata da kyau tana cutarwa sosai, musamman ma ga yarinya kamarta hakan yasa yake tsananin tausayinta.
Baizataba saiji yayi ta rungumeshi ta baya, haɗe da ɗaura kanta akan wuyanshi, me makon tace wani abu sai kawai ta fashe masa da kukan shagawaɓa.
Lumshe idanunsa yayi har a cikin zuciyarsa bayason kukanta idan tana kuka hankalinsa tashi yake.
Jawota yayi ta dawo gabansa.
"Menene?" yatambayeta yana me É—ora idanunsa akanta.
"Bazan iya jure fushinka ba, dan Allah kayi haƙuri wallahi inasonka banason kajuyamin baya, banda kowa sama da kai, idan kajuyamin baya bansan yanda rayuwata zata kasance ba, kayi hakuri kaji!!" kuka take sosai alokacin da take faɗar maganar.
Wani irin sanyine yaji yana ratsa zuciyarsa kalmar "Wallahi tana son shi" da ta faÉ—a yafi komai da É—aÉ—a masa rai, yaji daÉ—in maganar sosai, amma sai ya dake bainuna mata hakan afili ba.
"Ni nace miki ina fushi dake ne?" abunda yatambaya kenan.
Da sauri tashiga kaÉ—a kanta alamar "Eh"