← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 112

Sashe 49

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sunana Alhaji Ma'aruf,  kasancewar dare ne yasanya ka kasa shaida fuskata, domin ni ba ɓoyayyen mutum bane. Nazo gare ka ne domin nemawa ɗana Auren Ƴar Wajenka Zahrah, ina fatan bazaka watsa mini ƙasa a ido ba".......

(Kowani amsa Baffa Zai bawa Alhaji Ma'aruf🤔)

*19/December/2019*

*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
*Wattpad user name fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    
       *Written By*
*Phatymasardauna*
_(shalelen kainuwa)_

*Dedicated To MY Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

           *WATTPAD*
     @fatymasardauna

*(Wannan page ɗin gaba ɗayansa ƙyautane a gareku Maman Teemah, and Ummu Fateema, inaƙaunarku  Momy's ɗina)*

*Editing is not allowed📵*

  *CHAPTER 63 to 64*

Shirune yashiga tsakanin Baffa dakuma Alhaji Ma'aruf,  bakomai ne kuma yasa hakan ba face nazari da Baffa yashigayi, lallai wannan abu da mamaki yake, neman aure mace ɗaya duk alokaci guda.

"Naji kayi shiru, Allah yasa dai ba wata matsala bace ta faru" Alhaji Ma'aruf  ya faɗa, domin ko kaɗan baya fatan wani abun da zai zo ya gifta har ya katsewa  Zaid cikar burinsa..

Gyara zama Baffa yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya..

"A gaskiya Alhaji bazan ɓoyemaka ba, yanzu haka na bada auren Zahrah ga wani,  wanda kuma tariga da ta aminta dashi, sai dai bazan yi saurin yanke hukunci ba, idan har Zahrah ta aminta dashi ɗan wajen naka, shikenan, saboda ni bazan mata dole ba, duk wanda takawo tace shitake so, to  shi zan aura mata, amma kuma a iya sanina babu wani wanda yake zuwa wajenta, bayan likita'n dana bashi aurenta, sai dai kuma bansan shi ɗan wajen naka a ina yaganta har yaji yanada burin aurenta ba"

Ɗan jim Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya. Lallai yakamata yayi duk abun da zaiyi, domin shikansa yanaso Zaid  yayi aure, amma kuma yasan cewa nema cikin nema haramunne, tunda gashi har shi Baffan yarinyar ya ri ga daya shaida masa cewa yabada auren yarinyar ga wani, yazama dole suyi haƙuri kenan.

"Naji maganarka Malam Hayatu, nakuma gamsu, amma bayar da aurenta ga wani, ae  bashi yake nufin anɗaura aurenta ba, koda yaushe ra'ayin mutane yana iya sanjawa,  saboda haka zanbaka dama kayi tunani mai kyau" Alhaji Ma'aruf yafaɗi haka bayan yaciro wasu maƙudan kuɗi a cikin aljihun rigarsa ya ɗauramawa Baffa akan cinyarsa..

Ware idanu Baffa yayi sakamakon ganin  maƙudan kuɗin da Alhaji Ma'aruf yaɗaura masa akan cinyarsa, badai yana nufin duk nasa bane.

Murmushi irin na manya Alhaji Ma'aruf yayi haÉ—e da cewa "Kada kadamu bawai nabaka kuÉ—innan bane,don ka bawa É—ana auren Æ´arka ba, nabaka ne kawai saboda shi meyin alkhairi ako da yaushe baya rasawa"

Cikin sanyin jiki Baffa yayi masa godiya haÉ—e da buÉ—e murfin motar yafita, zuciyarsa cike da É—unbin mamaki...

Baffa na fita daga motar Alhaji Ma'aruf yamawa driver'nsa umarni akan cewa su tafi, aikuwa ba ɓata lokaci drivern yatada mota..

Saida suka ɓacewa ganinsa kafun Baffa ya iya ɗauke idanunsa daga kansu,  kuɗin dake hanunsa yashiga juyawa,  "Lallai wannan mutumi yanada ihsani, amma kuma yazo da babbar magana, da ace yanada dama to da a yanzu yabawa ɗan Alhaji Ma'aruf ɗin auren Zahrah, to saidai kuma yanzu ya saduda, sakamakon wa'azi mai tsoratarwa dayaji akan cutar da maraya, da kuma irin azabar da za'amawa mai cutar da maraya,  tundaga wannan lokacin yaƙudurta aransa cewa bazai sake cutar da Zahrah ba, yanzu ma dolensa zai bata zaɓi, domin ita zatayi zaman auren ba shiba...

Yanashiga gida Inna da takasa zaune takasa tsaye, ta ƙaraso wajensa da sauri tana me cewa "Lafiya naga ka jima, har nafara jin tsoro naɗauka irin mutanen nan ne masu garkuwa da mutane suka kamaka, domin na leƙa naga wasu fankama fankaman motoci a waje"

Harara Baffa ya wurgamata, haɗe da jan tsuka "Bazaki taɓa sanja halinki ba ko Salame, wato ke dai koda yaushe kai da kuma idanunki sunaga ƙofar gida, kullum cikin leƙe kike, wato dai har dare ma yanzu leƙe kikeyi, Allah ya kyauta" yafaɗi haka yana mai nufar hanyar ɗakinsa...

Fuska Inna ta ɓata haɗe da kafe aljihunsa da idanu, domin kuwa tuni idanunta sun ƙyallaro mata tudun da aljihunnasa yayi, ƙwafa tayi haɗe da rufa masa baya, koma mene sai
taje taganema idanunta, idan ma abuncine aci da'ita..

Sake gwalo idanu Inna tayi, ganin kuɗin da Baffa ya'aje akan gadonsa,   "Malam kace farar fita kayi, a shema baƙin arziki ne, nayi musu mummunar fahimta, ae irinsu muke fatan suta zuwa" washe da baki ta ƙare maganar...

"Akwai matsala Salame, amma jeki ƙiramin Zahrah" Baffa yafaɗa bayan yayimawa kansa mazauni, a bakin gadonsa.

"Yanzu kuwa" Inna tafaÉ—a tana me fita daga É—akin..

Zahrah ce zaune akan gadonta, game take bugawa a cikin wayarta, da'alama dai game É—in yayi mata daÉ—i, domin kuwa ita kaÉ—ai sai murmushi take.

Inna ce tashigo cikin ɗakin haɗe sa shaida mata ƙiran da Baffa keyi mata,  haka nan taji gabanta yafaɗi. Tare suka fito da Inna, dukansu suka ɗunguma zuwa ɗakin Baffa'n...

Gyara zama Baffa yayi haɗe da maida kallonsa ga Zahrah, wacce ta duƙar da kanta ƙasa.

"Bayan Likita akwai wani wanda kikasan yanasonki, ko kuma kika basa dama ya turo magabatansa wajena?"  Baffa yatambayeta cike da kulawa.

"A'A Baffa bana mu'amala da kowa sai likita, bankuma bawa kowa izinin zuwa wajenka ba" tafaÉ—i haka cike da girmamawa, duk da kuwa cewa kanta ya É—aure da jin tambayar da Baffa'n yayi mata...

Kai Baffa yajinjina haɗe da cewa "Ƙiran da akai min ɗazu wani ne yazo nemawa ɗansa aurenki, shine nayi tunanin ko kinsan da zuwansa"

Wani irin bugawa Zahrah taji ƙirjinta yayi, har batasan sanda ta ɗago da idanunta ta kalli Baffa ba.

Baffane yacigaba da cewa "Bansan ko su ɗin suwaye bane, amma ban ɓoyemusu komai ba, nasanar dasu cewa nabada aurenki ga wani, amma mahaifin yaron yace yabani lokaci nayi tunani,  saboda hakane ma naƙiraki domin ni bazan miki dole ba,  zanbaki dama ne ki zaɓi wanda kikeso"

Take idanun Zahrah suka kawo ƙwalla, sakamakon jin wani baƙon al'amari dayake shirin kunno kansa cikin rayuwarta.

"Kinyi shiru, ki kwantar da hankalinki bazan miki dole ba Zahrah, kema kina da ƴan ci, zan kuma baki ƴancin ki, sai dai abun da nakeson sani  shine wanene yaron nasa, saboda bai yiwuwa a haɗaki aure  da wanda  bamusani ba, amma idan ke kinsan sa shikenan ba damuwa"

"Bansan saba Baffa, kuma ma koda nasansa bazan aminta dashi ba, saboda idan nayi haka ban yi mawa Dr.Sadeeq adalci ba" Zahrah tafaÉ—i haka cikin sanyayewar murya...

"Adalci, kaji shirmen banza don Allah Malam, wani adalcine yarage miki, wanda yawuce ki kai kanki cikin arziki kicisa yanda yakamata,  saidai ko inkuma baƙin ciki kike mana"
Inna ta tsomo bakinta cikin maganar batare da angayyaceta ba...

"Tashi kije Zahrah, idan suka sake zuwa zan sanar dasu cewa hakan da sukeso bazai yi wuba" Baffa yafaÉ—a, yana mai wurgamawa Inna harara..

Cikin rashin ƙwarin jiki haɗe da ɗaurewar kai Zahrah tabar ɗakin..  Haushin Zahrah da Baffa ne yacika zuciyar Inna, amma ganin yanda Baffa yahaɗe fuska bai bata damar yin ƙorafi ba yasanya itama tafice daga ɗakin tana me ƙananan maganganunta wanda ita kaɗai tasan metake cewa..

Zama Zahrah tayi jigum haɗe da zurfafa tunanin ta,  ba'abun dake bata mamaki da ɗaure mata kai, kamar neman aurenta da Baffa yace anzo anyi,  "To waye zai zo neman aurenta batare da saninta ba? batare da ta kuma sanshiba, lallai koma waye baisan meyafaru da'ita ba, domin tasan daya sani, da baiyi gigin turo magabatansa nema masa aurenta ba" Haka dai tayita saƙawa da kuncewa har bacci ya ɗauketa......

Cike da tsananin mamaki Zaid yake kallon mahaifinsa, sakamakon ji da yayi mahaifin nasa nacewa "Wai anbada auren Zahrah'nsa ga wani"  " Anya kuwa gidan su Zahrah Dad ɗinsa yaje? kodai yayi mistake ne yaje wani gidan amadadin nasu Zahrah?" duk wannan tambayar kansa ya mawa.

"Inaga zaifi kyautuwa kanemi wata My Son, domin kafasan nema cikin nema haramunne"  Alhaji Ma'aruf ya faɗa yana me kallon ɗan nasa.

"Inaga ba gidansu kaje ba Dad,
domin ni nasan Zahrah tawace, baza'a bawa wani ita ba bayanni" Zaid yafaɗi haka bayan yayi sipping holandia milk ɗin dake aje cikin  glass cup ɗin dake gabansa.

Kallon mamaki Alhaji Ma'aruf, yashiga yi mawa Zaid, sakamakon jin abun daya faÉ—a.
Baisan me yake shirin faruwa da ɗansa ba, amma tabbas ya hango wata irin soyayya acikin idanun Zaid ɗin me matuƙar zafi, wanda Zaid shikansa baisan da'ita ba...

"Akwai matan aure dayawa Zaid, zaifi kyau ka zaɓi wata, koda a cikin ƴan uwankane" Alhaji Ma'aruf yafaɗi haka cikin lallashi. 

Murmushi kawai Zaid yayi haÉ—e da kallon mahaifin nasa...

"Kai mahaifinane saboda haka bana iya ɓoye maka komai,  a gaskiya banjin zan iya zama da wata daban, idan ba Zahrah ba, zanyi komai da kaina kawai" yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye...  Da kallo kawai Alhaji Ma'aruf yabi sa dashi har ya fice daga cikin  falon nasa. Ajiyar zuciya yayi haɗe da cewa "wataƙila idan kuɗi na magani, to zasu maya Zaid, ta hanyar samo masa auren Zahrah"
(hmm bakomai ake nema a samu ba, bakuma komai kuÉ—i yake iya saya ba)

Kai kawo Zaid yashigayi a tsakiyar tankamemen aljannar duniyar falonsa, gaba ɗaƴa yarasa me yake masa daɗi, shin maganar da Dad ɗinsa ya faɗa masa cewa anbada Zahrah, gaskiya ne kokuwa Dad ɗinnasa ne yayi mistake wajen gano gidan su Zahrah,  dudduniya babu wani mahaluƙi daya isa yimasa shamaki da muradinsa,   lallai lokaci yayi daya kamata ya bayyana kansa gareta,  baidamu da yanda zata ɗaukesa ba, shidai burinsa kawai shine ya mallaketa amatsayin matarsa,    lallai yanzune zai gudanar da babban takunsa, sannan kuma yazama dole yagano bayanshi wayake bibiyan Zahrah, har ake yunƙurin aura masa ita, dole yagano wannan, domin yayi imani cewa Zahrah tasa ce...

***

Fitowarsu daga lecture kenan, wayarta tayi ƙara alamar shigowar saƙo,, ko kaɗan batayi mamaki ba, domin zuwa yanzu tasaba da saƙonnin da'ake turo mata batakuma san waye yake mata hakan ba. 
Chapter 49 · 0% Book details