← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 112

Sashe 28

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe sakamakon gano abun dake damun Zahrah da yayi, duk da cewa baiyi mata gwajin ciki ba, amma a iya ɗan bincikensa da yayi ya gano cewa bata ɗauke da ciki, ulcer ce kawai tayi mata mummunan kamu, sakamakon yunwa daya samu mazauni acikin cikinta.

Kallonsa yamaida kan Baffa haÉ—e da cewa " Bawani babban damuwa bane ulcer ce, yanzu zanje na É—auko wasu allurai a asibiti sainazo nayi mata, insha Allah komai zaiyi dai dai"

"To likita Allah yayi albarka muna godiya sosai !" Baffa yayi maganar cike da yabawa ƙoƙarin Dr Sadeeq.

Miƙewa Dr Sadeeq yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin, yana fita su Inna ma suka mara masa baya.

Kwanciya tayi lamo tamkar wacce ruwa ya ƙare mawa a jiki, gaba ɗaya jinta takeyi bata da kuzari, gawani irin zafi da ƙuna da ƙirjinta keyi mata,,

Koda Dr Sadeeq ya ɗauko magunguna da Alluran da yakamata ace yayi mata, sai da ya biya ta wani katafaren wajen sai da kayan marmari yasaya mata dangin su apple da su inabi hadda abarba, bai tsaya anan ba hadda fresh milk saida yabiya ya saya,  gudu yashiga sharawa akan titi, burinsa ɗaya shine yaje yabata taimako mai kyau, sosai yakejin tausayinta,   saboda ta cancanci a tausaya mata,  daga wani ɓangare na zuciyarsa kuwa idan yatuno da cewa ba ciki bane da'ita, sai yaji wani irin sanyi da nishaɗi na ratsa zuciyarsa, wanda ya alaƙanta hakan da cewa bayason tasamu ciki saboda zata sake shiga wani hali marar daɗi. (kuji shifa😏 wai hakane reaɗers?)

Mintuna ƙalilan ya iso ƙofar gidannasu.
Koda yanemi Inna da tayi masa iso zuwa É—akin Zahrah'n, cewa tayi yashiga kai tsaye ai anzama É—aya su yanzu É—an uwa suka É—aukeshi (hmm)

Yanda ya barta haka yataradda ita sai dai yanzu idanunta a lumshe suke,  "Zahrah!!" yaƙira sunanta dai dai lokacin da yake ƙarasawa kusa da'ita.

A hankali ta buɗe idanunta tasauƙesu a kansa,  ɗan guntun murmushi yayi mata, wanda yasanya gabanta mugun faɗuwa, domin kuwa murmushin nasa yatuna mata da murmushin Oga Babba (ZAIDU manyan maza, lol), take taji wani irin abu ya toshe mata maƙoshi, yayinda zuciyarta tayi ƙunci.

Aje ƙatuwar ledan dake hanunsa yayi, haɗe da zama akan katifarta ta, "Tashi ki zauna" yafaɗa yana mai kafeta da ido,  kai kawai ta girgiza masa alamar bazata iya tashi ba,  ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya ɗagota zaune,  duk da cewa yana matuƙar jin shock idan yataɓa jikinta, amma babu yanda zaiyi dole hakan shine mafita.

Ledar daya shigo da'ita ya buɗe, haɗe da ɗauko apple guda ɗaya ya miƙa mata,  kallonsa kawai tayi haɗe da kau da kanta gefe, 

"Magani bazaiyi aiki a jikinki yadda ya kamata ba, harsai kinci abinci, idan kuwa kikasha magani bakici abinci ba zai wahalar dake sosai, dan Allah banason gardama Zahrah, nasan kuma kema kina buƙatar abinci, don haka ki karɓi apple ɗinnan kici,  ciwon ulcer bazai taɓa sake kiba matuƙar kina zama da yunwa!!" yaƙare maganar cikin lallashi.

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da ɓata fuska, sam batason cin wani abu daga garesa, amma yana ƙoƙarin tursasata dole, kuma yayi gaskia dayace tana buƙatar abinci, tabbas ita kanta tasan tana buƙatar abinci.

"Yauwa Zahrah nasan dama keɗin maijin magana ce, karɓa kici ko!" yaƙare maganar yana mai marairaice fuska, haɗe da kusanto da apple ɗin dai dai saitin bakinta.

Hanu tasa ta karɓi apple ɗin, a hankali take gutsuran apple ɗin kamar mai gutsuran magani, duk  da kuwa cewa taji test ɗinshi a cikin bakinta,,   tana cinye apple ɗin ya miƙo mata goran fresh milk mai sanyi.

"Ungo wannan ma ko kaÉ—anne kisha, nasan zai taimaka kuma idan kika sha bazanmiki allura ba!"

Saurin kallonsa tayi, don tabbatar da abun da ya faɗa, aikuwa idan dai har bazai yi mata allura ba idan tasha, to lallai zatayi ƙoƙari tasha ɗin,

"Ka tabbata bazakamin alluraba idan nasha?" tafaÉ—i maganar a sangarce, cikin kuma yanayi na marar lafiya,

"Bazan miki allura ba Zahrah, idan dai harkika sha, kuma koda zan miki ma kaɗan zanmiki kuma bamai zafi ba!" yaƙare maganar yana murmushi.

Take tasake turɓune fuska haɗe da turo baki.

"Nifa wasa nake miki bawata allura dazan miki !" Dr Sadeeq yafaɗa yana dariya ƙasa ƙasa.

Karɓan goran fresh milk ɗin dake hanunsa tayi, haɗe da kafa kanta tasoma sha, tun asalinta ita mai son madara ce, haka kuma fresh milk yana ɗaya daga cikin abubuwan da takeso, sabo da haka sosai tasha har saida taji cikinta yacika, take kuma  ɗan kuzari yasoma dawo mata, miƙo masa goran tayi alamar taƙoshi,

"Kishanye duka" yafaɗa a taƙaice,

"A'a naƙoshi" itama tabasa amsa ataƙaice,

"Okay to mai kikeson ci yanzu kuma?"  yatambaya yana mai tsareta da idanu.

"Babu" ta basa amsa a taƙaice,

Kansa kawai yajinjina haɗe da ɗauko drugs ɗin daya taho mata dasu yasoma ɓarewa yana bata, sai ta rufe ido haɗe da ƙanƙame jiki sannan take iya sha, shiko dariyama take basa, bai taɓa ganin mai tsoron allura da magani kamarta ba.

Yana gama bata maganin yace ta kwanta, batayi ƙoƙarin musa masa ba, ta kwanta domin kuwa kafun yace mata kwantan, idanunta harsun fara rufewa,, "Zahrah!" yaƙira sunanta, shiru babu amsa kuma bata ko motsaba sai idanunta da suke buɗewa suna rufewa a hankali, da'alama dai yabata wani magani ne mai matuƙar kashe kuzarin jiki.

Dariya yayi ƙasa ƙasa haɗe da cewa "Yarinta da daɗi" 

zuƙa zuƙan alluran daya taho dasu guda biyu, yaciro acikin ledan haɗe da haɗa komai da komai wanda ya kamata, 

Riƙe alluran yayi a hanunsa haɗe da mai da kallonsa ga Zahrah wacce take kwance lamo, a hankali yasanya hanunsa ajikinta haɗe da juyata,  saida ya rumtse idanunsa shima kafun ya'iya yi soka  mata alluran,  yana gamawa ya juyata ɗaya gefen ma yayi mata, sosai taji zafin alluran amma bata da bakin magana, sai dai hawaye da suka soma gangara daga cikin idanunta.

"kiyi haƙuri Zahrah ƴan mata, dolece tasa namiki alluran, inaso naga kinsamu lafiya ne!" Dr Sadeeq  yafaɗi maganar cikin tausasa murya, bayan yashare mata ƙwallan dake sauƙa a gefen fuskarta,  miƙewa yayi tsaye haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin, bayan yatattara kayan aikinsa.

Bai taradda Inna a tsakar gida ba sai Baffa, don haka a gurguje yayi masa sallama, yatafi sbd dare yasoma rabawa.

Ɓangaren Zahrah kuwa tun kafun Dr Sadeeq yafita bacci yayi awon gaba da'ita, domin daga magungunan har alluran da yayi mata suna saka bacci.

A hankali yake tuƙin motar tasa, fuskarsa cike take da annuri, Situation ɗin Zahrah kawai yake tunawa, sosai komai nata yake burgesa, musamman ma tsoronta,  hakanan yakejin kansa cikin nishaɗi idan yana tare da'ita, baikumasan dalilin faruwar hakanba.

Koda ya yi parking motarsa kai tsaye ɓangaren mahaifiyarsa ya nufa, domin yau ko gaisawa basuyi ba ya fice daga gidan,

Koda yashiga falonnata bai isketa ba, don haka kaitsaye yanufi bedroom ɗinta domin yanada yaƙinin cewa zai taradda ita acan.

Knocking ƙofar bedroom ɗinnata yashigayi a hankali,   jin knocking ɗin ya tsananta ne yasa taba wa mai knocking ɗin umarnin shigowa, domin dama tana da yaƙinin cewa shiɗinne kasancewar taji ƙaran shigowar motarsa cikin gidan.

Zaune ya'isketa akan sallaya, da'alamu idar da sallan nafilanta kenan.

Harƙasa ya durƙusa ya gaidata cike da girmamawa,  cikin sakin fuska itama ta amsa masa gaisuwarsa haɗe da cewa " Ina kashigane yau tunsafe ?"

Ƙeyarsa yashiga sosawa a hankali, yayinda fuskarsa ke ɗauke da ɗan murmushi.

" Am Hajiya aikin office ne ya ɓoyeni, dana tashi kuma sai na biya ta gidansu Zahrah domin duba jikinta, to danaje sai nasamu batajin daɗi !" ya faɗi maganar fuskarsa ɗauke da  alamar damuwa.

"Gidansu Zahrah kuma Sadeeq ?, to Allah ya sauwaƙa, a kwai a binci, a derny saika ɗebi iya yanda zaka iyaci, domin daganinka bakasa komai a cikin ka ba" Hajiya tafaɗi maganar cike da kulawa,

"To Hajiya zanci insha Allah" yaƙare maganar yana me miƙewa tsaye,  sallama yayiwa mahaifiyartasa kafun yasakai yafice daga cikin ɗakin.

Yana fita Hajiya tasaki ƙwafa haɗe da cewa
"Nasan maganinka aure zanyimaka ko da baka shiryaba, natabbatar hakan zai sa ka rage yawan kaiwa dare a waje, kullum kai baka da hutu aiki tamkar engine, duk kuma rashin iyali shiya jawo hakan ".

Yana isa ɗakinsa yasoma rage kayan jikinsa, ɗan ƙaramin towel ya ɗaura haɗe da faɗawa bathroom yasakar mawa kansa shower,   cikin zuciyarsa kuwa cunkushe take da tarin tunanuka kala kala, haƙiƙa yasan cewa yana buƙatar mace akusa dashi, domin dai shiba dutsi bane da zai zauna haka ƙiƙam ko da yaushe, dole yana buƙatar wacce zata na taimakawa wajen enjoying life ɗinsa,  tun ba yauba yagane cewa yana ɗaya daga cikin maza masu yawan buƙata,  amma kuma sosai yake ƙoƙari wajen shan pills wanda zasu sama masa relief,   a gurguje yayi wankan yafito, wata brown ɗin jallabiya mai kyau yasanya bayan yatsane ruwan dake jikinsa,    kulan abincin daya ɗauko a falon Hajiyarsa yajawo haɗe da buɗewa, jallof ɗin shinkafa ne sai coslow, kaɗan ya tsakura a cikin plate  yasoma ci,  gaba ɗaya tunanin Zahrah yacika masa zuciya wani irin feeling yakeji a kanta,  idan yatunota sai yaji nishaɗi ya sauƙa acikin zuciyarsa,  yanason komai nata, idan tana kuka tanayimasa kyau sosai, haka ma idan ta kwaɓe fuska bakaɗan ba take kyau, gaskia tana da abubuwan burgewa da yawa,   da tunaninta yasamu ya kammala cin abincin duk da cewa baiwani ci mai yawa ba, saida yafita ya ɗanƴi exercise kafun ya dawo ya kwanta, domin a matsayinsa na likita yasan illan dake cikin kwanciya daga cin abinci..

Washe gari

Alhamdulillahi tatashi da ƙarfi a jikinta, sai dai ɗan abun da baza a rasa ba, tun tashinta da haushinsa ta tashi,  domin jiya tanaji tana gani haka ya yaudareta yayi mata allura, bayan yagama kashe mata jiki da ƙwayoyin da ya bata,   don haka bakinnan a ɗane yake ita adole tana fushi da likita.
Chapter 28 · 0% Book details