← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 112

Sashe 80

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yajima tsaye akanta yana me ƙare mata kallo, mamakin yanda take kuka tsakaninta da Allah yake, a iya saninsa banda abun daya wakana atsakaninsu daren jiya baiyi mata komai ba, amma kuma sai gashi yanzu tana ruskar kuka, har a ƙasan zuciyarsa bayason kukanta, idan yaji kukanta jiyake gaba ɗaya nutsuwarsa ya ƙaura daga jikinsa,, ahankali yashiga takawa harzuwa inda take duƙe akusa da gado tana kuka, sam batamasan da shigowarsa ba kukanta kawai takeyi.... Hanunsa yasanya ya dafa kafaɗanta, da sauri ta juyo aɗan razane don bataji shigowarsa ba,,   idanunsa ya ƙanƙance haɗe da waresu alokaci guda,  zama yayi akan gado haɗe da  ɗagota zuwa jikinsa...

"Me yasa Zahrah? me nayi miki? meyasa kike ƙuntatawa rayuwarki akan wani dalili naki? ban aureki don nazuba miki ido kita cutar da kanki ba, please ki daure zuciyarki kidaina wannan kukan banaso!"  ya faɗi maganar cikin lallashi...  Saurin ɗauke hanunsa dake kan wuyanta yayi, kansa yaɗan ɗafe haɗe da zaunar da ita akan gado, direct wani ɗan madaidaicin drawer yanufa,  maganin da yasan zai sauƙar mata da zazzaɓi acikin mintuna ƙalilan ya ɗauko tare da ruwan gora ya dawo zuwa gareta. Maganin ya ɓalla ahanunsa tare da jawota jikinsa,  bakinta ya buɗe ya jefa maganin aciki haɗe da bata ruwa, babu musu ta haɗiye maganin bayan ta rumtse idanunta, sai kace wacce aka bawa guba... Aje goran ruwan yayi haɗe da sake jawota jikinsa, kwantar da kanta yayi akan ƙirjinsa, yayinda yake shafa  bayanta a hankali. Ajiyar zuciya haɗi da sheshsheƙan kuka kawai take sauƙewa.  Shikuwa Dr.Sadeeq wani tunani na daban yakeyi acikin zuciyarsa, hakanan Allah ya halittamasa tsananin tausayin Zahrah acikin zuciyarsa,   yana sonta sosai, bayason yaga tana cikin damuwa,  bayajin akwai wani abu aduniyar nan da Zahrah zata nema agaresa matuƙar yana dashi tarasa, zai iya mallaka mata komai nasa, matuƙar zataji daɗi, za kuma tayi farinciki,  bakinsa ya kawo daf da kunnenta cikin murya me sanyi yace

"Zahrah!"

Tanajinsa amma kuma saitayi sauri ta lumshe idanunta, tanaso ya É—auka cewa bacci take.

Jin tayi shirune yasanya yashiga goga mata lallausan sajensa akan fatar wuyanta, yayinda yake yawo da hanunsa akan bayanta a hankali.. 

Luf tasakeyi acikin ƙirjinsa, tana jin saƙonsa yana tsarga mata hartafin ƙafarta, yayinda daddaɗan ƙamshin turarensa ke ƙara sanyaya mata jiki, batajin bacci ko kaɗan, amma kuma yazama dole ta ƙwaƙulowa kanta baccin dole, kodan ta samawa zuciyarta salama.  "Ina laifin Dr.Sadeeq? mene bayi dashi wanda mace takeso tasamu ajikin ɗa namiji? miye laifin masoyin daya nuna maka haƙiƙanin so? ashe wani lokacin zuciya batasan menene halacci ba? me yasa SOYAYYA tazamo guguwa me hargitsa zuciyar ɗan adam tayi fatali da komai nasa?"   itakam ko da a yanzu soyayya ta barta haka ta gama iya cutarta, cuta me muni ma kuwa..   Yajima yana shafa bayanta, harsai da ya ji sauƙar numfashin dake nuna cewa da gaske bacci ya ɗauketa.  Kwantar da'ita yayi akan gado, haɗe da jawo blanket ya rufe mata duka jikinta, yasani sarai batason sanyi, don haka ya rage gudun A.C, kashe mata fitilan ɗakin yayi, kana ya jawo mata ƙofar ya rufe mata bayan yafita zuwa falo.. Laptop ɗinsa ya ɗauka haɗe da buɗewa, aikinsa ya shigayi cikin nutsuwa, ɗan kwana biyun nan da bai shiga office ba haryatara ayyuka masu yawa, gashi ansanar masa patients suna buƙatar taimakon sa, duk da ya ɗau hutu ma ashe bai tsira ba, ayyuka na nan akansa wanda yazamana dole sai shi zaiyisu...
***

*GERMANY*

Shikaɗai yake rayuwarsa acikin ɗakin, yau kwanansa ɗaya kenan baisanya komai na abinci acikin saba,  yayi matuƙar ramewa alokaci guda, yayinda gashi dakuma sajen dake kwance akan fuskarsa suka ƙara yawa fiye da na da, duk da dama cewa shi mutum ne me yalwan suma,  kallo ɗaya zakayi mai kasan cewa yana ɗauke da damuwa me tarin yawa acikin zuciyarsa,  Zaid ɗin da dana yanzu sun banbanta, wan can Zaid ɗin zuciyarsa cike take da isa, ɗagawa, girmankai, rashin sanin darajan ɗan adam, Zaid ɗin da mashayine, mazinaci, wanda bai ɗauki zina abakin komai ba, haka kuma Zaid ɗin da, baisan menene damuwa ba, baisan menene rashi ba, samu kawai ya sani, sannan kuma baisan menene ƙunci da ɗaci ba, baikuma san menene wani abu waishi soyayya ba.    Zaid ɗin daya kasance  yanzu kuwa, wani mutum ne dayake cikin ƙunci, zuciyarsa tana cike da tarin damuwa, Zaid ɗin yanzu yarasa duk wani farincikinsa, yarasa jin daɗi, yarasa nutsuwar zuciya data ƙwaƙwalwa.  "ko wannan baici yasa Zahrah ta tausaya masa ba? shin wai shi kaɗaine yataɓa aikata abun da baidace ba?"  yatambayi kansa,  abu biyune suke damunsa, zazzafar soyayya dakuma rashin nutsuwa da salama dake damunsa, yanzu shikaɗai yasan halin dayake ciki, baya iya bacci, baya iya cin abinci,  bayajin daɗin komai nasa, gaba ɗaya duhu ya mamaye rayuwarsa,  yanzu yafara zargin cewa zunubansa ma sunyi masa yawa,  yasani ƙwarai,  yasan abu me kyau da kuma marar kyau, amma saboda ruɗin duniya gaba ɗaya ya shagala.  (Yawancin mutane yanzu rayuwarsu sukeyi saka ka,  zasu aikata zina, zasu sha giya, zasu aikata duk wasu aiki dake jawo musu manya manyan zunubai, amma kuma yawancinsu sunfi gudun kunyar duniya data lahira, suna tsoron wani yakamasu suna aikata zina, amma basa tsoron kallonsu da Allah yakeyi, wasu sun maida zina manshafawarsu, suna ganin kamar hakan wayewace, bayan kuma suna sane dacewa aikata ta babban halaka ne, Ya ALLAH kaci gaba da karemu, kakuma tsaremu da sharrin zina, ka rabamu da zama da mazinata, Ameen Ya ALLAH!)

Yariga daya gama yanke hukunci cewa ko da su Dad ɗinsa basaso saiya koma Nigeria, bazai iya zama anan ba, zafi yakeji acikin zuciyarsa marar misaltuwa idan haryatuna da cewa Zahrah'nsa tana can gidan wani, sai yaji gaba ɗaya nutsuwarsa ta gushe, wataƙila ma wannan banzan Doctor ɗin ya kusanci Zahrah'nsa, ae kuwa baisan sanda ya ƙwalla wata irin ƙara ba, azuciye ya ɗauki wani flower dake gefen gadon, yayi jifa dashi, take kwalbar flower'n ya tarwatse a tsakiyar ɗakin, duk da haka hakan baiyi masa ba, saida yataka ya ƙarasa gaban mirror, da hanunsa ya daki mirror ɗin, take mirror'n ya tarwatse  har saida ya yanka masa hanu, amma saboda tsananin kishi'n dake cinsa, ko zafin ciwon baiji ba.
"Hakane ma, yakusanceta" wata zuciyartasa ta faÉ—a masa..

"No!!! it will never happen, i Know Zahrah will not do it, bazata taɓa  iya bawa  wani  kanta ba bayan ni, because she know we love each other" yafaɗi haka da ƙarfi cikin wata irin murya, me ɗauke da tsananin ɓacin rai,   durƙushewa yayi a ƙasa haɗe da sanya hanu ya dafe saitin zuciyarsa wacce take bugawa da sauri, da dukkan alamu dai ya tsokalowa kansa.  Haki yasomayi tamkar wani wanda yayi gudu,  tarine ya sarƙesa, take jini yasoma fitowa ta bakinsa, shi kaɗai yayi tarinsa harya ƙare, ya galabaita sosai da sosai, da ƙyar ya'iya jan jikinsa ya shiga toilet, wanke bakinsa yayi kana yafito daga cikin toilet ɗin, numfashi kawai yake maidawa cike da wahala,, wani ɗan abu yadanna, bayan kamar minti 1 saiga wata cleaner tashigo cikin ɗakin, nuni yayi mata da inda jininsa ya ɓaɓɓatata,  babu ɓata lokaci ta sanya kayan aiki ta gyara wajen, tana kammala gyaran kuwa wasu likitoti su biyu suka shigo cikin ɗakin.. Duba lafiyar jikinsa  suka sake yi haɗe da basa wasu magunguna, wata allura sukayi masa da take matuƙar sa bacci, domin kuwa gwaje gwajen da   sukayi masa yasa sungano cewa baya samun wadataccen bacci.

Suna fita ya lumshe idanunsa, wanda tuni suka zama jan gauta, saboda tsabar tsananin kishi dake cinsa,  jiyake ma kamar idan ya ƙara kwana ɗaya ba acikin Nigeria ba ya cutu, gwamma yaje ya ƙwace Zahrah tunkan  wanda ya ɗauka bakomai ba ya ɗanɗana masa zumarta.   (Hahhh guy ae ka makaro,yasin doctor yajima da ɗanɗanawa🙈) ****  Mintuna kaɗan dayi masa alluran, bacci me nauyi yayi gaba dashi...

Dad ne ya nutsu haÉ—e da dawo da kallonsa ga Mummy. "Inaga abu É—aya zamuyi masa yamanta da wannan yarinyar, kawai na yanke shawara aure zanyi masa."

Shaye da mamaki Mummy  take kallon Dad.    "Aure fa kace Alhaji? wakake tunanin zata iya zama da Zaid,  da irin wannan halinnasa? hmmm bana majin cewa Zaid zaiso wata mace bayan  wannan Zahrah'n, ni nama fara tunanin cewa asirce masa zuciya tayi, amma inbanda haka taya lafiyayyen ɗa namiji kamar Zaid zai maƙalewa mace ɗaya kamar maye"

Murmushi Dad yayi haÉ—e da girgiza kansa, "itadai Safara'u haka take, idan ana magana me hankali saikuma tana sako wasu abubuwa kamar na wasa." dad yafaÉ—i haka acikin zuciyarsa, afili kuwa gyara zamansa yayi haÉ—e da sake fuskantarta...

"A wannan karon dagaske aure zanyi masa, saboda aure ne kaɗai zaisanya Zaid dawowa cikin nutsuwarsa,  bandamu da ko yanason matar ko baya sonta ba, nasan watarana ahankali zai sota ya manta da waccar"

"To Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, amma gaskiya nima banjin daɗin ganinsa acikin wannan  halin dayake ciki yanzu,ko abincin kirki wallahi bana iya ci"   Mum tafaɗi haka cikin tausayawa ɗan nata.....     (Team Zaid kunji fa wai aure za'ayi masa me zakuce? wayaga Zaid da auren dole)

****

NIGERIA

Tunda ta kwanta bacci ba'ita ta tashi ba sai 11:30 am,   ko tsayawa nemansa yau batayi ba tafaɗa bathroom, wanka tayi  kana ta fito daga cikin bathroom ɗin... Mai kawai ta shafa kamar kullum sai kuma powder, itakam batason  cika meckup akan fuskarta.
Chapter 80 · 0% Book details