Sashe 74
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Wannan shagwaɓan da takeyi masa shiyake sanyawa yaji gaba ɗaya jikinsa ya mutu, har wani rufewa idanunsa keyi,, yabuɗe baki zaiyi magana kenan wayarsa tasoma ƙara, kobai ɗaga ba yasan dalilin ƙiran, yanzu haka yasan anacan antaru a wajen dinner su kawai ake jira, miƙar da'ita yayi tsaye bayan ya aje cup ɗin dake hanunsa,, amaimakon ya riƙe mata hanu su tafi kamar yanda suka zo sai gani tayi ya ɗagata caɗak yayi hanyar waje da'ita,, a tsorace tanemi sauƙa daga jikin nasa amma kuma kyakkyawan riƙon dayayi mata yakasa bata daman hakan....
Bai direta ako ina ba sai acikin mota, yanashiga driver yaja motar suka fice daga cikin gidan... Kwanciya tayi luf ajikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunta gaba ɗaya sanyin AC'n da motar ke busawa ne ke damunta, sam batason sanyi yacika yawa a waje. daga wani ɓangare kuwa amatuƙar takure take, saboda yanayin yanda yake murza hanunta dake cikin nasa. sosai hakan kesawa taji wani iri acikin jikinta, gani tayi gaba ɗaya yau ɗin ya sanja mata, yanayi mata wasu irin abubuwa da baitaɓa ƙoƙarin kwatanta yi mata shiba acan baya, ada sam baya taɓa yunƙurin kama hanunta sai dai idan yazama dole,kuma koda ma ya kama hanunta bawani jimawa zai sake, sannan kuma sam baya yawan jawota jikinsa kamar yanda yakeyi mata ayau, gashi gaba ɗaya taga yanayinsa ya sauya, idanunsa sunyi wasu kala tamkar wanda yakejin bacci... Zuciyarta nayi mata lugude haka suka iso wajen dinner inda mutane suka cika maƙil zuwansu kawai ake jira... Suna isowa waje yaɗauki sowa yayinda mc yasake musu daddaɗan kiɗa me daɗi ta romantic... kamar dai yanda kamu ya ƙayatar haka dinner ma yaƙayatar sosai Dr.Sadeeq yayiwa Zahrah ɓarin kuɗi lokacin da aka ƙirasu tsakiyan fili, sunsha liƙin kuɗi kam sosai, su Auntie Raliya ma sunzo sun liƙa musu,  amma duk yanda akaso amarya tayi rawa kasawa tayi, saboda bata iyaba, bakuma al'adarta bane yin rawa agaban mutane, kunya ma bazai taɓa iya barinta ba,, saida Dr.Sadeeq yariƙe hanunta yashiga juyawa da'ita afilin rawan, take aka hau musu tafi yayinda wasu daga cikin abokansa suka ci gaba da yi musu ɓarin kuɗi,, suna komawa kan kujeransu mc yasanya musu daddaɗan waƙar Ed sheeran, shiru Zahrah tayi tana sauraran waƙar sosai dama takeson waƙar domin kuwa duk waƙan Ed sheeran yanayi mata daɗi... Koda aka yanka haɗaɗɗen cake ɗin da aka ƙawatashi da sunan ango da amarya, da ƙyar Zahrah ta'iya bawa Dr.Sadeeq cake ɗin abaki, gaba ɗaya nauyi da kunya sun isheta gawani zazzaɓin daya sake kawo mata ziyara lokaci ɗaya,,, lokacin da aka tashi a dinner tuni amarya Zahrah tayi laushi, hartakai bata iya dogon tsayuwa da ƙafafunta, ƙarfe 10 na dare aka tashi a dinner Aunty Ladi da kuma Husnah su suka sanyata a wata mota, direct aka wuce da'ita asalin gidan da zata zauna wato gidan aurenta....  Gidane me matuƙar kyaun gaske wanda aka kashe kuɗi sosai wajen ƙawatasa,   baginin gidan sama bane amma kuma yanayin yanda akayi ginin yayi kyau sosai,    wata haɗaɗɗiyar ƙofa suka nufa, suna buɗeta kuwa suka tsinci kansu cikin wani ƙawataccen falo me kyaun gaske.  haɗaɗɗen falone wanda yasha kujeru light orange and milk colour, yayinda aka ƙawata jikin ƙofa da window'n da wasu irin haɗaɗɗun labulaye masu kyau, tsakiyar falon kuwa mamaye yake da wani haɗaɗɗen carpet Orange colour,, ga wani irin ƙaton tv plasma dake aje kan wani haɗaɗɗen glass,, falon dai ba'acika masa kayan ado ba amma kuma yaƙawatu sosai komai na falon me tsada ne,, direct wani ɗaki dake cikin falon aka wuce da Zahrah,, ɗakine me kyau wanda yaji royal furnitures milk colour, yayinda aka lailaye kan makeken gadon da wani irin zanin gado pink me kyawun gaske...  Akan gado sukayimawa Zahrah masauƙi,  Husnah dakanta ta haɗawa Zahrah ruwan wanka, koda tafito a bathroom ɗin hannayen Zahrah dake zaune kan gado ta kamo, haɗe da janta har zuwa cikin bathroom inda ta haɗa mata ruwan wanka...
Wani Turare ta bata tace inji Hajiya Shuwa, sannan kuma tayi mata bayanin yanda zatayi amfani dashi... Â
Zahrah tana fitowa a wanka Husnah ta shafa mata powder haɗe da lipstick, wani riga da sket na material marar nauyi Husnah ta bata tasanya, take tafito ɗas da'ita, a tsakiyar gado Husnah ta zaunar da Zahrah haɗe da rufe mata kanta da wani irin haɗaɗɗen mayafi me sheƙi da walwali, wasu turaruka masu ƙamshi Husnah takuma feshi jikin Zahrah dasu, take ɗakin yakuma ɗumamewa da ƙamshi,,  sake matsowa kusa da Zahrah Husnah tayi cikin murya ƙasa ƙasa tace
"Dan Allah Zahrah karkice zaki ci gaba da wannan kukan naki, ki ɗan daure zuciyarki kinji ƙawata, kuma sannan kada ki hana Doctor haƙƙinsa, nasan zakiji tsoro amma please ki daure kinji ƙawata, banaje falo na amsa waya " Husnah taƙare maganar tana me miƙewa tsaye, idanu tayiwa Auntie Ladi suka fice a tare....
Tun Zahrah na jiran dawowan su Husnah hartasoma jin tsoro, domin kuwa gaba ɗaya gidan yaɗau shiru babu alaman akwai motsin wani mutum bayan ita,,, abun da Zahrah bata sani ba shine su Husnah wayo sukayi mata suka tafi suka barta, sunyi hakanne kuma saboda taƙaitamata wahalan kuka, domin sun san sunace mata zasu tafi zata ƙara fawan kukanta.....
Gyangyaɗine yasoma ɗaukarta, dan haka saita jingina bayanta ajikin saman gadon haɗe da lumshe idanunta da suketa tsiyayar hawaye...
A hankali yaturo ƙofar ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, yasake shiga cikin wata farar shadda sabuwa ƙal sai sheƙi takeyi, ƙamshi ne kawai ke fita ajikinsa, daganinsa kasan yana cikin matsanancin farinciki,, ledan dake hanunsa ya aje, haɗe da takowa zuwa wajen datake zaune ta jingina bayanta da saman gado,,   zama yayi akusa da'ita haɗe da ƙiran sunanta,, cikin murya me sanyi da kuma alamar bacci ta amasa masa,,  ahankali yasanya hanunsa ya ɗan jaye mayafin dake kanta, hawaye yagani kwance akan fuskarta, hanunta yakamo haɗe da jawota jikinsa, hanu yasanya yashiga share mata hawayen dake kan fuskarta.
"Ki daina kuka kinji my wife, bacci zakiyi ne?" yatambayeta yana me ƙaremawa fuskarta kallo,, fuska ta kuma kwaɓewa, haɗe da kaɗa kanta, cike da shagwaɓa tace
"Ina Husnah?"
Ajiyar zuciya yasauƙe haɗe da sanya hanu yashafi lallausan gashinta dayasha gyara
"Husnah kuma Zahrah?" yatambayeta cike da mamaki..
"Eh tacemin zata amasa waya tana zuwa kuma haryanzu bata dawo ba!" yanzuma dai asangarce tayi maganar,, murmushi yayi mata haɗe da cewa
"Kada kidamu Husnah zata dawo gobe, taso muje kiyi alwala idan munyi salla saikici abinci ko"Â Â
Jitayi gabanta yayi wani irin faɗuwa amma kuma yazatayi da rayuwarta babu yanda ta'iya haka tabisa kamar jela harcikin bathroom,, saida yayi nasa alwalan kafun yabata waje itama ta ɗauro alwala,, tana fitowa daga cikin bathroom ɗin ya miƙo mata wata lufaya, a ɗaɗare tasanya lufayan daya bata, hanunta yakama suka hau kan sallaya, shi yajasu salla raka'a biyu,  suna idarwa yayi musu addu'o'i haɗe da kama kanta itama yayi mata addu'a... A tsorace ta zauna akan gado haɗe da sake takure jikinta waje ɗaya...
Wani ɗan madaidaicin carpet Dr.Sadeeq yashimfuɗa haɗe da cika tsakiyar carpet ɗin da kayan ciye ciye, hanu ya miƙawa Zahrah alamar tataho garesa, cikin ɗari ɗari haka ta shiga takowa zuwa inda yake, hanunta yakamo yazaunar da'ita acikin jikinsa, hijabin dake jikinta yasoma ƙoƙarin cire mata, da sauri tasake ƙanƙame jikinta, ganin haka yasanya shi yin murmushi, ya fasa cire mata hijab ɗin,, juice ya zuba acikin kofi haɗe da kai kofin bakinta, babu musu tabuɗe bakinta ta kurɓi kaɗan,  aje kofin yayi, haɗe da yago gasasshen nama yakai bakinta,, kanta tashiga girgizawa alaman bazataci ba.
"Kiyi haƙuri kici kinji Baby na, kaɗan zakici bamai yawa ba!" yafaɗi haka cike da lallami,,, shida kansa yake bata kazan, bata wani ci me yawa ba tace masa ta ƙoshi, dakansa yatattara wajen yakai kitchine,, yana dawowa ɗakin yasameta tsaye ajikin mirror tayi jigum,, fargabane yacika mata zuciya, wani irin tsoro ne taji ya ɗarsu acikin zuciyarta wanda bazata iya misaltashi ba,,
Kaitsaye drower ɗin dake cikin ɗakin ya nufa, wata doguwar rigan bacci sleeping dress yaciro haɗe da ƙarasowa gareta,, "Kije kiyi brush, wannan kayan kuma kisanya kizo kiyi bacci" hanunta na rawa haka ta amshi kayan sumi sumi ta wuce cikin bathroom, tana kammala brush tasoma cire kayan jikinta, warware rigan da Dr. yabata tayi tashiga ƙaremawa rigan kallo, doguwar rigace na bacci me net, amma kuma tana da faɗin wuya sannan kuma rigan irin me nuna jiki ɗinnan ne,, badon tasoba haka ta sanya rigan ajikinta, hmmm sam bazata iya fita da wannan rigan gaban Dr. Sadeeq ba, saboda gaba ɗaya rigan ta bayyana breast ɗinta, yayinda komai nata yafito fili, hijabin da tayi salla dashi ta ɗauka ta sanya,, a ɗaɗare ta fito daga cikin bathroom ɗin,, zaune tagansa akan gado tuni yasanja kaya zuwa farar jallabiya,  murmushi kawai Dr.Sadeeq kejifanta dashi,  cikin zolaya yace "Meye narufe jikin da hijabi?"
Ƙasa takumayi da kanta, yanzu kam ko ɗan shagwaɓan ma takasayi masa...