← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 112

Sashe 30

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zahrah kuwa tana shiga cikin gidan kaitsaye ɗakinta tawuce haɗe da banko ƙofar ta rufeta gam, faɗawa tayi kan katifarta tana mai sauƙe a jiyar zuciya, ko da taji ƙaran tashin motar Dr Sadeeq ɗin, wani sanyi taji a cikin zuciyarta, haka kawai yazo ya zurkuɗa mata wannnan maka makan alluran nasa, ai wlh bata saɓuwa.....

*New York City*

Kwance yake akan makeken gadon sa, daga shi sai ɗan wani 3 guater jeans, yayin da ya ware ƙafafunsa, duk da cewa akan gado yake, amma saboda tsabar iskanci irin na Zayd sanye yake da takalma (toms) aƙafarsa, yayinda hanunsa ke riƙe da wata zungureriyar kwalbar giya, gefensa kuwa wata kyakkyawar baturiya ce kwance tsirara bako ɗigon abun rufa tsiraici a jikinta, daganinta kasan irin cikakkun ƴan iskan nanne, gaba ɗaya ta tsare Zaid da idanunta, sai wani lasan baki takeyi tamkar tsohuwar mayya, bakomai yasa hakan ba, face yanda gaba ɗaya ta gama kwaɗaituwa da Zaid ɗin, amma kuma yaƙi amincewa ya kusanceta, gaba ɗaya wani irin muguwar sha'awarsa takeji, duk kuwa yanda ta nu namasa zallan karuwancinta a fili, yaƙi kusantar ta, saima sake je fata cikin kogin sha'awa da yayi,

Zaid kuwa da gangan yaƙi kusantarta, domin yanzu tsagwaran iskanci yake ji dashi, sai ya ɗauko mace yagama ƙwaƙuleta, yabarta batare da yayi sex da'ita ba, wayarsace tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, har ƙiran ya katse Zayd bai ko kalli inda wayar take ba balle yasan wake ƙiransa,,

Cike da salo irin na ƴan bariki wanda ta yarda cewa idan hartayi masa zai kusanceta, ta sake matsowa daf dashi, a hankali ta zura hanunta acikin 3 guater jeans ɗinsa, haɗe da soma shafa kan mararsa a hankali, yayinda ɗaƴan hanunta ke kan faffaɗan ƙirjinsa tana shafawa slowly, ta yadda zaiji abun har tsakiyar kansa, cike da ƙwarewa tashiga murza ....

A hankali yaɗago idanunsa da suka soma sauya launi ya sauƙesu akan baturiyar, ai kuwa yayi kyakkyawan gani, domin kuwa fuskar Zahrah yagani ta bayyana akan ta baturiyar, bakomai yasa hakan ba face giyar da yasha da tasoma yi masa aiki, da ƙarfin gaske yajawo baturiyar jikinsa, haɗe da matseta ƙam a ƙirjinsa, take jikinsa yasoma ɓari,lokaci ɗaya yashiga bata kyakkyawan romance wanda yasanyata tafara nishin daɗi.

Gaba ɗaya baturiyar nan tadawo masa Zahrah acikin idanuwansa, baisan sai yaushene matsanancin sha'awar da yakemawa Zahrah zata sake saba, a kullum a ko wani daƙiƙa sha'awar Zahrah sake ninkuwa masa takeyi acikin zuciyarsa,

Hmmm duk jaraba irin ta wannan baturiya yau fa sai dai ta haƙura, domin kuwa Zaid tun kan abunnasa yagama shiga jikinta, yayi saurin tureta gefe, wani irin masifaffen ɓacin raine yazo masa, ƙarya ne yasani ba Zahrahn sa bace wannan, sharrin giyane kawai, idan har giya zata iya sanyawa yaga fuskar wata a matsayin Zahrah, to bata isa sawa ɗanɗanon wata yakasance tamkar na Zahrah'nsa ba, Zahrah da ban take komai nata na dabanne, cikinta a cike yake, bakamar sauran matan dayake mu'amala dasu ba, wanda su gaba ɗayansu a wage suke daga ciki har waje, ita kuwa Zahrah daga ciki har waje a haɗe take, bakomai yasanyashi ture baturiyar nan gefe ba face jinsa da yayi ya faɗa zuruf tamkar anzura ƙwallo a raga, bathroom ya wuce kaitsaye yasakarmawa kansa shower.

Itakuwa mayyar baturiyar dolenta ta maida É—an fingilan rigarta ta fice daga cikin É—akin, cikin matsanancin sha'awa, Zayd ya jangwalo mata bala'i.

Zayd kuwa a daddafe yayi wanka, domin kuwa wani irin ciwo marar sa ke yi, koda yafito a wankan a daddafe yasha tea da lamon tsami, kwanciya yayi lamo yana mai sauƙe numfashi akai akai, lallai yazame masa dole yakoma Nigeria kodan Zahrah ma, yazame masa dole yakomawa Zahrah domin kuwa bazai zauna sha'awarta ta kashe shi ba, amma ya ɗau alƙawarin cewa wannan karon bazai mata da ƙarfi ba, lallaɓata zaiyi tabasa kanta cikin sauƙi, da wannan tunanin bacci yayi awungaba dashi,
(Hmmm ayi bacci lafiya Zaidun Munubiya,lol).

Nigeria.

Yaune ranar da Dr ya shaidawa Zahrah cewa zata koma makaranta.

Don haka tun tashinta, tatashi tanajinta wani iri, gaba ɗaya ji take gabanta na faɗuwa, hakanan take tsarge, gani take tamkar kowa yasan maiyafaru da'ita, a daddafe tayi wanka, wata simple gown tasanya ajikinta, wanda bata da ado ko kaɗan, wata ƙatuwar lufaya ta zura wanda tsawonsa ya wuce guiwarta. Jin maganarsa a tsakar gidan, yasa taji ƙirjinta ya ɗan buga kaɗan, cikin rashin kuzari tafito daga cikin ɗakin.

Kamar yanda yayi mata kyau, haka shima yaga tayi masa kyau, duk da cewa babu É—igon kwalliya akan fuskarta.

"Muje ko!" Yafaɗa a taƙaice, saurin ja da baya tayi haɗe da girgiza kanta, domin kuwa ko karen hauka ne ya cijeta, bazata yarda ta shiga motarsa ita kaɗai ba.

"Muje Baffa na jiranmu a waje" Dr Sadeeq yafaÉ—a domin yaga alamar a tsorace take,

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauƙe haɗe da bin bayansa, domin kuwa tuni yariga da yayi gaba.

(Please two days zakuna haƙuri dani domin typing ɗin ba ya yawa, ina busy ne sosai, dan Allah kada kuyi ƙorafi, insha Allah next page zanmuku da yawa)

*27/November/2019*

*Voted, Comment, and Share please...follow me on wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

                *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
     @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

*Chapter 42 to 43*

Suna fita kuwa ta iske Baffa yayi ɗare ɗare agaban motar Dr Sadeeq sai washe haƙora yake kai kace anmasa kyautar ƴan kuɗaɗe ne.

Dakansa ya buɗe mata murfin motar ɓangaren gidan baya, cikin sanyin jiki ta shiga cikin motar, kaitsaye yashige ɓangaren driver haɗe da mawa motar key...

Tunda suka ɗau hanyar makarantar tasu Baffa ke faman zuba kamar wani kurna, yayinda Doctor Sadeeq ke amsa masa jefi jefi, domin hankalinsa gaba ɗaya yana ga Zahrah, wacce ke zaune tayi jigum a gidan baya,  akai akai yake satan kallonta tacikin madubi.. 
A haka dai harsuka iso cikin makarantar tasu,  dai dai bakin ƙofar hall ɗin da zasu gudanar da lecture yau, ya yi parking motar tasa, domin dama already ansanar dashi cewa yau a wannan hall ɗin zasu gudanar da lecture.

A hankali ta buɗe murfin motar ta fito kafaɗarta ɗauke da jakar makarantar ta,  cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa ta nufi cikin hall ɗin kai tsaye, ko wai gensu batayi ba,  tanashiga hall ɗin kallo yadawo kanta, take taji wani irin muguwar faɗuwar gaba haɗe da karyewar zuciya, gani take tamkar kowa yana ganin abun da yafaru da ita rubuce akan goshinta.

Karab idanunta suka sauƙa akan Husnah wacce take faman aikin haɗa wasu takardu dake gabanta. wani irin sanyi taji zuciyarta tayi sakamakon ganin husnah, domin kaf makarantar bata mu'amala da kowa bayan husnah,  da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah, domin koda wasa batayi tunanin ganinta ba.   

"Kamar mafarki nakeyi gaskia naji daɗi sosai ƙawata!" Husnah tafaɗa cike da tarin farinciki.

Zama sukayi a tare dai dai lokacin  Sir Bature yashigo cikin hall ɗin, tsit haka ajin ya ɗauka ana ta sauraran lecture ɗin dayake yi musu, a zahirin gaskia tanajin abun da yake cewa, amma kwata kwata bata fahimtarsa,  awa biyu suka ɗauka chur suna lecture, kafun daga bisani yafita daga ajin,    gyara zama Husnah tayi haɗe da mai da kallonta ga  Zahrah cike da kulawa tace " Yanzu ina likitan yake ?" 

Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa " Ba maganar Doctor bace damuwata Husnah, babban damuwata shine gani nake tamkar abun da Zaid yamin yana rubuce a gaban goshina, Husnah gani nake tamkar kowa yasan abun dake damuna !" Zahrah taƙare maganar cikin raunin zuciya.  

" Kada kice haka Zahrah, babu wanda yasan abun da yafaru dake, kada ki ɗaga hankalinki ƙawata kinfasan kowa da irin tasa ƙaddaran, kuma zuwa yanzu na tabbatar kin mai da al'amuranki ga Allah, shima Zaid nasan kinbarsa da Allah "

Murmushi mai ciwo Zahrah tayi haɗe da kallon ƙawarta ta, cike da ƙuna tace " Banda wata hanya wanda tawuce barinsa ga Allah, nasan nan bada jimawa ba Allah zai bimikin haƙƙina " taƙare maganar cikin raunin zuciya,

Hannayenta Husnah ta kama suka fice daga cikin ajin, kai tsaye cafeteria suka nufa don cin abinci. Balaifi sosai tasamu nutsuwa a yau ɗin domin kuwa Husnah bata barta tayi kaɗaici ba. Ƙarfe  5 dai dai suka fito daga  cikin lecture ɗin ƙarshe na ranan yau ɗin, kasan cewar ta kwana biyu bata zo makarantar ba, sai take jinta gaba ɗaya duk ta gaji,   cikin nutsuwa take takunta yayinda kanta ke duƙe a ƙasa, ba abun da zuciyarta keyi banda bugawa, gaba ɗaya tsoron fita daga cikin school ɗin takeyi, gani take tamkar tana fita za'a kamata, da ƙyar take iya ɗaga ƙafafunta, dagani kasan bason tafiyar take ba. a hankali ta matsa gefe, haɗe da waigowa don ganin waye wannan ya matsa mata da horn ɗin motarsa, karab idanunta suka sauƙa akan sa, kasancewar  gilasan motar tasa gaba ɗaya a sauƙe suke, sam batayi tsammanin ganinshi ba,  murmushi yasakar mata haɗe da cewa " Da baki matsaba ai dana take ki !" yafaɗi maganar cikin yanayin tsokana, ɗan guntun murmushi itama tayi haɗe da taɓe baki, "ai idan haka ta kasance zanfikowa jin daɗi " Zahrah tafaɗi hakan da iya gaskiyarta.

"Shigo mutafi!" yafaÉ—a cikin tsare gida.

Saurin kallonsa tayi bakinta É—auke da tarin tambayoyi, amma kuma takasa koda motsa bakinta ne balle ta furta wata kalman.

"Kintsaya kina kallona, ba dole idan bazaki bini ba, saina yi tafiyata!" yaƙare maganar yana mai niyar tada motar tasa.

Da sauri ta zagaya haÉ—e da buÉ—e murfin motar, gefen mai zaman banza ta shiga haÉ—e da tamke fuskarta tamau tamkar wanda yagayamata magana marar daÉ—i.

Da ƙyar ya iya ɓoye dariyan dake cinsa, domin kuwa tsoro ya hango ƙarara akan fuskar Zahrah,     "Naɗauka ai zakijamin ajine, da sai na tafi na barki ba ruwana!" yafaɗi hakan cike da shauƙi.

Harara ta watsa masa haɗe da sake turo baki gaba, cike da shagwaɓa wacce batasan tayi ba tace "Nifa idan surutu zakamin ka sauƙeni nayi tafiyata"
Chapter 30 · 0% Book details