← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 112

Sashe 83

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali yake taka matattakalan sauƙowa daga cikin jirgin, sanye yake da riga da wando irin na sanyi navy blue colour,  hatta takalman  dake sanye a ƙafafunsa navy blue colour ne, yayi kyau sosai yaƙara haske, sai dai kuma sosai rama ta bayyana kanta ajikinsa.  Yana gama saƙƙowa daga kan matattakalan yanufi wajen da motocin da sukazo ɗaukarsu ke fake,  4matic yabuɗe yashiga haɗe da hakincewa agidan baya, bayasan damuwa shiyasa bayason shiga mota ɗaya dasu  Dad ɗinsa..    Harsuka isa gida tunani yakeyi, maiya kamata yayi? sai kuma yanzu daya dawo yakeji gaba ɗaya Nigeria'n tayi masa ƙunci haɗe dayi masa duhu,daya kulle idanunsa Zahrah kawai yake gani...    Yana fita daga cikin motar direct ɓangarensa dake cikin gidannasu ya nufa.     Falo'n sa tsab-tsab yake tamkar wanda wani yake rayuwa aciki, bedroom ɗinsa ya wuce, yana shiga yaƙarasa gaban wani tangamemen hotonta da yasa aka masa  kalanda (Calender)  dashi yakafa ajikin bangon ɗakin,  rungume ƙaton kalandan yayi haɗe da lumshe idanunsa.

"I really Miss you My Zahrah!"

ya faɗi haka cikin murya me sanyi da kuma tsananin rauni, hanu yasanya yashafa daidai saiti laɓɓanta dake jikin hoton calender'n.
"Bana tunanin zan daina kewarki Zahrah na,  tunaninki yazama abincin ruhina, inasonki sosai,  lokaci yayi daya kamata  ki dawo gareni, muyi rayuwar auren mu cike da tarin farinciki, nadaina komai Zahrah shan giya, zina, duk na daina please ke nake jira har yanzu, ina fata baki bawa wanina kanki ba?"  yanayin yanda yake magana da hoton idan ka gansa kaitsaye dasunan mahaukaci zaka ƙirasa, domin kuwa me cikakken hankali bazaiyi haka ba..       Wayarsa ya ɗauka yayi dialing number'n Abid, bugu uku Abid ya ɗauki wayar baijirayi abun da Zaid ɗin zaice ba yace
"Wow surprise kenan?"

Ƴar ƙaraman tsuka Zaid yayi cikin muryarsa me rauni yace "Inason ganinka Abid, yanzu agidan mu please!"  baijirayi me Abid ɗin zaice ba ya katse wayar haɗe da cilla wayartashi kan gado, yasan Abid bazaiƙi zuwaba shiasa baijirayi amsar saba yakashe ƙiran.  Zama yayi akan wata kujera dake cikin ɗakin,  kan ɗan madaidaicin fridge'n dake aje cikin ɗakin ya maida idanunsa, jiyake kamar yatashi yaje ya ɗau wine ɗinsa yasha, sai dai kuma wata zuciyar tana gargaɗinsa da cewa, Zahrah bataso, tun randa ta gayamasa wata baƙar magana akan shan wine da yake, bai ƙara shaba harkuwa rana me kamar ta yau, duk da kuwa irin azabtuwan da yakeyi idan baisha wine ɗin ba, saboda yariga daya saba.  Shiru kawai yayi haɗe da kama kansa ya rumtse idanunsa..    Abid ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo bakinsa ɗauke da sallama, ciki ciki Zaid ya amsa masa sallaman haɗe da watsa masa idanunsa da sukayi jajur dasu.. Cike da mamaki haɗi da tsoro Abid ya matso kusa da Zaid da ɗan sauri.

"Zaid meke damunka haka? yaushe kuka dawo? yajikin naka?" duka waÆ´annan tambayoyin Abid yayiwa Zaid su a lokaci É—aya kuma duk amsarsu yake nema idan zai samu..

"Abid nakasa mantawa da ita, itace nutsuwar tunani na, banajin zan iya kaiwa lokaci me tsawo batare da na sanyata acikin idanuna ba, Inasonta sosai kai kasani!"

Kallon Zaid kawai Abid keyi yamarasa me zaice masa..  Kallon ɗakin yashiga yi sai alokacin ya Lura da maka makan hutunanta dake manne ajikin bangon ɗakin Zaid ɗin,wasu zane ne wanda Zaid ɗin yayi wasu kuwa hotunanta ne.  Wani irin tausayin Zaid ɗinne ya tsirga masa me tsanani, shidai bazaice baitaɓa soyayya ba, amma kuma baita ɓayin kwatan kwacin irin wannan son me tsanani da Zaid keyi ba. Zama yayi akan kujeran dake fuskantar na Zaid, hanun Zaid ɗin yakamo haɗe da cewa "Kazama jarumi Zaid, kada kamanta fa yanzu Zahrah matar wani ce kuma...."

"Ya isheka haka Abid!!" Zaid ya katse Abid cikin tsawa sosai.

"Matar wani, Matar wani, abun da kuke ta faɗa kenan, meyasa ni bazaku duba halin danake ciki ba? shikenan don tana matar wani sai nadaina sonta? kafun wanda kuke ikirarin matarsace yasota nine nan nafara sonta,  kada kataɓa tunanin zan daina son Zahrah Abid, bakuma zan taɓa samun nutsuwa ba harsai Zahrah ta zamo mallakina, kataimakeni Abid kazo muje gidanta mu ɗaukota tazo nan mu rayu tare nasan itama tana sona!"  cikin murya me tsananin rauni yake faɗan maganar..

Kai kawai Abid yake girgizawa azuciyarsa kuwa wutar tausayin Zaid ne ta kunno, So yamakantar da zuciyar Zaid yasanya harya kasa tuna cewa Zahrah a yanzu ta haramta a garesa, shi duk iskancinsa baya tunanin Zaiso matar da take da aure,  dukansu shida Zaid sunsani cewa shangiya da zina duk haramunne amma kuma saboda son zucia irin tasu suke aikatawa,  yanzu kuma ga wani sabon saɓon da Zaid yafito dashi, yana goya masa baya akan komai, amma a wannan karon kam baya tunnin zae goya masa baya yaci gaba da son matar aure, haƙiƙa Zahrah takai macen da kowani ɗa namiji zai sota, amma kuma tunda ayanzu tazama mallakin wani babu amfanin Zaid yata takura kansa akanta.   "Zaid!" Abid yaƙira sunansa araunace.  Kansa kawai ya ɗago ya kallesa batare dayace dashi komai ba.  

"Kada kaga laifina Zaid, mun hau wani mataki da yanzu dole ne  mufaɗawa kanmu gaskiya, menene ribar da zakasamu idan kacigaba da dakon soyayyarta acikin zuciyarka? tazarar dake tsakanin ka da Zahrah a yanzu yanada matuƙar yawa,  tana tare da mijinta kuma nasan zuwa yanzu tajima da zama shi kuma shima yazama ita, me yasa to kowannan bai isa yasanya kacireta acikin zuciyarka ba, akoda yaushe kada kana tunanin cewa wai Zahrah zata dawo gareka,  so ne yasa mijinta ya aureta, kaga kenan haka nan kawai bazai rabu da ita ba, kasa aranka ma idan ƙaddara ta rabasu babu yiwuwar Zahrah zata amince ta aureka,  kai da kanka kasan haka amma zuciyarka tana yaudaranka, haƙiƙa nima shaidane akan cewa har yanzu Zahrah tana sonka, amma hakan bawai yana nuni da cewa zata iya kashe aurenta ta aureka ba ne, kai koma da ace tafito agidan aurenta to bana tunanin Zahrah zata amince ta aureka,  kamanta da ita Zaid, kasawa zuciyarka salama, akwai mata da yawa acikin ƙasarnan dama sauran wasu ƙasashen kasamu wata kabawa ajiyar zuciyarka, na tabbatar watarana komai zai zamo labari!" Abid yaƙare maganar yana me dafa ka faɗan Zaid almar son ƙarfafa masa guiwa..

Wata tsuka me ƙarfi Zaid yaja haɗe da ture hanun Abid dake kan kafaɗansa...    har abada bazai daina yiwa wanda yace yarabu da Zahrah kallon mahaukaci ba,  wai Zahrah'nsa ake so yamanta ya daina sonta, sai yaushe mutane zasu gane cewa cire so bakamar cire takalmi bane? miƙewa yayi daga zaunen da yake   haɗe da shigewa cikin bathroom ko sake kallon inda Abid ke zaune baiyi ba.. Ajiyar zuciya Abid ya sauƙe  haɗe da gyara zamansa akan kujeran, yana nan yanajiran fitowarsa koda awa ɗaya zai share a banɗakin bazai tafiba saiyajirasa,  Zaid bayason gaskiya wani lokaci, kuma kozai mutu saiya faɗamai gaskiya, ae soyayya ba hauka bane, son matar aure mezai jawo maka inbanda wahala da ƙarin zunubai....

Zaid kuwa yajima tsaye ruwa na fitowa daga  shower yana dukan jikinsa....  Ɗaure da towel a ƙugunsa yafito daga cikin bathroom ɗin,  kallo ɗaya yayiwa Abid yaɗauke kansa,  Abid na kallonsa   har yagama shafa man lotion ajikinsa...

"Saboda nace kamanta da Zahrah shine kake fushi dani? kai kanka kasan abun da kakeyi ba daidai bane Zaid sannan....."

"Ya isa Abid!" Zaid ya katsesa aɗan kausashe. 

Murmushi kawai Abid yayi haɗe da sa kai yafice daga cikin ɗakin, yasan Zaid ya hau sama bazai taɓa sauraransa ba, wanda yayi nisa bayajin ƙira.

****

Tun fitarsa ta shige cikin kitchine  yau bataso ya sayo musu abinci tafiso ta girka musu da kanta,  fried rice tayi wanda taji zallan tsokan kaza,   da kanta ta haɗa shaka ta sanya acikin fridge, takammala komai yanzu saura kawai tayi wanka.. Ƙaran wayarta take ta jiyowa, da sauri tanufi ɗaki inda wayartata take.  Wata number ce  special ke yawo akan screen ɗin wayar, ɗan tsayawa tayi tana ƙarewa number'n kallo, har ƙiran ya katse bata ɗauki wayarba, wani ƙiranne kuma sake shigowa.... A hankali ta ɗaga wayan ta kara akan kunnenta.   

"Zahrah!!!" taji wata murya wacce bazata taɓa mantawa da itaba ta ƙira sunanta, jikinta ne yasoma rawa yayinda bugun zuciyarta yaƙara tsananta shin dagaske ne kokuwa kunnuwanta ne basuji da kyauba,  kusan mintuna biyar ba asake cewa komai daga cikin wayarba haka kuma itama bata ce komaiba..

"Wa....y..e?"

tayi tambayar cikin wararrun kalmomi yayinda tsoro ke sake É—arsuwa acikin zuciyarta.

"Zahrah na! me yasa zaki barni? kin barni cikin ƙunci da tarin damuwa, yazanyi da soyayyarki ne Zahrah, bazan iya rayuwa ba idan babu ke, please ki taimaki rayuwata dakuma zuciyar da ta jima da matowa akan ƙaunarki!!"

Jikinta ne gaba ɗaya yaɗauki rawa harbatasan sanda wayar ta zame daga hanunta ba, take ta faɗi ta tarwatse a ƙasa.  Itakanta batasan sanda ta zame ta durƙusa guiwowinta a ƙasa ba,  hawayene suka shiga fitowa daga cikin idanunta.   "Zaid" shine sunan da take ta nanatawa acikin zuciyarta, sai yaushene Zaid zai barta ta huta tayi rayuwar aurenta cikin nutsuwa? anya kuwa Zaid baisamu matsalan ƙwaƙwalwa ba? ta tambayi kanta, shiru tayi haɗe da lumshe idanunta ƙirjinta kuwa har yanzu bai daina bugawa da sauri ba.   

Cikin tsananin mamaki yake kallonta, da sauri ya ƙaraso inda take durƙushe haɗe da tsugunnawa yaɗaura hanunsa akan kafaɗunta
"Meke faruwa?" yatambayeta cike da kulawa.

Da sauri tabuÉ—e idanunta da suke a lumshe, batasan yaushe yashigo ba.
Kallonta yakeyi sosai da alama amsa yakeson ji daga bakinta.

Dasauri tashiga goge hawayenta haɗe da tashi tsaye,   kallonta yakeyi harta shige cikin toilet,  idanunsa yasauƙe akan wayarta wanda ta tarwatse akan tiles gaba ɗaya ma screen ɗin wayar ya fashe, mamaki  haɗi da ɗaurewar kaine matuƙa suka kamashi, "Meya faru? yaganta tana hawaye gakuma wayarta daya gani aƙasa a tarwatse"  yayi mawa kansa tambayar cike da son sanin amsa. Tattare wayar yayi haɗe da komawa kan gado ya zauna zuciyarsa cike fal da tarin tambayoyi..
Chapter 83 · 0% Book details