Sashe 9
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaban Malam Manu yayi wata irin bugawa,jikinsa yafara rawa cikin sauri yataka burkin mota yafashe da wani irin kuka,cikin sauri motocin dake biye dasu na security suma suka taka burki sannan suka futo da sauri suka fara duba motar ko wani abu ne yasamu Alhaji Mekudin.
Alhaji Mekudi yazuge glass d'in motar yayi qasa,sannna ya kallesu yace"no problem we're fine"
Security suka juya cikin sauri suka koma motarsu,Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya ya kalli Malam Manu, wanda kai tsaye bazai ce Malam Sulaiman ba saide Man Sulaiman, yace"Man Sulaiman meyake faruwa haka?kode nayi laifi ne dalilin tambayar danayi ma?"
Cikin sauri Malam Manu ya girgiza kansa,sannan yashare hawayen idonsa yace"kodaya Alhaji,bakamin laifin komai ba Alhaji,tsakanina dakai saide nace Allah ya azurtaka da Aljanna mad'aukakiya,Alhaji kakaini Hajji,kakaini Umara,kabani muhalli nazauna tare daku,kabani ci da sha da kudi,saide duka abinda nasamu banida kwanciyar hankali,haqqin iyalina yana nan yana kan bibiyata,bana cikakkan kwana uku banyi mummunan mafarki ba"
Alhaji Mekudi yace"subhanallah duk me yayi zafi haka?"
Malam Manu yace"Alhaji na gudu nabar iyali na da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe,talauci yamin katutu,bamuda cin yau bamuda na gobe,har takai takawo idan naci bashi banida wanda zai biyamin nima bazan Iya biyaba saide ayimin dukan kudin,iyayen Bilkisu sun damqamin amanarta a hannuna kafin su rasu,naci amanar Bilkisu natafi nabarta,bansani ba tana raye kota mutu,abinda tahaifa yana nan koya mutu,duk lokacin dana daura aniyar zuwa gida sai inji gabana yana faduwa inji tayaya ne zan iya kallon Bilkisu in fuskanceta in nemi yafiyarta?
da hannunta take aikin qarfi tatara mana kudi muyi buqatun gida dashi,kai hatta kudin motar dana samu nagudu Lagos itace tabani su alokacin kudin sunada daraja tace nafara tarawa dan musamu abinda za'a yankawa yaron cikinta na suna,Bilkisu tanada haquri,ta yarda dani,tana mutuqar sona amma duka na rusa komai,bazan iya kallon idon Bilkisu ba,hakan yasa nakasa zuwa gida nazauna anan ina jira kafin Allah ya dauki raina"
Alhaji Mekudi yacire medical glass din idonsa yagoge qwalla sannan yamaida glass din yace"Ash'sha,Man Sulaiman kayi kuskure,ai ba'a gudun annoba,Allah yana sane da halin dakuke ciki especially ma kaida Allah ya azurtaka da mace irin wannan,ya kamata ka shirya kaje ka fuskanci iyalinka karoqesu gafara sannan ka daukosu kudawo nan gaba dayanku"
Malam Manu yagoge hawayen idonsa yace"to Alhaji,insha Allah zanyi yanda kace, nagode"
Daga nan yaja motar suka qarasa wajan d'aurin auren,saide kafin su qarasa har anriga an d'aura sai gaggaisawa dasukai da mutane.
Da daddare wajan qarfe takwas,Alhaji Mekudi yana zaune acikin tangamemen falonsa na sama,wanda yaji wasu lafiyayiyun kujeru 'yan gajeru ruwan cement,fruit ne agabansa yanasha yayinda Hajiya Zaliha take gefensa a zaune tana ganin labarai a bbc.
Tasake zama hamshaqiyar uwa matar Alhaji,haka kuma uwar Alhaji,wuyanta da zoben hannunta da awarwaron hannunta gaba daya na gold ne,stone work din jikinta sai walwali yake.
Alhaji Mekudi ya'ajiye fork din hannunsa wanda yake daukan apple dashi, ya kalli Hajiya Zaliha yace"d'azu munyi magana da yaron ki,nayi masa maganar aure yace yabamu dama munema masa,lokaci yayi daya kamata ace yayi aure,muma muga 'yan jikokinmu agidan"
Hajiya Zaliha tasaki murmushin farinciki sannan ta d'aga hannunta sama tace "Alhamdulillah,Alhamdulillah,yau-yau d'innan kuwa zansa abinciko min yaran garinan,daga kan 'ya'yan 'yan kasuwa har zuwa na siyasa duk zanyi magana sai muga wacece ta dace dashi"
Alhaji Mekudi yagyad'a kansa cikin gamsuwa da bayanin nata yace"hakan yayi,nima munyi magana da Aminina Alhaji Auwal,saboda haka zan kira Jawad d'in insashi yakira can Nijar d'in su gaisa da Fauziya da Ummi ko za'a dace sai muyi musu had'in gida"
Hajiya Zaliha tace"hakanma yayi,nima daga nawa 6angaren zanta bincikawa,har muga abinda hali zaiyi, idan yaza6i 'ya'yan Alhaji Auwal d'in shikkenan,idan kuma na nan Nigeria yaza6a shikkenan"
Sunacikin wannan farinciki gidan tv na bbc suka fara karanta labarin Babban matashin d'an kasuwa Jawad Mekud'i yabiya wa yaran talakawa daliban University's kudin registration kimanin naira million talatin.
Alhaji Mekudi yayi murmushi yad'auki wayarsa yakira Jawad,bugu biyu Jawad yad'auka,cikin miskilancinsa kamar bayason yayi magana yace"Daddy..."
Alhaji Mekudi yace"yanzu nake ganin labarai kabiyawa yara kudin Registration,ka kyauta sosai,musanman yanzu dana samu labari ana cewa kud'in karatun yara yaqaru,kaci gaba da taimako idan da hali,na tabbatar kaima Allah zai taimaka maka"
Cikin tsananin biyaiya yace"ok Daddy insha Allah"
Alhaji Mekudi yasake cewa "yawwa idan kasamu dama kakira Babanka na Nijar yanzu-yanzu ku gaisa"
Cikin mamaki Jawad yace"Daddy Babana?"
Yayi tambayar cikin sigar rashin gane wanda ake magana a kansa.
Alhaji Mekudi yagane hakan,dan haka yace"Aminina Alhaji Auwal na Nijar"
"Daddy i don't have...."
Cikin sauri Alhaji Mekudi ya katse shi yace"you don't have his number,hakane?"
Cikin sauri Jawad yace"Yes Daddy"
Alhaji Mekudi ya girgiza kansa yace"you don't have a girl friend,you don't have his number,Jawad kai shikkenan komaima babu?,rayuwa zata iyu da haka? kaida ya kamata ace kacemin kanada number sa kana kiransa ma kuma gaisawa, wanne irin zumunci ne wannan,?zan turoma number sa yanzu,saika kirashi"
Yana fadin haka yakashe wayar, Jawad ya lumshe idonsa mecike da jin bacci,dan yanzu haka qarfe goma shadaya dayane na dare a agogon qasar Dubai.
Bayan yagama waya da Jawad kai tsaye Alhaji Auwal yakira, bayan sun gaisa yace masa "nasa Jawad yakira ka,idan yakira,ka had'ashi da yaran gaba d'ayansu su gaisa ko Allah zaisa su daidaita kansu da d'aya daga cikinsu"
Alhaji Auwal yayi godia daga nan suka kashe wayar.
Bayan Alhaji Mekudi ya ajiye wayarsa agefe Hajiya Zaliha tagyara zamanta ta kalleshi tace"Alhaji yaron nan fa yana kashe kudi dayawa"
Alhaji Mekudi yayi mata wani irin kallo sannan yace"gaskiya kam,amma kuma maimakon raguwa kullum kud'in sake qaruwa suke,kinga amfanin taimako ko?"
Hajiya Zaliha tayi wani irin murmushi mai ciwo ganin cewa cikin hikima Alhaji Mekudi kamar magana ya gwa6a mata,kokadan bataji dadi ba,tasaki ajiyar zuciya tasake cewa"to Alhaji mezai hana muyiwa Jawad magana Fu'ad ma a bashi wani 6angare na dukiyar yana juyawa?"
Kai tsaye yace"Fu'ad be goge akan kasuwanci ba"
Cikin damuwa ta sauya salon zancen nata tace"hakane,to amma Alhaji aikin yayiwa Jawad yawa,kana gani kwata-kwata baya samun damar da zaizo ya zauna tare damu,yaron nan tun yana qarami kakaishi wata qasa ka ajiye,yagama karatu ka d'orashi akan harkokin ka nacan,qarshe ma duka dukiyarka ka maidata hannunsa komai da komai yazama nasa,tokai mezai hana ka dinga tayashi dawani abun ko shima zai samu ya huta ya dinga zuwa gida muna ganinsa akai-kai yanzu fa tsakaninmu da d'anmu saide gani daga nesa,saide mu ganshi a tv"
Alhaji Mekud'i yasaki ajiyar zuciya sannan ya fuskanceta yace"nina tsufa,har yaushe ne zanci gaba da wannan harkar kasuwancin? Fu'ad kuma bai karanci kasuwanci ba idan zaiyi kasuwanci ma saide yayi abu daka,Jawad d'in de shine matashi beyi yarinta da kasuwanci da gwagwarmaya ba kuma baiyi tsufa ba,shine matashi sabon jini wanda zaiji da matasa da manyan 'yan kasuwa,ina ganin mubarshi yayi abinda yaga yadace kawai, maganar namaida sunansa akan dukiyata kuma idan kin manta bari in tuna miki yaron nan karki manta bashida gadona ko d'aya,kuma dukiyar tareda shi na tarata,abar maganar dukiya ko wani qyale-qyalen duniya ma mune iyayen Jawad,bayan mu bashida kowa,sannan karki manta Fu'ad da Jawad abu d'aya ne,yarannan sun taso suna son junansu,ko bayan babu ranmu NI DAKE,nasan cewa Jawad zaici gaba da kulawa da dan'uwan sa,hakane?"
Sai alokacin Hajiya Zaliha tasaki wata irin ajiyar zuciya,sannan tace"eto hakane kuma,to shikkenan,Allah ya tayashi ruqo,Allah yatemaka"
****
Acan Dubai kuwa Jawad yasa p.a dinsa yakira masa number da Daddy yaturo masa,kasancewar Alhaji Auwal yasan da kiran nasa hakan yasa bayan sun gaisa dashi yakira yaransa 'yanmata guda biyu yace"ku kar6i waya ku gaisa da yayanku"
Babbar ce tafara kar6a wato fauziya,ta gaida shi taji baya magana dajan zance irinna samari daga lafiya,sai kina karatu ko?,sai ok.... (♀️🤭)
To itama dayake bawani yawan magana ne da'ita ba kasancewar ta 'yar Alhaji Auwal babban attajiri a qasar Niger,abunka da 'ya'yan manya tataso cikin gata,sai kawai tace masa "ga qanwata Ummi bye bye" (🤭)
To itade Ummin tad'an jashi da surutu har tana tambayarsa yaushe zaizo qasar tasu,kasancewar bai iya qarya ba hakan yasa babu 6oye-6oye yace mata "babu rana"(🙆)
Baby dake zaune agefe 'yar gidan Antyn su ce,jikar gidan ce,tana zaune agefe tana jinsu dataga zasu kaiwa Alhaji Auwal waya cikin sauri ta wullar da teddy din hannunta tace"Anty Ummi bani shi,bani shi"
Ummi ta kalli Baby da sauri tana ganin ikon Allah, tasan halin Baby da surutu amma batayi tunanin abun nata yakai haka ba,babu musu tabata wayar.
Baby ta kara wayar a kunnanta tace"Hello Yaya,ni ba kace abaka niba gashinan ni nace subani kai,Sunana Baby"
Jawad yadaga girarsa guda d'aya yasaki wani miskilin murmushi,daga ji yarinyar irin yaran nan ne masu surutu da shiga rai,ahankali yace mata "ni Sunana Jawad Mekudi"
Baby tace"nasani,Yaya Jawad kasan me?jiya aka kaini wajan wasa,nayi wasa nahau doki,saboda nice nazo ta d'aya a ajinmu,kai nanawa kazo?"
Jawad yayi murmushi yace"nine na biyu,kinga kece first nikuma second"
Baby ta qyalqyale da dariya tace"to kaima ankaika wajan wasa ne?"
Wannan lokacin ma murmushi yayi yace"Daddy na bekaini ba, yace dole sainazo na d'aya,amma zan dage next time naqwace miki position d'inki nima sai akaini wajan wasa"
Baby tace"tabdi,wallahi bazan yarda ba,to bari kaji Kullum idan Uncle Farouq yazo nice nake fara yimasa bayanin lesson d'in dayayi mana abaya,nafi kowa qoqari,bazaka qwace min position ba"
Kai tsaye Jawaad yace mata "waye Uncle Farouq?"
(masu karatu Uncle Farouq d'innan da yarinyar nan take maganar sa shine Farouq mahaifin Inaas,Qanin Bilkisu me gwanjo,inba ku manta ba nace muku yana yiwa yaran Alhaji Auwal lesson,yawwa🤒)
Baby tace"shine yake mana lesson,shima yace nice best student d'insa"
Jawad yayi murmushi ya girgiza kansa yace"ok,tokici gaba da karatu,idan kika sake zuwa ta d'aya zan kawo miki chocolate da kaina"
Cikin murna Baby tasakar masa kiss ta wayar sannan tatafi da gudu ta kaiwa Alhaji Auwal wayarsa.
*** *** ***
Abuja Nigeria