← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 63

Sashe 24

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

P.a yayi sauri yakira masa manager,bayan manager yadauka Jawad yakirashi da asalin sunansa yace"Ilyasu"

Manager yace"na'am Yalla6ai"

Jawad yace"yarinyar nan da'aka kora yakamata tadawo bakin aiki"(🤭)

Ilyasu manager yace"to Yalla6ai angama"

Jawad yayi shiru nawasu second,shibe kashe wayar ba,shi beyi magana ba, haka shima manager daga nasa 6angaren bashida ikon dazai Iya kashewa Yalla6ai Jawad waya,haka yatsaya qam da waya a kunne.

Saida yadauki minti d'aya, sannan yasake cewa "ilyasu"

da girmamawa manager yace"na'am Yalla6ai"

Jawad yace"ba aikinta nada zata koma ba,Ina nufin abata aiki mekyau,babban office inda yadace". (🙆🏻‍♀️🤭)

(manager yau kaga ta kanka kaima😂irin wannan kira haka)

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

17&18

Lokaci d'aya ilyasu manager yagano shi,yayi murmushi ya jinjina kansa yana tunani tofa shi da alama lokacin qarin girman sa yazo,to amma lokacin daya koreta daga aiki aibata zo kamfanin ba, a'ina yaganta? a'ina suka had'u? to koma de menene yakamata ya dinga shigewa yarinyar nan idan tadawo bakin aiki ko Allah zaisa shima asan dashi(🤭)
cikin ladabi yace"to Yalla6ai,yanzu-yanzu za'a tura mata letter tadawo bakin aikinta"
Jawad baice komai ba yakashe wayar yana sakin wata irin ajiyar zuciya,sai yaji ransa yayi sakayau kamar yasauke wani nauyi daga kansa,daga nan yayi gaba domin zuwa daki yayi wanka ya shirya kafin lokacin yin break fast dinsa yayi.
P.a yayi murmushi ganin tabbas da gaske Yalla6ai Jawad yakamu da soyaiya,ko banza shima zai d'an huta da wannan aikin nasu dasuke fama dare da rana babu hutu inda ace sunada iyali to wataran za'a ce adan huta saboda a kula da iyali,ya sunkuya yadauki computer Jawad din sannan ya biyo bayansa.

*** *** ***

Niger Republic

Qarfe tara na safe,suka jiyo ana doka sallama a qofar gidansu,Bilkisu datake gyaran waken awara tad'aga murya tace"Inaas zoki duba ana sallama"

Inaas tafuto daga daki tayafa mayafi ta leqa qofar gidan,wani matashi tagani a tsaye ya jingina da motarsa, ta kalleshi tace"kaine kake sallama?"

Yace" eh, dama daga kamfanin Mekudi Oil ne,akace nakawo miki wannan letter,koba kece Madam Inaas ba?"

Inaas ta kalleshi dakyau tace"nice Inaas de,amma ba madam ba, muga wasiqar" (😂)

Yabata takardar hannunsa wanda manager da kansa yazauna ya rubuta yakuma gargad'eshi akan ya girmamata idan yakai mata,sannan yayi magana da'ita cikin ladabi domin itadin ba qaramar mace bace yanzu.

takardar tagama karantawa tsaf, sannan ta kwashe dawata irin dariya tace"waini za'a yaudara"
ta kalleshi tareda bashi takardar tace"kakoma ka cewa wanda yabaka wannan saqon inada hankali,baza'a min shigo-shigo ba zurfi ba"

Dan aiken yatsaya saroro yana kallonta,ita kuwa bata lura da kallon dayake mataba tasake yin wata dariya tace"tabdi,saikace wata marar wayo ni zan yarda inkai kaina inda za'a kashe ni"

Mekawo saqo yayi ajiyar zuciya yace"Madam manager nefa yabani saqon da kansa,kuma yace nabaki hannu da hannu,saboda haka saqo yazo hannun ki,ni kinga tafiya ta nabarki lafiya"

Yafadi haka yana qoqarin juyawa zai shiga mota,Inaas tace"tsaya tsaya ka kaimasa takardar sa"

Bilkisu da taji shirun yayi yawa taqaraso bakin qofar gidan tace"meyake faruwa ne?"

Yajuyo ya kalli Bilkisu ya gaidata sannan yace"manager ne yabani saqo nakawo mata,shine tace lalle saina kar6a na maida masa,nikuma bazan Iya maida masa ba"

Bilkisu tace"jeka mungode"
Babu musu yashiga motarsa yatafi, tajuya ta kalli Inaas tace"takardar menene?"

Inaas tabata takardar tace"duba kigani Ammiy waini za'a rainawa hankali saikace marar wayo"

Bilkisu tace"takarda duk turanci mezan fahimta aciki? kifadamin ta mecece?"

Inaas tace"wai turomin sukai in koma bakin aikina,kuma Ammiy kingani fa harda qarin matsayi tsabar yaudara,sarai nasan cewa wannan Jawad din dayazo rannan shine yayi wannan aikin,ai yajini lokacin danake cimasa mutunci,so yake na koma inyaso idan naje su had'u sukamani sumin shegen duka,ni kuwa babu inda zanje Ammiy"

Bilkisu ta kar6i takardar ta kalla kamar tana fahimtar abinda aka rubuta sannan tadago kanta ta kalli Inaas tace"kin tabbatar abinda yake cikin takardar kenan aiki suka maida ke da gaske?"

Inaas tace"emana,gashinan harda haquri suka bani akan korar dasuka min"

Bilkisu taja hannunta suka dawo cikin gida suka zauna sannan tace"toke wannan ai abun farinciki ne Inaas,na tabbatar yaron nan Jawad ba zaice ki koma aiki kawai danya kamaki ya dakeki ba,idan yayi niyyar dukanki ai yasan gidanku,har nan zaizo yakama ki yadaka,yaron nan yanada nutsuwa Inaas, kuma yanada hankali,sannan yasan Alkhairi, da alama shimfidar fuskar dana masa ne yasa yace kidawo bakin aiki,ai kinga amfanin mutunta d'an Adam ko?"

Inaas tayi shiru tana nazari,tayi ajiyar zuciya tace"to Ammiy ai nayi tunani dukana zaisa ayi,saboda ranar nan har cemasa nayi yana kama da 'yan dambe,yace zai dakeni nace tome yake jira yadaken mana"

Bilkisu tazaro idonta waje tace"wai keda shidin duk kukai hakan?"(😳)

Inaas tafara zare ido alamun tsoro kana ganinta kasan a tsorace take,tace" eh wallahi Ammiy,kuma bakiga dantsan hannun saba gabjeje lokacin daya fara cire suit dinsa ya'iyo kaina, shiyasa nace miki da biyu aka turomin wasiqar nan, ni nasan mena aikata"

Bilkisu ta jinjina kanta sannan tace"kema na hanaki surutun nan naki kinqi ji,dan Allah kidinga sawa bakinki linzami,ki shirya gobe kije aikinki, amma de ki kasance a ankare,dakinga wata alama ta duka toki fece,karki tsaya ata6a lafiyar ki"(😂)

Inaas ta jingina kanta alamun amsawa sannan tace"to Ammiy,aikuwa kinban dabara takalmi zansa marar tudu, zaifi dad'in gudu"

Suna cikin wannan zance Abban Inaas yadawo,Bilkisu ta zayyane masa komai shima yasake bata qwarin gwiwar zuwa kamfanin.

*** *** ***

Abuja Nigeria

Hajiya Zaliha tasake gyara daurin da kwalin kanta na gogaggun matan manya, yatsun hannun nan nata duk zoben gold,Jawad yana kwance a kujera yana kallon labarai, yayinda Fu'ad yake danna waya agefe,Daddy kuma yana gefen Hajiya Zaliha.

Biron hannun ta ta ajiye sannan ta kalli Daddy yace"Alhaji munyi magana da mahaifin Amal dakuma ita yarinyar,tace tana buqatar million goma na gyaran jiki,sannan zasuyi ladies party itada qawayenta gaba daya wajan partyn da abunda za'a ci asha zasu kashe million dari,sai bridal shower zasu kashe million hamsin,sannan tanaso ayi wasan polo zasuje su kalla itada Jawad din,shima suna buqatar kudi,sai maganar kayan lefe"

Tayi wani miskilin murmushi Sannan taci gaba da fadin"wannan kam bansan nawa zamu kashe ba"

Daddy yasha ruwan dake gabansa sannan yace"duk kudin dakuke buqata ki dauka kiyi uzurin ki dashi kawai,auren Jawad ne, dole zamu kashe kudi,yanzu ne fa zamu aurar da yaro muma, ranar damuke jira ce tazo, dole za'a yi abinda akeso, sonake duk qasar nan dama sauran qasashen duniya su san da wannan aure"

Fu'ad ya jinjina kansa yayi murmushi hankalinsa yana kan waya.

Shikuwa Jawad fuskarsa a cunkushe take, kokadan babu walwala kamar de yanda take kullum,ana magana akan aurensa amma kamar ana magana akan mutuwar sa.

*** *** ***

Niger Republic

"Farouq zuba cikon daga nan,wajan zaifi kyau sosai"
cewar Ammiy.

Farouq yasake debo wasu duwatsun yazuba a'inda ta nuna masa,yasake kallon tsakar gidan nasu koda wani wajan dayake buqatar ayi masa ciko, adede lokacin Inaas tadawo daga wajan aiki,Bilkisu tana ganinta ta qarasa wajanta tana kallon jikinta tareda fadin"babu wanda yata6a ki deko?"

Inaas tayi murmushi wanda yasake qara mata kyau sannan tace"Babu abinda akamin Ammiy,bakiga yanda ake ji dani ba,manager da kansa yaketa nan-nan dani,bansan dalili ba sai wani girmama ni yake, yanuna min sabon office dina,amma aikin da wahala saida yasake koyamin yanda zan dinga yi,Infada miki Ammiy office din ga esi,harda wani dan qaramin fridge aciki, ga ruwa da lemuka aciki,kingama nataho miki da wasu lemukan ma kema kisha,gobe ma idan na koma zan sake d'ebo miki wasu"(🙆🏻‍♀️)

Bilkisu tafara tafa hannu tana fadin"yanzu Inaas lemukan office din kika d'ebo?,Ina kikaga ana haka? oh ni Bilki me gwanjo yau naga takaina"

Inaas taturo bakinta gaba cikin shagwa6a tace"to Ammiy sai insha lemo kekuma inbarki baki shaba? nide gashinan ku shanye keda Abba"
Tafadi haka tareda ajiye musu lemukan sannan tawuce ciki.

*** *** ***

Abuja Nigeria
Chapter 24 · 0% Book details