← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 63

Sashe 22

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

___

Man Sulaiman yanajin duk abinda Jawad yagama fada akan irin matar dayakeso,lokaci daya matarsa Bilkisu tafad'o masa arai,yanda Jawad ya siffanta sai yaji gaba daya kamar siffar Bikisun sa yafad'a,cikin sauri yafaki idon yaran yagoge hawayen daya zubo masa.

Fu'ad dayayi tagumi hannu bibbiyu yana sauraren yayan nasa yasaki ajiyar zuciya yace"yaya,duk yanda ake fadar kyan Amal adangi to ko kama qafar wannan batayi ba,yanzu babu irin wannan yarinyar daka siffanta Yaya, babu irinsu ko kad'an "

Jawad ya kalleshi ya motsa lips dinsa kamar ba zaice komai ba,sai can kuma yace"akwai"

Fu'ad yace"amma larabawan qasar Dubai ko? yaya siffar aljana fa kagama zayyanowa"(😂)

Jawad ya motsa lips dinsa kamar zaiyi magana amma baice komai ba, ya lumshe idonsa yatuno Inaas,yasake tuno yanda ake turara mata wannan dogon gashin nata.

Yanaji Fu'ad yana cewa"ai Yaya yanda ka lissafo irin yarinyar da kakeson ka aura dinnan da'ace nima zan samu irinta tuni zanyi wuf da'ita"

Ya fadi haka yana kallon gefen Jawad sai yaga ashe ma idonsa a rufe yake, kenan shi yagama tashi maganar shikuma yaje yayi tayi ko?

Jawad kuwa Cikin ransa yake tunani, baisan menene soyaiya ba,baisani ba wanne alamomi zaiji domin yasan yakamu da son mace kobe kamu da son taba, abinda yasani kawai shine kasuwanci, dashi aka raine shi,tun yana yaro dashi yabude ido.

A hankali yabude idonsa ya kalli Fu'ad yace"Fu'ad wanne alamomi mutum yakeji yagane yanason mace?"

Fu'ad yayi murmushi ganin yau de yayan nasa da gaske yake, yagyara zamansa sannan yace" wow! Yaya gaskiya you're in love...,nafarko zakaji fad'uwar gaba, yawan tunanin yarinya, kaji komai tayi tana birgeka,kaji zuciyarka kanason kasancewa da'ita,kaji komai nata yana birgeka"

Jawad ya jinjina kansa yayi shiru kamar ba zaice komai ba, sai can yace"ok thanks"

Malam Manu dake driving duk yana jinsu,yayi tunanin Jawad din zai sake cewa wani abu kuma sai yaji shiru,Jawad kuwa lumshe idonsa yayi yana tunanin maganar dasukai shida Na'im,wannan kalmar da Na'im yafada masa rannan cewa he's in love, gashi yauma ita Fu'ad yafada mata,son qaryata abinda yakeji din yayi, hakan yasa ya girgiza kansa batare daya furta komai ba.

Bayan sunje wajan, saida suka gama uzurin su sannan suka juyo gida ba tareda 6ata lokaci ba.

Tunda suka dawo gida yashiga dakin karatu yafara aiki,yaduba wannan takarda yaduba waccen,yaduba computer yayi danne-danne,yakoma kan takarda, haka yamaida kansa busy sosai har zuwa dare wajan qarfe goma nadare yanata aiki babu abinda yake tadashi sai sallah, kasancewar yayi busy dayawa hakan yasa da daddare yagaji sosai, yana zaune afalon dakinsa p.a yana fada masa wasu bayanai idan yace a shigar dasu saiya amsa masa da baki, shikuma p.a saiya shigar.

Bayan sungama p.a yashiga yanar gizonsa zai duba saqonni,anan yaci karo da saqon wata sabuwar number,kai tsaye yaduba sunan wanda yaturo saqon anan yaci karo da sunan Amal,tun bayan lokacin da'aka sakawa ubangidan nasa rana yake jin sunan Amal din, hakan yasa cikin girmamawa da farinciki ya kalli Jawad yace"yalla6ai madam taturo saqo"

Jawad daya jingina ajikin lafiyaiyar kujerar falon ya lumshe idonsa yabude bakinsa kamar baison magana yace" who's she?"

P.a yace"Madam Amal"

Jawad dayaji sunan saida ya danyi jimmm sannan yayi ajiyar zuciya yace"kuyi magana"

Mamaki yakama p.a, yayi wani sararo yana kallonsa,matarda zai aura guda? anya kwa Yalla6ai yanason hadin nan?
ganin bashida damar yimasa wannan maganar hakan yasa p.a ya amsa mata sallamar tata sannan yace"yakike?"

Daga 6angaren Amal datake kwance male-male akan lafiyaiyan gadonta tace" I'm fine Yaya Jawad,Mummynku tacemin zakazo na shirya zuwanka,but bakazo ba,yakamata kazo Ina missing dinka"

tatura masa saqon sannan tasake rungume fillo tana jiran reply dinsa.

P.a ya dan kalli Jawad yaga har yanzu idonsa a lumshe,yanaso ya tambaye shi wacce amsa zai bata? zaije dinne kokuma zai bata lokaci ne? ahankali yayi gyaran murya sannan yace"yalla6ai tace tana kewar ka,sannan Hajiya tace zakaje amma baka samu zuwa ba wai yaushe zakaje?"

Idonsa har lokacin a lumshe yake,yabude bakinsa ahankali yace"kace mata ( koh?)"

(koh?) p.a ya maimaita Kalmar a bakinsa, yanzu duk wannan dogon jawabin datayi amsar itace 'koh?'

Babu yanda ya'iya haka ya turawa Amal amsa yace"koh?"

Amal tasaki wani irin murmushi sannan tafara typing cikin sauri tabashi amsa tace"ina so kazo naganka,ko abokinka, zamuyi maganar anko"

P.a ya kalli Jawad yace"yalla6ai madam tana so taganka,zakuyi maganar anko"

Idanun Jawad a lumshe yace"banda lokacin zuwa p.a,nawa take buqata?"

P.a ya kalleshi da sauri yaga idonsa a lumshe har yanzu,Amarya guda ace babu lokacin zuwa wajanta?, Anya?🤔

Ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan ya janye idonsa daga kan Jawad yamaida kan wayar hannunsa ya turawa Amal cewa"nawa kike buqata?"

Amal taga amsar tayi murmushi tace"million daya"

P.a yasake kallon amsar data bashi,ya daga kafadunsa alamun babu damuwa sannan ya kalli Jawad yace"yalla6ai tace 1 million"

"kafada mata Mummy zata bata"
Cewar Jawaad.

P.a yatura mata amsa,bayan tagani tajuya fararan idonta sannan tasake turo masa wani saqon tace"to yaushe zakazo? inaso musha ice-cream tare"

P.a yayi murmushi bayan yagama karantawa,da alama madam din tasu batasan waye ogan nasu ba,Ina Yalla6ai Jawad yaga lokacin ire-iren wannan abubuwan?
duk da yasan cewa abu ne me mutuqar wahala hakan ta'iyu,baiyi qasa a gwiwa ba ya kalli Jawad yace"yalla6ai Madam tace tana so kusha ice-cream tare"

Sai alokacin Jawad yabude idonsa me cikeda gajiya,ya kalli p.a yace"Ina naga lokacin fita shan ice-cream p.a? ko batasan cewa chat dinma badani take yiba? kafada mata banda lokaci,shi kansa chat dinma banda lokacin sa dakai take magana"(🙆🏻‍♀️😳)

P.a de yayi shiru yana sauraren Jawad,tayaya zai fada mata haka ai da nauyi, ba zataji dadi ba, danhaka saiya tura mata "lol"

Amal ta karanta amsar da'aka bata,tasake turo wani saqon tace"da alamu bazaka samu zuwa ba,baka tambayi photo naba?"

P.a ya kalli Jawad yace"yalla6ai Madam tana neman iznin turo photo,taji baka tambaya ba"

Ataqaice Jawad yace"taturo"

P.a yafada mata,aikuwa dama kamar jira take taturo wasu shedanun pictures,p.a yana bude photunan yazaro ido jikinsa ya dauki rawa ganin duk rabi nonuwanta sun futo waje,hannunsa yafara karkarwa yana qoqarin bawa Jawad wayar, Jawad da baisan halin da p.a yashiga ba ko ajikinsa,p.a yamiqo masa wayar yace"yalla6ai gashi taturo"

Jawad bai kar6i wayar ba yace"kaduba photon kagani tana da gashi har gadon baya?"

Cikin sauri p.a dayake Allah-Allah Jawad ya kar6i waya ya girgiza kansa yace"a a Yalla6ai gashinta bekai gadon baya ba"

Jawad yasake cewa"bakinta dan qarami ne?"

Nanma p.a yace"a a Yalla6ai"

"Yaya kalar fatar ta?"

Cikin sauri p.a yace"fara ce Yalla6ai, ga wayar duba kagani da kanka"

Yabashi wayar jikinsa yana rawa cikin sauri yafice daga falon nasa yana mamakin wannan Amarya ta Yalla6ai Jawad,kawai daga cewa turo photo saiki turo irin wannan photon tun kafin ma a daura auren?

Jawad ya yashiga yaduba photon nata yaga kwata-kwata batada abubuwan daya lissafa irinna yarinyar nan ta qasar Niger(🤭)

Yadauke idonsa daga kan fuskarta yamaida zuwa suturar jikinta anan yaci karo da manya Mayan nashanun ta,saida gabansa yayi wata irin fad'uwa,saboda bayason ganin irin wannan photunan yasan cewa shi mabuqaci ne, yanzu ma dabaya kalla kusan kullum yana fama da shan magani inaga kuma yana ganin irinsu?
Kai tsaye yayi mata reply yace"thanks"
Sannan yagoge chatting din gaba daya ya lumshe idonsa yafara tunani,dama haka ake soyaiyar? babu wani nishadi da mutum yakeji?
ajiyar zuciya yasauke,sannan yatafi tunanin inda zuciyarsa tafi karkata wato wajan yarinyar nan ta qasar Niger.

Yadade yana tunanin Inaas,lokaci daya maganar Fu'ad tafad'o masa,lokacin dayake cemasa ( duk yarinyar dakake so zakaji kana yawan tunaninta...)

Cikin sauri ya girgiza kansa,a fili yace"kai bahaka bane..."

*** *** ***

Niger Republic

Tana zaune tazubawa kayan gwanjon dayake gabanta ido,gidan tela zata kai za'a rage wand'anda Bilkisu take d'ad'd'aga wa tana nuna mata"Kinga wannan kar arage shi dayawa,manya zasu iya sakawa"

tasake d'aga wasu kayan tana nuna mata tace"wannan kuma kinga ai madedeciya ce,sai arage ta sosai masu yara zasu siya"

Inaas tagama jin bayanin nata, tayi ajiyar zuciya tace"Ammiy wai dan Allah ahaka zamu qare ne? mu kenan kullum tallar gwanjo nida nakeso musamu kudi dayawa a sauya wannan kayan dakin namu,da wannan cinikin gwanjon tayaya zamu samu kudin?"
Chapter 22 · 0% Book details