← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 63

Sashe 7

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan yayi shiru itama Jamila tad'ora daga inda yatsaya,haka suka zauna su biyun sukai amfani da kalamai masu dad'i da hikima suna yi mata nasiha suna qara lallashinta.
Aranar babu inda Farouq yasake fita,yazauna agida yana taredasu,sai yamma yafita kai tsaye yaje wajan limamin unguwarsu yayi masa bayanin halin datake ciki,yanemi yabashi taimakon wasu addu'o'in wanda zai dinga yimata ko Allah zaisa ta kwantar da hankalin ta,babu musu kuwa liman yazauna ya rubuta masa addu'o'i kala-kala,sannan yayi masa rubutun dangana yace akai mata tasha, sannan kullum ya dinga zuwa yana kar6a mata rubutun.

hakan ce ta kasance kuwa,kullum Farouq zaije wajan liman ya kar6o mata rubutu,agabansa zata shanye sannan ne hankalinsa zai kwanta,cikin ikon Allah da taimakon Farouq Bilkisu tafara dawowa cikin nutsuwarta,tadena suma tadena kuka.

****

Haka kwanaki suka dinga tafiya suka koma satittuka har zuwa watanni,acan Nigeria kuwa har Jawad yafara rarrafe,abincin sa idan za'a bashi ma'aikata kusan guda uku ne suke kula da abincin,idan yafara 6arna babu wanda yake masa magana,ko anyi magana tofa Hajiya Zaliha zatace a barshi yayi wasansa qwaqwalwar sace take bud'ewa a wannan lokacin,ma'aikatan gidan mata suna so su dinga d'aukar sa saboda yanda yake basu sha'awa amma basu Isa su doshi inda yaron yakeba Hajiya Zaliha zata hana,komai sai ita,haka idan anayi masa wani abu kamar wanka kokuma idan yana wasa yad'an bige hannunsa yafara kuka,ma'aikaciyar datake kula dashi alokacin batayi saurin daukar mataki akan kukan Jawad ba, to kai tsaye Hajiya Zaliha zata koreta daga aiki,kwata-kwata batason ganinsa yana kuka,da Jawad yayi kuka gara taita korar ma'aikatanta.(🙆🏻‍♀️)

Lokacin da aka sakashi a makaranta yana playgroup motoci guda biyar ne suke kaishi,haka guda biyar ne suke zuwa d'aukoshi gaba d'ayansu security ne acikin motocin suna bashi kariya,har gaban motar Hajiya Zaliha zata kaishi tasa shi a motar har motarsu tafita daga get d'in gidan bata daina yimasa bye bye.

Lokacin daya fara koyon magana da sunan MAMA yafara a bakinsa,amma Hajiya Zaliha saita hanashi cemata Mama saide Mummy.

****
Niger Republic

Acan Nijar kuwa Bilkisu takasa sukuni, koda yaushe zaka sameta shiru babu um bare um-um,yauma photon Jawad ne a hannunta tana kallon photon da'aka yi masa tun yana jariri kafin subar jihar jigawa,photon ma ko kala babu irin farin photon nan ne nada fari marar kala.

Jamila datake zaune agefenta tana tufke dogon gashinta wanda yazo mata har gadon bayanta,ta kalli Bilkisu sannan tayi wani irin murmushi na damuwa,cikin lallashi tace"Yaya Photon nanfa ba yaron ne zai futo daga ciki ba"

Hawaye yazubo daga idonta,tasaka hannunta ta share hawayen " yatafimin da d'ana..."

Abinda tace kenan.

Jamila ta matsa kusa da'ita tace"Yaya kiyi haquri,kwana biyun nan kinsake saka damuwa aranki kamar baya,tun safe kin riqe photon nan kinkasa saka komai acikin ki ina tsoro kada ulser ta kamaki yaya"

Cikin sauri tasaka bayan hannunta ta share hawayen,sannan tamaida photon ma'adanar sa ta6oyeshi,ta dauki butar shayinsu ta zuba tafara sha.

****

Lagos Nigeria

Lokacin da Jawad yayi shekara uku,a lokacin yana yawo ko'ina yana gudu,haka kawai Alhaji Mekudi da Hajiya Zaliha zasu sa ad'aukeshi a kaishi wajan wasan yara,awajan wasan ma duk inda yatafi da gudu guard din dasuka rakashi suke binsa su kamo shi,ko da yaushe idonsu yana kansa saboda kada wani abu yasame shi,sosai suke masa gata kamar d'an shugaban qasa.

A shekarar 1996 Jawad yayi shekara goma,har zuwa wannan lokacin Malam Manu yana taredasu,yanzu yazama shine yakejan Alhaji Mekudi zuwa duk inda zasu.
Har zuwa wannan shekarun Malam Manu bai koma gida ba,bai nemi Bilkisu ba.
daga wannan lokacin ne kuma abun mamaki Alhaji Mekudi yake daukar Jawad da kansa ya kaishi kasuwa,ya had'ashi da wasu 'yan kasuwa su dinga d'ora masa tallar pure water,gashi tun yana yaro kasancewar kafin ya nemi abu anyi masa hakan yasa yazama baqin miskili,duk lokacin da Alhaji Mekudi ya kaishi yayi tallar pure water baya fad'awa Mummy,haka kullum yake sashi agaba ba tareda wasu security ba ya kaishi a wuni ana dora masa tallar pure water yana yawo dashi cikin kasuwa waje-waje yana siyarwa,saida yagama gogewa a fannin saida ruwa sannan yafara daukar sa yana kaishi wajan dako,kullum zai kaishi wajan 'yan dako yashiga cikinsu shima yayi dako yasamu kudinsa.

Da Hajiya Zaliha taga fitar tasu tafara yawa kai tsaye ta tambayi Alhaji Mekudi cewa Ina yake kai Jawad ne? Shima Alhaji Mekudi kai tsaye yafuto fili yafad'a mata wajan dako da tallar ruwa yake kaishi, Hajiya Zaliha tanajin haka tafashe da kuka harda shashsheka.

Alhaji Mekudi yakama hannayen ta yariqe ya sassauta murya yace"Zaliha, ki saurareni dakyau,sonake nakafa Jawad dakyau yanda zai zama cikakken mutum yasaba da gwagwarmayar rayuwa,abinda nake kaishi yakeyi yanzu nima dashi nafara har Allah yakawoni wannan matsayin a yanzu,inaso Jawad ya goge a fannin kasuwanci karki manta yaron nan shine goben mu,idan muka ce ahaka za'a ci gaba tayaya zaisan rayuwa har ya'iya kula damu idan muka tsufa?,duk abinda kikaga inayi kiyi haquri nasan kinajin ciwo to kiyi haquri ki kawar dakai"

Hajiya Zaliha bata sake magana ba, amma qunci iya qunci tana jinsa,a wannan lokacin ne kuma kasuwancin Alhaji Mekudi yasake ha6aka,yana harka da manyan mutane yasake bude wasu kamfanunnika a jihohi daban daban na Nigeria harma da qasashan qetare,yazama babban mutum ganinsa sai ansha wahala saboda yanda yamaida kansa busy saboda aikin,ya mallaki abubuwan duniya dayawa kama daga jiragen ruwa,dana sama,helicopter,babu wanda Alhaji Mekudi bashi dashi,ganin capital d'in Nigeria yakoma Abuja yabar Lagos kuma yana harkoki dayawa a Abujan hakan yasa suka tattara suka bar Lagos da zama suka koma Abuja.

Shekarar dasuka koma Abuja a shekarar Hajiya Zaliha tasamu ciki ta haifi d'anta namiji aka sanya masa suna FU'AD.

2003 Alhaji Mekudi yatura Jawad karatu qasar Italy.

****

Tsawon wannan shekarun Bilkisu ta d'auki dangana tasawa ranta haquri akan 6atan yaronta,Farouq yabata Jari taci gaba da saida kayan Gwanjo.

A da mutane suna cewa tanada nasibi akan saida kayan gwanjo bata tabbatar da haka ba sai yanzu,gida gida take shiga takai tallar kayanta kuma nan da nan kayan zasu qare tasake saro wasu,zamansu lafiya kalau itada Jamila,tana al'amuran rayuwarta cikin kwanciyar hankali saide fuskarta babu walwala,babu fara'ah,haka babu yawan magana,abinda tasa agaba kawai shine saida kayan gwanjo,nan da nan kuwa sunanta na BILKISU ME GWANJO yadawo.

Acikin shekarar 2005 Allah yabawa Jamila ciki,Farouq da Bilkisu me gwanjo sunyi farinciki,gaba d'aya su ukun kowa yana qoqarin ganin sun taru sun kula da cikin Jamila kasancewar sun dad'e shekara da shekaru babu haihuwar,cikin ikon Allah 2006 Jamila ta haihu,tahaifi 'yarta mace mai tsananin kyau kamar Jamila,babu abinda yarinyar ta d'auko na ubanta,komai da komai na Jamila ne,uwa uba gashin kan yarinyar yayi yawa,idan 'yan barka sukazo ba koda yaushe suke nuna yarinyar ba saboda bakin mutane.

Ranar suna aka sanyawa yarinya suna INAAS ma'ana (ME 'DEBE KEWA).

Tunda aka haifi Inaas Bilkisu tafara walwala saboda gani take kamar Muhammad d'inta ne lokacin dayake yaro,tana tsananin qaunar yarinyar, Jamila bata mata komai,kullum Bilkisu ce takewa Inaas wanka,wanki da duk wani abu daya shafeta.

2007 Jawad yagama Degree dinsa,adede lokacin shekarar Inaas d'aya a duniya,a wannan yanayin ne kuma tashin hankali ya sauka a gidansu Bilkisu,inda suka wayi gari sukaga Jamila tarasu sakamakon zazza6in kwana d'aya (😭)

Sun shiga tashin hankali sosai,daga nan ne ruqon Inaas yadawo hannun Bilkisu,Farouq yace yabata ita halak malak.

2010 Jawad yagama masters dinsa,alokacin shekarar Inaas hud'u,tayi bala'in wayo ga surutu kamar aku,gashi de gidan nasu babu mutane daga Bilkisu sai Farouq amma idan tazaro wata maganar tafad'a sai Bilkisu tayi mamaki.

Tun tana shekara hud'un gashinta ya sauko har d'uwawunta,haka Bilkisu zata sa abu ta rage mata shi saboda yayi yawa,rana guda take warewa tazauna kawai wannan ranar ta gyaran gashin Inaas ce,sau tari idan tana gyarawa yarinyar gashinta ba kowa ne yake zuwa ranta ba sai Jamila mahaifiyar Inaas,itama haka take fama da gashi kamar 'yar India.

Inaas tashiga ran Bilkisu,tanaji da'ita kamar Muhammad d'inta,ta shagwa6a yarinyar kamar goyon kaka,tun Inaas tana qarama Bilkisu ta lura yarinyar tanada masifar kyau mai fizgar mutum,wanda kallo d'aya zaka mata kaji tatafi da imanin ka,haka kawai sai tasa yarinyar agaba tana kallonta tana tunani inama ace Muhammad d'inta yana nan ta had'ashi aure da Inaas?

Farouq daya dawo daga makarantar kud'i (private school) inda yake koyarwa ya dinga yiwa Bilkisu magana amma Inaaaaaa!,Bilkisu tatafi tunani tana kallon Inaas datake wasa tana tunanin inama ace d'anta yana nan, Farouq yadafa ta,tayi firgigit tadawo hayyacinta,yayi zaton tunanin d'anta takeyi,hakan yasa ya sassauta murya cikin lallashi yace"kiyi haquri insha Allah watarana zakiga d'anki"

A shekarar 2014 Jawad yagama p.h.d dinsa a fannin kasuwanci,saiya kasance tundaga Degree har master's zuwa p.h.d gaba d'ayansu a fannin kasuwanci yayi bisa umarnin Alhaji Mekudi

Alokacin Inaas tana primary,surutu sai abinda ya qaru,duk lokacin da za'a rubuta sunan 'yan surutu a aji to kana dubawa zakaga sunan tane nafarko (😂)
______

2024
(yanzu kenan,nagama baku labari, mun bar shekarun baya mundawo zamanin mu,zamu cigaba da labari taurarinmu sun girma💃🏼)

Agidan Alhaji Mekudi kula da komai yadawo hannun Jawad,duk wasu takardu na kadarorin Alhaji Mekudi sunkoma sunan Jawad,acikin shekaru 37 d'innan arziqinsu yaci uban nada, Jawad yatsaya tsayin daka babu abinda yake face kasuwanci,tun kafin amaida sunan kadarorin izuwa sunansa haka yake aiki baya zama, bayan komai yadawo qarqashin sama bai zauna ba,saima himma daya qara, saida ya kasance Jawad yanada resuna na kamfanin-nikansa sama da guda talatin aduniya,yana zuwa manyan qasashe daban-daban,har yanzu yana nan yanda yake tunda can baya magana,babu abinda yaragu daga miskilancinsa sai qaruwa ma da abun yayi kasancewar tun yana yaro kafin yanemi abu,anriga anyi masa basai yabude baki yayi magana ba,hakan yasa yasake zama miskilin gaske,matsalar sa d'aya bashida kirki a fannin kasuwanci,inde zakai wasa da aikinka to bazaka shirya dashi ba.
Chapter 7 · 0% Book details