← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 63

Sashe 37

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inaas tazaro idonta waje, yayinda gabanta yafara wata irin mahaukaciyar fad'uwa,bata ta6a aikata hakan ba,abin yazo mata wani irin sabon abu ne awajan ta wanda saide taga anayi a tv,hannunta aware suke takasa koda yunqurin dorasu ajikin Yalla6ai Jawad,meyasa yake son karya mata duk wata Garkuwa ta jikinta? meyasa duk lokacin dazata had'u dashi yake zuwa mata da sabon abu wanda qwaqwalwar ta take kasa dauka? jikinta ne yake wani irin mazari,shi kansa Jawad yanajin yanda jikinta yake karkarwa,amma maimakon yasaketa,saima yasake qanqameta sosai a qirjinsa yanajin yanda nashanunta suke ta6o masa faffadan qirjinsa,daga ita harshi sunji alamun tahowa falon,hakan yasa Inaas tafara tureshi daga jikinta, amma Yalla6ai Jawad ko gizau beyi ba, saima idonsa daya sake lumshe wa,cikin wani irin yanayi yad'ora lips dinsa daidai saitin kunnanta,cikin wata irin murya me kashe jiki yace"pleace karki sake yin nesa dani,inaso ki kasance ME 'DEBE MIN KEWA"

Yana fad'a mata haka yayi sauri yasake ta yakoma kan kujera ya zauna yadauki wayarsa saika rantse da Allah ba shine ya aikata hakan ba.

Jikin Inaas sai karkarwa yake tana neman hanyar guduwa,shikuwa gogan ko ajikinsa yana zaune yamaida hankalinsa kan waya sai ajiyar zuciya yake saki cikin tsananin farinciki,saide bazaka gane yana farincikin ba ta hanyar fuskarsa,domin kuwa fuskarsa tana nan babu alamun wasa.

Hajiya Zaliha ta qaraso falon tayi turus awajan,ta kalleshi da tsananin mamaki tace"Jawad? menake gani haka? kaida kake gaggawa? meyasa baka tafi wajan taron ba?"

Koda wasa Jawad bai kalli inda Inaas take ba,yanda ya maze yayi fuska bazaka ta6a zargin cewa ma magana ta had'asu ba,ya kalli Mummy yace"bawani taro bane mai muhinmanci nafasa zuwa"(🤭)

Mamaki yasake kama Mummy tace"kaid'in Jawad?"

Jawad ya sunkuyar da kansa qasa tareda sosa kansa,sannan ya maida hankalinsa kan waya.

Hajiya Zaliha tayi ajiyar zuciya takamo hannun Inaas tace" mu zauna Inaas,nabarki a tsaye shima kuma wannan baimiki kara yace ki zauna ba"

Jawad yadan saci kallon Inaas,adede lokacin itama ta kalleshi, idonsu yana haduwa Inaas tayi sauri ta janye nata idon.

Daddy ne ya sauko falon yayi shirin sa tsaf cikin manyan kaya,yazauna a kusa da Jawad sannan ya kalli Inaas yace"yanmatan Mummy zance ne ko yanmatan Ammiy?"

Hajiya Zaliha tayi murmushi,yayinda Inaas tayi sauri ta sauko daga kan kujera tace"Daddy ina kwana?"

Daddy yayi murmushi yace"lafiya kalau,naga takardun ki yanzu,Mummynku takai min,nagani sunyi kyau sosai,wacce irin makaranta kikeso a nema miki?"

Gaban Jawad yayi wata irin fad'uwa,annurin fuskarsa ya 6ace 6at,tunani yafara aransa, wacce irin makaranta kuma? meyasa takeson tayi karatu? idan maza suka ganta fa? duk wahalar dayasha yayi nasa karatun hakan bai ishesu ba shida ita,? itama saitayi? dole ne karatun?.

Inaas tayi murmushi batace komai ba,Daddy yajuya ya kalli Jawad yace"Jawad wannan qanwar ka ce,Qanin matar Man Sulaiman shine mahaifinta,nabaka labarin dawowar su nan,shine nakeso takoma makaranta,kayi bincike kaga wacce makaranta yadace a nema mata,saikayi magana da shugaban makarantar"

Nan take Jawad yagane cewa kenan mahaifin Inaas ya bawa matakin MD jiya,to idan Qanin wannan matar shine mahaifin Inaas,wacece mahaifiyar ta? Ina take?
Daddy yaji shiru Jawad ba amsa yata6oshi yace"Jawad!!"

Cikin sauri Jawad yace"ok Daddy"

Sannan yadan dago kansa ya kalli Inaas,kamar ba Daddy ne agefensa ba yazuba mata ido yana kallonta,Inaas ta kalleshi sau daya tayi sauri ta sunkuyar da kanta qasa,
Duk wannan maganganun dasuke Inaas tana jinsu,saide ba komai take fahimta ba,abinda Yalla6ai Jawad yamata shine abinda yafi tsayawa aranta,me Yalla6ai Jawad ya aikata? meyake nufi da maganar sa?.

Me qunshi ce tayi sallama tashigo falon,Daddy yatashi yayi Dining,ta rissina ta gaida su gaba dayansu,Hajiya Zaliha tace"kifara yiwa yata"
Tana fadin haka tajuya wajan Daddy domin zuba masa abinci.

Me qunshi ta zauna tafara zanawa Inaas a farar fatarta,Jawad yadauki wayarsa cikin dabara yafara yiwa Inaas photo,ta dan dago tasaci kallonsa, yayi sauri yasake dauka,cikin sauri ta sunkuyar da kanta,tazubawa zanan fulawar da'ake mata ido,hakan datayi sai dogon gashin idonta yahadu waje d'aya,nan take Jawad yasake yimata wani photon.

Haka ya zauna afalon shi baitashi yaci abinci ba, shi bai koma dakinsa ba, haka shibai fita ba,yanaji aransa cewa kasancewar ta awajan duk ya wadatar dashi wannan abubuwan.

Saida aka gama mata qunshi duka hannayen ta,kasancewar akwai sanyin esi afalon nan da nan kuwa qunshi ya bushe,aka fara yiwa Hajiya Zaliha nata,Inaas ta kalleta tace"Mummy zanje wajan Ammiy"

Cikin farinciki Hajiya Zaliha tace"bazaki zauna muyi firar mu ba?"

Inaas tayi murmushi,haqiqa taso ta zauna,saide zaman Yalla6ai awajan yasa a takure zata zauna,hakan yasa tace"Mummy anjima zan dawo"

Hajiya Zaliha tace"to saikin dawo,ki gaida Ammiyn taki"

Inaas ta amsa mata,sannan tadan juya ta kalli Jawad,cikin sauri ya d'ora yatsun hannunsa biyu akan kunnansa alamar ta kirashi.(🤙)

Inaas kam kokadan batada nutsuwa aranta,Allah Allah take ta fice daga falon,hakan yasa tafice da sauri kamar wacce ake kora,ahanya tana tafiya kana ganinta zakasan cewa babu nutsuwa atare da'ita.

Tana komawa falonsu ta zauna kusa da Bilkisu tana nuna mata zanan qunshin hannunta tace"Ammiy kinga qunshi na"

Bilkisu ta kalli qunshin tace"masha Allah,kice ke gayu kika tsaya aka miki shiyasa naji ki shiru"

Maimakon tabata amsa saita marairaice ta shagwa6e fuska sannan ta kalli gefen da Abban ta yake zaune yana shan shayi tace"Ammiy dan Allah abani wayata kinji"

Abban ta ya kalleta sannan ya kalli Bilkisu, kai tsaye yace"abata"

Bilkisu tayi murmushi tace"to"

Sannan tatashi tayi daki,Inaas ta doru a bayanta,suna zuwa daki Bilkisu tabata wayar,tayi sauri ta yage ledar dake jikin kwalin sannan tabude kwalin tafuto da wayar,ta sakata a caji.

Tunani tafara tana so ta kirashi amma kuma wayar ba caji,hakan yasa ta dauki wayar Ammiy zata kirashi,kafin tayi kiran tajuya tana fuskantar Bilkisu sannan tace"Ammiy,wai idan mutum yace yanaso ina d'ebe masa kewa,meyake nufi?"

Mamaki ya kama Bilkisu,iya saninta de Inaas bata kula kowa,waye zaiyi mata wannan maganar,? cikin hikima tace"waye yafad'a miki hakan?"

Inaas taturo d'an qaramin bakinta gaba cikin shagwa6a tace"Ammiy dan Allah"

Bilkisu ta ruqo hannunta,tajata jikinta cikin sigar lallashi tace"Inaas,kinada wacce tafi ni ne?"

Cikin sauri Inaas ta girgiza kanta,alamun babu.

Bilkisu tace"to fadamin waye yafada miki hakan?"

Cikin rawar murya Inaas tace"Ammiy dama...dama....Yalla6ai Jawad ne ya...ya..."

tanaso tace ya rungume ni,saide tana shakkar fada saboda ta tabbatar idan ta fada daga Ammiy har Abbanta sai sunyi mata shegen duka, hakan yasa takasa gaba ta kasa baya,takasa fadar komai.

Bilkisu tasake matse hannun Inaas dake cikin nata tace"yayi me? me Jawad din yayi?"

Saida ta daidaita kanta sannan tace" dama Yalla6ai Jawad ne ya fadamin haka dazu danaje wajan Mummy"

Bilkisu ta runtse idonta, sannan tasaki ajiyar zuciya ta bude ta kalli Inaas tace"yana nufin koda yaushe ki kasance tare dashi,kidinga yimasa wasu abubuwan wanda zai dauke hankalinsa ya daina tunanin komai,bansani ba Jawad yana sonki ne kokuma sa6anin haka,amma koma menene banason alaqar soyaiya ta shiga tsakanin ki dashi,Jawad yafi qarfinmu Inaas,kinga de inda suke rayuwa,nasani cewa tabbas banaso ki auri talaka futuk wanda basu da cin yau bare na gobe,saboda ina guje miki irin rayuwar auren danayi abaya,banaso kisha wahala irin wacce nasha,karki ga nace banaso ki auri talaka kiyi tunanin sai me kudi nakeso ki aura,a a, ina nufin nafiso ki auri tsaka-tsaki,kamar de mu d'innan,koda kin fara son Jawad,kiyi qoqari ki cireshi aranki kirufa mana asiri Jawad yafi qarfin mu,kinga de inda suke rayuwa,basai nasake tunatar dake ba kinsan komu su waye, duk da inason yaron acikin raina bazan daure miki gindi ki saurareshi ba,ina gudun zuciya,kada mutane suce daga zuwanmu gidansu har munyi shige da fice kin auri d'an gidan"

Lokaci d'aya jikin Inaas yayi sanyi,kokadan ba zatayi jayaiya da maganar Ammin ta ba,amma taso kiransa,saide maganganun Ammiy yasa tafasa kiran nasa, cikin sauri ta rungume Bilkisu,saida tasamu nutsuwa sosai, sannan ta saketa tashige toilet domin wanke qunshin hannunta.

Jawad kuwa ganin cewa yafada mata suyi waya,hakan yasa har dare yana jiran kiranta,yasaba barwa P.a wayoyin sa, amma yau duka suna wajansa saboda yana tunanin kiran Inaas,saide har yayi shirin kwanciya shiru bata kirashi ba,har wajan shadaya na dare yana tunanin zata kirashi amma shiru,ahankali yatashi ya qarasa jikin window din dakin, ya janye labulan windon yazubawa Plat dinsu Inaas ido kasancewar dakinsa yana sama sai yake hango Plat din nasu sosai,ganin duhu yahade ko'ina hakan ne ya tabbatar masa da cewa sunyi bacci,badan yaso ba haka yadawo yakashe wutar dakinsa yashige cikin bargo ya kwanta,kokadan baiji dadin rashin kiran nata ba, saide daya tuna cewa yanzu suna tare da'ita a gida,sai hakan ya dan kwantar masa da hankali.

Washegari da safe Hajiya Zaliha takira wayar Ammiy tace idan sun gama abinda suke suzo,cikin nutsuwa kuwa suka shirya itada Inaas suka tafi bayan sungama aikin komai.

Suna zuwa falon Hajiya Zaliha tace"haba Bilkisu,menene amfanin zaman namu tare? kudinga shigowa mana muna wuni tare"

Bilkisu tayi murmushi tace"to Hajiya insha Allah zamu dinga shigowa"

Fu'ad dake cin abinci a Dining yana hango Inaas yayi sauri yatashi yadawo falon ya zauna,yagaida Bilkisu, ta amsa masa cikin sakin fuska, yajuya ya kalli Inaas yace"ke kuwa shiru ake jinki kod'an leqowa bakyayi"

Inaas tayi murmushi tace"jiyama fa nazo,nadade anan"

Fu'ad yace"ok jiya bana nan,naje unguwa,yakike ya zaman Nigeria, akwai dadi?"

Inaas Uwar surutu dama abokin zance take nema,hakan yasa tagyara zama suka dinga zance itada Fu'ad kamar dama can sun san juna,Hajiya Zaliha da Bilkisu suma suna nasu zancen na duniya, Fu'ad da Inaas kuwa zance yayi zance Fu'ad yace"bani number ki"(🤭😂)

Inaas kuwa tsabar ta dade bata samu abokin zance wanda zasu dade sunata zuba ba,hakan yasa tasake sosai da Fu'ad,tace"ai in fadama banida Sim card,kaga wayar ma jiya daqyar na kunna ta,saida nasa Email dina sannan ta bude,har yanzu narasa gane kan wayar,bansan ya take ba"
Tafadi haka tana bashi wayar ta.

Fu'ad yana ganin wayar yace"laaa ai irin wayar Yaya Jawad ce dake,wallahi irin tasa sak,yanzu yana bacci bai tashi ba,idan kika ganshi duk abinda baki gane ba, ki tambayeshi zai gwada miki komai,amma kiyi ahankali bayason surutu,idan kika bashi kikaga yana cika yana batsewa toki kar6e wayarki salin-alin kibar wajan, bashida da niyar koya miki"(😂)

Inaas ta kalleshi tace"to"
Chapter 37 · 0% Book details