← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 63

Sashe 46

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana futowa Compound yasaki wata irin ajiyar zuciya yanaji aransa kamar ya sauke wani irin babban nauyi daga kansa,kai tsaye wajan P.a yawuce,suka fara rage wasu ayyukan cikin kwanciyar hankali.

Jawad baisamu kansa ba sai yamma lis gab da magrib,hakan yasa suka wuce masallaci shida P.a sukai sallar magrib da isha'i,sannan yadawo gida,yana shigowa falo yaci karo da Inaas tana kuka,sai zuba shagwa6a take tanata faman kuka, ya tsaya ya harde hannunsa a qirjinsa yana ganin yanda Mummy da Mama Bilkisu suka rikice akanta sai tambayarta suke abinda aka mata.

Ya girgiza kansa ya d'aure fuska yazo yawuce su zaije dakinsa,babu buqatar ya tsaya awajan,idan ya tsaya ma tayaya ne zai iya lallashinta? ko kad'an baisan yanda zai lallashi mace ba,macen ma budurwa,saboda tun asali Mummy da Daddy basu yi masa rainon da zaiyi kuka ba,bare yasan yanda ake lallashin.

Yanajin Inaas tana magana cikin shagwa6a" Ba Aljannu ne suke ta6a min waya taba,duk lokacin dana sake sabon Sim sai sun karya min shi"

Mummy ta kalli Jawad dayake shirin hayewa sama,ta d'aga murya tace"Aljannun nan kam nima abun nasu yafara yimin yawa,kuma sai sun kalli ko'ina,sunga babu me kallonsu,saisu karya Sim Card din suyi wulli da wayar"

Jawad yanajin abinda Mummy tafada gabansa yafadi,ya runtse idonsa batare daya juyo ba.

Mummy tasake kallonsa tace"Jawad"

Ahankali kamar bayason had'a ido da'ita yajuyo yana sosa kansa,yace"Na'am Mummy"

Mummy tanuna masa Inaas tace"kaita wajan wasa tad'an sha is'ka"

Inaas ta kalleshi da idanunta dasuka cika tab da qwalla,ta tuna masifar daya mata dazu da safe, cikin shagwa6a tace"Mummy ni bazan jeba,yayi tafiyar sa"

Jawad yasake daure fuska yayi mata kallo daya yace"nabaki minti biyar"

Bilkisu ta kalli Inaas tace"kinga tashi kutafi,banason musu"

Inaas taturo d'an qaramin bakinta gaba sannan tatafi tafice tabi bayan Jawad.

Suna fita,Bilkisu tace"narasa yanda ake Sim Card din nata yake karyewa,kusan sau biyu kenan ko uku"

Hajiya Zaliha tace"Hmm Jawad nefa"

Bilkisu tafara tafa hannaye tana fadin"Amma kiduba kiga yaron nan yanda yawani maze kamar ba shiba?"(🤔)

****

Ahanya suna tafiya kowa yayi shiru babu wanda yayiwa dan'uwan sa magana,fuskarsa ad'aure ya d'an juyo ya dubeta,yaga itama tata fuskar ad'aure take,idonta yana kan window ko kad'an taqi kallon inda yake ta hard'e hannunta a qirjinta, ya danyi qasa da idonsa kad'an zuwa nashanunta,yanda ta hard'e hannun nata hakan yabawa doguwar rigar ta damar futo da shacin brar dake jikinta,ahankali ya d'an lumshe idonsa yahadiye wani irin saliva,sannan yaci gaba da driving dinsa.

Har sukaje wajan baice da'ita komai ba,haka itama,wajan ya birgeta sosai,taji dadin yanda ake jere mata ice-cream kala-kala sai wanda taza6a,banda kayan maqulashe dangin gishiri,yanda guard suke zagaya wajan suna basu tsaro hakan ne yasa babu wani saurayi dayayi gigin kawo kansa wajanta.

Qarfe tara dawani abu suka dauki hanyar dawowa gida,har zuwa wannan lokacin babu wanda yace da dan'uwan sa uffan a tsakanin su.

Suna tsayawa agida tayi sauri zata bude motar ta fice,yayi caraf ya ruqo hannunta,tajuyo ta kalleshi.
Ya tsatstsareta ta da idanunsa, cikin muryar rad'a yace"Meyasa bakya son zaman lafiya me?"

Inaas taturo d'an qaramin bakinta gaba,tatuno masifar daya dinga zuba mata yau da safe,lokaci daya qwalla ta cika idonta,ahankali ta zama hawaye ta sauko akan kumatunta, takai hannu zata share yayi sauri ya riqe hannun nata, sannan yakai nasa hannun ya goge mata hawayen,cikin muryar sa me kamar rada yace"Banason ganin fuskarki haka,idan kina murmushi kinfi kyau,murmushinki yana 'DEBE MIN KEWA,kidena sauraran samari, inde zaki dinga rabawa maza number ki sau dubu,to zan dinga karya layin ki sau dubu..."

Cikin sauri ta kalleshi tace"dama kaine?"

Jawad ya murza hannunta dake cikin nasa,wanda hakan yasa dagashi har ita suka tsinci kansu acikin wani irin yanayi sakamakon yanda yake murza tafin hannun nata,ya lumshe idonsa ya bude sannan cikin shaqaqqiyar yace"Yes nine..."

Inaas ta kalleshi tace"to meyasa?"

Kai tsaye ya kalli qwayar idonta yace"Saboda ina sonki..."

(to tsuntsayen soyaiya, nabarku lafiya🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️)

Yaude Jawad yafad'a 😂inajin yaga uwar bari ne

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Amnah El Yaqoub✍
[1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne, kibiya ki karanta cikin salama,idan kika karanta baki biya ba keda Allah

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

17&18

Daddy ya kalli Man Sulaiman yabashi hannu cikin farinciki yace"to Alhamdulillah,Allah yasanya Alkhairi Man Sulaiman,Allah yabaku Zaman lafiya,sannan ka kiyaye duk wani abu da kasan cewa zai 6ata ran Bilkisu,ita din abar tausayi ce"

Man Sulaiman yayi murmushi yace"ai Alhaji ban ta6a ganin Bilkisu tayi irin wannan 6acin ranba tunda nake,ban ta6a bata haquri sau d'aya taqi haqura ba,amma tunda naga nine nake bawa Bilkisu haquri har tsawon lokaci taqi haqura,hakan yasa dole zan sake kiyaye wa inyi taka tsantsan da'ita,yanzu de gashinan Allah ya temakeni Jawad yana saka baki ta haqura"

Murmushi Daddy yayi yace"to Alhamdulillah,Allah yabada Zaman lafiya,sai a kula da Amarya,nima bari nawuce"

Daga nan Daddy yawuce,shima Man Sulaiman yanufi wajan amaryar sa.

Daddy yana zuwa falo Mummy tahada masa dinner,yana faraci yace"ina yaran nan suke ne?"

Mummy tace"Fu'ad kam yafita yawonsa,Jawad kuma sun fita shida Inaas,har yanzu basu dawo ba"

Cikin mamaki Daddy yace"naga motocin dayake fita a Compound,gaskiya sun dawo, may be sun wuce wajan Bilkisu ne"

Mummy tace"eto inaga,Allah yasa de sun daidaita kansu da yarinyar nan,Alhaji inaso Jawad yayi aure wallahi,amma shi naga ko ajikinsa"

Daddy yayi murmushi yace"waye yafada miki cewa ko ajikinsa? shima ai yanaji ajikinsa,tun kwanaki naso inyi masa maganar Inaas din cewa idan yasan yana sonta toya fadamin,to bansamu zama dashi ba,saboda naga nace masa ya nema mata makaranta yatsaya yanamin kuskunda,tundaga nan na fahimci kamar de qoqarin dakike masa akan yarinyar yafara tasiri,to ki zauna dashi idan yashigo kuyi magana,inde yana sonta to ga mahaifin yarinyar nan muna tare dashi agida,kinga sai ayi komai tuwona maina,muma mufara ganin yan jikoki agidan namu,idan kuma yasan baya sonta toki fada masa yayi gaggawar futo da matar aure,dan bazan cigaba da saka masa ido yana zaune babu aure ba,ga mata nan dayawa sai wacce ya za6a bazai iyu ya dinga shiga halin buqata har abun yakai ga ganin likita ba"

Mummy ta kalleshi da sauri tace"Jawad dinne yake ganin likita Alhaji? Yaushe? nifa nayi tunanin ma yaron nan ba qalau yake ba,gashinan de mutum cikakke,babu abinda Jawad ya nema yarasa,amma ko kad'an mata basa gabansa,har gara Inaas dinma itace naga kamar yana kishin ta,jiyama datayi baqo karka ga yanda ya rufeta da fada kamar zai kai mata duka,yarinyar ma saida ta tsorata da fadan nasa, domin kuwa da kuka tabar falon nan"

Daddy yayi murmushi yace"kalau yake,lafiyar sa kalau sai iskanci,kwanaki can nima na ta6a yin wannan tunanin,nayi maganar da Man Sulaiman nace ina tsoro ko Jawad bashida sha'awa kwata-kwata,to saida likita yazo gida duba shi rannan sannan ne na tabbatar lafiyar sa kalau shegen miskilanci ne ya hanashi sauraren yanmatan,to tun a wannan lokacin naso nayi masa magana amma wani abun ya dauki hankali na"

Mummy ta jinjina kanta alamun tabbatar wa,ta tuna lokacin tanajan bargon dayake ciki shima yayi sauri yaja bargon bai barta ta bude ba,tasaki ajiyar zuciya tace"Allah yarufa asiri,zanyi magana dashi"

Daddy yace"Amin ya Rabbi,Yaya Mariya tace agaida ki,daga can muke nida Man Sulaiman,a masallcin gidanta aka maida aurensa da Bilkisu"

Cikin farinciki Mummy tace"au har an maida auren? to Alhamdulillah"

Daddy yace"an maida,bayan mun idar da sallah aka maida,Yaya Mariya tasake yimasa gargadi akan Bilkisu sannan muka dawo gida,kinga ikon Allah duk tsawon wannan shekarun da suka dauka basa tare da juna tun kafin a haifi Jawad, sai gashi basu shirya da juna ba saida Jawad din ya shirya su da kansa"

Mummy tayi dariya tace"Ai yaron naka ba daga nan ba"

****

Cikin sauri Inaas ta zaro idonta sannan ta kalli cikin qwayar idon Jawad,gabanta yayi wata irin fad'uwa,sakamakon jin Kalmar da batayi tunani ba.

Shima zuba mata ido yayi,yayinda har lokacin hannunta yake cikin nasa yana murza mata shi,cikin wata irin murya acan qasan maqoshinsa yasake tabbatar mata yace"ina sonki INAAS"

Yana fad'a mata haka yaja hannayen ta zuwa qirjinsa,yanda ya dora masa hannunta akan faffadan qirjinsa hakan yasa taji yanda bugun zuciyar sa ya tsananta,nan da nan jikinta yafara karkarwa.

Ahankali Jawad yafara matso ta har saida ya kasance tanajin yanda numfashin sa yake sauka akan fuskarta, Inaas tana ganin yafara kawo fuskarsa dab da tata,ta runtse idonta tafara girgiza masa kai,cikin sauri tace"A a,Yaya..."

Cikin wata irin shaqaqqiyar murya yace"Plaese Kiss d'aya kawai"

Cikin sauri ta girgiza masa kanta tace"nide a a,kabari banaso,ni ban ta6a yiba"

Jawad yayi d'an qaramin murmushi yazuba mata ido ganin yanda jikinta yake rawa gashi ta maqe ajikin murfin mota ta runtse ido,ahankali yace"waye yace miki ni d'in nata6a yi? ki bude idonki kiyi min..."

Gabanta yasake tsananta fad'uwa ganin yanda yacire kunya kamar ba shiba yake nema yayi mata wannan abun, cikin fad'uwar gaba tace"nide a a"

Jawad ya lumshe idonsa,sannan yabude yace"kiss me... inba hakaba ni zan miki"

Cikin sauri itama tasake cewa"nide a...."

Kafin tagama cewa a a,Jawad yahade bakinsu waje daya,abun yazo wa Inaas a bazata,bata ta6a tunanin Yalla6ai Jawad zai iya hakan ba.
Jawad kuwa idonsa ya lumshe, yakama harshanta yanasha cikin kwanciyar hankali.

Kasancewar motocin dayake fita dasu dukansu baqin glass ne dasu hakan yasa kokadan babu wanda yasan wainar dasuke toyawa acikin motar shida ita.
Chapter 46 · 0% Book details