← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 63

Sashe 32

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

___

Yau kwana biyu kenan da dawowar Inaas gida,tun ranar data tafi Jawad yake saran zata kirashi,yanason jin muryarta, yanason yasake magana da matar data had'a masa shayi koda na second biyar ne,yanason jin muryar matar sosai,baisan meyasa matar ta tsaye masa arai ba,yanajinta wata ta daban acikin zuciyarsa.

Yafi minti talatin yana zagaye dakinsa dagashi sai dan qaramin gajeren wando,hakan daya tsaya shine yasake baiyana qaqqar fan jikinsa cikinsa har wani hawa-hawa yake kamar dan wasan dambe,ayyukan sa da sukai masa yawa hakan yasa baya riqe wayarsa wayoyin suke tsayawa awajan p.a, amma yau wayoyin suna hannunsa saboda yana tsammanin kiran Inaas,amma haka yagaji da zagayen dakin yagaji bata kiraba,cikin damuwa yashiga wanka yana addu'ar Allah yasa ya futo daga wanka yaga missed call dinta.

*** *** ***

Abuja Nigeria

Daddy ya kalli Man Sulaiman yace"yanzu kaga Man Sulaiman wannan auren damuka dawo shekaran jiya, naso ace Jawad ya auri wannan babbar yarinyar fauziya,saboda batada hayaniya,zasu zauna lafiya,kuma zumuncin mu zai sake qarfi tsakani na da Aminina Alhaji Auwal saboda tun muna matasa tare muka fara fafutukar kasuwanci dashi har Allah yadafa mana,to amma kasan halin yaron naka firrr yaqi, gashi har tayi aurenta"

tunda Daddy yafara wannan maganar kwata-kwata Man Sulaiman baisan me Daddy yake fada ba,zuciyarsa tatafi wajan Bilkisu, tun bayan tahowarsu daga Niger kowanne cikin dare baya bacci sallah kawai yake yana sake godewa Allah akan bayyana masa Bilkisu dayayi.

Daddy dayaji shiru yajuyo ya kalli Man Sulaiman yana nazari a kansa,kafin yayi magana wani gurd yazo wucewa sukaci karo da Man Sulaiman, sai alokacin Man Sulaiman yadawo hayyacinsa,cikin sauri yabawa guard din haquri,Daddy yayi ajiyar zuciya sannan yaja hannun sa suka qarasa wajan wasu had'ad'd'un kujeru farare wanda suka qara qawata grass carpet din wajan, suka zauna sannan Daddy yace"Man Sulaiman meyake damunka? tun dazu inama magana amma hankalin ka baya kaina kwata-kwata,tunanin mekake haka?"

Man Sulaiman ya kalli Daddy yace" wallahi Alhaji cikin matsal..."
kafin ya qarasa cewa matsala wani irin kuka yazo masa,bai iya hana kansa ba saida ya rushe da kuka,Daddy yace"Subhanallah,Man Sulaiman kuka fa kake,meyake faruwa ne?"

Man Sulaiman yagoge hawayen idonsa yace"Alhaji zuwan mu Niger naga matata,da qyar nasamu qwarin gwiwar kallonta,na roqi tayafe min taqi,na roqi Alfarma tayi haquri tazo mu zauna domin in wanke laifina a'idon ta amma bata bani damar hakan ba"

Daddy ya jinjina kansa ya kalli Man Sulaiman yace"amma ka tabbatar ita kagani da idonka Man Sulaiman?"

"itace Alhaji,ko shekara dubu nayi,inde zan sake dora idona akan Bilkisu to tabbas zan ganeta,itace"

Daddy yace"to amma ina labarin yaron data haifa? ka ganshi?"

Man Sulaiman ya girgiza kansa,wani sabon hawaye mezafi yazubo masa,yace"bangan shi ba,banasa ran zan ganshi inajin saide a lahira,domin kuwa Bilkisu ta tabbatar min da cewa yaron ya salwanta, sannan nima banga kowa agidan ba bare ince shine,daga ita sai qaninta Farouq,haka shima dan'uwan nata naga yana goyon bayanta"

Daddy yace"Subhanallah,Hasbunallahu wa ni'imal wakeel,haqiqa Man Sulaiman kana ganin qaddara,kayi haquri kayi Addu'ah har Allah yabaka damar cinye wannan jarabawa,maganar qaninta kuma dole zaibi bayan yar'uwarsa,saboda abunda yafaru aiba qarami bane,yanzu kayi haquri kaje ka kwanta kahuta, qwaqwalwar ka tasamu nutsuwa,gobe da sassafe saika shirya muje,zanje dakaina zamu taru mubata haquri insha Allah komai zai wuce"

Cikin sauri Man Sulaiman ya tsugunna zaiyi wa Daddy godia,Daddy yayi sauri ya ruqo kafadunsa yace"A a tashi-tashi, ai mun zama daya Man Sulaiman, babu damuwa kaje kahuta"

Malam Manu yasake yiwa Daddy godia sannan yatafi,shima Daddy yawuce ya qarasa ciki.

Yana zama afalo yakira Yaya Mariya,yayi magana da da'ita, Hajiya Zaliha tazo takawo masa ruwa yadauka yasha,ta zauna akusa dashi ta kalleshi tace"Alhaji lafiya de ko? naga kamar akwai abinda yake damunka"

Daddy yayi ajiyar zuciya yace"wallahi batun Man Sulaiman ne yake ta6ani,yana cikin matsala,yana buqatar taimakon mu"

Hajiya Zaliha tace"meyake faruwa haka Alhaji?"

Kafin Daddy yayi magana Yaya Mariya tashigo falon nasu a fujajan, tanemi waje ta zauna tace"Aliyu meyake faruwa haka katasoni daga gida Ina fatan de bawani abune yasamu Fu'ad da Jawad ba?"

Hajiya Zaliha tace"Yaya nima yanzu naganshi haka kamar marar lafiya,nayi masa magana yace lamarin Man Sulaiman ne"

Daddy yayi ajiyar zuciya sannan ya kwashe komai yafada musu tun daga farko duk da sunsan labarin Man Sulaiman din,sannan ya qarasa da fadin"yanzu maganar danake muku daurin auren da mukaje Niger gidan Alhaji Auwal,to yaga matar tasa,saide yabata haquri taqi haqura,maganar cikin daya gudu yabarta dashi kuma ta tabbatar masa cewa yaron ya6ata, ta nemeshi ta rasa"

Gaban Hajiya Zaliha da Yaya Mariya yayi wata irin bugawa,lokaci d'aya suka hada baki wajan fadin"ya6ata?"

Daddy ya jinjina kansa alamun tabbatar wa.

Lokaci d'aya Hajiya Zaliha tafashe da wani irin kuka,cikin kuka tace"ni de wallahi ba Jawad dina bane,suje can su nemi d'ansu"

Yaya Mariya ta daka mata harara tace"da kina son nasa amma kika fifita danki a kansa? idan Fu'ad ne zaki masa abinda kika yiwa Jawad ne?"

Daddy ya girgiza kansa sannan yayi murmushi irinna manya ya kalli Hajiya Zaliha yace"wacce irin magana kike haka Zaliha? daga cewa yaron Man Sulaiman ya6ata shikkenan saiki kawo maganar Jawad? yara nawane suke 6ata anemesu arasa wasu a asbiti wasu azo har gida asace su, wasu kuma wata qaddarar tasa arasa su, sai kawai wannan ne zai zama dansu? kokadan ni ban kawo hakan araina ba, ko wani waje najeni naji mutane suna maganar Yara yan tsuntuwa kokadan bana kawo Jawad a cikinsu,manta wa nake cewa ba nine na haife shi ba, kuma ina fatan inci gaba da wannan mantuwar har abada,sannan bamusan dalilin 6acewar nasu d'an ba,kuma bana sonji,ina tsoron ranar da Jawad zaisan cewa ba nine mahaifin sa ba, tabbas ina tsoron wannan ranar, yanzu abinda yasa nataraku anan shine inaso ku shirya muje mutaru abawa wannan baiwar Allah haquri tayi haquri tazo suci gaba da zama da Man Sulaiman"

Yaya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"to Allah yarufa asiri,Allah yabaiyana mata d'anta, idan kuma ya mutu Allah yaji qansa ,idan yana raye Allah yasa yana gidan da zasu riqe shi kamar dansu,kar ayi masa irin ruqon Jawad"(🤭)
Ta qarasa maganar tana hararar gefen Hajiya Zaliha.

Daddy ya girgiza kansa yace"yaya ayi haquri mana,kuskure de anriga anyi,kuma Zaliha ta tuba,inada yaqinin insha Allah zuwa gaba bazata sake aikata haka ba"

Yaya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"Allah yasa,yanzu yaushe zamu tafi?"

Daddy yace"gobe dasafe insha Allahu"

*** *** ***

Niger Republic

"Inaas yaufa kin makara,tun dazu kike nuqu-nuqu bazaki futo kitafi aiki ba,a'irin haka ne wancan lokacin kikaja suka koreki ai"

Farouq daya futo shima yana sake gyara nad'in rawaninsa na asalin buzaye ya kalli Bilkisu yace" a a, Yaya kuda kuke da Jawad,aina zata sai wajan azahar zaki mata magana tafuto tatafi aikin"(😂)

Bilkisu ta kalleshi ta gyada kai ganin magana yafad'a mata saboda yaga tana son Jawad din,tasake daga murya tace" 'yar me gwanjo bazaki futo kitafi ba kinaji ana fada mana magana?"

Inaas tafuto tayi kyau sosai cikin shigar ta ta kullum wato laffaya,dan qaramin bakinta taturo gaba tace" kai Ammiy dan Allah, kuma har yanzu de wannan sunan yana nan?"

Kafin Bilkisu tayi magana,akayi sallama aka shigo gidan,Alhaji Auwal ne agaba,sai Alhaji Mekudi,Hajiya Aisha matar Alhaji Auwal,Hajiya Zaliha, Yaya Mariya,dakuma Man Sulaiman a qarshe.

Inaas taja ta tsaya ganin baqin fuska sai shigo musu gida suke,Bilkisu tana ganin Man Sulaiman tayi sauri ta dauke kanta kamar bata ganshi ba.

Farouq kuwa yana ganin uban gidansa wanda yake yiwa yaransa lesson wato Alhaji Auwal,cikin sauri ya qarasa wajansa yace"Alhaji sannunku da zuwa"

Alhaji Auwal ya kalli Farouq yace"A a,Uncle din yara wai dama gidanka mukazo?"

Farouq yace"eh Alhaji,ai anan nake"

Yajuya ya kalli Inaas yace"Ke shimfida musu tabarma"

Inaas ta ajiye jakar hannunta sannan ta dauko babbar tabarma ta shimfida.
Hajiya Zaliha tunda suka shigo idonta yake kan Inaas,kyawun yarinyar da nutsuwar data gani atare da'ita lokaci d'aya ya fuzgeta har taji tana yiwa Jawad sha'awar ta(😲)

Tana so ta wanke laifin datayi wa yaron ta hanyar nema masa matar data dace.

Zama sukai Inaas ta gaida su sannan ta wuce zata tafi aiki,Alhaji Mekudi ya kalleta yace"dawo ki zauna mana,ina zakije haka?"

Inaas tayi murmushi tadawo ta zauna acan gefe kusa da Bilkisu.

Bayan anyi gaishe-gaishe Alhaji Auwal ya kalli Alhaji Mekudi, sannan ya nuna Abban Inaas yace"Alhaji wannan shine yake yiwa yarana lesson,kullum zaije sugama karatunsu sannan yayi mana sallama yatafi"
Chapter 32 · 0% Book details