Sashe 21
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bilkisu tace"yaushe zan bari sai rana tatake zata futo talla,najira najira naga bata tashi ba saina qyale ta nafuto, baccin babu inda zai kaimu,gara mutashi mu nemi na aure"
Hajara tasake daga wani wando na yara ta ajiye shi akan cinyarta sannan tace"auren 'yar me gwanjon?ikon Allah auren ta zakiyi kenan tun yanzu?"
Bilkisu tace"aure kuwa,ada kam banyi niyar aurar da'ita ba,yanzu kuwa na cire wannan tunanin araina,saboda naga yarinya tun ba'aje ko'inaba ta had'a wannan uban nonuwa,kinga kuwa yaushe zan sata agaba ina kallonta?,dauki abinda zaki siya in qara gaba"
Hajara tayi murmushi tace"ai Inaas din takice nima de naga saurin girman ta,batafi shekara sha takwas ba amma kamar wata babbar budurwa, nadauki guda uku, za'a aiko miki kudin"
Bilkisu tace"to nagode"
Tatashi ta dauki qullin kayan gwanjon ta tashiga gida nagaba.
*** *** ***
Abuja Nigeria
Washegari aka kai goron Jawad gidansu Amal,duk wasu kudi da al'ada ta nuna Alhaji Mekudi ya bayar,bai bar gidansu Amal ba saida aka saka ranar Jawad da Amal tsawon sati biyu kacal, Alhaji Mekudi yanemi hakan ne domin yanaso idan Jawad zai tafi to yatafi tareda iyalinsa.
Washegari goro yasamu Yaya Mariya,batayi qasa a gwiwa ba tadira agidan Alhaji Mekudi,a falonsa na sama ta sameshi, bayan ya gaidata ta kalleshi tace"yanzu Aliyu kade dage sai an had'a auren Jawad da wannan yarinyar? Fisabilillah menene hadin Jawad da wata Amal? yarinyar nan ba sa'ar auren Jawad bace, Jawad yafi qarfinta nesa ba kusa ba, uban yarinyar nan babu abinda ya'iya sai shegen son kudi kamar shine yafi kowa son kudi aduniya,itama kanta Zaliha tasan da haka,kawai son kanta ne ya rufe mata ido"
Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya yace"yaya shi aure ai babu ruwansa da wannan,idan kika duba zakiga kwata-kwata Jawad bashida niyar aure, mun zuba masa ido mun barshi yana yawo agari Yaya karki manta fa mutanen gari zasu iya zaginmu,ita kuma Zaliha tahada Jawad da Amal ne domin tasake qarfafa zumunci"
Cikin damuwa Yaya Mariya tace"dan de Zaliha tadage ne akan auren nan saboda yarinyar nan dangin su ce, amma banda haka ina Jawad ina wata Amal nafadama yarinyar nan kullum tana nan tana raye-raye a tik tok, rawa ta fitsara babu mutunci aciki"
Alhaji Mekudi yace"to mubawa Zaliha dama Yaya,idan muka bari akai auren muma kamar munyi mata kara ne duba da yanda ta riqe wannan yaron Yaya kema fa kinsan komai"
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Allah ya kyauta, ai sai ayi musu auren, amma de zansa aci gaba da sawa yarinyar ido gaskiya"
Alhaji Mekudi yayi na'am da shawarar data yanke, daga nan suka futo daga falon nasa zuwa qasa, anan suka tarar da Hajiya Zaliha a zaune afalo, tana ganin futowar su ta kalli Yaya Mariya tace"Yaya ina kwana"
Hajiya Mariya taci gaba da tafiya batare da ta tsaya ba ta amsa tace"lafiya"
Daga nan tafice tabar gidan.
Washegari Fu'ad yadawo,duk da Jawad yasan da batun saka ranar kokadan bai fadawa Fu'ad ba,ayyukan dake kansa gaba daya sunsa ko tunawa da batun auren ba yayi,shikuwa Fu'ad tunda yaji batun saka rana yafara tsare-tsare kamar shine angon, haka yasa Jawad agaba har dakinsa yana tambayar sa wanne irin shagali za'a yi awajan bikin, amma Jawad baice komai ba,saboda yana daukan auren da zaiyi ne amatsayin kawai yayi aure iyayensa su dena yimasa maganar mata,har yau baije inda yarinyar take ba, haka bai buqaci number wayar ta danya kirata su gaisa ba,babu abinda ya sauya daga al'amuran dayake yauda kullum.
Alhaji Mekudi yayiwa Fu'ad waya cewa su shirya shida Jawad zasuje wajan rantsar da dan abokinsa anbashi minister.
Fu'ad yamiqe yace"yaya Daddy yace mu shirya zamu fita,zanje dakina na shirya I'm waiting for you"
Yana fadin haka yafice da sauri,Jawad yayi ajiyar zuciya yatashi yafara shiryawa shima,daya daga cikin shaddodin da Fu'ad yasa aka dinka masa yadauka yasaka,farar shadda ce wadda tayi masa kyau ta kar6i kyakykywar fatar jikinsa,idan wani ya ganshi babu tantama zaice shidin ango ne, yatsaya agaban mirror yana gyara zaman hular tasa, Daddy ne yayi sallama yashigo dakin nasa anan ya ganshi yana fama da gyaran hula yace"mekake jirane Jawad? kawai saka hula ma saiya daukeka wasu mintunan? banason wannan shirman,qananun kaya da zaman qasar waje yasa kana nema ka manta da al'ada"
Yafadi hakan yana saka hannunsa yasake gyara masa Zaman hular sannan suka futo.
Afalo ya tarar da Fu'ad harya shirya,shima manyan kaya yasaka saide shi bai saka babbar riga ba, Jawad kuwa yasa, sallama suka yiwa Daddy da Mummy sannan suka futo yayinda Hajiya Zaliha tabisu da kallon sha'awa.
Suna futowa compound guard suka qaraso da sauri suka rufa musu baya Fu'ad yana tafe yana danna wayarsa, yayinda Jawad yake takunsa na qaqqarfan namiji ingarma maiji da kansa.
Malam Manu suka tarar a tsaye ajikin daya daga cikin jerin motocin da'aka shirya domin fita dasu, Jawad yana ganinsa ransa yayi baqiqqirin, suna qarasawa wajan Guard yabude musu bayan motar suka shiga, Malam Manu yashiga yazauna Fu'ad yana gaida shi.
Jawad yadaga kansa ya kalli Man Sulaiman yace"Uncle fita ka koma ciki kawai,sai aturo wani driver yakaimu"
Malam Manu yayi murmushi yace"Jawad aini nasa kaina zan kaiku,Hajiya ta dade da fadamin kace nadena aikin komai, to zaman danake waje daya yafara damuna, kabarni muje daku inda zakuje, inajin nutsuwa araina duk lokacin dana daukeka dakaina amota nakai ka har inda zakaje"
Jawad ya kalleshi da mamaki,menene hadinsa da maganar malam Manu dayake cewa yanajin nutsuwa idan ya kaishi wani waje shida kansa? Saikace irin uba da d'a? to ai ko Daddy bai ta6a cewa yanajin nutsuwa duk lokacin dasukai tafiya tareda shi ba.
Ajiyar zuciya yasauke yace" Alright,we can go"
Cikin farinciki Malam Manu yaja motar suka fice daga gidan.
Sunyi nisa atafiya motocin su suka fara rage gudu suna tafiya ahankali qarshe ma sai suka tsaya saboda yanda garin yacika sakamakon taron yan siyasa,Jawad ya kalli baqin agogon dake daure a farar fatar hannunsa yayi tsaki,Fu'ad ya kalleshi yace"yaya kagaji ne?"
"no Fu'ad banason jira ne"
Fu'ad yayi murmushi yace"yaya kaida zaka fara zuwa zance ai dole yanzu ka koyi yanda ake jira,wallahi na matsu ranar nan tazo"
Man Sulaiman dayake gaban mota hannunsa yana kan sitiyari yayi murmushi yanajin yanda firar yan'uwan take kasancewa,gashi de bawani tsiran shekaru ne a tsakanin suba amma sosai Fu'ad yake girmama yayan nasa.
Jawaad ya kalli Fu'ad yace"ko naje wajanta bazan jirata ba"(😳🤭)
Fu'ad yayi wani malalacin murmushi yace"yaya kenan,dan de bakaga Amal bane shiyasa kake fadar haka,nina ta6a ganinta sau daya lokacin munje gidan nida Mummy kaikuma baka qasar alokacin,tanada kyau sosai, amma fa gaskiya andade, to kaga sanin dana mata da kenan, zuwa yanzu kuma Yaya zaka ganta? ada canma tun kafin na ganta adanginmu suna cewa duk yanmatan family din su Mummy babu mai kyanta to inaga yanzu? kaga kuwa kaima Yaya idan kaje zance dole zaka jirata kodan kaga wannan kyakykyawar da'ake cewa baya'ita a dangi, wai Yaya saina tsaya Ina siffantama itama? nasan ma ka dade da ganinta awaya yau kwana nawa da saka muku rana?"
Jawad yayi ajiyar zuciya yace" ban gantaba,but inaso duk lokacin da zan ganta tota kasance..."
saiyayi shiru yana hango Inaas acikin ransa, yatuna kalar farar fatarta sannan yaci gaba da fadin"ta kasance fara"(🤭)
Fu'ad ya gyara zama yayi murmushi yana kallon Jawad ganin yau kamar an yiwa yayan nasa baki sai sakin zance yake da alama yafara nisa.(😂)
Jawad kuwa baima lura da kallon mamakin da Fu'ad yake masa ba, haka yariga ya manta cewa Malam Manu yana cikin motar, dan haka zuciyarsa daya yasake tafiya duniyar tunanin 'yar me gwanjo, yatuno dogon gashin ta, sannan yasake kallon Fu'ad yace"gashinta ya kasance dogo har gadon baya"(🤭)
Fu'ad yanajin haka yazaro idonsa waje yana kallon yayan nasa.
Jawad yasake tuno d'an qaramin bakin Inaas sannan yace"kuma bakinta ya kasance d'an qarami, surutun ta yazama yana 'DEBE MIN KEWA akoda yaushe"
(Man Sulaiman kanajin d'anka yana sakin zance ba zakayi masa gyaran murya bane? 🤔)
(munkusa shan bikin Jawad 💃🏻💃🏻)
(Inaas ya kamata fa ki sakarwa Jawaad dinmu mara yayi fitsari 😎😂)
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.
300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.
Amnah El Yaqoub✍
[1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

Masu turomin 500 da masu turomin data duk da kunsan bahaka ne kudin littafin ba, nagode Allah yasaka da Alkhairi,Allah yabar zumunci,wanda suka sai littafina badan ya musu dadi ba saidon qaunar su agareni banida bakin dazan gode muku,koda yaushe bakwa gajiya da zaran nafara littafi zakuce kunaso ku siya,nagode sosai,Amina tana tare daku yanda kuke tare da'ita, nagode🙏