Sashe 8
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Manya-manyan 'yan kasuwa da 'yan siyasa sun san Jawad amatsayin shugaban kamfanin jiragen sama,idan aka had'a kud'ad'en dukkanin kasuwancin sa za'a iya cewa yana samun ribar million dubu talatin a kowacce shekara,kasancewar tun yana qarami yatashi da koyon kasuwanci hakan ne yasa yazama me mutuqar basira a fannin kasuwanci, tun zamowarsa mamallakin dukannin company's dinsu daga nan yafara ruguza kishiyoyin kasuwancin sa,kafin abokan kasuwancin sa su farga har ya musu tazara bakajin sunan kamfanin kowa saina Jawad Mekudi,duk yanda d'an kasuwa yakai gayin takarar kasuwanci dashi to lokaci d'aya Jawad zai daqusheka ta hanyar rage farashin kayan kamfanin sa nad'an wasu lokaci,daga nan kuma mutane su dinga tururuwar neman kayan kamfanin sa,hakan yasa sauran manyan qasashen duniya sukasan da Jawad Mekudi.
Lokacin dayayi Degree na farko akan kasuwanci yayi project dinsa,lokacin dayayi masters akan kasuwanci yayi project dinsa,haka p.h.d dinsa ma, bayan yagama karatu saida ya rubuta littattafai dadama duka a fannin kasuwanci domin na qasa dashi su amfana da irin salonsa.
Yawan ayyukan dayake dasu hakan yasa yana iya kaiwa kusan shekara ko fiye da haka baishigo Nigeria ba.
Jawad yahad'u sosai maqura,d'an gayu ne nabugawa a jarida,uwa uba ga kudi,ba qaramin d'aukan hankalin 'yanmata yake ba.
Shine matashi na farko dayake d'aya daga cikin masu manyan kamfanin nika acikin Nigeria dama wasu qasashen.
*** *** ***
Niger Republic
Zuwa wannan shekarar damuke ciki ta 2024 Inaas tacika shekara goma sha takwas,tayi Candy shekara d'aya data wuce,tagirma ta zama budurwa me bala'in kyau kamar mamarta Jamila,yawan gashin ta tun tana qarama har yanzu gashi yana nan har gadon bayanta,tanada tsananin kyau me daukar hankali,rana d'ai-d'ai ne ba zakaji sallamar samari a qofar gidansu ba amma Bilkisu tahana ta kula kowa,idan Inaas tafara zuba surutu saika dakatar da'ita hakan yasa takeda mutane sosai,shagwa6ar da Bilkisu tasaba mata dashi tun tana qarama hakan yasa data girma ma tacika shagwa6a,batajin kunyar kowa agaban kowa saita fara buga qafafu tana yiwa Mamanta Bilkisu shagwa6a,Allah yayi mata baiwar surar jiki da qira,uwa uba diri kamar budurwa me shekaru dayawa,tanada madedetan nashanunta wanda bazaka kirasu yan qananu can ba,kullum suna nan atsaye daram wanda yaci ace tun tuni tafara saka musu brezia amma qememe Inaas taqi sakawa ko irin na kayan gwanjonsu ne dasuke siyarwa,Bilkisu tayi mata magana harta gaji tarabu da'ita,gani take atsaye suke mezaisa tadinga saka wata brezia tana fama.
Sana'ar saida gwanjonsu tana nan sunayi babu abinda suka daina,sunan Bilkisu yakoma Bilkisu Me gwanjo,yayinda ita kuma Inaas yawancin mutane suke kiranta da 'YAR ME GWANJO.
kowanne lokaci Inaas bata kunyar kowa haka zata d'auki kayan gwanjonsu takai musu gida-gida kuma dayake tanada surutu nan da nan zatayi ciniki tadawo gida.
Sun tashi daga garin Dungas,sunkoma cikin Niamey,sakamakon aiki da Babanta Farouq yasamu yana koyarda yaran wani attajiri mesuna ALHAJI AUWAL..., "
(me karatu in baku manta ba Alhaji Auwal shine aminin Alhaji Mekudi,wanda yakira Alhaji Mekudi awaya cewa angama kammala komai na aikin kamfaninsa kawai shi ake jira yazo yabude,yazo nijar yabude kamfani a hanyarsa ta dawowa gida ya tsinci Jawad,to Alhaji Auwal yadauki Farouq Baban Inaas aikin koyawarwa,yana zuwa kullum yana yiwa yaransa lesson, kasancewar sa tsohon malamin makaranta)
Farouq yanema musu d'an qaramin gidan haya daidai na talakawa gida,gidan nasu yana daga can baya-bayan gari inda babu cukowar mutane dayawa a unguwar.
Suna rayuwar su cikin farinciki,Inaas bata barin Bilkisu tayi tunani tana qoqarin sanyata farinciki,tasan ba'itace ta haife taba,haka tasan labarin 6atan yaron ta,tasan komai kasancewar Bilkisu bata 6oye mataba,hakan yasa tadage wajan ganin ta maye mata gurbin d'anta data rasa,tana sata tanajin idan d'anta ya6ata to tanada wata yarinyar yanzu.
Kamar kullum,cikin sauri tashigo gidan nasu tana qwalawa Bilkisu kira "Ammiy.., Ammiy!"
Cikin sauri Bilkisu tafuto daga d'aki tana sake gyara d'aurin dankwalinta,tana nan har yanzu kyawunta bai gushe ba,mace mai haquri da hangen nesa,jikinta yana nan da kyansa kamar ba'ita ta haifi Jawad d'an shekaru 37 ba,kafin tayi magana Inaas tasaki kayan gwanjon su aqasa yayinda ta damqawa Bilkisu wasu takardu a hannunta,ita kuma tashige bandaki da gudu saboda wani mugun fitsari datake ji.
Bilkisu taja kujera ta zauna,ta ajiye takardun agefe sannan tabude qullin kayan gwanjon nasu tana dubawa.
Inaas tafuto daga bandaki tad'aga bakin buta ta wanke fararen qafafunta,sannan ta tsugunna tafara alwala,dogon gashinta kuwa Ammiy ta nannad'e matashi a qeyarta kamar ribon,saida tagama alwala sannan tadawo kusada Ammiy ta zauna tace"Ammiy albishir..."
Bilkisu tayi ajiyar zuciya tasan halin Inaas yanzu haka surutu zata fara, danhaka ta katseta tace"kafin albishir d'in de,yanaga kayan kin dawo dasu kwata-kwata baifi qwaya biyar kika siyar ba?"
'Dan qanqanin bakinta taturo gaba cikin shagwa6a sannan tace" Ammiyyyyy...."
taja sunan,sannan taci gaba da fadin"Ammiy ina miki maganar albishir kinata gwanjo,to kwanan nan za'a daina cemiki Me gwanjo nima adena cemin 'yar me gwanjo,nasamu aiki a kamfanin Mekud'i Oil,danaje na zauna Ina tsara wani ma'aikacin nasu,wallahi yana ganin takarduna ya kaiwa manager,bayan sunmin gwaje-gwaje kawai saiji nayi ance an daukeni"
Bilkisu ta zaro idonta cikin farinciki sannan tasaki murmushi tace"Inaas da gaske kinsamu aiki a wannan babban kamfanin? kai Alhamdulillah,to kuma sai akai Yaya? bani labari mana"
Inaas ta kwashe da dariya sannan tace"bakece kikemin maganar ban saida kayan gwanjonmu ba,to ai ajiyar kayan nabayar awani gida natafi kamfanin na basu takarduna,da har yafara yatsina fuska wai da secondary zamu daukeki aiki?"
(ta gwada yanda mutumin yake magana)sannan taci gaba da fad'in
"nikuwa danaga zai kwafsa min ai tuni nagyara zama naketa zuba masa zance wallahi Ammiy sai gashi yanata dariya,yanzu gobe babu zuwa tallar gwanjo,nazama ma'aikaciyar kamfani"
Ammiy tayi murmushi tana kallon Inaas tanajin wani irin farinciki,akoda yaushe tana Alfahri da Inaas,ajiyar zuciya ta sauke tace"to Allah yasanya Alkhairi,kidinga nutsuwa de idan kinje ba kowa zaki dinga sakewa dashi kina wannan surutun naki ba"
Inaas tayi fari da idonta tace"angama Ammiy"
Bilkisu tamiqe takawo mata abincinta, bayan tagama cin abincin tayi sallah, sannan suka zauna Bilkisu tafara gyara mata gashin kanta,already gashin nata a wanke yake,saita had'a wani turaren wuta na gashi me mutuqar qamshi,ta warware mata gashin tataje mata shi,gashin nata yayi wani irin tsawo har yanaso yawuce gadon bayanta yata6o mata duwawu kamar lokacin datake qarama, bayan tagama taje mata tadaga gashin sama tasaka turaren wuta aqasa tana turara mata gashin, yayinda Inaas ta lumshe idonta tanajin dadin yanda Ammiyn take gyara mata kanta.
*** *** ***
UAE.
(Abu Dhabi)
Ya kasance kowacce rana baya cikakkiyar awa biyar,batare da yaji muryar mahaifinsa ba,duk yawan ayyukan dake gabansa kokad'an baya sakaci da kiran Daddy,yana qaunar mahaifin nasu,kallo d'aya yayiwa P.a dinsa dake tsaye agefensa p.a yagane abinda yake nufi,cikin sauri yakira masa Alhaji Mekudi.
Adede lokacin Alhaji Mekudi yana cikin mota Malam Sulaiman yana jansa da sauran motoci a bayansu zasuje d'aurin auren yaron wani Sanata.
Cikin sauri Alhaji Mekudi yad'auka tareda fadin"Jawad"
Daga nasa 6angaren ya lumshe idonsa sannan yace"Daddy good afternoon"
Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya,maimakon ya amsa masa gaisuwar tasa saiyace"Jawad Ina hanya zanje wajan d'aurin auren yaron Senator Hamza"
Jawad yanajin haka yasake lumshe idonsa fuskar nan tasa kokad'an babu walwala akanta,yasan cewa Daddy Ishara yake masa akan shi yaqi aure gashi zaije d'aurin auren yaron abokinsa.
Shima maimakon yabawa Daddy amsa sai yace"Daddy i hope you're fine...."
Alhaji Mekudi yace"maganar danakema kenan? yaushe zaka shigo Nigeria? ya kamata ka sassautawa kanka wannan aikin kadawo gida ka ajiye iyali kuma,Jawad shekarunka 37 yanzu,sai yaushe zakai aure? mahaifiyar ka kullum maganar datake kenan".
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.
Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝
('yar me gwanjo)
Writing By Amnah El Yaqoub
Dedicated to Bilkisu's name
https://chat.whatsapp.com/FzjixDJbvvWCUd7az9a0K0
9&10
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne.
300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number

___
Runtse idonsa yayi sannan yabud'e,yanda ayyuka suke hanashi samun sukuni ina yaga lokacin dazaima fara duba yarinyar dayake so?,ita kanta soyaiyar idan yahad'u da yarinyar ma bazaice ga yanda zaiyi ba,ko irin kula 'yanmatan da samari sukeyi alokacin dasuke taashan balaga shikam baiyi ba,abinda yasani kawai shine kasuwanci,dashi aka bud'e masa ido,akan turbar kasuwanci aka fara d'orashi,baida lokacin dazai bawa mace,idan yace zai'iya kulawa da'ita ma to yayiwa kansa qarya,ahankali yayi ajiyar zuciya sannan yace"Daddy i don't have any girl friend,nabaku dama,kuza6omin duk wadda tamuku"
Alhaji Mekudi yakashe wayar cikin taqaici,sannan ya lumshe idonsa, Malam Manu dayake driving yanajin duk abinda yake faruwa,yayi murmushi yace"Alhaji aida kun barshi yakawo wacce yakeso da kansa,'ya'yan yau idan sukaqi mace abun ba dad'i,Jawad d'in har yanzu ai yaro ne,nawa yake?"
Alhaji Mekudi yabude idonsa yayi wani murmushi irin nasu na manya najin dad'i,duk wanda zai shagwa6a masa Jawad d'insa yana sonsa,aduniya in kanason kwanciyar hankalinsa to ka yabi d'ansa Jawad,ya kalli Manu driver yace"Man Sulaiman bakasan halin d'annaka ba,idan muka barshi to ina tabbatar ma ahaka zamuyi ta tafiya ba zaiyi auren ba,saboda agabanka yatashi shiyasa kake masa kallon qaramin yaro,duk sa'anninsa fa sunyi aure,wani lokacin idan na nutsu nayi duba akan sabgoginsa sai naga idan yazo qasar ma ko sau d'aya ba zakaji yana wayar nan irinta samari kaji Jawad yana waya da mace ba,sai Inga kamar ko bashida sha'awa ne"(🙈)
Malam Manu yayi murmushi baice komai ba,ganin yanda salon maganar Alhaji Mekudin ta sauya wannan maganar kuma tsakanin sane da d'ansa.
Alhaji Mekudi ya kalli Malam Manu wanda yake driving cikin qwarewa,yatuna lokacin daya daukeshi aiki alokacin baqi ne,amma yanzu ya washe yakoma chocolate,girma yafara futowa ajikin sa,amma yanayin jin dad'i da hutun dayake samu yasa girman ya 6uya,ga wani haqorin makka daya saka tun zuwansa Hajji da umara wanda Alhaji Mekudin shine yabiya masa,haqorin Makkan yasake qawata haqoransa yayi masa kyau sosai,ya sassauta muryarsa duk da su biyu ne amotar yace"nikam Man Sulaiman tsawon shekarun nan damuke tare banta6a jin kayi min maganar iyalinka ba,bakada yarinya ne ko yaro?sannan meyasa bazaka d'auko matarka kuci gaba da zama tareda muba?"