← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 63

Sashe 36

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun qarasa wajan bude kamfanin,suma suka samu waje suka zauna kamar kowa.

Wajan yayi kyau sosai,manya manyan 'yan kasuwar qasashen duniya sunzo,Jawad yamiqa hannu daya daga cikin guard dinsa yasaka masa Scissors, sannan yayanka zaren da akai docoration,lokaci daya aka dauki tafi fuskar kowa d'aukeda farinciki,sannan suka nemi wajan zama kowa ya zazzauna,me gabatar da taro yafara gabatar da Jawabi daki-daki kamar yanda suka tsara,saida akayi abinda ya dace sannan me gabatar da Jawabi yace"Dayawa daga cikinmu nan munsan wanda muke zaune anan domin sa,muna kira ga Babban d'an Kasuwa Mr. Jawad Mekudi,mamallakin kamfanin Oil da Kala-kalar meterial,shugaban masana'antun Jiragen ruwa dana Sama,muna kira ya futo fili yazo yayi Jawabi ga taro"

Cikin nutsuwa Jawad yatashi,yayi mutuqar kyau cikin wata baqar Suit,ahankali ya qarasa yatsaya a'inda aka tanada domin magana,ya kalli mutanan wajan ganin yanda waje yayi tsit kowa yana so yaji nasa Jawabin.

Abban Inaas dayake zaune kusa da Man Sulaiman ya zubawa Jawad ido yana kallonsa,mutumin dayake hanga daga nesa ranar da'akai rasuwa agidan Alhaji Auwal,wai yau shine agabansa a zahiri tsakanin sa dashi bai wuce taku goma ba,yatuna kyautar daya bawa 'yarsa Inaas,Masha Allah Yalla6ai Jawad ya hadu sosai,shi din mutum ne mai kwarjini da haiba,haqiqa baiyi kuskure ba daya hana 'yarsa kunna waya,domin kuwa ruwa ba sa'an kwando bane, auren qwarya tabi qwarya irinsu Yalla6ai Jawad sukeyi.

Jawad ya katse masa tunani ta hanyar fad'in" Assalamu Alaikum jama'ah,nasani cewa dayawa daga cikin mutanan dasuke zaune anan kusan kowa yasan cewa nine Jawad Mekudi,Jawad d'in da mutane da 'Yanmata suke muradi da rububin son haduwa dashi,saide a zahiri da bad'ini wanda yafi kowa sanina shine mahaifina,dashi muke fafutuka wajan ganin munzo wannan matsayin,shine ya dafani har na kawo yanzu,shine ya riqe hannu na ya koya min kasuwancin danake Alfahri dashi a yanzu,shine ya tsaya min harna kawo hakan,taimakon Allah dakuma aikin danake ba Dare ba Rana shine ya ha66aka kasuwanci na,Ina Addu'ah da kuma fatan kasuwanci na yaci gaba da ha66aka ta yanda zan zamo d'aya daga cikin manyan mutum goma na masu kudin Duniya"
Yana kawowa nan,gaba daya waje yadauki tafi,wata Baturiya ta matso kusa dashi tabashi wasu file file na takardu tace"yalla6ai Jawad wadannan takardun suna buqatar saka hannun ka"

Babu musu Jawad ya kar6i takardun yasaka hannu,sannan yakoma wajan zamansa,ba'a dauki tsawon lokaci ba aka kammala taro lafiya.

Bayan sun dawo daga wajan taro suna zaune afalo gaba dayansu,Jawad yana daddana waya, yanajin wata irin fad'uwar gaba atare dashi,yarasa meyasa tun da safe yake jin wata irin fad'uwar gaba,rabon dayaji wannan fad'uwar gaban tun zuwansa qasar Niger.

Daddy ya kalli Jawad yace"yaya maganar Farouq damukai dakai jiya? Ina fatan baka manta dashi bako?"

Jawad yace" ban manta ba Daddy,already nasa sunansa acikin jerin wanda za'a bawa babban muqami a kamfanin,za'a bashi MD na kamfanin insha Allah"

Daddy yayi murmushi yace"to Alhamdulillah,Allah yayi ma Albarka"

Jawad ya amsa da "Amin Daddy".

Da daddare yana zaune a Compound da guard guda biyu a tsaye a bayansa,ice-cream ne agabansa yana sha lokaci zuwa lokaci yana kallon Plat din da Daddy yace masa iyalan Man Sulaiman suna ciki,yana iya hango hasken fitilar falon saide akwai labule ba sosai ake hango cikin falon ba.

Yajuya gefen hannun hagunsa yaga yanda sojoji suke shawagi agidan,yajuya ya kalli P.a bayan yagama yanke shawarar zuciyarsa, sannan yace"P.a"

P.a yace"na'am Yalla6ai"

Jawad yace"ka shirya mana tafiya zuwa qasar Niger gobe da sassafe idan Allah yakaimu"

P.a yayi d'an qaramin murmushi bayan yagano shi yace"angama Yalla6ai"

Yadade a zaune awajan yanashan is'ka sannan yayi sallama dasu P.a yayi ciki.

Washegari tunda sassafe yatashi yahau shirin tafiya Niger,yariga yagama yanke hukuncin zuwa ya tunkare ta,yanaso yaje ya ganta ko wannan zafin na gefen zuciyarsa zai daina damunsa(🤭)

Yasa kaya kusan Kala biyar yana cirewa,duk wanda yasaka saiya ga beyi masa kyau yanda yakeso ta ganshi ba, daga qarshe yasaka wata farar shadda wanda akayi mata aiki da zare ruwan toka,ba qaramin kyau shigar tayi masa ba,tsananin kyawun sa yasake futowa kamar sabon ango haka kayan yayi masa kyau sosai.

A gaggauce ya futo daga dakinsa,ko agogon hannu bai daura ba,yana sakkowa falo yana d'aura agogon hannunsa,Fu'ad tun shekaran jiya baya gida yaje gidan wani Uncle dinsu.

Mummy tana jera abinci Jawad ya gaida ta a gaggauce yana qoqarin ficewa daga falon,kana ganinsa basai anfada maba kasan cewa yanda yake zuba saurin nan to tabbas akwai wani waje muhimmi da zaije.

Cikin sauri Mummy ta kalleshi tace"ina zakaje haka kake ta wannan saurin ne? ko Breakfast bakayi bafa"
Cikin gaggawa yace"Mummy zanje wajan wani taro ne,sauri nake"(🤭😳)

Yafad'i hakan yana qoqarin wucewa, cikin sauri ta ruqo hannunsa tace"tsaya kasha kunun Madara saika tafi"

Jiyayi kamar yafashe da kuka wannan d'an jinkirin da Mummy zatasa yayi,babu yanda ya'iya haka yatsaya ta dauko kunun madarar tafara bashi,ahankali yakeshan kunun yana tauna kwakwar dake ciki ahankali kamar bayaso,a tsaye yakeshan kunun,hakanne yasake tabbatar wa da Mummy cewa lalle wannan taron da Jawad zaije ba qaramin taro bane.(😂)

Adede lokacin Inaas tashigo falon bakinta dauke da sallama,hannunta daukeda Takardunta wanda Daddy yace takawo masa,tunda sukazo gidan bata ta6a saka riga da siket ba sai yau,tana Sanye cikin Riga da siket na wata Holland Atamfa, dinkin ya zauna ajikinta sosai, hakanne yasa Hips dinta wanda Jawad bai ta6a sanin tana dashi ba ya futo sosai acikin siket din kamar Hips din babbar mace yanda tacika siket din nata dam, idon Jawad ya sauka akanta,gabansa yayi wata irin fad'uwa,lokaci d'aya ya qame a tsaye idonsa qyam akanta,tunani yake ita din ce kokuma de gizo tafara yimasa?
Wayar dake hannun sa tayi qara,hakanne yasa yadawo hayyacinsa yadauki wayar saide idonsa yana kanta yakasa janyewa,daga can 6angaren P.a yace"yalla6ai jirgi yazama Ready,kai muke jira"

Idon Jawad akan Inaas kai tsaye yace"anfasa tafiya"

(😳🤭😂🥰uhm banda tacewa yau)

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Amnah El Yaqoub✍
[1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

31&32

Ganin yanda yazubawa waje daya ido kamar yama manta da abinda yake sha hakan yasa Hajiya Zaliha ta juya ta kalli abinda yake gani,nan take taga Inaas a tsaye,kan yarinyar aqasa tana dan jujjuya takardun hannun ta,tunda tashigo taga Yalla6ai Jawad gaba daya sai jikinta yafara rawa,tanemi qwarin gwiwar ta tarasa.

Hajiya Zaliha tayi murmushi tace" Inaas yau kece? meyasa bakyason shigomin ne?"

Inaas tayi murmushi ta qaraso wajan Hajiya Zaliha tace" Mummy Ina kwana?"

Cikin jin dadi Hajiya Zaliha tace"Lafiya kalau Inaas ya samari?"

Inaas tayi sauri tarufe fuskar ta da hannunta cikin kunya sannan tace"dama na kawowa Daddy takardu nane"

Mummy tameqa hannu ta kar6i takardun Inaas sannan tace"bari nakai masa,amma karkije ko'ina, yau anan zaki wuni,dama nayi waya me qunshi zatazo tamin kema sai tayi miki"

Tajuya ta kalli Jawad daya qame a tsaye mamaki yagama kasheshi,alamu de sun nuna masa dama can suna cikin gidan nasu,hakan yanuna sune iyalan Man Sulaiman kenan dasuka dawo nan,Mummy ta bashi cup din hannunta tace"Jawad riqe cup dinnan ka qarasa da kanka 'yata tazo"

Jawad ya kar6i cup din yariqe,yayinda Hajiya Zaliha tawuce sama da sauri zuwa dakin Daddy.

Inaas tana ganin tafiyar Hajiya Zaliha tazaro idonta ta kalli Jawad, cikin sigar rad'a tace"yalla6ai,dama kana nan?"

Jawad ya rissina ya ajiye cup din hannunsa,cikin wani irin farinciki yayi taku daya ya qarasa wajanta,ido yazuba mata yafara qare mata kallo da gasken de itace,wani irin farinciki ya kamashi har saida fuskarsa ta nuna,cikin jin dadi yashafa sumar kansa sannan yasaki wata irin ajiyar zuciya, yad'aga kansa ya kalli babban falon nasu yaga cctv Camera dake falon bata kansu,babu 6ata lokaci yayi sauri ya fuzgota,lokaci d'aya tafad'a kan faffad'an qirjinsa,cikin jin dadi yayi mata wata irin runguma ya lumshe idonsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya kamar yaron dayayi wuni d'aya baisha nonon uwarsa ba. (🙈)
Chapter 36 · 0% Book details