← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 63

Sashe 43

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilkisu tadago fuskarta wadda tayi jajir,hatta kumatunta duk yayi ja alamun tasha kuka,ta kalli Alhaji Mekudi tace"Alhaji,shekaru talatin da bakwai dasuka wuce,tara ga watan d'aya,a shekarar Alif d'ari tara da tamanin da shida, cikin dare,adede qauyen Dungas na qasar Niger,na ajiye yarona Muhammad acikin mota me d'aukeda lambar qasar Nigeria cikin garin Lagos,mun fita nida Jawad d'azu,naga wannan motar a gareji,Jawad ya tabbatar min motarka ce,Alhaji dan girman Allah kafadamin ina yarona Muhammad yake?,yamutu ko yana raye? katemaka ka fadamin Alhaji"
Ta qarasa maganar tana saukowa daga kan kujera ta zuba gwiwar ta aqasa tareda hade hannunta waje d'aya (🙏🏻)
Tana roqonsa.

Gaba daya sai falon yayi tsit...,shashshekar kukan Bilkisu ne kawai yake tashi,yayinda Man Sulaiman yayi qasa da kansa shima yana goge hawaye,haqiqa ya zalunci Bilkisu,baisan iya gararin datayi ba lokacin daya gudu ya barta.

Daddy ya runtse idonsa yakasa dago ido ya kalli Bilkisu,yadade a wannan yanayi,haka duk tsawon lokacin daya dauka baice komai ba Bilkisu tana tsugunne agabansa kamar me neman gafara tana aikin kuka.
Daddy yadago kansa ya kalli Bilkisu da idanunsa wanda sukai jajir yace"Bilkisu kece...?"

Bilkisu tagyad'a masa kanta,idonta yana tsiyayar da hawaye,cikin kuka tace"Alhaji ka temaka min,inason dana"

Tana fadin haka,numfashinta yafara sama-sama tana qoqarin faduwa awajan tanajan numfashi da qyar kamar zata shid'e.
Dawani irin gudu Man Sulaiman yataso zai rungumota tafad'o jikinsa(🙆🏻‍♀️)
Lokaci d'aya yatuna cewa yanzu fa Bilkisu ba matarsa bace,yanzu ba da bace,hakan yasa yaja yayi turus,yayinda Hajiya Zaliha da hawaye yake sauka a tata fuskar,tayi sauri ta ruqo Bilkisu suka koma kan kujera suka zauna,tana goge mata hawayen idonta.

Daddy ya kalli Bilkisu yace"Bilkisu bayan nagama jin dukkan hujjojinki,hakan ma ya gamsar dani,basai kin tsugunna agabana kina roqona akan haqqin ki ba,a wannan ranar bayan na zaga nakama ruwa,kai tsaye nashiga mota ta natafi,saboda saina shigo cikin kano sannan zan hau jirgin dazai kawoni Lagos,bansan cewa akwai mutum acikin mota ta ba,saida nayi nisa naji motsin jariri,na dakata nazo na daukeshi,muka dawo inda na ajiye mota ta saide banga kowa awajan ba,hakanne yasa na daga yaron sama nayiwa Allah godia bisa kyautar dayayi min wadda mun dade muna neman haihuwa nida matata Zaliha amma Allah bai bamu ba,hakan yasa muka rungumi wannan kyauta da Allah yamin amatsayin yaron mu,a halin da'ake ciki yanzu Bilkisu JAWAD shine yaron ki"

Cikin sauri Man Sulaiman ya kalli Alhaji,hakan yana nufin Jawad yaronsa ne? Cikin Jawad ne ajikin Bilkisu ya gudu yabar su? still abinda ya gudu yabari shine yadawo yake aiki a qarqashin sa? ashe wannan dalilin ne yasa yakejin Jawad acikin zuciyarsa?
Lokaci d'aya yafashe dawani irin kuka,sosai yake kuka kamar ransa zai fita,tunani yake meya aikata haka? meyasa yayi sanadiyar rabuwar uwa da d'anta?
Farouq ya matsa yafara bubbuga bayansa alamun lallashi,shi kansa abun ya daure masa kai,sai yanzu ne yagane dalilin da yasa ko kad'an Bilkisu batason laifin Jawad.

Bilkisu ta share hawayen idonta tana jan wata irin ajiyar zuciya idanunta duk sun kumbura,Hajiya Zaliha ta goge hawayen idonta sannan ta kalli Bilkisu dake gefenta tace"yanzu Bilkisu Jawad dina shine Muhammad dinki? dan Allah Bilkisu na roqeki kada ki qwace Jawad daga wajena,ki fada masa komai,kiyi masa komai duk abinda kika so,amma dan Allah karki rabani dashi,wallahi tallahi ina sonsa"

Cikin kuka Bilkisu ta rungume Hajiya Zaliha,sannan tace"har gobe,har abada Jawad nakine Hajiya"

itama Hajiya Zaliha bata jira komai ba tasake rungume Bilkisu sukaci gaba da kuka,sosai suke kuka kamar anyi musu mutuwa,babu wanda basu karya wa zuciya ba afalon.

(bari mu leqo wad'ancan tsuntsayen soyaiyar 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️)

****

Bazata iya jure kallon cikin idon Yalla6ai Jawad ba,tanajin kamar wani abu ne yake futowa daga cikin idonsa yake shigewa cikin nata idon,cikin sauri ta janye idonta daga qwayar idonsa.
Ahankali Jawad yatako ya matso dab da ita qiris yarage yahad'e jikinsu waje d'aya,cikin sauri Inass tayi qasa da kanta,gabanta yafara fad'uwa,tanajin yanda kusancin nasu yayi kusanci dayawa,cikin wani irin salo Jawad ya sassauta muryar sa takoma rad'a, sannan yace"mekike so?"

Inaas ta girgiza kanta alamun babu komai,daga nan tafara tunani me zata ce masa? ce masa zatayi yana birgeta? kokuma ce masa zatayi shid'in had'ad'd'e ne? tasan cewa yayi mata nisa,nisan da koda wasa ba zatayi kuskuren saka sonsa acikin zuciyar taba,saboda ta riga tagama gane cewa shi d'in yayi mata nisa.

Ahankali tajuya zata tafi,yayi sauri ya fuzgota tafada jikinsa,tanajin yanda numfashinsa yake bugar gefen wuyanta.

Ahankali Jawad yafara matso da fuskarsa dab da tata fuskar,sannan ya lumshe idonsa ya karkatar da kansa,yanufi lips dinta gadan-gadan zaiyi kissing,tana ganin abinda yake qoqarin yi,tazaro idonta, cikin sauri ta qwace daga jikinsa tabar wajan da gudu, ta nufi qofa, zata fice daga falon.

Jawad yazuba hannunsa acikin aljihun wandon sa yana sakin ajiyar zuciya, yabi bayanta dawani irin kallo mai cikeda shauqi sai hadiyar wani irin yawu yake(🙈)
Cikin qasan maqoshinsa yace"i luv her..."

Inaas takama handle din dakin zata fita,aka turo qofar falon dawani irin qarfi,cikin sauri tayi baya tana tunanin duk wanda yabude qofar nan,afusace yake.
Kafin tagama tunanin datake wani Babban mutum yashigo dagashi sai Jallabiya kana ganinsa kasan cewa ba'a hayyacinsa yake ba,yadaga Murya cikin Masifa yace"ina Zalihan take!!?"

Jawad ya kalli Uncle Bature mahaifin Amal yarinyar daza'a hadasu aure aka fasa,cikin mamaki yace"Uncle meyake faruwa?"

Cikin Masifa Uncle Bature yace"dakata Jawad,waye Uncle d'in naka? kaje can kanemi Uncle d'inka,wallahi tallahi nafi qarfin zama Uncle d'in d'an tsuntuwa..."

Inaas datake tsaye abakin qofa ta kalleshi da sauri tana bude baki cikin tsananin mamaki.

Jawad ya qaraso wajansa yace"what? mekake magana akai Uncle?"

Cikin tsananin Bala'i Uncle Bature yace"wato saboda nace bazan baka 'yata Amal ba,nakuma bugi Qirji nace wa Zaliha na cinye kudin data bani shine hakan bai isheku ba saida kuka sa akaje aka bankawa gidana wuta komai da komai ya qone ban tsira da komai ba,to inaso kasani,kaiba kowa bane face d'an tsuntuwa,bazan had'a jini da kai ba,taqamar kade shine kanada kudi kanada masu tsaya ma amatsayin iyaye,to kasani ko duk abinda na mallaka zai qare wallahi, tallahi sai kotu tabimim haqqina akanku..."

Jawad ya runtse idonsa yanajin kansa yayi nauyi kamar an d'ora masa wani gingimeman dutse,me Uncle Bature yake fad'a haka? Meyake shirin faruwa dashi ne?
Lokaci d'aya yafara ganin duhu-duhu ga jiri yana dibarsa,yaji falon nasu yana juyawa,hakan yasa yafara laluben kujera yanaso ya dafata gudun kada yafad'i.

Inass tajuya ta kalli yanayin da Jawad yake ciki kamar wanda yasha wani abu na maye kamar ma shirin faduwa qasa yakeyi.
Cikin wani irin gudu tafi ce daga falon ta nufi Plat dinsu.

Adede wannan lokacin Yaya Mariya ta kalli Bilkisu da Hajiya Zaliha dakuma Man Sulaiman dasuke faman kuka ta goge qwallar idonta tace"kukan nan ya'isa haka,tunda an fahimci juna ubangiji ya kamata muyiwa godia,tunda komai yazo cikin sauqi"

Kafin wani daga cikinsu yayi magana Inaas ta banko qofar falon har tana fad'uwa qasa,cikin tashin hankali tafara nuna musu qofar falon da hannunta amma takasa magana.

Abban ta yatashi yadawo wajanta ya jijjigata yana fadin"ke meyake faruwa? me aka miki?"

Cikin tashin hankali Inaas tace"Yaya Jawad ne....shida wani afalo...Yaya Jawad ne....Abba idonsa yana rufewa zai fad'..."

Kafin Inaas tagama cewa zai fad'i,Bilkisu ta miqe,cikin sauri Yaya Mariya tace"Subhanallah"

tamiqe suka fice da sauri suka nufi falon Mummy.

Suna zuwa falon sukaga Jawad yakama gwiwar sa yariqe yana qoqarin fad'uwa.
Bilkisu da Mummy sukai kan Jawad,Man Sulaiman yana tsaye agefe har lokacin hawaye yake daukewa daga fuskar sa.
Daddy yayi qarfin halin d'ago Jawad sannan yace"meyake faruwa Jawad?"

Cikin tashin hankali Jawad ya kalli inda yake jin maganar Daddy sannan yace"Daddy bana gani...,duhu nake gani"

Cikin 6acin rai Daddy ya kalli Bature yace"wallahi,tallahi Bature duk abinda yasamu yarona,saina makaka a Court anyi maka daurin rai agidan yari"

Yaya Mariya ta kalli Uncle Bature tace"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un...ni Mariya yau nake ganin Bala'i,yau kuma masifa ta sauka a gidanmu,Bature meya kawoka gidannan? Bayan cin amanar da kuka mana mekake nema kuma?"

Adede lokacin Fu'ad yadawo,hannunsa riqeda ledar daya siyo musu ice-cream,yana shigowa falon yatsaya yayi turus ganin mutanan gidan ba lafiya,ga Inaas agefe sai kuka takeyi,ga Mummy da Bilkisu da Daddy sun rirriqe Jawad kowa hankalinsa atashe.

Uncle Bature ya kalli Yaya Mariya yace"cin amana yawuce wanda kukamin,dan me zaisa aje a qonamin gidana saboda na hanashi auren Amal? shi awa zan dauki yartawa qwalli d'aya jal na bashi,asalinsa nasani kokuma tushensa nasani dazan had'a 'yata da d'an tsuntuwa? Wallahi kotu ce zata rabani daku"

Fu'ad yasaki ledar hannunsa yace"What? Uncle mekake fada haka?"

Lokaci d'aya Yaya Mariya data gama jin dalilin komai,ta hayaiyaqo masa da masifa tace"yanzu ko naji,lalle Bature ka tabbatar min da cewa kai jahili ne,inde baka yarda da qaddara ba,naji dadin wannan gobara saboda dama kariga kahada kudin ka da kudin haram,Allah ne yabi wa Jawad haqqin sa,Amal kuma kaje kajiqata kasha,wallahi tallahi Jawad yafi qarfinta,dama can ba kalar aurensa bace,kotu kuma ka dade baka kaiba,daga kotun farko har kotun qoli daidai muke dakai"

Cikin 6acin rai Uncle Bature yace"Mariya haka kikace?"

Yaya Mariya tace"ban'isa nafadi hakan bane?"
Ta daga murya tace"security!!!"

Cikin sauri wasu sojoji guda biyu suka shigo.
Yaya Mariya ta nuna musu Uncle Bature tace"ku kamashi kuma sa duka ku wullar dashi awaje,tayaya zaku dinga barin mahaukata suna shigo muku gida?"

Uncle Bature Yajuya ya kalli Yaya Mariya da tsananin 6acin rai,kafin yace wani abu Sojojin nan suka d'aga shi sama cak, sukai waje dashi.

Daddy yajuyo ya kalli Abban Inaas yace"Farouq matso mu kaishi daki"

Jawad yadago kansa,ya kalli Daddy da idanunsa dasuka rine sukai jajir yace"Daddy me kuke 6oyemin ne? da gaske ne abinda Uncle Bature yaje fada ba kune iyayena ba?"

Daddy ya sunkuyar da kansa qasa cikeda taqaicin abinda Bature yayi,yaso ace sun zaunar da Jawad din cikin fahimta sun sanar dashi komai.
Wani irin hawaye yazubo daga idon sa,baya jin ko Man Sulaiman dayayi silar zuwan Jawad duniya zai kaishi son yaron,yana qaunar Jawad tun ranar farko da Allah yabashi shi.
Kokadan bai hana kansa zubar da wannan hawaye ba.

Ganin Daddy ya sunkuyar da kansa qasa yana hawaye babu amsa,hakan ne ya tabbatar wa da Jawad cewa kenan gaskiya Uncle Bature yafada.

Yajuya yasake kallon Mummy,hawaye yazubo daga idon Hajiya Zaliha ahankali ta kawar da kanta gefe takasa kallon Jawad din,bata sake tabbatar wa tana qaunar Jawad ba sai yau,yayi mugun bata tausayi.
Chapter 43 · 0% Book details