Sashe 51
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wajan yayi kyau ya tsaru iya tsaruwa da adon furanni,anyi komai da tsari kasancewar abun sune na Manya,ga abinci nan kala kala ruwan gorar faro da lemuka kamar banza.
Sai a wannan lokacin Jawad yaga Inaas,yanda tayi masifar kyau hakan yasa yaji wani irin Kishi ya kamashi,shi kansa daya Santa ba qaramin gigitashi tayi ba,doguwar riga ce ajikinta fara daga Bayan rigar ansaka mata net yana bin bayanta har qasa,yayinda Jawad yayi mutuqar kyau cikin manyan kaya farare,hannunsa cikin nata suka shigo,bayan sun zauna aka fara gabatar da taro,yanda manyan yan siyasa suke tiqar rawa abun har mamaki zai baka,daga baya aka kira ango da Amarya suka futo fili,aka kunna musu hayaqin soyaiya,hannun Jawad yana kan hips dinta,yayinda ya dora fuskarsa akan tayaya yana mata magana qasa-qasa wanda su kadai sukasan me suke fada,wata waqa ce take tashi awajan me sanyi wadda babu tashin hankali acikinta sai zallar kalaman soyaiya da'ake fad'a.
Na'im babban abokin ango yataso tareda abokan Jawad yan qasar waje,suka fara yimusu kari da dala, yayinda Fu'ad yataso dawata jaka me d'aukeda kudi yana watsa musu cikin farinciki.
Lamarin daya jawo cece-kuce a social media,ta wani Fannin kuma zallar kyawun Amaryar Jawad din yasa wasu yan bani na'iya a social media suke fadin cewa da alama Jawad din wata qasar larabawa ya tsallaka yasamo matar.
Qarfe goma daidai aka gama dinner kai tsaye falon Daddy Hajiya Zaliha ta wuce da Amarya,ba tafi minti goma da kaita ba,Jawad yashigo ya zauna akusa da'ita,Man Sulaiman da Abban ta da Bilkisu da Daddy da Yaya Mariya duk suka had'u,nasiha suka musu,tareda jan kunne da gargadi akan su had'e kansu suyi zaman lafiya.
Abban ta ma yayi musu nasiha,itade Inaas kanta yana qasa cikin net.
Acan Compound kuma su Na'im da Fu'ad suna waje tareda sauran abokan ango,suna fafatawa da qawayen Amarya akan kudin siyan baki,bayan dogon kace nace wani abokin Jawad yayi magana guda d'aya yace tunda harka ce ta manyan yara abasu million biyar,nan take aka tura kudi ta account din babbar qawar Amarya,ita kuma ta kar6i account number kowa zatayi magana da Amarya sannan a turawa kowacce qawa nata.
Bayan angama yimusu nasiha Hajiya Zaliha takamo Amarya suka futo,yayinda Jawad yabi bayan Bilkisu domin yin sallama da baqi, Su Fatsime da Bintu suna zaune sunata fira,Jawad ya tsugunna yayi musu godia akan halartar taron da sukai,sannan ya kalli Bilkisu yace"Mama kifada musu daga nan zasu wuce Saudia tare daku idan kunyi Umarah saisu wuce gida"
'Dayyaba ta fashe da kuka tace"Allahu akbar,haihuwa me rana,yau Muhammadu ne yabiya mana Umarah,Allah yayi maka albarka Muhammadu"
Cikin nutsuwa Jawad ya amsa mata,daga nan suka futo shida Bilkisu har zuwa gaban motoci,Bilkisu ta rungume Inaas tayi qasa da murya a setin kunnanta tace"Inaas banda wasa da abubuwan dana fada miki kinji ko? ki nutsu ki kula da Yayanki kiyi masa biyaiya"
Cikin sauri Inaas da tasha kuka saboda zafafan nasihohin da iyayen nasu suka musu tace"wai ina zamuje ne Ammiy?"
Bilkisu tace"mijinki yace yanaso kutafi qasar Qatar daga wajan dinner,Daddy yace bazai iyu ba dole saikun dawo gida kunyi sallama da mutane tukunna,muma cikin satin nan zamu wuce Saudia bayan mun gama sallamar baqi"
Inaas tafashe da kuka tasake rungume Ammiy cikin kuka tace"to haka akeyi,kawai kuma Ammiy saiku barshi daga daura aure yatafi dani,meyasa bazamu zauna tare daku ba? Ammiy gaskiya ni bazan bishi ba"
Hajiya Zaliha ta kallesu tace"to ya zamuyi Inaas? mijinki ne yace yafi so kutafi yau,dole zaki yiwa mijinki biyaiya"
Daddy ya kallesu yace"me ake jira ne? Man Sulaiman shiga mota muje"
Man Sulaiman da Abban Inaas da Daddy suka shiga mota,Inaas tana kuka Bilkisu tana kuka haka sukaja mota suka tafi, yayinda Jawad yashiga daya motar,iya maza ne kawai suka rakasu Airport,Mummy da Bilkisu da Yaya Mariya suna gida.
Saida jirgin su yatashi,sannan Daddy da Abban Inaas da Man Sulaiman suka juyo gida.
har cikin jirgin ma Inaas kuka take sosai,Jawad ya kalleta ya lumshe idonsa,sannan yajata jikinsa ya shigar da'ita cikin faffadan qirjinsa ya rungume ta yana sakin ajiyar zuciya.
Sunyi tafiya me nisa sannan suka sauka cikin dare,P.a da sauran guard dasuka riga su zuwa,sune sukazo Airport daukarsu,Inaas kam batasan sunzo ba,tunda tajita ajikin Jawad batasan lokacin datayi bacci ba.(🙈)
Hakan yasa yadauketa cak daga cikin jirgi zuwa mota,saida suka sauka awani hadaddan gidansu wanda yayi shahararran kyau sannan yafara qoqarin tashinta daga bacci,amma bata tashi ba,hakan yasa guard dinsa suna bude masa mota yasake dauko ta cak suka futo,saida ya danyi tafiya kad'an zuwa hanyar da zata kaisu falo sannan yajuyo yace"P.a"
Cikin sauri P.a ya qaraso yace"na'am Yalla6ai"
Yadan motsa lips dinsa kad'an sannan yace"zaka iya barin wayoyin ka a kunne kaci gaba da tafiyar da al'amura,amma ni ka kashe wayoyina"(🙊)
Cikin girmamawa P.a yace"ok sir"
Sannan Yajuya yana murmushi.
Jawad kuma ya qarasa ciki,Suna shiga cikin falo ya rufe qofar sannan yazubawa kyakykywar fuskarta ido yana kallon yanda take bacci ajikinsa tayi luf kamar tasamu katifa.
Yayi murmushi ya qarasa ciki ya zauna akan wata irin hadaddiyar kujera sannan ya sunkuyar da kansa yadora lips dinsa akan nata lips d'in yayi kissing,amma shiru Inaas bata tashi ba,hakan yasa ya lumshe idonsa yamaida bakinsa kan nata yakama lips dinta na qasa yana tsotsa cikin wani irin salo kamar maye.
Jin kamar a mafarki anasha mata baki hakan yasa tafarka a zabure,adede lokacin yabude rinannun idanunsa yasaka shi cikin nata idon,cikin wata irin murya acan qasan maqoshinsa yace"ina miki barka da shigowa gidanki,Mrs. J. Sulaiman"
Inaas ta yunqura tatashi ta zauna sosai akan cinyarsa tafara waige waige tana qarewa falon kallo yanda aka kafa photunan ta tako ina,tsananin mamaki ya kamata ganin wani photon tun ranar da sukaje wajan Birthday dinsa,wani tasan anyi wani bata sani ba,wani kuma ranar da ake mata qunshi ne afalon Mummy,sosai aka yiwa pictures din editing ta ko'ina itace a manne afalon.
(Qarfi da yaji ango ya dauke Amaryar sa ya barmu da hayaniyar biki 🤔🤔)
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.
300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.
Amnah El Yaqoub✍
[1/20, 14:36] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne, idan kika karanta baki biyani haqqina ba banyafe ba nabarki da Allah 👌🏻

____
Sosai Bilkisu take kuka adaki tun bayan tafiyar Inaas,baqinta 'yan biki sai haquri suke bata,amma kokadan batayi shiru ba,hakan yasa d'aya daga cikinsu tatafi wajan Hajiya Zaliha ta sanar da'ita,bayan Hajiya Zaliha tazo dakin tanemi waje ta zauna abakin gadon ta dafa Bilkisu,da muryarta wadda take gab da dashewa saboda yawan magana tace"Bilkisu har yanzu de kukan ne? kiyi haquri mana aure fa yagaji haka"
Cikin kuka Bilkisu tace"Hajiya dede da kwana d'aya,ban ta6a rabuwa da Inaas ba tunda mahaifiyar ta tarasu,tare muke komai,tare muke shawara,kullum tana gefena"
Fatsime tace"to Balki aure ai ya gaji haka,bare ita data auri dan'uwan ta,menene zai dameki?"
Hajiya Zaliha tace"Bilkisu saide kiyi kukan rabuwa da Inaas saboda sabo,amma ba saboda ta fada hannun Jawad ba,na tabbatar zai bata kulawa fiye da wadda kike bata,kidena kukan haka dan Allah"
Bilkisu ta gyad'a mata kai alamun amsawa,sannan suka dinga bata baki harta dan ware akaci gaba da fira.
*** *** ***
Saida tagama kallon photunan tsaf sannan ta juyo ta kalleshi,ya lumshe idonsa sannan yasake maidata cikin jikinsa yacusa hancinsa cikin wuyanta yana goga mata dogon hancinsa awuyan nata yana shaqar qamshin dake tashi ajikinta,ahankali tasaka hannunta tad'ago masa kansa alamun yadena abunda yake,hakan yasa yad'ago kansa yadauketa cak,suka nufi dakinsa, ya direta akan gado sannan yace"ga toilet nan,ki shiga kiyi wanka,muyi sallah,muci abinci mukwanta muhuta"
Yafadi haka yana qoqarin cire agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa.
Inaas ta gyada masa kai,sannan tatashi tashige toilet din,tasa mukulli ta rufe qofar saboda tsaro.
Tacire kayanta ahankali sannan ta nufi wajan kunna ruwa tarasa yanda zatayi ta kunna,saboda babu irin toilet din a house(😂)
Ta ta6a tasake ta6awa taji shiru ruwa baizo ba alamun de bata kunna daidai ba,hakan yasa ta kalli toilet din sosai taga wasu towels kala-kala acan gefe,taja guda daya ta daura,ta dauki dankwalin kanta data cire ta yafa ajikinta sannan tabude toilet din tadan leqo kanta tace"Yaya!"
Jawad daya cire babbar rigar jikinsa yajuyo ya kalli toilet d'in yace"what"
Tace"nakasa kunna komai,bansan ya zanyi ba"
Jawad yayi murmushi yatashi yanufo ta,tana ganin zai shigo toilet tasake matsawa can gefe tana saka hannu tana rufe fararen cinyoyinta,ya kalli cinyoyin nata yazuba musu ido sannan ya kawar da kansa yace"keda gidanki tayaya zaki kasa gane komai? zoki gani"
ya qarasa maganar cikin bata umarni.
Inaas ta matso kusa dashi yafara nuna mata komai,sannan yabata dama ta kunna yagani,tasa farin hannunta me zanan ja da baqin lalle tafara gwada masa yanda taga yayi,ya kalli hannun nata yanaji kamar yadora hannunsa akai yatsotse qunshin,sannan yamaida kallonsa zuwa qirjinta saboda yanda yake d'an hango shi ta saman towel din,yakawar da kansa daqyar, yayi qoqarin seta kansa yace"yayi"
Yajuya ya futo daga toilet d'in.
Inaas tasaki wata irin ajiyar zuciya,sannan ta kulle qofar tafara wanka.
Akan gadon ya zube yana maida numfashi,daqyar ya lallashi kansa ya daure,yadauki remote ya kunna kayan kallon dakin, yarage volume, yajirata harta futo daga wankan,yanajin motsin futowar ta yajuyo yazuba mata ido,kasa janye idonsa yayi akanta,saida wani 6angaren na zuciyar sa yatuna masa cewa ba suyi sallah ba, sannan yatashi yashige toilet din,agurguje yayi wanka ya futo qugunsa daure da towel,dantsan hannunsa dasuke a mummurde ya futo fili,gawani gashi baqi me laushi da ya kwanta akan faffadan qirjinsa,Inaas data maida kayan jikinta tana ganinsa ahaka tayi sauri ta runtse idonta,ya kalleta yayi wani miskilin murmushi sannan yabude wardrobe yadauko riga yasaka,itama ya dauko mata wasu riga da wando me santsi ya ajiye agabanta.
hararar kayan tayi,taqi dauka tasa,ya kalleta yace"kisa kaya ga hijab can a wardrobe kisa kizo muyi sallah.