Sashe 45
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wajan takwas da rabi Ammiy ta sauko daga sama,tabar Jawad adaki zaiyi wanka yashirya,Hajiya Zaliha dake zaune tayi murmushi tace"Bilkisu kin tashi? yaya Jawad din yake?"
Ammiy ta nemi waje ta zauna yace"lafiya kalau yake Hajiya,yanzu ma na barshi zaiyi wanka,nima zuwa zanyi nayi wanka na shirya"
Hajiya Zaliha tace"A a,ki dakata kici abinci tukunna,yau harda 'yar dakina a kitchen din,ta dage saitayi aikin breakfast din itama"
Bilkisu tayi murmushi ta daga muryar ta wadda tafara dashewa saboda kuka tace"Inaas!!"
Cikin sauri Inaas tafuto daga kitchen bakinta a washe,tace"Ammiy kin tashi?,ina kwana?"
Cikin farinciki tace"natashi lafiya Inaas,ina Abban ki?"
Kafin Inaas tabata amsa wani guard yashigo falon ya rissina awajan Hajiya Zaliha yace"Hajiya wani matashi ne yazo yace yanason magana da Inaas"
Cikin sauri Hajiya Zaliha da Bilkisu suka hada baki wajan fadin"Inaas kuma?"
Guard din ya jinjina kansa alamun tabbatar wa,Bilkisu tace"Inaas da bata fita tayaya wani zaizo wajanta?"
Hajiya Zaliha tace"A a,ai bamusan waye ba"
Tajuya ta kalli Inaas tace"jeki gano ko waye"
Inaas ta gyada kanta,sannan ta warware Mayafin Abayar data daura akanta,tabi bayan guard din.
A Compound taci karo dawani matashin saurayi dan gayu,cikin mamaki ta qarasa wajansa bakinta dauke da sallama,yadubeta da wani irin murmushi sannan yace"sannu da zuwa gimbiya"
Kalmar daya fada ta gimbiya ta daure wa Inaas kai tace"Nice Gimbiya?"
"Yes,kece mana,amma fa Gimbiyar zuciyata,ni Sunana Haneef,mahaifina sanan nan mutum ne a wannan garin,ina aiki agarin nan sannan lokaci zuwa lokaci ina zuwa qasar India order kaya,bazan 6oye miki ba tun lokacin dana ganki keda Yayanki da Mamanki a Super Market naji kin kwanta min,naji cewa tabbas na samu matar aure,najira ku awaje har kuka gama abinda kuke kuka futo,na biyo bayan motarku,har naga gida,Allah da ikonsa ina zuwa danayi wa security kwatancen ki, sai suka cemin sunan ki Inaas,ina fatan zaki kar6i soyaiya ta?"
Inaas tayi ajiyar zuciya sannan tace"to nagode,amma inaso kabani lokaci zanyi tunani kuma zanyi shawara da Mamana"
Cikin jin dadi Haneef yace"Hakan ma yayi,kuma kin birgeni,inason mutum mai mutunta mahaifiyar sa"
Inaas tayi murmushi d'an kadan sannan tace"to zan wuce gida nagode"
Cikin sauri Haneef yace"to kinga,please Number kifa?"
Yafad'i haka yana miqo mata wayarsa.
Inaas ta kar6a ta saka masa number,sannan tajuya takoma ciki.
Tana zuwa falon Bilkisu tace mata"ke waye yazo wajanki?"
Inaas tayi murmushi tace"Ammiy ashe jiya da mukaje Super Marke wani ya ganni,shine ya biyo bayan motar mu yaga gidannan,shine yazo yacemin sunansa Haneef kuma shima anan garin yake,wai yana sona,nace masa nide sainayi shawara dake tukunna,shine yace na bashi number ta, nabashi nayi masa sallama na taho"
Dukkan wannan bayanin da Inaas takeyi gaba daya sun shiga cikin kunnan Jawad tsaf,yagama jin komai,fuskar nan tasa kuwa tahadu tayi baqi kamar hadarin dake shirin sauko da ruwa,babu wanda yasan ya qaraso wajan saijin maganar sa sukai yana fadin"ke wato ko wanne jaki,da kowanne mahaukaci,da kowanne daqiqi yace yanason ki saiki tsaya harma ki bashi number ko?"
Cikin sauri Hajiya Zaliha da Bilkisu suka juya suna kallon Jawad,Hajiya Zaliha ma duk da bataji dadin zuwan baqon Inaas dinba haka ta daure ta kalleshi da kyau tace"Haba Jawad!,meyayi zafi haka?"
Jawad dayake ji gaba daya duniyar ta masa zafi saboda jin Inaas tayi saurayi ya kalli Hajiya Zaliha kamar zai fashe da kuka yace"Haba Mummy,wannan abun kunya ne awajena,wani yazo ya tsallake ni,duk irin tsaron gidannan,yazo yace yana sonta"
Bai saurari amsar Mummy ba yajuya ya kalli Inaas yace"kifada masa karya sake zuwa,idan kika sake saurarar sa saina kakkarya ki"
Cikin sauri Inaas tatashi tafice daga falon da gudu cikin wani irin kuka.
Bilkisu ta girgiza kanta ta kalli Mummy tace" Hajiya kijawa danki kunne,mu bamu saba da irin wannan fad'an ba,bari naje na lallashi abata"
Tafadi haka tareda miqewa tabi bayan Inaas.
Jawad ya zauna cikin 6acin rai yace"Mummy ina Daddy?"
Hajiya Zaliha tayi ajiyar zuciya tace"Daddynka yafita shida Fu'ad da Man Sulaiman,zasuje dubiya ne,sun jiraka baka tashi daga bacci ba,nace zan je na tasoka amma ya hanani tashinka,amma nasan sun kusa dawowa saboda ko Breakfast ba suyi ba suka fita"
Jawad yayi ajiyar zuciya yace"Allah yasawaqe"
Mummy tace"Amin ya Allah,muje nabaka abinci"
Babu musu Jawad yamiqe suka nufi Dining,Mummy tana tambayar sa yanayin jikin nasa.
****
Ganin Inaas bata falo hakan yasa Bilkisu tabi bayanta zuwa daki, tana shiga kuwa ta ganta a kwance akan gado tanata faman kuka,Bilkisu tajata jikinta tafara bubbuga mata bayanta alamun lallashi sannan tace"kukan nan ya'isa haka Inaas,menene abun kuka saboda Yayanki yayi miki fada? so kike yabarki kizama marar jin magana?,shi dinfa yayanki ne,tunda bayaso daga yau kidena kula samarin"
Inaas dake kuka cikin shagwa6a tace"Ammiy shima fa ba sona yake ba,kuma ya hanani kula wasu"
Bilkisu ta lumshe idonta,taja Inaas jikinta ta rungume ta,ita kanta tarasa dalilin da yasa Jawad din yadauki irin wannan zafin haka,kawai saboda ta kula saurayi,haka ta dinga lallashinta harta samu tayi shiru.
****
Acan falon Mummy kuwa saida ta tabbatar Jawad ya qoshi,sannan tabar Dining din tawuce daki zata dauko wayarta.
Shima Jawad tashi yayi yadawo kan kujera ya zauna,yana juyawa yaga wayar Inaas agefe,cikin sauri yabude wayar yafito da Sim Card dinta ya karya shi.
Karaf akan idon Mummy wadda ta futo daga cikin dakinta,tana ganinsa yagama karya layin,sannan ya ajiye ya koma gefe ya zauna kamar ba shiba.
Tasaki murmushi taqaraso zuwa falon tana kallon Jawad,yanzu kam tagama gane cewa tabbas Kishi ne yake damun Jawad.
Hakan yana nufin yanason Inaas din kenan,miskilanci dakuma zurfin ciki ne ya hanashi bayyana mata.
Ta dubeshi zatayi magana sai su Daddy suka shigo falon,Jawad yana ganin Daddy yatashi ya nufeshi ya rissina ya gaida shi,sannan ya gaida Man Sulaiman.
Daddy ya kama hannun Jawad yace"muje can wajan Bilkisu akwai maganar danake so muyi"
Babu musu Jawad yabi bayansa,sannan Mummy da Fu'ad da Man Sulaiman suka suka biyo bayansu.
Suna zuwa falon,sukaga Farouq ne kawai a zaune,bayan sun zauna Farouq yakira Bilkisu da Inaas dake cikin daki, suma suka futo falon baki d'aya,Inaas ta saci kallon gefen da Jawad yake zaune ta murguda masa baki,sannan ta zauna agefen Bilkisu,Jawad sarai ya ganta,bai nuna alamun komai ba ya sunkuyar da kansa qasa,Mummy dake kallon Inaas da Jawad tayi murmushi tana girgiza kai.
Daddy ya kalli kowa sannan yace"Farouq bude mana taro da Addu'ah"
Abban Inaas yace"salati goma ga Annabi....S.A.W"
Saida suka gama Addu'ah suka shafa, sannan Daddy yace"Dukkannin ku,kunsan dalilin taruwar mu anan,naso tun daren jiya munyi wannan zama amma hakan bata samu ba,Jawad kayi haquri,kowanne bawa dakake gani da irin tasa qaddarar,Allah yasoka taka qaddarar mai kyau ce,domin kuwa bakayi maraici ba,sannan adede lokacin da kasan cewa ba mune muka haife ka ba alokacin ne kagano su waye asalin iyayanka,hakan bawai yana nufin mu din mun tashi daga kan yanda muke bane,ina roqon Alfarmar iyayenka akan subarmin kai muci gaba kamar yanda muka saba,babu wanda yasan wani abu yafaru a wannan ahali namu, banaso kuma asani,mu riqe sirrin juna mu taru mu rufawa kanmu asiri,Bilkisu da Man Sulaiman kuma gasunan kajasu a jikinka,haqiqa sun soka,bakada tamkar su,gasunan saboda ka 6ata har yanzu Bilkisu taqi su daidaita kansu amaida wannan aure, inajin de kaine zaka qarasa sauran aikin"
Daddy ya qarasa maganar cikin barkwanci, gaba d'aya falon saida kowa yadan daara,yayinda Bilkisu ta kauda kanta gefe tana karkad'a qafa.
Man Sulaiman yasaci kallonta ta watsa masa wani irin kallo.
Daddy ya kalli Farouq yace"to Abban Inaas nadawo gareka,Inama albishir danka yabaka matsayin MD na sabon kamfanin daya bude,nan da wasu yan kwanaki zaka fara fita aiki insha Allah,kafin asamo wa Inaas wata sabuwar Antyn"
Farouq yayi murmushi yace"Alhaji mungode sosai,irinku basuda yawa awannan lokacin,Allah ya rayama zuri'arka,haqiqa bamuda bakin dazamu gode muku,Allah yaqara hade kan wannan ahali daga yanzu har zuwa qarshan numfashinmu"
Gaba d'ayansu suka amsa da "Amin"
Farouq ya maida kallonsa wajan Jawad yace"Jawad nagode sosai da irin wannan muqami,insha Allah bazan baka kunya ba,zamuyi aiki yanda ya kamata"
Jawad yayi sauri ya sunkuyar da kansa qasa,wata irin kunyar surukin nasa tana mamaye shi.
Daga nan gaba dayansu suka futo daga falon,a kabar Jawad da Bilkisu da Man Sulaiman.
Inaas takama hannun Mummy ta riqe suka futo yayinda Fu'ad yake janta da zance aikuwa tasamu abinda takeso nan da nan tasaki jiki tana zuba surutu.
Bayan anbarsu su uku afalon babu wanda yayi yunqurin yin magana,Jawad yatashi yakoma kan kujera kusada Bilkisu ya zauna,yakama hannunta ya riqe yace"Mama ki yafewa Uncle,nikaina kwanaki can bayan naji abunda yafaru awajan Daddy banyi wa Uncle uzuri ba,Bansan cewa qaddarar akaina take faruwa ba,dan Allah Mama kiyi haquri nasan kinsha wahala,amma kiyi haquri amaida muku aurenku,nima hankali na zaifi kwanciya Mama"
Bilkisu ta kalli Jawad tace"Muhammad,nifa na riga na dade da yafewa mahaifinka,maganar aure ce de nace bazan sake aurensa ba,lokacin daya tafi yabarni da cikin ka yayi tunanin wannan ranar ne? qarewa kudin dana bashi nace ya dinga tarawa har zuwa lokacin dazan haihu mu sai abun suna dashi,da kudin ya gudu,yatafi yabarni nida kai ko tausayi babu,in aure shi ince na auri me?"
Cikin sauri Man Sulaiman yace"kice kin auri mutum,kuma mutum cikakke wanda kika samu santalelan yaro dashi"
Jawad ya runtse idonsa ya bude yace" Mama,abar kaza cikin gashinta,babu dad'i tone-tone"(😂)
Bilkisu tace"kanajin abinda yake fada fa,in banda yaci darajar ka tayaya zan dinga magana yana bani amsa bayan laifin dayamin,gara a fige kazar kowa yahuta"
Jawad yace"A a Mama,abarta de cikin gashin ta,idan kikai tunani kin riga kin hada jini dashi,Mama zamanku ahaka nima bazanji dadi ba,kowanne iyaye suna zaune tare saboda 'ya'yansu da dad'i ba dad'i,kiyi haquri ki yafe masa amaida aurenku kada mutane sumin dariya"
Cikin rawar murya Bilkisu tace"amma kanajin abinda yake fadamin fa, meyasa shi bazaka masa fad'a akan laifin dayayi min ba,lokacin da kana jariri nayi ma hud'uba cewa duk lokacin daka girma saimun bawa Babanka kunya,ashe bazaka tayani ba?"
Jawad ya lumshe idonsa,yabude,yajuyo ya kalli Man Sulaiman sannan yace"Uncle Please...,Kabawa Mama haquri"
Babu musu Man Sulaiman ya sauko yadawo gabanta,ya tsugunna, sannan yakama fararen qafafunta ya riqe,ya sassauta murya yace"Bilkisu...kiyi haquri,inaso ki yafemin amaida mana aurenmu kodan saboda Jawad"
Jawad ma ya kalleta ya marairaice yace"Plaese Mama,Allah yanason masu yafiya"
Bilkisu tayi ajiyar zuciya sannan ta kalli Man Sulaiman tace"shikkenan na amince,kaje amaida auren,kaci darajar d'anka"
Tana fadin haka tatashi tawuce daki,Jawad yayi murmushi ya shafa sumar kansa shima yatashi ya futo yabar musu Plat din.