← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 63

Sashe 10

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari sassafe Man Sulaiman yayi sallama da Abuja yatafi Jigawa kamar yanda Alhaji Mekudi yabashi shawara jiya.
Kasancewar jirgi yabi hakan yasa wajan shabiyu na rana ya isa garin,tunda yashigo garin yake kalle-kalle yana tuna baya,agefe guda kuma banda fad'uwa babu abinda gabansa yakeyi,duk wanda yake had'uwa dasu babu wanda yasani shima babu wanda yagane shi,kai tsaye gidansa yanufa anan yaga gida yazama gidan tarihi domin kuwa sai fili,d'akinsu qwaya d'aya na qasa shima babu yazube,nan take ya zube awajan yadira gwiwar sa aqasa yafashe dawani irin matsanancin kuka,hakan yasa yara suka fara taruwa a kansa ana kallonsa,daga nan manyan gari sukaji labari suka nufo wajan,d'aya daga cikin manyan ne yace"kamar Malam Manu"

Man Sulaiman yad'ago kansa da sauri ya kalleshi,kallo daya yayi masa yagane shi, cikin kuka yace"nine malam jafaru"

Mutumin da'aka kira da malam jafaru yace"ikon Allah,ashe muna raye Allah zai nuna mana wannan ranar,Malam Manu Ina kashige?munyi tunanin kaida Balki Me gwanjo rai yayi halinsa"

Cikin sauri malam Manu yanufeshi yace"Ina take? Bilkisu tana raye? meta haifa malam jafaru?"

Malam jafaru yagoge qwallar idonsa yace"malam Manu kad'au haqqi,Balki me gwanjo tatafi,haqqinta bazai barka ba,mu qarasa wajan Maigari sai kaji komai"

Tunda malam jafaru yace Balki me gwanjo tatafi daga nan jikinsa yayi sanyi,saboda yayi tunanin tafiyar mutuwa yake nufi.

Lokacin dasuka qarasa wajan Megari saiyaga ba Megari daya sani da bane,wancen Megarin yamutu,d'ansa ne akan kujerar yanzu,bayan kowa ya nutsu ya zauna daya daga cikin tsofaffin fada wanda yana raye akayi komai,ya girmi Manu sosai, tsoho ne, ya kalli Man Sulaiman yace"kalleni nan Manu,bakaji kunyar zuwa garin nan ba? Manu me Balki tama har haka dazaka gudu kabarta,Ina kakeso taje? gidan uwaka kakeso tatafi bayan kasan bayan kai batada kowa agarin nan? meyasa bazaka sata agaba kutafi ko nanda bangon duniya bane? to Balki ta haihu,da haifi d'anta namiji kuma Washegarin suna takama hanya tatafi qasar su,marigayi Megari yace tazauna damu abata jari har Allah yadawo dakai lafiya idan kana raye,amma Balki tace gida zata tafi,saboda haka bamu saniba itada abinda ta haifa suna raye ko sun mutu,sai kaje can qasar Niger din kaita bilayin nemanta qila ma idan kun had'u tahad'o maka matasan unguwa suyima shegen duka"(🤭😳😂)

Malam Manu ya sunkuyar da kansa qasa yana kuka,sosai yake kuka harda shashsheka yakasa cewa komai.

Maigari yayi gyaran murya yace"ayi haquri Baba Muntari,komai yawuce tunda gashi yatuba yadawo mahaifarsa,saide muyi masa Addu'ah Allah ya baiyana masa iyalinsa idan tana raye"

Gaba daya fada aka amsa da "Amin"

Megari ya kalli wani yaro yace"zakariyya a rakashi cikin gidana abashi masauqi da abinci"

Ahankali malam Manu yadago kansa yayi godia sannan yace"inaso nafara biyan bashin dana tafi nabari akaina"

Megari ya kalleshi yace"kaje kahuta Kaci abinci tukunna, zaka biyasu insha Allahu"

Malam Manu yatashi aka kaishi gidan Megari dakin da ake saukar baqi,yayi wanka yaci abinci yazauna yayi shiru yana tunanin baya,lokaci zuwa lokaci yanajin hawaye yana zubowa daga idonsa,acikin wannan garin yahadu da iyayen Bilkisu sun kawo tallar magani,kafin su rasu suka bashi ita tareda amanarta,a wannan Garin iyayen Bilkisu suka rasu,yasan cewa tanada qaninta wanda suke uwa daya uba daya dashi wato Farouq,yasan Farouq sosai tun kafin a bashi Bilkisu,bayan iyayensu sun rasu sai shi Farouq yakoma Niger,yanzu shekaru talatin da bakwai baisan ta'ina zai fara neman Bilkisu ba,dole zaije qasar Niger cikin garin Dungas yanemota aduk inda take, hawaye suka sake zubo masa,yabuga kansa da bangon dakin yanajin kamar yadawo da baya gaba.

Saida yayi sati daya agarin,duk wasu abokan sa nada dasuka gujeshi yanzu duk sun dawo,duk wani bashi da yasan ana binsa saida yabiya harda ninki,idan dubu daya kake binsa zai ninka maka saboda darajar kudin da d'in dana yanzu ba d'aya bane,abinda dubu d'ayan da zata maka yanzu saide dubu uku ko hud'u.

Filin gidansa yasa mutane suka sake gyara shi aka fara yimasa ginin cement,samarin dasuka suka masa dukan kudin bashi a wancen lokaci yanzu d'aya bayan d'aya suka dawo suna bashi haquri.

Saida yayi kwana goma cif,sannan yadora wani abokinsa akan harkar ginin gidansa, shikuma yayi sallama da mutane cikin aminci.
Daga nan kai tsaye qasar Niger yanufa,bai zame ko'inaba sai garin Dungas,saida yayi kwana biyu yana tambayar su Bilkisu da Farouq amma babu wanda yagane su saboda kawai suna yake fada babu inkiya,yasha wahala kafin yasamu wanda yagane su Bilkisu,hakan yasa mutumin yayi masa jagora har gidansu Bilkisu,saide basa gidan wasu 'yan haya ne aciki,maqotan su sun tabbatar masa cewa su Bilkisu sun saida gidan tun shekarun baya,sunkoma cikin Niamey da zama.
Man Sulaiman yarasa yanda zaiyi,acikin Dungas ma yayi kwana biyu yana nemansu,to idan yashiga Niamey ta'ina zai fara nemansu? wa zai kama?,hakan yasa yabi jirgi yakoma Abuja da nufin idan yasake shiryawa saiya dawo ya bazama neman Bilkisu.

*** *** ***

Niger Republic

Tana dawowa daga wajan aiki tafara warware laffayar jikinta fara,ya kasance sai wata riga aciki 'yar qarama,ta zauna a kusada Bilkisu tace"Mom kinsan me?"

Bilkisu tace"baki abun magana, yau kuma da mom kika dawo abakinki?"

Inaas tace"emana,ai talaucinmu bazai hanamu walwala ba"

Bilkisu tazuba mata ido tana kallonta,tana ganin tsantsar kyawun Inaas,kyawu me fizgar duk wanda yayi tozali da'ita,cikin farinciki tace"fad'amin,meyafaru yau kuma? yaya aikin naki?"

Inaas tace"yawwa Ammiy,aiba dole sai masu kudi ne sukeda damar dazasu ce mummy ba,muma zamu iya fad'a,aikina lafiya kalau,dad'i nakeji wata yakusa qarewa,nakusa jin qaramm.... albashi ya fad'o in siyo mana kayan kallo,kede kimin Addu'ah kawai"

Bilkisu tayi murmushi tace"tunda kikace zaki siyo mana kayan kallon nan nasan zaki iya Inaas,kina qoqarin sanyani farinciki,Allah yasa shima idan yana raye,yana qoqarin saka nakusa dashi a farinciki,saboda daga ke har yayanki Muhammad kuna zagaye da sanyawar albarka ta,kullum cikin saka muku ita nake babu ranar banza, Allah yasake yimuku albarka,yarinyata 'yar albarka ce,nasan duk mijinda kika aura yayi sa'ah"

Farinciki yakama Inaas,tana so taji Ammiy tana yabonta tana zuzutata fiyeda mijinda zata aura, cikin farinciki ta rungume ta, sannan tayi cikin daki.

*** *** ***

Zaune yake akan kujera,fuskarsa babu walwala kawai aiki yake yamaida hankalinsa kacokam kan laptop din dayake daddannawa qirar apple,yayinda guards guda biyu suke tsaye a kansa gaba d'ayansu su biyun suna sanye da baqaqen suit,p.a dinsa yana gefe shima a tsaye yana shafa wata babbar iPad d'in Jawad.

Yashiga cikin yanar gizon Jawad d'in yana fada masa abubuwan dake faruwa dakuma saqonnin da'aka tutturo masa,bayan yaci karo dawani posting da'akai a Instagram yadago ya kalli maigidan nasa yace"yalla6ai gawani masallaci yazube,mazauna wajan suna buqatar a tallafa musu zasu sabunta ginin"

Ba tareda yadago kansa ba,idonsa akan computer gabansa yace"atura musu"

Cikin sauri p.a ya russuna yace"ok sir"

Yaci gaba da duba saqonnin yana bawa mutane amsa, saida yadauki kusan minti ashirin sannna yasake kallon Jawad yace"yalla6ai gawani shafi sun dora photon wani yaro qashin bayansa yasamu matsala sakamakon daukar buhun shinkafa,za'a yi masa aiki ana buqatar one million naira,yanzu sun had'a seven hundred thousand Naira "

Wannan lokacin ma batare daya kalleshi ba yace"atura musu two million,please p.a kayi abinda yadace, banason magana"

p.a yanajin haka yayi gum da bakinsa (🤫)

Da yamma kamar yanda yasaba da gashi sai wani gajeren wando yashiga cikin swimming pool din gidan yana swimming,yadade sosai yanayi sannan yafara taka wata matattakala zai futo,yana futowa ruwan dabe gama barin jikinsa ba yake tsiyaya aqasa,yayinda lafiyaiyar farar fatar jikinsa take daukan ido tana wani irin shinning,yayinda gajeren wandon jikinsa yaffida shatin abubuwan sa muraran(🙈)
Kasancewar yashiga ruwa.

yana qarasa futowa wayarsa tafara qara,p.a ya matso da sauri yabashi,guard dinsa kuma sukai sauri suka sanya masa wata farar riga ta towel kawai shide hannunsa yabude musu sukuma suka zura masa rigar daga bayansa.

Wayar yakara a kunnansa, daga dayan bangaren baby tace"Hello Yaya"

Yasan cewa su Daddy basu da wata yar'uwa sai Yaya Mariya kuma batada qananun yara,haka Mummy batada wata alaqa da yara,hakan yasa mamaki ya kamashi jin muryar yarinya tana kiransa,cikin mamaki da rashin sani yace"wacece?"

Daga d'ayan bangaren Baby tace"oh kama manta dani Yaya? Baby ce,Babyn Niger,yaushe zakazo kakawo min chocolate din?"

Lokaci d'aya yatuna da yarinyar,yasaki wani irin murmushi sannan ya zauna yace"Baby waye yabaki number ta?"

"wajan Papa naje yabani,Yaya zakazo gobe? inaso inganka inaso kakawo min chocolate"

Cikin sauri Jawad yazaro idonsa yace"gobe gobe Baby? kinga nayi miki alqawari very soon zanzo,amma sai kinyi qoqari a school kinzo ta d'aya"

Cikin zumud'i tace"to zaka siyomin teddy?"

"harda jirgin sama metashi Babyna,zan daukeki mutafi Europe kiyi wasa"

Cikin farinciki yarinyar tace"to Yaya saikazo,I luv you bye bye"

Bata jira amsar sa ba ta kashe wayar,Jawad yasaki ajiyar zuciya yana murmushi,sannan yabawa p.a dinsa wayar tareda fadin "kiramin Daddy"

P.a ya kar6i wayar yafara neman layin Daddy cikin ransa yana mamakin yanda Yalla6ai Jawad yake son mahaifinsa,wani lokacin ko awa uku ba'a yi zaice akira masa shi.

*** *** ***
Niger Republic

Tsaf tagama shiryawa cikin baqar laffaya,laffayar ta tsufa amma ta goge ta sosai babu alamar datti ko tattarewa ajikinta,ta dauki kibiya ta tsaga dogon gashinta tarabashi abiyu,sannan tafuto tsakar gida wajan Babanta da Ammynta ta tsugunna agaban Bilkisu sannan tace"Ammiy dauremin"

Babu musu Bilkisu tasa hannu ta daure mata gashin nata sosai yanda bazai kunce ba,tamiqe tsaye tasake gyara laffayar sannan ta kalli Bilkisu tace"to Ammiy nikam nagama bani kud'in kayan gwanjon"

Bilkisu tace"kije ki kar6o kawai sai akai mata kud'in daga baya idan ansamu"

Cikin sauri tace"kai Ammiy dan Allah,ni wallahi banason naje nace mata tabamu kayan nan babu kud'i,nikam Allah ki kawo kudin natafi"
Tafadi hakan cikin sigar shagwa6a.

Cikin sauri Bilkisu tajata jikinta cikin sigar lallashi tace"kinga ya'isa haka,haba Inaas,kayan nanfa duk sati muke kar6a,kuma bamu ta6a cinye mata kudi ba,yau d'aya de fisabilillah kije ki kar6o mana,itama ai tasan za'a bata ko?,yi maza kije ki kar6o karkuma ki tsaya awani wajan"

Dan qaramin bakinta taturo gaba sannan ta amsa mata tatafi.

Bayan fitar Inaas,Farouq dayake zaune yana karatun qur'ani yasaki ajiyar zuciya bayan yagama kallon dramar tasu yace"Yaya kenan,kina mata irin wannan soyaiyar tayaya zaki barta tayi aure?"

Bilkisu ta zauna ta fusukance shi tace" nikaina ina tunanin wannan ranar wallahi,nikam Farouq auren nan dolene ne sai anyi?"

Farouq yace"aure ba wajibi bane Yaya, amma sunnah ce mai qarfi"

"to gaskiya banajin Inaas zatayi aure, gara tabarshi tunda kaima yanzu gashinan kace ba dole bane,banaso tayi nesa dani,shiyasa nake Addu'ah Allah ya bayyana min d'ana inbatashi insa abata agaba inta kallonta" (🤭)
Chapter 10 · 0% Book details