← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 63

Sashe 23

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilkisu tayi ajiyar zuciya tace"Inaas, nita kayan dakinki nakeyi ba nawa ba,yanzu ni in sauya kayan daki ince nayi me? nida ba miji ba inani Ina wani sauya kayan daki,kayan dakinki ne agabana nida mahaifinki, musamu kafin lokacin bikin kema amiki kaya me tsadar gaske,d'an aikin kamfanin dakika fara muna murna shima yanzu babu,da ina tunanin inje ni dake da babanki mubawa manajan kamfanin haquri ko Allah zaisa su maida ke, to shugaban kamfanin yazo har gida kingama yimasa zagin duniya,kinga kuwa Ina zamu samu gwarin gwiwar zuwa basu haquri?,ko munje musu kamfani idan yaji labari zai musu waya yace karsu maidake,inda ace baki cimasa mutunci bane ma toda sauqi,amma lokacin dazai tafi ma inaji kina cewa dole ne saina rakashi? kuma shima yanajin ki sarai,shiyasa nake hanaki wannan shegen surutun naki, dan wata rana sai kinja anzo har gida an kamamu"

Inaas tahade girar sama data qasa,dan qaramin bakin nan nata tacunoshi gaba,batace komai ba ta dauki qullin kayan gwanjon nasu tadora akanta sannan tafice daga gidan fiya-fiya cikin sauri kamar zata tashi sama.

*** *** ***

Abuja Nigeria

Washegari sassafe yatashi,ya shirya tsaf cikin baqar riga, baqin wando,fuskarsa tana sanye da glass jan duhu kamar kullum, yayi kyau sosai sai zuba uban qamshi yake gefe guda kuma farar fatarsa tafuto sosai acikin kayan.

Wayoyi ne a hannunsa guda biyu yana tahowa main falon gidan nasu yana magana qasa-qasa,gakuma takardu yana dubawa gaba daya yaraba hankalinsa biyu, ga waya ga duba takardu,atsakiyar falon yatsaya yana magana tareda cigaba da duba takardun,Mummy tataso hannunta daukeda cup din tea tanufeshi tana bashi tea din da spoon, babu musu yake bude bakinsa take bashi tea din saide saiya dan rissina mata sannan take bashi kasancewar yafita tsawo.

Wayar yakashe sannan suka zauna akan kujera taci gaba da bashi tea din,Daddy dayake zaune a dining yana breakfast ya kalleshi dakyau yace"idan kunje gonakin nan fa kakula dakyau"

Cikin nutsuwa yad'ago kyawawan idonsa ya kalli Daddy sannan yace"okay Daddy"
Daga haka yamiqe zai fice, Daddy ya kalleshi yace"yazaka fita bayan ko tea din baka gama shaba? Koma ka zauna,ayyukan nan sunada yawa Jawad bazasu qare ba,wannan dalilin ne yasa nakeso ka ajiye iyali,inda kayi auren ka toda tun aciki matarka zata baka breakfast bazata yarda ka futo bakaci komai ba"

Jawad yakoma ya zauna tareda murmushi kad'an.
Mummy tajuya ta kalli Daddy tace"Alhaji ai komai yazo qarshe,kwana nawane yarage ayi masa auren? ni munyi magana da Amal dinma, tacemin tayiwa Jawad maganar kudin ankon biki suna buqatar million goma sha biyar itada qawayenta"

Jawad yayi jimmm! yana tunani,million goma sha biyar kuma? just anko kawai million goma sha biyar har mezasu saka itada qawayen nata? idan bai manta ba ai million daya yarinyar tace tana buqata,kamar haka p.a dinsa yafada masa,kuma p.a yasan aikinsa, bazai fadi ba daidai ba.

Daddy ya kalli Jawad ko zaiyi magana dangane da kudin da Hajiya Zaliha tafada,but yaga Jawad din yayi shiru kamar yana nazari,to ganin yadade baiyi aure ba, kuma Jawad yasan meyake akan kashe-kashen kudi hakan yasa yayi shiru, duba da cewa Hajiya Zalihan tace ita yarinyar sunyi magana da Jawad din.

Jawad yadawo daga tunani kafin yayi magana wayar gefensa tafara qara,Mummy tasa hannu ta kashe wayar, sannan tace"lokacin cin abincinka ne yanzu"

Ko minti uku ba'a yi ba,p.a yashigo dakin bayan yagaida Mummy da Daddy ya rissina yabawa Jawad waya yace"yalla6ai ana kira"

Mummy tadafe goshin ta da hannunta tana girgiza kai alamun baza'a barshi yayi breakfast din bade.

Jawad yayi d'an qaramin murmushi yace"Mummy kibarshi naqoshi"
Yajuya ya kalli Daddy yace"Daddy saina dawo"

Daddy yace"Allah yadawo daku lafiya Jawad,kafin kasa musu hannu ka tabbatar idan kabasu kudin to noman zasuyi,wasu idan sukaga anbasu kudin taki saisu kashe kudin suqi yin noman"
Cikin nutsuwa ya amsa masa sannan yayiwa Mummy bye bye suka fice daga falon,zasu wuce wajan manoman dasukazo kwanaki ganinsa, akan aron kudi dazasu kar6a awajansa zasu sai takin gona, idan sunyi noman zasu dawo masa da kudin takin.

*** *** ***

Niger Republic

Da daddare suna kallo wani yaro yashigo kiran Inaas,babu musu tamiqe ta dauki mayafin abayar jikinta baqa tayafa sannan ta fice,kamar yanda ta tsammata yauma Is'haq dinne,yau bata koma da wuri ba, sun dad'e suna zancen su sannan tayi masa sallama yadauki kyautar kudi yabata,da farko qin kar6a tayi saida yadage sannan ta kar6a takoma gida.

Kudin daya batan ta ajiye agaban Bilkisu sannan tace"Ammiy gashinan, Is'haq ne yabani"

Bilkisu ta kalli kudin tayi ajiyar zuciya sannan tace"Allah yabaki miji nagari"(😂🙆🏻‍♀️🤭)

Farouq dake zaune yayi murmushi tareda girgiza kansa,da alama de har yanzu Is'haq begama samun kar6uwa awajan Bilkisu ba.

Har suka gama kallon suka kwanta Bilkisu bata daina tunanin wannan saurayi na Inaas ba,yanzu shekarar Inaas goma sha takwas,tunda basuda halin dazasu tura ta makaranta to gara tun kafin zaman gidan nata yayi yawa ita ba aure ba ita ba karatun ba gara kawai ayi mata aure,kullum sake zama budurwa take,wannan yaron Is'haq yadage,idan kuma yace zai futo ayi aure tasan cewa Farouq bashi ita zaiyi,harga Allah ita kuma batason Inaas dinta tayi irin rayuwar datayi shekaru talatin da bakwai baya.

Bata samu ta runtsa ba har tsakiyar dare tana tunane-tunane, daga qarshe tatashi Inaas suka fara gabatar da nafilfili, bayan sun idar haka Bilkisu tadaga hannunta sama tana Addu'ar data saba wato Allah ya bayyana mata d'anta,sannan Allah yabawa Inaas miji nagari (😂)

*** *** ***

Abuja Nigeria

Bikin Jawad yanata matsowa,gida anata murna musanman Mummy da Fu'ad.

A6angaren ango kuwa kana ganinsa kasan cewa auren baya gabansa,uzurin gabansa kawai yake,Amarya bata sake nemansa ba, shima bai nemeta ba, haka Mummy ma bata sake yimasa maganar taba, tun lokacin datayi maganar zata bawa yarinyar million goma sha biyar tun daga lokacin babu wanda yasake yimasa maganar ta,har yanzu bata kirashi tace anbata kudin ba, bata kirashi tafada masa cewa million dayan data fara tambaya ta yimata kad'an ba shiyasa tanemi qari, shiruuu babu wata magana.
Yauda safe yana gama motsa jiki yazauna awajan yana qarewa gidan nasu kallo yanda sojoji suke shawaginsu a compound din gidan,p.a yana tsaye daga bayansa yana duba wasu file.

Fu'ad yazo wajan ya ajiye wa yayan nasa Coffee me zafi akusa da computer sa datake ajiye awajan, sannan yajuya yafice daga wajan.

Jawad ya kalli coffee din yanaso yasha amma kuma zuciyarsa tana tunzurashi akan yayi abinda take so.
Ajiyar zuciya yayi sannan ya kalli p.a yace" p.a,kiramin manajan kamfanin Mekudi oil na qasar Niger"

Cikin sauri p.a yace"ok Yalla6ai"

Sannan yasaka hannunsa akan iPad din hannunsa cikin qwarewa yakamo number wayar manaja sannan ya doka masa kira, saida manager ya dauka sannan yabawa Jawad wayar yace"gashi Yalla6ai"

Jawad ya kar6i wayar sannan yace"manager"

Cikin sauri manager yace"na'am Yalla6ai,barka da wannan lokaci, Allah yasa de ba laifi mukayi ba"

Jawad ya girgiza kansa kamar manager yana kallonsa sannan yace"katuro min jadawalin sunayen ma'aikatan ku tareda bayanan su yanzu yanzu"

Cikin sauri manager yace"angama ranka yadade"

Jawad yabawa p.a waya sannan yaja computer gabansa yashiga cikin Email dinsa yana sauraron manager, ba'a dauki tsawon lokaci ba kuwa sai gashi sun shigo, cikin sauri yafara dubawa har hakan yabawa p.a mamaki,tsaf ya dinga bin d'an qaramin photon dayake kan bayanan kowa, amma baiga nata photon ba,ko tsayawa ya karanta sunayen ma'aikatan ba yayi, kawai Iya photon yake dubawa, cikin 6acin rai yarufe computer yasaki tsaki tareda lumshe idonsa yana shafa goshinsa da hannunsa alamun damuwa.

Cikin wata irin murya ya kwadawa p.a kira kamar p.a din baya gefensa.

P.a yace"na'am Yalla6ai"

"asake kiramin manager"

Cikin sauri p.a yasake dokawa manager kira,manager yana ganin wani kiran jikinsa yayi sanyi, yayi tunanin wani za'a sake kora acikin su, ahankali yadauki wayar, p.a yabawa Jawad waya,ahankali Jawad yace"wannan sunayen ka tabbatar iyakar ma'aikatan dakuke aiki tare dasu kenan?"

Manager yace"eh gaba daya ne Yalla6ai,kowa da kowa yana cikin list din dana turoma,saide wanda aka kora daga kamfani ne kawai babu sunayen su"

Cikin masifa dawani irin 6acin rai Jawad yace"A a, to saboda me babu bayanan wanda aka kora? idan kuma suka aikata laifi awani wajan da sunan kamfanin mufa?"

Cikin sauri manager yace"ayi haquri Yalla6ai bayanansu yana nan bari aturo maka"

Batare dayace komai ba yakashe wayar tareda dungurar da'ita ya lumshe idonsa,p.a ya kalleshi yarasa dalilin damuwar ogan nasa kawai saboda sunayen ma'aikata,yasaka hannu ya dauki wayar adede lokacin kiran manager yashigo, ya shaidawa p.a cewa yaturo saqon.

P.a ya kalleshi cikin ladabi yace"yalla6ai anturo saqon

Cikin sauri Jawad yabude idonsa sannan yabude computer cikin wata irin qwarewa yafara shafata yana ganin bayanan ma'aikatan d'aya bayan d'aya,har saida yaci karo da nata bayanan,gabansa yayi wata irin faduwa, cikin sauri yashiga yayi zooming din photon ta,kyakykywar fuskarta ta bayyana qarara,yazubawa fuskar tata ido yana kallo yasaki ajiyar zuciya yanajin wani irin nishadi aransa.

P.a dayake tsaye abayansa yasaki wani irin murmushi bayan yaga photon yarinyar da Yalla6ai Jawad din yazubawa ido yana kallo,sai alokacin yagano wayo da dabarar Yalla6ai Jawad din.

Shikuwa Jawad saida yagama kallonta tsaf, sannan yasaka hannunsa akan torch screen din computer yadan maida photon nata baya, sannan yaduba qasan photon inda sunanta yake,cikin ransa ya maimaita kalmar sunan nata INAAS OMAR FAROUQ,yasaki wata irin ajiyar zuciya a fili, sannan yasake zooming photon yaci gaba da aikin kallonta.

Fu'ad yadawo wajan cikin hanzari hannunsa riqeda waya yace"yaya!"

Shiru Jawad bai amsa ba,p.a ya kalleshi yace" Yalla6ai ana magana"

Amma kwata-kwata Jawad baisan sunayi ba, gaba daya daga tunanin sa har zuciyarsa sunakan photon Inaas.

Fu'ad ya qaraso yata6a kafadarsa yace"yaya!!"

Sai alokacin Jawad yayi firgigit yazabura yadawo daga duniyar tunanin daya tafi,cikin sauri ya rufe computer tasa,dariya tana so takama p.a amma haka yayi fuska ya maze.

Fu'ad ya zauna kusada Jawad yace"yaya,munyi magana da mawaqin dazai yi muku waqar bikinku, yace yaturo ma wayar kaduba kaji idan tayi shikkenan, idan batayi ba sai asake wata, amma nafada masa idan zaizo ya gabatar da waqar kada yazo da mutanan dasuka wuce biyar, saboda a America Mummy takeso ayi dinner,kuma awajan dinner za'a saka waqar,already an qayyade adadin mutanan da zasuje"

Jawad yad'aga kafadunsa alamun rashin damuwa yace"inde kaji waqar tayi ma is okay Fu'ad"

Fu'ad yace"okay yaya"

Sannan yajuya yatafi, bayan Fu'ad yatafi Jawad yamiqe tsaye ya kalli p.a yace"p.a, akiramin manager"
Chapter 23 · 0% Book details