← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 63

Sashe 35

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilkisu tafara duba kayan tana dagawa dogayen riguna ne Abaya masu kyau,da takalma,da mayuka na gyaran jiki dana gashi,da hand drayer, dakuma jallabiya da takalman maza da alamu wannan na Abban Inaas ne.

Bilkisu ta dago kanta ta kalli Hajiya Zaliha tace"Hajiya kayan nan ai sunyi yawa,Ina zamu kaisu Hajiya? Ina laifin ma guda bibbiyu?"

Hajiya Zaliha tasaki murmushi sannan ta miqe tsaye tace"to nide kinga tafiya ta"

Fu'ad ma yamiqe yabi bayan Hajiya Zaliha yana satar kallon Inaas wadda bakinta yakasa rufuwa da ganin kayan nasu.

Bilkisu da Farouq suka biyo bayan Hajiya Zaliha har Compound suna zuba mata godia kamar ba gobe.

*** *** ***

Yasaba duk lokacin dabai fita wani waje ko office ba to yana aiki a Computer sa agida,hakan ce ta kasance yauma,babu inda yafita saboda hutun dole da Likita yabashi,computer sa tana gabansa a ajiye, saide maimakon yayi aiki,photon ta yazubawa ido yana kallo,har mamakin kansa yake yanda yarinyar ta hargitsa masa lissafi,yana mamakin yanda soyaiyar ta take nema ta maidashi mahaukaci qarfi da yaji,tayaya ne zai sameta awaya? ta wacce hanya zai yi magana da'ita,? yanason jin muryar mahaifiyarta but ta yaya?, ahankali yarufe computer sannan yakoma cikin kujera ya kwanta yayi luf.

*** *** ***

Abuja Nigeria

Tsawon wasu kwanaki dasukai agidan Fu'ad baisake saka Inaas a'idon sa ba,da niyya yake futowa Compound yayi shawagi ko zai hango ta amma kokadan baya ganinta.

Zuwa wannan lokacin kuwa daga Bilkisu har Inaas sun sake yin fresh dasu,cimar dasuke ci yanzu, dakuma hutun dasuke basa fita ko da yaushe suna waje daya, hakan yasa fatar jikinsu tasake yin kyau uwa uba mayukan dasuke amfani dashi na gyaran jiki,yau tagaji da zaman waje daya,tafuto daga falon nasu tana zagaya compound din gidan,jikinta sanye da wata Atamfa mai kyau dinkin doguwar riga,kayan yayi mata kyau sosai kasancewar bata saba saka irin kayan ba, lungu da saqo takebi tana ganin gidan sai nishadinta take tana kalle-kalle,hakan da takeyi sai yaja hankalin security na gidan dayawa,kowa sai kallonta yake saboda sude a sanin su babu yarinya budurwa agidan, saide baqin dasuka zo ne tareda Alhaji, Inaas kuwa ko ajikinta, batasan ta dauki hankalin mazan dasuke tsatstsaye a Compound dinba, saida tagama kalle-kallenta sannan takoma falo, tana zama Man Sulaiman yashigo falon hannunsa janye da jaka Farouq yana biye dashi,Inaas tatashi da sauri ta kar6i jakar hannunsa takai masa wani daki kusa da dakin Ammiy.
Man Sulaiman yasaci kallon Bilkisu yaga tasake yin wani irin kyau tasake zama cikakkiyar matar manya kamar de baya,kasa janye idonsa yayi daga kanta,tayi mutuqar kyau cikin leshi riga da zani, taja wani daurin dankwali kamar ba'ita ba,wata sabuwar qaunar tace ta sake ninkuwa a ransa,Farouq ya kalleshi yayi murmushi yawuce kan kujera ya zauna,Bilkisu tadago kanta ta kalleshi sau daya ta watsar kota kansa bata sake biba, cikin sauri shima ya janye idonsa sannan ya zauna daga can gefe nesa da'ita,ya kalleta adan tsorace yace"Bilkisu ina kwana"

Batare data kalleshi ba tace"Lafiya"

Man Sulaiman yayi ajiyar zuciya yace"dama Alhaji ne yace Inaas dinki takai masa takardunta zata koma makaranta"

Bilkisu batace masa uffan ba,asalima ko inda yake bata kalla ba,ba zakace da'ita yake magana ba,Farouq zaiyi mata magana saide kuma dawowar Inaas falon yasa yayi shiru ya sauya akalar zancen da fadin"Allah yasaka masa da Alkhairi,zata kai masa"
Yajuya ya kalli Inaas data zauna yace"ai Takardunki suna nan ko?"

Inaas tace" eh Abba suna nan"

Yace"to Alhaji yace ki shirya su kikai masa zai nema miki makaranta"

Cikin farinciki Inaas tace"to Abba"

Man Sulaiman ya kalli Inaas da murmushi a fuskarsa,yaga alama dole saiya kama qafar yarinyar nan sannan zai iya samun kan Bilkisu,duba da yanda yaga tanaji da yarinyar, cikin sakin fuska yace"Inaas kinajin dadin garin ko?"

Inaas ta kalleshi tace"Eh Uncle inaji"

Bilkisu tajuya ta watsawa Inaas harara,harda wani Eh Uncle ko'a'ina yazama Uncle dinta oho.

Man Sulaiman yayi murmushi yace"to Alhamdulillah,anjima saiki shirya muje nakai ki yawo kiga gari kinji?"

*** *** ***

Tunda yarasa mafita akan yanda zaiyi yayi magana da da'ita hakan yasa yasake shiga damuwa yarasa gane kansa,bayan kwanaki biyar din da Likita yabashi yasake warware wa sosai yakoma bakin aikinsa,saide ga wanda ya sanshi kallo daya zaiyi masa yagane cewa Jawad din yana cikin damuwa,saide yanayin fuskar sa da kullum take daure babu fara'ah hakan yasa ba zakace yana cikin damuwa ba, saboda dama haka yake kullum babu fara'ah.

Yaci gaba da harkokin kasuwancin sa saide gefen zuciyarsa yana jin wani irin zafi wanda yariga yasani cewa hakan baya rasa nasaba da rashin jin muryar Inaas.
P.a ne yakawo masa waya,ya karba yakarata a kunnansa, daga can 6angaren akace"Yalla6ai maganar kamfanin nan fa jibi ne ranar budewa"

Jawad ya lumshe idonsa sannan yabude,yasaka hannunsa yadafe goshin sa, cikin damuwa yace"banace a sauya date din ba,? why not amaida zuwa next year? banason shiga Nigeria kwana kusa saboda inada ayyuka?"

"Ranka ya dade kayi haquri de,mun riga mungama sanarwa jibi ne taron,uwa uba duk wasu mutanan mu dasuke qasar waje suma an sanar dasu"

Fuska babu walwala yace"ok I will be there insha Allah"
Daga haka yabawa P.a wayar yaci gaba da aiki da computer.

Washegari sassafe suka shirya da shirin zuwa Nigeria agama taron bude kamfani subar qasar,kokadan bashida niyyar yin kwanaki samada uku a Nigeria,baison zuwa qasar kokadan,yaso ace de abar batun budewar zuwa next year.

Suna sauka a Airport guards suka bude masa mota yashiga baya yazauna computer sa tana kan cinyarsa yana dube-duben wasu ayyuka.

Kasancewar zuwan dayayi zuwa ne wanda ba'a san dashi ba, hakan yasa suna qarasowa gida sukaga yan Jarida danqam abakin get din gidan,kowa yanaso yaji ta bakinsa,bai saurari ko mutum daya daga ciki ba yayi umarnin cewa abasu haquri, baya cikin yanayin dazai iya magana dasu,motocin dasuka dauko shi suna tsayawa ya futo yayi gaba yana tafiya hannunsa guda daya yana cikin aljihun wandon sa, yayinda daya hannun yana riqe da waya akan kunnansa, cikin sauri yake tafiya yana waya da wasu baqi dazasu samu damar halartar taron da za'a yi gobe,yanda yake tafiya da cikakken kuzari ba zakace shine kwanaki biyar baya aka bashi hutun dole ba.

Yana qarasawa cikin hamshaqin falon nasu Mummy ta taso da sauri tatare shi tana murmushi har saida ta sadashi da qirjinta ta rungume shi,Fu'ad ya kar6i briaf Case din Jawad a hannun P.a, yawuce da'ita yakai masa dakinsa,Daddy yayi murmushi yace"yanaga ka d'an rame? meyake damunka? zo,zo,zoka fadamin"

Yafadi haka yana meqawa Jawad hannu, Mummy ta riqe hannun Jawad suka qarasa wajan Daddy.

****

Acan Plat din su Bilkisu kuwa,da daddare duka su hudun suna zaune afalo,ko kad'an basuji labarin zuwan Jawad ba,suna zaune afalonsu sunata zance,Man Sulaiman qasa-qasa suke magana shida Farouq suna tattauna wa akan yanayi dakuma halin da qasarmu take ciki,suna firar su suna cin abinci, Man Sulaiman ya kalli Inaas datake gefen Bilkisu, saida yafara satar kallon Bilkisun sannan yace"Inaas kin kaiwa Alhaji MEKU'DI takardun naki kuwa?"

gaban Inaas yayi wata irin bugawa,Abban Inaas ya dakata da cin abincin dayake yazubawa Man Sulaiman ido,yayinda Bilkisu ma ta qwara masa ido, gaba dayansu suna neman qarin bayani,cikin mamaki Abban Inaas yace"Alhaji Mekudi kuma? wai dama shine?"

Gaban Inaas ya tsananta fad'uwa,yayinda Bilkisu ta zubawa Man Sulaiman ido,tunda abun nan yafaru ita de da kanta bata ta6a yimasa magana ba, amma yau saita tsinci kanta da jefa masa tambaya tace"wai Mahaifin yaron nan Jawad? to yanzu ina Jawad din yake? yana nan lafiya?"

Farouq yazubawa Yayar tasa ido yana kallo, yarasa meyasa Yaya Bilkisu ta damu sosai da lamarin Jawad,baisani ba ko haduwar jini ce.

Inaas kam idonta yana kan Man Sulaiman tana jira taji amsar dazai bayar.

Man Sulaiman kuwa ganin yau Bilkisu ta masa magana,hakan yamasa dadi,ya tabbatar Addu'ar dayake akan Allah ya huci zuciyarta tafara kar6uwa,yajuya ya fuskanci Bilkisu yace"Jawad ai baya zama,a shekara befi yazo qasar sau d'aya ba"

Cikin sauri Inaas tace"to inje nakai masa takardun yanzu?"

Man Sulaiman yace" yanzu dare yayi Inaas,kibari gobe saiki kai masa insha Allah"

Cikin ladabi ta amsa masa sannan tatashi ahankali tashige dakinsu tafara bincike saida ta nemo katin da Jawad yabata wanda yake daukeda numbers dinsa,tazubawa katin ido kamar tanaso ta haddace numbers din jiki,ahankali tasaki ajiyar zuciya,tajuya gefen damanta ta kalli wayar Bilkisu,tanaso ko sau daya ne takira shi a wayar tayi masa godia akan kyautar dayayi mata,tanaso ko sau daya ne takirashi su gaisa,amma bazai iyu ta qetare Umarnin Mahaifinta ba,ahankali tatashi tamaida katin inda take 6oye shi,sannan tawuce toilet domin ta watsa ruwa.

****

Qarfe shadaya da kwata suna zaune shida Daddy afalon Daddy din,Alhaji Mekudi yazubawa d'an nasa ido yana nazarinsa,ya tabbatar akwai abinda yake damunsa,amma zurfin ciki irinna Jawad sunyi masa tambayar duniya yaqi fada musu komai.

Daddy yadauki ruwan Zam-Zam din dake ajiye a gefensa awata qatuwar gora ya tsiyaya yasha, sannan yasake kallon Jawad yace"Man Sulaiman yaga matarsa"

Cikin ladabi Jawad yace"Eh Fu'ad yafada min Daddy"

Daddy yagyada kansa sannan yace"sun dawo nan muna zaune tare dasu gaba daya,akwai Qanin Matar Man Sulaiman yana nan Sunansa Farouq, inaso idan kungama taron bude kamfanin nan gobe, ka bashi aikin daya dace dashi,yayi karatu me Zurfi tun irin karatun shekarun baya, amma bai samu kyakykywan aikin gwamnati ba hakan yasa yake yiwa yaran Alhaji Auwal lesson, na rabo shi da aikinsa,bai kamata in hanashi wani aikin ba"

Jawad yayi shiru yana tunani, yatuna lokacin dasuke waya shida Baby kafin ta rasu, har take cemasa Uncle Farouq ma yace tafi kowa qoqari,ikon Allah ashe shidin Qanin matar Man Sulaiman ne,Allah da iko yake,ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan yace"to Daddy insha Allah za'a yi abinda yadace"

Washegari bayan sungama Breakfast Bilkisu taga Inaas sai walwala take,batasan menene dalilin farincikin yarinyar ba,saide tana hasashe cewa tun lokacin da Man Sulaiman yace nan gidansu Jawad ne daga lokacin ne taga Inaas din tanata nishadi,mamaki ya kamata,to kode son Jawad din take?

Man Sulaiman ne ya futo cikin Shiri ya kalli Abban Inaas yace"Farouq mu wuce wajan taron nan,dazu Alhaji yakirani yace akwai taron bude kamfani da za'a yi, yanaso muma muje"

Farouq yadauki tissue ya goge bakinsa sannan yamiqe suka fice daga falon,ahanya Man Sulaiman yakalli Farouq yace"jiya muna zancen Jawad kaji ashema yashigo qasar jiyan,kuma shine ma zai bude kamfanin"

Farouq yayi murmushi yace"Allah sarki, Allah yasanya Alkhairi"
Chapter 35 · 0% Book details