← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 63

Sashe 50

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inaas tabude bakinta da sauri cikin mamaki, sannan cikin shagwa6a tace"Yayaaaa"
Taja sunan nasa.

Jawad ya lumshe idonsa yace"Plaese,inason jinki acikin jikina,inason in dora kaina akan cinyarki nayi bacci,nifa maraya ne"

Inaas batasan lokacin data saki dariya ba tace"who is maraya? kai ko ni?, kai dan gatane nesa ba kusa ba, kuma kanada iyaye har guda hud'u dukansu suna raye"

Murmushi yayi yace"wayo zaki min? ok fadamin, ya shirye shiryen biki,? me kika fara shiryawa?"

" Yaya ai Shiri yana wajansu Ammiy,ni babu abinda nake,ande fara yimin gyaran jiki"

Cikin jin dadi ya lumshe idonsa,yace"wow,idan za'a yi miki zan kiraki vedio call Inga yanda ake miki,inason nasake ganin wannan kyakykywan surar taki kamar yanda naganki adakin Mummy"

Inaas ta zaro idonta cikin tsananin mamakin Jawad din,tarasa meyasa yau din yake mata wasu irin baaqin kalamai,wanda abaya zata iya rantse wa cewa shi din bazai iya zaro irin wannan manyan kalmomin masu nauyin fada ba, cikin tsananin kunya tashige cikin bargo ta rufe kanta kamar yana ganinta sannan tace"Yaya nide saida safe gaskiya"

Jawad yayi murmushi cikin wata irin muryar shagwa6a wadda Inaas bata ta6a sanin yanada itaba yace"kiss me please,zanyi bacci me dadi idan kikamin"

Inaas tasa tafin hannunta ta rufe idonta dashi duk da tana cikin bargo,tace"Yaya kana bani kunya fa,wai meyake damunka ne?"

Daga nasa 6angaren ya lumshe idonsa cikin zallar buqatarta yace"Ke ce..."

Dan qaramin bakinta taturo gaba tace"ni ban iyaba"

Ajiyar Zuciya yasaki yace"rufe idonki"

Cikin sauri ta rufe idonta tace"na rufe,meyafaru?"

Baice da'ita komai ba yafara sakar mata wani irin kiss ajajjere.
salon yanda yake yimata Salo ne wanda zaisa dole ya karya mata dukkan wani qwarin gwiwar ta,Salo ne wanda zaisa dole jikinta ya kar6i saqonsa,yanda yake yin kiss din dawani irin Salo saitake jin kamar ajikinta yake mata hakan,batasan lokacin data rungume fillon gefenta ba,ko kad'an bata bude idonta ba,Jawad yana jiyo yanda yanayin saukar numfashinta yafara sauya wa,ya tabbatar cewa taji dadin saqonsa.

Ahankali Inaas tafara janye wayar daga kunnanta,saboda wani irin yanayi data jita aciki wanda bata ta6a tsintar kanta a cikinsa ba,hakan yasa tayi qundunbala ta kashe wayar tasake rungume fillon jikinta,batasan lokacin da bacci ya dauketa ba.

Shima anasa 6angaren hakan ce ta kasance,yanajin ta kashe wayar ya lumshe idonsa dake cike tsananin buqata,daqyar yasamu yayi bacci,lokacin sallar asuba daya tashi saida yayi wanka,sakamakon yanayin yanda yatashi ya ganshi yayi jalaf...(🙈)

Cikin wasu yan kwanaki gyaran jikin Inaas sai wanda yagani,sosai suke gyara ta abun har mamaki yake bawa Hajiya Zaliha da take tunanin dauko masu gyaran jiki daga qasar Sudan,ashe muma acikin gida ba baya ba,iya gyaran jiki kawai suke mata sai maganin sanyi,haka na tsugunno dana turare dana wanka duk babu wanda Inaas bata gani.

Man Sulaiman yaje gida Jigawa ya taho da gayyar yan'uwa da abokan arziqi,maza da mata,acikin matan harda Bintu da Fatsime maqotan Bilkisu na da,wanda suka taimaka mata sukai kaita wajan Maigari ranar da Man Sulaiman ya gudu yabar gari,dakuma 'Dayyaba matar maigari wadda ta kar6i haihuwar Bilkisu acikin dakinta.

Lokacin da suka sauka afalo Man Sulaiman shida kansa ya gabatar musu da abinci, sannan yatafi falon Hajiya Zaliha yakira Bilkisu,suka taho harda Hajiyan.

Bilkisu tana ganin matar maigari wato 'Dayyaba ta qame awajan a tsaye tace"Yaya 'Dayyaba ke nake gani ko wata?"

'Dayyaba tayi murmushi tace"nice Balki,ashe da rabon zamu sake ganinki Balki? ina kayan gwanjo Balki? kinganni tareda Fatsime da Bintu maqotanki,kin sheda su?"

Bilkisu tajuya ta kalli matan guda biyu dasuke zaune agefe,kwata-kwata bata ganesu ba saida 'Dayyaba tace mata Fatsime da Bintu ne,wahala tasa sun sauya,wahala tasa sun tsufa,bazaka ta6a cewa su d'in kusan sa'annin ta ne ba.

Wani irin kuka ya tahowa Bilkisu,cikin gudu ta qarasa wajansu suka fashe da kuka,kamar dakin makoki haka suka maida falon sai kuka suke kamar ransu zai fita,mazan dasuka taho dasu mutum uku sune suka fara basu baki.

Hajiya Zaliha ta goge qwallar idonta tace"kuyi haquri ku daina kuka Bilkisu,murna zakuyi kuma kuyiwa Allah godia tunda gashi yasake hada fuskar ku da Alkhairi"

Bilkisu ta share hawayen idonta sannan tace"Haka ne,Hajiya bazan iya kwatanta miki irin halaccin su agareni ba,sune suka kar6i haihuwar Jawad,suka yanka min ragon suna,jama'ar gari suka had'a min kudin mota natafi qasar mu"

Hajiya Zaliha tace"Allahu akbar,Allah abun godia,sannunku da zuwa"

Bintu tace"sannu Hajiya"

'Dayyaba tace"Balki Muhammad din naki suna kuka sauya masa ne? naji kina cewa jawal"

Bilkisu tayi murmushi jin yanda 'Dayyaba tafadi sunan,tamayi kokari,ko a wancen shekarun na baya ita din babba ce,kuma mutane suna girmamata kasancewar ta matar maigari,tace"Haka muke kiransa,an6oye Muhammad din, sai muke cemasa JAWAD"

Fatsime tace"Balki kiga jikinki fes dashi kekam yarinya ma kika sake komawa wallahi"

Gaba daya falon sukai dariya,Man Sulaiman yaji kansa yasake girma anyabi matar tasa,shi kansa yasan cewa shi me sa'a ne,domin kuwa Samun mace kamar Bilkisu sai me sa'ah.

Bilkisu ta kalli mazan wanda bata ganesu ba tace"Meyasa bakuzo da Megari ba?"

Gaba dayansu sai sukai shiru aka rasa me bata amsa,sai 'Dayyaba ce tace" Allah sarki,Balki Alhaji aiya dade da rasuwa,yanzu babban d'anane akan kujerar,kinganshi nan"

Ta qarasa maganar tana nuna mata wani matashi daga cikin mazan guda uku dasuke zaune.

Nan take tayi musu ta'aziyya,sannan sukai masa Addu'ah, daga nan kuma fira ta 6alle ana bawa juna labarin baya.

Washegari baqin Niger suka iso,ciki harda Maman Is'haq saurayin Inaas,da mutanan dasuke mutunci dasu maqota,sai matar Alhaji Auwal,suma baqin Niger ba'a barsu Abaya ba,domin kuwa kullum da daddare idan Inaas zata kwanta sai sun bata magunguna masu kyau tasha irin nasu na qasar Niger,Bilkisu dai nata idanu,tariga ta saddaqar cewa Inaas zata d'and'ana kudarta awajan Jawad.

Mutanan Niger sosai suka yiwa Bilkisu gudunmawa amma taqi kar6a sai kad'an daga ciki ta kar6a.

A satin biki baqin qasar waje suka iso,gida yacika yayi dam da jama'ah,Hajiya Zainab tayiwa Inaas sababbin qawaye yan Boko mutum hudu,biyu yaranta ne,sauran biyun kuma yar gidan minister ce da yar gidan tsohon matemakin gwamnan jihar kaduna.

Idan mutum yazo gidan zaiyi tunanin anfara bikin,duk baqin kusa suma sunzo,Yaya Mariya ma ta debo tawagar ta sun dawo gidan gaba daya.

Tunda biki yarage saura kwana hudu,Hajiya Zaliha tahana Inaas fita ko'ina,tana can wajan masu gyaran jikinta suna jiqata da humra kala-kala,tayi masifar kyau yanda mutane basa zato.
Ana saura kwana biyu Jawad yasamu ya qwato kansa yashigo qasar,so yake yayi tozali da Inaas, ba qaramin kewar ta yayi ba, hakan yasa kai tsaye yawuce wajan Bilkisu,yana shiga falon ya ganshi acike da jama'ah,kowa sai kiransa yake yana gaida su,haka yasamu yashiga dakin Bilkisun,ya tsugunna yagaida mutanan daya ganta tare dasu.

Bilkisu tayi murmushi tace"yanzu ka sauka Jawad?"

Jawad yadan juya gefe yana kalle kalle ko zaiga Inaas amma shiru ba bayani,yayi qasa da kansa yace"yanzu muka sauka Mama,mun same ku lafiya?"

Bilkisu tace"lafiya kalau, Jawad wadannan yan'uwanka ne daga jihar jigawa,dukansu kamar dangin Babanka suke,sune suka kar6i haihuwar ka ranar dana haifeka"

Cikin sauri Jawad ya kallesu.
Fatsime taqura masa ido tace"ikon Allah Muhammadu kaine ka girma haka?Bintu kinga Muhammadun Balki"

Tafadi haka hawaye hana zubowa daga idonta.

Bintu tace"ikon Allah kenan Fatsime,sainaga kamar yau aka haife shi,girman d'an mutum ba wuya"

'Dayyaba tayi murmushi tace"Muhammadu kayiwa mahaifiyar ka biyaiya kaji? tayi qoqari a kanka kuma tasha wahala ita din abar a tausaya wa ce"

Jikin Jawad yayi sanyi qalau,yaji wata irin soyaiyar Bilkisu tasake ninkuwa acikin zuciyarsa, haqiqa Mama taga rayuwa,daga yanda mutanan nan suke magana kadai zai tabbatar masa cewa tayi garari abaya.

Cikin nutsuwa yace"insha Allah zanci gaba dayi"

Bilkisu tace"kaci abinci kuwa?"

Yace"A a Mama, yanzun nan na shigo,ko wajan Mummy ban shiga ba,zanje nafara yin wanka tukunna"

Tace"to shikkenan,itama qanwar taka tana can wajan Hajiyan"

Ahankali yayi wata ajiyar zuciya a 6oye,sannan ya kalli baqin nata yace"akwai abunda kuke buqata ne akawo?"

Cikin sauri Bintu tace" a a Muhammadu,wallahi bamason komai,Balki tana bamu duk abinda muka nema"

Cikin nutsuwar sa ya gyad'a kansa alamun amsawa sannan ya kalli Bilkisu yace"Bari inje Mama"

Bilkisu tayi masa Addu'ah sannan yatashi ya futo daga dakin,yanajin wasu mata afalon suna cewa "wannan ko shine angon?"
Yaji wata daban daga gefe tace"eh shine,yanzu yazo yawuce,kina daki kina waya lokacin"

Shide cikin sauri yayi wuf yafice daga falon.

Ta qofar baya yasamu yashiga yahaye sama,sannan yakira Mummy wadda ta kacame cikin baqi,sai itace ta bishi dakin nasa,yana ganinta ya rungume ta yace"Mummy I'm hungry,yarinyar nan takawo min abinci"

Mummy tace"yarinya takawo abinci kokuma Mummy takawo? Inaas bata gidannan,saide zuwa jibi idan an daura aure zaku hadu awajan dinner,hayaniya zata samata ciwon kai shiyasa na tura ta gidan qawata"
Jawad yaji wani irin fad'uwar gaba yaji kamar ya rusa kuka,haka dan dole yace"to Mummy abincin"
Hajiya Zaliha tajuya tafice daga dakin,shima yashiga wanka.

Washegari aka yiwa Amarya qunshi,ja dakuma baqi,aka gyara mata dogon gashinta aka turara mata shi da wasu sinadaran qamshi,sannan tayi wanka da ruwan lalle, mai kwalliya tazo tafara aikinta.
Garin Abuja yacika da manyan baqi,duk wasu mutane na qasar waje sun iso aranar,qalilan ne zasu qaraso gobe.
Washegari daurin aure manyan 'yan siyasa dakuma manyan 'yan kasuwa sun halarci Central mosque na Abuja inda za'a daura aure acan,dayawansu sunzo ne domin taya Alhaji Mekudi murnar auren Babban d'ansa da za'a yi.
Jiragen sama sai shawagi suke basai mutum ya tambaya ba anriga ansan cewa bikin Jawad Mekudi ake.

Man Sulaiman shine Waliyin Amarya,yayinda Alhaji Auwal yazama waliyin ango,ba'a dauki wasu tsawon lokaci ba bayan angama abinda addini ya tanada domin dauren aure nan da nan aka daura auren Jawad Aliyu Mekudi da Amaryar sa Inaas Omar Farouq akan sadaki naira Million d'aya,lakadan ba ajalan ba.

Kasancewar akwai baqi na nesa wanda zasu juya zuwa qasar su,hakan yasa daga wajan daurin aure aka fara wucewa da baqi zuwa hall din da zasuyi dinner, andauki lokaci sosai mutane suna tafiya wajan,saide duk wanda kagani kallo daya zaka masa kasan cewa wani qusan ne.
Chapter 50 · 0% Book details