← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 63

Sashe 61

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inaas tayi masa hararar soyaiya, kafin tayi magana Beauty datake zaune tana sanye cikin Riga da wando na bacci irinna yara tana ganin photunan bikinsu Inaas a computer ta juyo ta kalli Jawad tace"Dad gaka ga Mom,amma babu ni"

Jawad ya kalli Inaas yayi murmushi sannan yamaida dubansa wajan Beauty yace"yes,lokacin Mom dinki tanajin zafi"

Beauty bata fahimci meyake nufi ba,tace"Dad zafi ake ko?"

Jawad yayi dariya yace"eh"

Beauty ta maida hankalinta kan kallon photunan,Inaas ta harari Jawad ta zauna agefensa,yayinda ya zuro hannunsa ta bayan qugunta ya rungume ta,Inaas tayi qasa da murya tace"miye hakane?"

Kallonta yayi,cikin sigar rad'a yace"Matar Yalla6ai,Yalla6ai fa a hannu yake,yau satina d'aya da dawowa har yanzu babu wani labari,Beauty bata bacci dawuri,bana samun damar dazan huta dake,kinsan cewa kuma nayi qoqari ba d'an qarami ba,see my legs"

Inaas tayi ajiyar zuciya ahankali takai dubanta zuwa tsakanin cinyoyinsa,lokaci d'aya ta tabbatar da maganar sa duk da yana Sanye cikin sutura hakan bai hana idan ka kalli wajan kakasa gane halin da mijin nata yake ciki ba,saida tagama ganin yanayin sa sannan yamaida qafafunsa ya had'esu waje d'aya ya6oye abunsa.

Ta saussauta murya zata masa magana saide kafin tace wani abu Beauty tataso tazo wajan Jawad tahaye jikinsa itama tace"Dad"

Jawad ya had'esu duka su biyun itada Inaas ya rungume sannan cikin soyaiya ya kalli Beauty yace"Na'am Beauty"

Cikin sauri tace"Dad a school dinmu ko,? idan nace my name is Beauty sai school mates dina suce wai Beauty is not a name,Dad why?"

Jawad yariqe fuskar Beauty yayi kissing goshinta sannan yace"Ki dinga fad'a da comfidance d'in ki cewa your name is Beauty,Dad dinki ne da kansa yasa miki Sunanki Beauty Because You're Beautiful"

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/24, 20:34] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,idan kika karanta ba tareda kin biya ba keda Allah saboda ban yafe miki ba.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

31&32

Jin jina da dubun godia agareku,haqiqa kun taka rawar gani wajan taimako na ta hanyar bincike wajan ganin na kammala wannan littafi.
Sister Wasila nagode da yanda kika taimakeni wajan fadamin abubuwan da bansaniba na qasarku,gidan radio na qasa,al'adu dakuma ruwan dakuke amfani dashi(DALLOL) yanda mutanan qasar Niger su manager suke bawa Jawad gorar ruwan Dallol,nima muddin nazo qasar Niger zan nemi ruwan gorar Dallol nasha 😜
ban manta dakaiba Yaya salahuddeen yanda ka taimaka wajan fadamin wasu daga cikin sunayen garuruwan qasar Niger,da taimakon labari ya qara armashi😍
Saboda haka na sadaukar da page izuwa gareku💃🏻.

____

Beauty zata sake magana Inaas tace"shiru!,muje ki kwanta"

Jawad yamiqe da Beauty a hannunsa suka wuce daki,saida suka lalla6a ta tayi bacci,sannan Jawad yaja Inaas jikinsa ya rungume ta tabaya,rad'a yafara yimata a kunne yace"yarinyar nanfa surutun ki tabiyo,idan tafara magana abun har mamaki yake bani,kema haka kike kina qarama ko?"

Cikin shagwa6a Inaas tace"nifa bahaka nake ba"

Cikin jin dad'in shagwa6ar tata ya lumshe idonsa,ahankali yafara kissing dinta cikin jin dad'i,batare da 6ata lokaci ba itama tasaki jiki suka fara mayarwa juna martani,saida suka gama fita hayyacinsu Jawad yafara sakin wani irin nishi,hakan yasa Beauty tatashi,cikin muryar bacci tace"Mom"

Daga Jawad,har Inaas sai kowa yayi d'if suka dakata da abunda suke,ahankali Inaas ta matsa daga jikinsa takoma can gefe kusada Beauty tana bubbuga bayanta,Beauty tashige jikin Inaas ta qanqameta sannan taci gaba da bacci.

Jawad ya lumshe idonsa yana sakin numfashi a jejjere,ahankali ya matso jikinta daga bayanta yaci gaba da shafa wuyanta,cikin rada yace"kidawo mana"

Inaas ta kalli Beauty duk da duhu ne sannan ta girgiza masa kanta alamun a'a,cikin 6acin rai ya kaiwa gadon duka sannan yajuya bayansa yadena kallon inda suke kwata-kwata,gaba d'aya hankalin sa atashe yake,sai had'a uban gumi yake yana cizon lips,da qyar yasamu yayi bacci bayan yaga itama Inaas din ba tashi take ba, ta kama 'yarta sunyi baccinsu.

Da asuba baije masallaci ba,afalo yayi sallah,ko takan Inaas baibi ba yatashi yashiga toilet yayi alwala yawuce falo,har gari yafara haske yana zaune akan sallaya yarasa mafita,wayarsa dake gefe tayi haske alamun shigowar saqo,saqon yaduba yaga P.a ne yake sanar dashi yau sunada meeting da manyan 'yan kasuwar Malesia,saboda haka jirgin su zai tashi qarfe goma nasafe.

Jawad ya runtse idonsa,yakai hannu yata6a qasan mararsa yaji bawani sauqi tun daren jiya,haka ya sunkuyar da kansa qasa yarasa tunanin da zai kama.

Inaas tafuto falon zata duba fridge ta ganshi a zaune,cikin mamaki tace"Qauna dama bakaje masallaci b...."

Kafin ta qarasa maganar da zatayi yawani irin fuzgota,tafad'o kansa,nan take yafara yamutsa ta,batayi masa musu ba,domin kuwa itama kanta a hannu take,sosai take tayashi gudanar da abubuwan,hakan yasa yafara zame mata kayan jikinta,lokaci d'aya,sukaji Muryar Beauty tana fad'in "Mom,natashi"

Cikin sauri Inaas tatashi tsaye tana gyara hijabin jikinta,yayinda Jawad yaji wani irin abu yatsaya masa awuya,jiya ke kamar ya fashe da kuka.

Inaas ta qarasa wajan Beauty tace"kin tashi? muje ki gaida Dad sai ayi wanka ko?"

Beauty ta qarasa wajan Jawad ta shige jikinsa tace"Dad,inaso muyi wasa"

Jawad da idonsa yake a lumshe cikeda 6acin rai yace"Beauty...please leave me alone"

Beauty taturo mitsitsin bakinta gaba,kamar yanda uwarta takeyi sak,sannan ta kalli Inaas tafashe da kuka.
Inaas tajata jikinta tafara lallashinta tace"yi haquri,muje kiyi wasan dani,Dad baida lafiya"

Cikin kuka tace"ni da Dad d'ina nakeso muyi"

Inaas ta lumshe idonta tabude sannan ta sunkuya dede tsawon yarinyar yace"Beauty,bakyason Dad ya warke?"

Cikin kuka tace"ina so"

Inaas tace"to kije wajan Mama,kice kinzo kuyiwa Dad Addu'ah keda ita,ta dinga fada miki addu'ar kunayi tare,kafin kidawo ya warke,saikuyi wasan ok?"

Cikin sauri Beauty ta goge hawayen idonta sannan taje wajan Jawad tayi masa kiss,tafice da gudu daga falon tatafi wajan Mama Bilkisu.

Inaas tasaki ajiyar zuciya ta kalli Jawad tace"wai dan Allah Qauna meyake damunka ne? kaine ka sabawa yarinyar nan da wasa dakai,meyasa zaka dinga yi mata magana haka? zatayi tunanin wani abu kokuma tasa damuwa aranta"

Cikin 6acin rai Jawad yamiqe tsaye yace"amma nafada miki halin danake ciki,almost 8 day's ina yin bacci daqyar,kinsan yanayi na,amma haka zaki juya min baya ki rungume 'yarki kuyi bacci,danayi bacci da karnayi duk ba damuwar ki bace,ai kinsan hanyoyin da zakibi yarinyar taje wani wajan,amma bakiyi ba,yanzu dakika so ba gashinan kina mata magana ta jiki ba,yanzu kinji dad'i?,anjima zan bar muku qasar,saiki sata agaba kiyi ta rungume ta kinajin dad'i"

Bai saurari amsar ta ba yawuce dakin yafara loda kaya acikin jaka kamar wanda zaiyi tsaraba da kayan.
Inaas tabiyo bayansa daki ta dakata daga bakin qofa tana ganin yanda yake loda kaya ajaka daga gani ba'a hayyacinsa yake ba,6acin rai ne yasa shi loda wannan uban kayan shida ko wacce irin tafiya zaiyi baya daukan komai bayan takardu?
Jawad yana ganin shigowar ta d'akin yaci gaba da sababi yana fad'in"kwana takwas mutum yana fama da abu d'aya saikace marar iyali? garama mutun yayi tafiyar sa,ko aure ne mutum yaje yanema"

Inaas ta harde hannunta a qirjinta ta kalleshi,taga abun nasa sai qara gaba yake,sai wata magana yake yana fad'in mutum,mutum, tasaki ajiyar zuciya tace"Qauna wai dama an ta6a fad'ama cewa ina tsoron kishiya ne?"(🤭)

Cikin 6acin rai ya kalleta yace"ok haka kikace?"

Tace"yes"

Baisake cemata komai ba yaci gaba da loda kaya ajaka,Inaas tajuya tafice tabar masa dakin,taje ta rufe qofar falon nasu da key,sannan tabude fridge ta dauko wani tsumi wanda aka aiko mata shi daga Niger,yanayin aiki cikin sauri,ta d'aga bakin gora tasha sosai,sannan ta maida cikin fridge takoma dakin, Jawad yanajin shigowar ta ko kallon inda take baiyi ba,kayan jikinsa yafara cirewa zai shiga wanka,saida ya cire kayan yarage daga shi sai gajeren wando,sannan yanufi toilet din,Inaas ta kalleshi,takai dubanta zuwa ga gajeren wandon sa gashinan qiri-qiri tana ganin komai gajeren wandon bai rufa masa asiri ba saima qara tona masa asiri dayayi saboda bashida kauri santsi ne da wandon.
tasaki ajiyar zuciya, shida yake cikin wannan halin shine yake fada yana sababi.
Yakama handle din toilet din zai shiga tayi sauri ta qarasa ta rungume shi tabaya,ta dora kanta abayansa,sannan takai hannunta kan qasan marar shi tariqe sosai tana yi masa wani irin matsa,cikin wata irin murya tace"fishi baya yimaka kyau Qauna..."

Jawad dake cikeda 6acin rai ya lumshe idonsa saboda dadin dayake ji sakamakon yanda take masa,yanaso yaraba jikinsa da nata amma yakasa,so yake ya tureta daga jikinsa ya nuna mata laifin data masa amma kokadan yakasa sakamakon yanda ta riqe abunsa tanayi masa wani abu wanda baisaba ji tanayi masa makamancin haka ba.

Daqyar yabude bakinsa cikin muryar kasala yace"bari...,kibari fa nace"

Yafadi hakan yana sakin wani irin numfashi tareda sake lumshe idonsa.

Cikin shagwa6a Inaas tace"ni bazan bari ba..."

Wani irin numfashi Jawad ya sauke cikeda jin dad'in abinda take masa yace"niki denamin banaso faaaa...."

Inaas tad'an kalli idonsa taga a lumshe idonsa yake kuma sarai yanajin dad'in abinda take masa,hakan yasa cikin wani irin salo tasakar masa kukan shagwa6a wanda yasake jefa shi cikin tsananin buqatar ta, cikin muryar jin dad'i yace"me kike buqata namiki danki rabu dani?"

"nide ka barni nikad'ai,kadena min zancen kishiya"

Cikin jin dad'i yace"saboda kinga kin riga kin zama ni shiyasa kika raina Yayanki ko?"

Qafafunta tafara bubbuga wa aqasa cikin shagwa6a tana sake goga masa nashanunta a bayansa sannan tace" Yaya na dena fa"

Idonsa a lumshe yace"ni banga hakan ba,ki nuna min a aikace nagani"

Murmushi tasaki tace"yanzu zaka gani"
Tana fadin haka taja gajeren wandon nasa yayi qasa.
Basusan cewa sun dauki lokaci suna abu daya ba saida suka kalli Agogo,sannan ne ya dauketa cak fuskarsa cikeda annuri suka shige toilet sukai wanka,bayan sun shirya taga ko kallon jakar kayansa daya hada ba yayi tace"Qauna ga jakar kayanka fa"

Jakar ya kalla yace"kinga ni bansan ma nahada kayan ba,maidasu kawai"

Inaas tayi murmushi tamaida kayan,sannan tahada yan qananun abubuwan datake buqata tace masa "muje Qauna,nikam nagama shiryawa,idan muka yiwa Ammiy sallama saimu dauki Beauty mutafi"

Cikin mamaki ya kalleta yace"ina zakije? hutun fa?"

Ajiyar zuciya tayi ta kalleshi tace"mijina yafiyemin duk wani hutu da zanyi,zan bika mukoma na haqura da hutun,saimu koma muhuta tare"
Chapter 61 · 0% Book details