← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 63

Sashe 26

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Idan kika karanta min batare da kin biya ba keda Allah saboda ban yafe ba👌🏻

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

Wani irin hawaye mezafi yazubo daga idon Hajiya Zaliha tasa hannunta tashare hawayen idonta.

Yaya Mariya taci gaba da fadin"mekike tunani idan yaron nan Jawad yasan abinda kuka aikata keda d'an uwanki? ganinki yake amatsayin mahaifiyar sa wacce tafi kowa sonsa aduniya menene kudi Zaliha?"

Daddy yayi ajiyar zuciya yace" Yaya kin barni aduhu,kiyimin bayanin abinda yake faruwa"

Yaya Mariya ta kalleshi tace"da niyya tayi wannan hadin auren,sun shirya hakane itada Bature domin su samu yan kud'ad'en su, kuma sun samu, domin kuwa Bature yacemin kudi sun riga sun riqe bazasu bayarba,yace kuma bazai bawa Amal dan tsuntuwa ba, saboda haka nina gama yanke hukunci Jawad yahado kayansa yadawo gidana, nizan masa ruqon d'a, ba ruqon d'an tsuntuwa ba"

Daddy yana gama jin wannan bayani yaji kansa yayi wani dumm! kamar an buga masa wani abu, ya runtse idonsa cikin baqin ciki sannan ya kalli Zaliha yace"hakane wannan maganar Zaliha?"

Hajiya Zaliha ta share hawayen idonta sannan tace" ka gafarce ni Alhaji"
Sannan tajuya tasake kallon Yaya Mariya tace"kema Yaya kiyimin aikin gafara,Yaya Bature ne yake fadamin cewa ina zaune Alhaji ya maida duka kadarorin sa sunan Jawad,kamata yayi ace shida Fu'ad kowa yanada damar da zaiyi amfani da dukiyar bawai Iya Jawad ba,tun bana amincewa da maganganunsa har shaidan yayi nasara akaina,nayiwa Alhaji magana akan yanda ya bawa Jawad dukkan kadarorin sa kamata yayi abasu shida Fu'ad,Alhaji ya nunamin da Jawad da Fu'ad duk d'aya ne,saida natura masa kud'ad'en yariqe gaba daya ya hanani komai,qarshe ma yace idan kuskura nasake yimasa maganar kudin to zaizo har wajanku ya tonamin asiri"
ta qarasa maganar tana share hawayen idonta.

Daddy yayi ajiyar zuciya yace"Zaliha bansan meyake damunki ba,idan yaron nan yaji abinda kikayi mekike tunani zai dauka? har abada banaso Jawad yasan cewa ba nine mahaifinsa ba saboda ubangiji shine yasakamin qaunarsa araina,yanzu gashi kin fitar da maganar damuke 6oyewa kowa,kinfadawa Bature Jawad ba danmu bane,ban ta6a tunanin haka daga wajanki ba,shi da Fu'ad ni duk d'aya na dauke su,kuma ko bayan raina nasan Jawad bazai yada dan'uwan sa ba,kinyi min maganar kudin nan nafada miki da Jawad da Fu'ad duk dayane,Jawad zai kula musu da kudin su sannan yaron nan nafada miki ko mutuwa nayi bashida gadona,Zaliha yaron nan ATM dinsa yadauka yabaki kiyi abinda kike buqata da kudi tome wannan kudin zai qara miki? naga alama tunda kika samu Fu'ad shikkenan shi Jawad din kin yadashi,danhaka ki dauki yanaki yanaki kibarmin gida kije caaan! ki zauna da Alhaji Bature ni bazaki rabamin kan 'ya'yana ba"

Cikin sauri Mummy ta dago kanta ta kalli Alhaji Aliyu Mekudi cikin tsananin mamaki.

****

Tunda suka shiga dakin Jawad, Fu'ad ya zauna fuskarsa cikeda alhini ya kalli Jawad yace"gaskiya uncle Bature yayi qaranta,saida aka tura masa wannan uban kudin?"

Jawad dayake kwance yayi matashi da hannunsa ya motsa lips dinsa kad'an sannan yace"ra'ayin sane"

Fu'ad yace"ni Yaya sainagama kamar baka damu ba"

Jawad yasaki wani irin murmushi sannan yace"gaskiya I'm happy sosai da hakan tafaru"

Fu'ad yadauki fillo yajefa masa cikin taqaici sannan yafice daga dakin, yana fita yaga har lokacin Yaya Mariya tana nan itada Daddy a zaune afalon saide babu Mummy, falon ya qarasa yanufi fridge zai bude yadauki ruwa adede lokacin Mummy tafuto hannunta janye da trolley tana share hawaye,Fu'ad yadago da sauri ya kalleta fuskarsa daukeda mamaki,Fridge din yafasa budewa yanufeta yana qoqarin riqe jakar kayan nata yace"Mummy meyafaru ina zakije?"

Daddy da fuskarsa tayi baqiqqirin ya kalli Fu'ad fuska babu alamun wasa yace"kai saketa ka koma ciki"

Gaban Fu'ad yayi wata irin faduwa,hakan da Daddy yayi shine ya tabbatar masa da cewa lalle ba lafiya ba, saboda bai ta6a ganin sunyi hakan ba, cikin sauri ya juya aguje yayi dakin Jawad,adede lokacin Jawad yafara duba computer sa zai nemo picture din Inaas ya kalla,sai ga Fu'ad aguje yashigo dakin, cikin firgici yace"yaya!! Mummy"

Jawad yafasa daukan computer yadago da sauri ya kalli Fu'ad yace"meyafaru? meyasameta?"

Cikin sauri Fu'ad yace"gida zata tafi,nahana ta tafiya Daddy yace nabarta tatafi"

Gaban Jawad yayi wata irin fad'uwa yace"what!?"

Baijira amsar Fu'ad ba yafice daga dakin cikin gudu, yana zuwa falon yaga tana qoqarin ficewa,cikin sauri yacinmata yariqe jakar yace" Mummy what happened? ina zakije?"

Hajiya Zaliha ta share hawayen idonta takasa had'a ido da Jawad,muryar ta can ciki tace" Jawad kayi haquri"

Cikin damuwa yace"Mummy wai meyake faruwa ne? meyasa kike bani haquri? please dawo,bani jakar"

Mummy takasa bashi jakar kuma takasa tafiya,Jawad yajuya ya kalli Daddy sannan yace"Daddy kayi mata magana zata tafi fa,wai meyake faruwa ne?"

Daddy yace"kabarta taje,ba buqatar cigaba da zamanta"

Jawad ya lumshe idonsa cikin damuwa yabude ya kalli Yaya Mariya yace" Hajiya Mama kisa baki mana"

Yaya Mariya tace"to Jawad kace karta tafi kuma taqi ji basai kabarta taje ba"

Wani irin taqaici yakama Jawad,yarasa meyake damun Daddy da wannan rikicacciyar tsohuwar.

Ya girgiza kansa yadauki jakar cak,sannan yakamo hannun Mummy suka wuce dakinta, suna zuwa dakinta tafada jikinsa tasaki wani irin kuka,haqiqa tasan cewa abunda tayi bata kyauta ba,sauqinta daya Alhaji dakuma Yaya Mariya basu fadawa Jawad din abinda tayi ba.
Jawad yasake rungume ta yana lallashin ta,Fu'ad ya kallesu yace"Mummy kiyi shiru please"

Bata saurari Fu'ad ba taci gaba da kukan ta,Jawad yajata suka zauna abakin gado yafara bubbuga bayanta sannan cikin sigar rada yace"Mummy kiyi shiru,babu inda zakije muna nan tare dake idan yadage akan saikin tafi to tare zamu tafi"

Ahankali tasaki ajiyar zuciya sannan tace"kayi haquri Jawad"

Jawad yadafe goshin sa da hannunsa yace"Mummy haqurin nan ya'isa haka,bakimin komai ba,kuma bazaki min ba,babu wata uwa dazata yiwa d'anta laifi Mummy, maganar Daddy kuma zamuyi settling komai nida Fu'ad,ki kwanta kihuta please"

Wani irin tausayin Jawad din da tsananin kunyar sa ya kamata,ahankali tagyada masa kanta alamun amsawa sannan ta share hawayen idonta tana sakin wata irin ajiyar zuciya sannan ta kwanta akan gadon,yatashi yaja mata blanket ya rufe mata qafafunta sannan ya kalli Fu'ad yace"muje"

Futowa sukai suka zauna afalon anan suka tarar Yaya Mariya tana sallama da Daddy zata tafi gida,Daddy yajuyo ya kallesu yaga sun zauna kowa ya tsare fuska su ala dole gaadin uwarsu suke, ko idan yayi niyar korar tata sune zasu hanashi oho(😂)

Bayan yaraka Yaya Mariya ma daya dawo falon shima waje ya nema ya zauna yadora qafa daya kan daya babu wanda yacewa wani uffan tsakanin shi da su,haka akai zaman kurame afalon kowa da abinda yake ransa.

Saida aka kira sallar magrib suka tashi daga falon suka wuce masallaci, dasuka idar da sallar ma basu dawo ba saida sukayi sallar isha'i, dasuka dawo dinma a falon suka zauna anan Na'im yakira Jawad yace gashinan zuwa,Jawad yaji dadin wayar tasa,hakan yasa yatashi ya kunna musu kallo har Na'im din yazo sukaci gaba da fira suna kallon labarai.

Daddy yashigo ya gansu, Na'im yatashi ya gaidashi, sannan Daddy yawuce sama, bai dade da zamaba Mummy ma tafuto tawuce dakin Daddy domin sake bashi haquri,Jawad yaganta, hakan saiya masa dadi koba komai insha Allah zuwa wayewar gari zasu daidaita kansu.

Har wajan qarfe tara na dare suna falon a zaune, har lokacin Mummy bata futo daga dakin Daddy ba, saida suka gama kallon labarai sannan Fu'ad ya sauya tasha yajuyo yana kallon Na'im tareda fadin"babu wasu zafafan yanmata ne? tunda Yaya yagwada na family ba'a dace ba yanzu saimu koma wajan bare"

Na'im yace"kamarya? mekake nufi?"

Fu'ad yayi murmushi yace" wallahi anfasa bikin Yaya, but issue ne na family dinmu kasan halin auren dangi"

Na'im ya girgiza kansa alamun rashin jin dadi sannan ya kalli Jawad yace"sorry bro...,banji dadi ba wallahi, ko shiyasa naga kayi shiru kabarmu munata zuba?"

Jawad ya kalleshi ya shafa sumar kansa yace" no,ni dadi ma naji da'aka fasa,ni har yanzu babu macen da take gabana"

Fu'ad yayi murmushi ya jinjina kansa baice komai ba, yayinda Na'im yasaki dariya yace"kaide bakaga wata zazzafar bane,akwai yanmata masu aji wallahi,kazo kayi biyaiya in hadaka da d'aya"

Jawad yamiqe yadauki wayarsa yana fadin"banda lokacin wannan shirman"
Chapter 26 · 0% Book details