← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 63

Sashe 19

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jawad ya kalleta fuska babu walwala sannan ya kawar da kansa,ya lura yarinyar batajin magana,saide kuma abun mamakin maganar Inaas din batasa yatafi ba,saida yatsaya Ammiy taqaraso wajansa sannan cikin lallashi tacemasa "muje yarona,rabu da'ita"

Saida Yajuya yasake kallon Inaas wadda batasan yanayi ba, sannan cikin sauri Yajuya yayi gaba yana zura hannunsa d'aya cikin aljihun wandon sa.

P.a da driver suna ganinsa suka qaraso da sauri suna bashi haquri,baice dasu komai ba yajuya yasake kallon Ammiy wadda take tsaye daga qofar gida,yarasa meyasa yakeji kamar bayason barin matar,kafin yace wani abu Bilkisu ta d'aga masa hannu sannan tace"Allah yatsare hanya,Allah yayima albarka"

Cikin jin dadi yace"Amin Mama"

Daga nan driver yabude masa motar yashiga suka tafi,saida suka qule sannan Ammiy tasaki ajiyar zuciya tadawo ciki zuciyarta fal da farinciki,ta zauna taci gaba da turarawa Inaas gashinta,Inaas tace"Ammiy daga ganin baqo? keda bakya yiwa mutane haka amma wannan sai qara liqe masa kike?"

Bilkisu tayi murmushi tace"ina laifi dannayi masa hakan? bakya ganin yaron yanada nutsuwa sosai?"

Inaas da mamakin Ammin nata yagama kasheta tayi ajiyar zuciya tace"nagani kam,naga nutsuwa Ammiy...".

Cikin jin dadi Bilkisu tace"ai shine abinda nake fad'a miki,kuma da alama babban mutum ne,naga ana bud'e masa mota da rawar jiki,kuma abokan tafiyar tasa banji sun fad'i sunan saba kowa Yalla6ai yake cewa,kinga yatafi ma ni kwata-kwata na manta ban tambayi sunan saba,Shima kuma bawan Allah babu magana shima bai tambayi namu sunan ba"

Inaas de datake cikeda mamaki tace"aikam hakane babu magana gashinan gim azaune"

Abangaren su Jawad kuwa kai tsaye gidan tvn dazasuyi fira dashi nan suka wuce,yana qarasawa guards suka matso da gudu suka bude masa mota, sannan suka qarasa ciki domin fara gabatar da shirin.

Tsawon minti talatin firar tasu ta d'auka sannan yawuce gida,daya koma gidan ma bai zauna ba yasake shiryawa ya futo zai wuce Nigeria,gaba d'aya 'yan gidan na Alhaji Auwal sukai masa rakiya zuwa wajan motocin dazasu kaishi Airport,Ummi sai fari take masa da'ido tana masa yanga,shikuwa bihim baima gane metake nufi ba.
Yayinda fauzy yayar Ummi ta dakata daga gefe ta hard'e hannunta a Qirji tana kallonsu,dama itama 'yar shan qamshi ce kamar shi, Ummi tafita sauqin kai.

Saida motocin suka fice daga gidan sannan suka juya ciki,kafin motocin su Jawad su qarasa Airport Fu'ad yakira wayar Jawad,p.a dake zaune agaban motar yajuyo yabashi wayar,yana d'auka Fu'ad yace"yaya zan wuce Germany ba lalle kadawo ka sameni ba"

Jawad yayi murmushi yace"ok har birthday party d'in naka yazo?"

"yes Yaya"

"ok kanada kud'i enough awajanka?"

Fu'ad yace"yes Yaya akwai,kuma shaddodinka ankawo sun zama ready,Yaya I will miss you,but bazan dad'e ba zan dawo may be 2 to 3 day's"

Cikin sauri Jawad yace"no Fu'ad,karka damu kayi zamanka kahuta sosai,lokacin danake kamar kai niban samu damar wannan hutun ba,saboda haka kayi rawa,kayi yawo,kahuta sosai saika dawo"

Cikin farinciki Fu'ad yace"thank you Yaya,I'm proud of you"

Jawad yayi murmushi yakashe wayar yabawa p.a sannan ya jingina da motar ya lumshe idonsa,yana ganin fuskar Bilkisu acikin idon zuciyar sa.

Bayan sun dawo Abuja kai tsaye d'akinsa yawuce,yayinda Daddy da Mummy suke zaune afalo.
Alhaji Auwal yakira wayar Alhaji Mekudi,bayan sun gaisa sungama yiwa juna jaje akan rasuwar Baby, Alhaji Mekudi yace"Jawad yadawo gida yanzu,ina fatan sun daidaita da Ummi ko fauziya"

Alhaji Auwal yayi murmushi irin nasu na manya yace"Inaaa!, banga alamar hakaba Alhaji,ina ganin kawai arabu dasu,suma zansa musu rana da samarin su nanan Niger kawai,kasan sud'in gaba d'ayansu daga Jawad d'in harsu fauziyan dukansu qananun yara ne,kada a takura musu su shiga damuwa".

Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya cikin damuwa,ko kad'an baiso hakan ba, yaso ace sun sake had'a danqon zumunci tsakanin sa da aminin nasa,cikin damuwa yace"to shikkenan Alhaji,Allah yasa hakane yafi Alkhairi"

Bayan sun gama wayar Hajiya Zaliha tace"Alhaji banji kace komai akan maganar Jawad da Amal ba,Yaya Mariya tazo tace ita bata amince ba,Alhaji ina laifin Amal? yanzu Yaya Mariya tana nufin kenan d'an'uwana bai iya bada tarbiya ba?"

Alhaji Mekudi yayi murmushin su na manya yace" Zaliha kenan,wani lokacin kina yin abu kamar bakisan halin Yaya ba,sanin kanki ne Jawad tun yana yaro take ji dashi,kamar yanda na lalla6a ta shekaran jiya insha Allah idan auren ma yataso zanji da'ita, tunda de kedin kinga yarinya kuma yarinya tayi miki to shikkenan,shima yaron da kansa yace tunda za6inki ce bashida damuwa to dan Allah kibar maganar nan"

Hajiya Zaliha tayi ajiyar zuciya tace"to shikkenan Alhaji,yawuce"

*** *** ***

Niger Republic

Da daddare suna zaune suna kallo itada Ammiy bayan sun idar da sallar isha'i,ganin babu abinda ake a tashar tauraruwa sai tallace-tallace hakan yasa Inaas ta d'auki remote ta sauya tasha zuwa gidan television na qasa,adede lokacin aka hasko fuskar Jawad yana zaune yayi kyau cikin suit dinsa ta d'azu da safe da yabar gidan nasu,gaban Inaas yayanke yafad'i tazaro idonta waje,takamo hannun Bilkisu tace"wanake gani haka Ammiy?"(😳)

Bilkisu ma tazubawa Tv ido tana kallo,tabbas yaron da yabar gidansu ne d'azu dasafe,to meyake a tv ko aikin jarida yake?(🤔)

Kafin su sake magana matar datake zaune akan kujera tana fuskantar Jawad da alama itace zata masa tambayoyi ta kalleshi fuskarta fal murmushi,sannan ta juyo kad'an ta kalli camera tace"masu kallo barkanmu da sake kasancewa acikin wannan shirin namu mai suna 'musan junanmu', ayau mun kar6i baquncin shahararran d'an kasuwa,wanda ya qirqiri kasuwanci dayawa afad'in duniya,jagoran talakawa,wanda ya kasance yana taimakon talakawa,matashin da yake samun nasara a kasuwancin sa,shugaban kamfanin Mekudi Oil, wato JAWAD MEKU'DI"

Inaas tanajin sunan Jawad tamiqe tsaye tad'ora hannunta akanta tafara zagaye falon nasu tana fadin"innalillahi!,shikkenan Ammiy,shikkenan na kashe kaina,ko sunyi niyar mayar dani aiki wallahi yanda na zauna naci masa mutunci yanaji na sarai dole su fasa"

Ammiy ta gagara magana saboda tsananin mamaki,ta tattara hankalin ta kacokam tamaida kan tv,tunani take aranta yanzu dama yaron nan shine shugaban kamfanin Mekudi oil?

Inaas takoma ta zauna adede lokacin da matar tasake kallon Jawad tace"Mr. Jawad,kwatsam saigaka a qasar Niger,muna tunanin idan har hamshaqin d'an kasuwa kamarka zai shigo qasar Niger to muna fatan zaka sake kawowa qasar wani cigaban ne kamar yanda kakawo mana kamfanin ka a baya kuma har yanzu oil din Mekudi yana nan ana damawa dashi acikin jerin mayukan da'ake amfani dasu a qasar Niger"

Jawad yayi murmushi d'an kad'an sannan ya motsa lips dinsa kamar bayason magana yace"ziyara ce kawai takawoni dakuma ta'aziyya"

Zamanta tagyara sannan tace"Allah yaji qan rai, Mr. Jawad,kamfanin Mekudi oil ya shahara,sannan yagama kerewa dukkanin sauran kafaninnika na oil's dake cikin qasar Niger,yana d'aya daga cikin jerin manyan kamfanin nika dasuka samu damar shiga cikin jerin kamfanin nika aduniya, kunada resuna na Mekudi oil samada guda talatin a qasashen aduniya ciki harda qasar Niger,Mr. Jawad menene sirrin nasarar ka?"

(Ammiy na tace duk wanda ya aureni yayi sa'ah,saboda nid'in tadaban ce ....)

Maganar Inaas ce tafad'o masa cikin ransa,cikin sauri yayi nasarar kawarda tunanin yarinyar aransa sannan ya girgiza kansa ya kalli 'yar jaridar yace"sirrin nasarata shine addu'ar mahaifiyata"

"mezaka cewa sauran matasa 'yan kasuwa masu tasowa? Wacce shawara zaka basu?"

"Ina bawa matasa shawara su tashi suyi aiki tuquru domin inganta gobensu,abaya babu abinda banyi ba domin in temaki kaina,suyi qoqari,su tashi tsaye, su jajirce,insha Allah ubangiji zai taimakesu"

"Mr.Jawad,kasancewar ka babban d'an kasuwa,sananne a'idon duniya,mutane dayawa suna saran ganin matarka,wacce me sa'ar ce tayi nasarar sace zuciyarka? shin babu 'yanmatan ne, kokuma kaine baka ra'ayinsu?"

Kallonta yayi yace"Jawad d'an kasuwa ne, babu abinda na'iya sai kasuwanci,har yanzu de babu yarinyar datayi nasarar sace zuciya ta"

"Mr. Jawad,kashiga cikin jerin hamshaqan masu kudi a Africa,menene burinka nagaba?"

Murmushi yayi wanda yasake futo da tsantsar kyawun sa sannan yace"babban burina shine in shiga cikin jerin masu kudin Duniya"

'Yar jaridar tayi murmushi tace"muna tayaka Addu'ah Allah yacika ma wannan burin naka,mungode sosai da ziyara,muna fatan zuwa gaba zamu sake kar6ar baquncinka"

Kansa yagyada mata alamun insha Allah,daga nan tarufe tattaunawar tasu da fatan Alkhairi.

Har inda yafuto zai shiga motarsa domin yatafi gida saida suka nuna,da yanda wasu daga cikin yan jarida suka tareshi yake yi musu sign,wasu kuma selfie suke dauka dashi.
Saida yagama da jama'ar sannan yanufi mota yayinda guards kusan guda goma sha biyar suke kakkareshi saboda kada acutar dashi, cikin sauri aka bude masa mota yashiga sannan suka tafi.

Inaas ta janye tagumin datayi da hannu bibbiyu bayan tagama kallon firar su Jawad da yanda taga guard's suna take masa baya, ta tuna dazu dasafe lokacin da take gwada yanda zata Shaqe masa wuya idan taganshi,harce masa tayi bashida mutunci,meya kaita? Ita 'yar wacece? ina ita ina takalar wannan mutumin da fada? dama ance idan baka san mutum ba kada kayi gaggawar cimasa mutunci,ta lumshe idonta taja wata irin ajiyar zuciya sannan ta bud'e idonta tajuyo ta kalli Ammiy taga sai murmushi take,cikin muryar shagwa6a tace"Ammiy sai murmushi kike kamar ba shine ya koreni daga wajan aiki naba"

Bilkisu ta kalleta tace"ina kallon sane, kalar fatarsa kamar ta d'ana, fari tas dashi,nasan nima da Muhammad d'ina yana nan,zuwa yanzu zekai shekarun wannan Jawad d'in"
tasake kallon Inaas sosai sannan taci gaba da fad'in "kinga dalilin dayasa banason kidinga wannan shegen surutun naki agaban baqi ko? yanzu de gashinan kingama zageshi tsaf,kuma yanad'e wannan zagin tas a kunnansa,keda aiki a kamfanin sa kuma shikkenan zance yaqare yariga yazama tarihi,shiyasa naga kafin yatafi yajuyo sai kallonki yake ashe shi sake ganeki yake da kyau ko wataran zaki koma masa kamfani dan yasan irin hukuncin dazai miki"

Inaas taturo bakinta gaba cikin shagwa6a tace"to Ammiy korata fa yayi"

Bilkisu tace"to ai saiki yi tunda bazaki rissina ba"

*** *** ***

Washegari da rana ya shirya tsaf ya futo domin cin abinci,haka kawai yake jinsa cikin nishadi, kafin yaje qasar Niger zuciyarsa cike take fal da d'aci ahaka yatafi saboda maganar yarinyar da shine yace yabasu dama su nemo, kuma sun nemo din amma yana fishi akan haka,amma tunda yabar qasar Niger din yadawo Nigeria yakejinsa cikin walwala,dazaran yatuna da Matar nan data bashi shayi sai yaji hankalinsa ya kwanta,sai yaji wata irin nutsuwa wadda bai ta6a jin makaman ciyar taba.

Kai tsaye dining yawuce anan ya tarar da abinci kusan kala biyar, Mummy ta kalleshi da kulawa tace"wanne kakeso nabaka dana?"
Chapter 19 · 0% Book details