← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 63

Sashe 5

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta waiga gefenta,cikin sa'ah taga wata hamshaqiyar Mota a adane,da alama motar wasu matafiya ne suka tsaya uzuri,ahankali tafara tafiya tana nufar inda motar take,taku take sid'af sid'af ahankali hartaje wajan motar,duka glasses d'in motar a rufe suke,tana ganin idan tashiga cikin motar tarufe,ba zasuji kukan yaron ba,batasan cewa shikam yaro yariga ya suma ba(😭)

Cikin ikon Allah tana bud'ewa motar ta bude alamun ba'a kulle motar ba,tana shiga cikin motar wani irin qamshi me dad'i ya bugeta da wani sanyi-sanyi da motar takeyi alamun ba'a dad'e da kashe esin ciki ba,ahankali ta ajiye Muhammad tasaka hannu zata rufe motar wannan 'yan fashin suka ganta,cikin 6acin rai suka qarasa suka fuzgota,d'ayan yasaka hannunsa ya rufe motar ga Muhammad acikin Mota (🙆🏻‍♀️)

Janta sukai can bayan bishiyar data 6uya musu,Mayafin jikinta dayake hannunsu wanda suka fuzge matashi d'azu,dashi sukai amfani suka d'aure mata baki,yayinda mutum biyu suka rirriqe mata hannayenta tabaya,ogansu ya matso cikin zilama yad'ora hannayen sa duka biyu akan qirjinta yafara murzawa,baqin ciki yasa tasaki wani irin kuka gashi sun rufe mata baki,hawaye sai zarya yake a fuskar ta yayinda take girgiza masa kai alamun a'a,tanajin wani irin baqin ciki kamar zata mutu.

Adede wannan lokacin Alhaji ALIYU MEKU'DI,yazo yabud'e motarsa yashiga ya zauna ya kunnata,danjar mota takawo haske alamun mota tatashi,gaban Bilkisu yayi wata irin fad'uwa ganin an kunna motar kuma Muhammad yana ciki,lokaci d'aya ta zaro manyan idonta waje,tafara fuffuzgewa daga hannun su,amma sai suka sake riqeta,hasken wannan fitilar motar shine yasake haskawa har taga number motar,tanaji tana gani mota tafara tafiya,ganin yanda taqi tsayawa waje d'aya sai faman fuzge-fuzge take hakan yasa oga ya wanke fuskarta da wani zazzafan mari,zafin Marin yasa ta sunkuyar da kanta qasa,dogon gashinta ya sakko ya rufe mata fuska,tad'ago kanta da sauri ta kalli motar tagade da gaske fa motar nan tafiya take gakuma d'anta yana cikin Mota,lokaci d'aya tasa qafarta tadaki abunsa(🍌)
Tsananin azabar dayaji ne yasa ya janye hannunsa daga kan qirjinta yamaida hannun zuwa gabansa ya tsugunna yana runtse ido,ganin Mota tafara nisa yasa Bilkisu ta qwace ta kwasa aguje tabi bayan motar,tacire mayafin dasuka rufe mata baki tayi wulli dashi,tabi bayan motar da mahaukacin gudu tana kuka tana fad'in " d'ana,d'ana yana ciki,Muhammad karka tafi kabarni,...."

Tasake daga murya tace" me Mota ka tsaya!!! "

Amma inaaa,Alhaji mekud'i kokad'an baiji taba,saima gudu daya qarawa motarsa sakamakon lokacin tashin jirgin su yana gab da qurewa gashi ko cikin Nigeria bai shigaba bare yaqarasa jihar kano yagana da wasu baqi sannan yahau jirgin zuwa Lagos,haka Bilkisu tasake bin bayan motar da gudu tana d'agawa Mota hannu tana magana kamar ta6a66iya.

kasancewar gudun mutum dana mota ba d'ayaba,hakan yasa Bilkisu tanaji tana gani,Mota tatafi da d'anta idonta akan Number wannan Mota,lokaci d'aya ta tsugunna awajan tasaki wani irin qarajin kuka me tsoratar wa,adede lokacin kuma 'yan fashin suka sake zuwa zasu kamata, a wannan yanayin zuciyar Bilkisu ta bushe,ta tsinke,bata tsoron koma mezai faru yafaru,wani qaton itace dayake gefenta tad'auka tayi kukan kura ta maka musu shi,sannan tasaki itacen ta gudu,bata hango nisan tafiyar da tayi tana gudu ba,harta qaraso cikin Garin 'Dungas' a wahale,alokacin masallatai suna kiran sallar farko,tana tafiya tana had'a hanya kamar 'yar maye,ga dogon gashin kanta yayi buzu-buzu ya hargitse yana rufe mata fuska kamar na mahaukaciya,saida tazo qofar gidansu idonta ya rufe ruf...tadena ganin komai tazube awajan Sumammiya.

(so Sad....😭Sorry Bilkisu)

(masu karatu karfa ku manta har yanzu labarin 1986 mukeyi shekaru talatin da bakwai dasuka wuce Kenan 🤒yauwa)

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne, 300 ne kacal

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Tareda turo shedar biya ta wannan number 08033300034

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝
('yar me gwanjo)

Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Bilkisu's name

https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu

5&6

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Alhaji Aliyu Mekudi,yayi nisa atafiya yaji kamar motsi abayan motarsa,juyawar da zaiyi yayi tozali da jariri wanda ubangiji cikin ikonsa yasa ya farfad'o da kansa sai d'aga qafafu da hannu yake sama irinna jarirai.
Alhaji Mekud'i yataka wani irin birki ya futo daga mota yazo yabud'e gidan baya,idonsa ya sauka akan kyakykywan yaro masha Allah fari tas dashi,gabansa yayi wata irin fad'uwa ganin jaririn kyansa yayi yawa kamar ba d'an Bil Adama ba,yakai hannu zai d'auki yaron hannunsa yafara karkarwa,haka ya daure yad'auki yaron wanda yunwa tasa yasaka d'an yatsansa a bakinsa yanata tsotsa,Alhaji Mekudi yasake kallon jariri yace"innahu min sulaimana wa'innahu bissmillahirrahmanirrahim"

Yayi tunanin ba d'an mutum bane Aljanine.
Yajuya ya kalli gabas da yamma yaga babu kowa,to waye zai saka masa jariri amota idan ba aljannu ba?(🤔)
ga yaro kwata-kwata babu inda zakace bahaushe ne saide Balarabe duk yanda akayi yaron aljannu ne.
Cikin sauri ya lalla6a kamar yana tsoron aljannun zasu kamashi yamaida yaron cikin mota yarufe, yakoma yatada mota yajuya baya zaije inda ya ajiye motarsa ko Allah zaisa aljannu suzo su dauki d'ansu,cikin gudu yaja motar yajuya,saide yana zuwa wajan yaga babu kowa,yaduba yasake dubawa babu alamun komai, yabude murfin motar gidan baya yakoma gefe ya yatsaya yana jira masu d'a su dauke d'auke d'ansu, wato aljannu.

Saide tsawon mintuna babu abinda yafaru,saima wasa da Muhammad yakeyi da yatsansa abakin sa idonsa abude kar ko alamun kuka bayayi.

Alhay Mekudi daya gaji da jira yakoma wajan motar yasaka hannunsa ya d'auki Muhammad,yad'aga shi sama sannan yace"ya ubangiji na,haqiqa ni bawankane mai yawan godia agareka,na kasance tsawon wasu shekaru Ina neman haihuwa ubangiji Allah baka bani ba,amma rana irinta yau ya Allah ka azurtani da wannan wanda bansan daga inda yake ba,Allah nagode maka da wannan kyauta dakamin,bazan baka kunyaba wajan yiwa yaron nan tarbiya kamar nine na haifeshi,haqiqa zan riqe amanar wannan yaro kamar yanda kayiwa sauran iyaye umarni su riqe amanar 'ya'yansu"

Ya sauke hannunsa qasa yasaka Muhammad a qirjinsa ya rungume shi,sannan ya zagaya dashi yabude motar yasaka shi a cinyarsa, yaci gaba da driving.
Da yaron a hannunsa ya gana da wasu baqin turawa akano,saida yagama dasu sannan yanufi Airport d'in Malam Aminu.
Lokacin daya qarasa filin jirgin already har jirgin dazaibi yatashi, saida yasake yin booking yajira lokaci yacika, sannan jirgin su yasake tashi zuwa Lagos.(👋🏻)

*** *** ***

Niger Republic

Azabure Bilkisu me gwanjo tafarka daga baccin datake,gefenta ta kalla tana dube-dube da alama Muhammad take nema,ganin babu Muhammad babu dalilinsa sai qaninta dayaci uban wani nad'in rawani irin wanda buzaye sukeyi, da matar qaninta wadda take Sanye da laffaya ruwan toka dasuke gefenta babu kowa,hakan yasa tagane cewa ba mafarki takeba da gaske ne shima Muhammad yatafi,shikkenan yatafi yabarta,cikin d'acin zuciya da qunci tafashe dawani irin kuka,matar qaninta ta dafa kafad'arta cikin sigar lallashi tace"Yaya kiyi haquri kidena kuka,tunda Allah yakawo ki gida lafiya ai Alhamdulillah"

Qanin nata ma yadubeta cikin hausarsa da bata goge sosai ba yace"kiyi shiru"

Daga haka baisake cewa komai ba ya kalli matarsa JAMILA,wadda yasha fama yayi yaqi da samari bila'adadin domin ya aureta saboda yanda takeda tsananin kyau,hakanne ma yasa mahaifinta yasa mata suna Jamila,yayi ajiyar zuciya yace"JAMI, ki kula da'ita nizan fita nema..."

Jamila ta kalleshi tagyad'a kanta sannan tace"to FAROUQ saika dawo"

Farouq yasa hannu yad'auki butar shayinsa dawata jaka 'yar qarama arataye a wuyansa, yafice daga gidan.

Tun bayan fitar Farouq Bilkisu me gwanjo take hawaye,idonta yayi jajir kawai hawaye ne masu zafi suke zarya akan kuncinta,tsabar kuka har muryarta ta dashe,jamila tayi lallashin tayi ban baki amma Bilkisu shiru,har zuwa la'asar hawaye take,haka kuma taqiyin magana,taqi cewa komai, kawai de ta zubawa waje d'aya ido tana kallo ga hawaye yana zuba,agefe guda kuma ga nonon ta dayake zubarda ruwa kasancewar anwuni ba'asha ba.

Sai yamma lis,farouq yadawo,ya kalli Yaya Bilkisu sannan ya maida kallonsa ga Jamila yace"Jami,yanaga Yaya a zaune tayi shiru har yanzu kukan takene?"

Jamila ta kalleshi tace"ka ganta nan tunda kafita har yanzu kuka take taqicin komai sannan kuma taqiyin magana"

Farouq ya girgiza kansa ya zauna a kusada Bilkisu sannan yacewa Jamila"had'o mata shayi"

Jamila tatashi da sauri tahad'owa Bilkisu shayi acikin wani d'an qanqanin kofi irin wanda buzaye suke amfani dashi,tazo ta ajiye mata shayin itama tazauna awajan.

Farouq ya kalli Bilkisu yace"Yaya kid'auki shayin nan kisha hanjin cikinki ya warware"

"na salwantar da d'ana"
Shine kawai abinda Bilkisu tace.

Jamila ta kalli Farouq tace"kamar fa bata cikin hayyacinta,Yaya da batada kowa kana jifa maganar yaro takeyi"

Farouq ya jinjina kansa yace"um ina tunanin haka,inaga iftila'in data had'u dashi ahanya shine bai barta ba,bari inje wajan liman yabani rubutu na kawo mata tasha ko Allah zaisa tadawo hayyacinta"

*** *** ***

Lagos Nigeria

Gudun kada mutane Susan abinda yake faruwa hakan yasa Alhaji Mekud'i yana sauka a Airport babu wanda yasan da dawowar sa kai tsaye yawuce gidan yayarsa qwalli d'aya aduniya wadda suke uwa d'aya uba daya kuma iya sukad'ai suka rage a duniyar wato YAYA MARIYA,ita kanta gidan datake ciki abun kallo ne,basai an fad'aba kasan cewa gidan ya amsa sunansa na gidan yayar Mekudi.

Tana ganinsa da yaro tatashi tsaye ta tareshi tareda fad'in "Mekudi ina kasamo yaro haka tubarkalla masha Allah?"

Zama yayi acikin luntsuma luntsuman kujerun falon sannan yayi kissing Muhammad yace"Allah ne yabani shi Yaya,kar6eshi kisa masa albarka"

Cikin sauri Yaya Mariya ta kar6i yaron fuskarta fal farinciki tana fadin"ikon Allah,Aliyu wannan yaron aid'an larabawa ne,Ina kasamo shine?"

Murmushi yayi, sannan yatashi yaje inda wayar gidan nata take ajiye yakira layin gidansa yacewa zaliha matarsa lalle lalle duk abinda take tabari tasa driver yakawo ta gidan Yaya Mariya, kasancewar gidan babu nisa hakan yasa nan da Nan Hajiya Zaliha matar Alhaji Aliyu Mekudi tazota cikin sauri, bayan sun gaisa nan take Alhaji Mekudi yafara basu labari tiryan-tiryan yanda akai yasamu wannan jariri.

*** *** ***

Niger Republic

Bayan Farouq yakawo mata rubutu Jamila tajuyeshi a kofi takawowa Bilkisu tace"Yaya gashi ki kar6a kisha"
Chapter 5 · 0% Book details