← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 63

Sashe 44

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan daya gani daga wajansu shine yasake tabbatar masa cewa tabbas shi d'in ba dansu bane,may be ma bashida iyaye kokuma agidan marayu suka dauko shi.

Cikeda damuwa ya runtse idonsa yanajin duniyar gaba daya ta masa qunci,to su waye iyayensa? meyasa suka rabu dashi? daqyar ya'iya bude idonsa wanda yake jin yanason rufewa ya sake kallon Mummy da Daddy yace"Mummy,Daddy! kufadamin su waye iyayena?"

Hawaye yazubo daga idanun Bilkisu,ta matso ta riqe fuskarsa da tafin hannunta biyu sannan ta kalli cikin idon Jawad,cikin muryar kuka tace"nice mahaifiyar ka,nice na haifeka,ina sonka sama da kowa a Duniyar nan"

Inaas da Fu'ad da basusan abinda yake wakana ba,suka dago kansu da sauri suka kalli Bilkisu.

Jawad kuwa yanajin furucin Bilkisu ya lumshe idonsa,wani irin hawaye me d'umi yazubo daga idanunsa,ahankali yafurta kalmar "MAMA"

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,idan baki biyaba kika karanta min littafi to ban yafe ba👌🏻

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

17&18

Hawaye yazubo daga idon Bilkisu,cikin kuka yace"na'am Muhammad"
Jawad ya lumshe idonsa,wani irin hawaye me d'umi yazubo daga idanunsa.

Daga wannan lumshe idon dayayi, baisake budewa ba yaji qafafunsa bazasu iya daukarsa ba,daga nan yazube awajan bai sake sanin meke faruwa ba.

Cikin sauri Fu'ad yayi wani irin tsalle sai gashi a gaban Jawad yataroshi,Daddy da Man Sulaiman da Farouq suka qaraso suka kinkimi Jawad sukai sama dashi,Mummy da Bilkisu da Inaas dakuma Yaya Mariya sukabi bayan mazan.

Wannan shine karon farko da Inaas da Bilkisu suka ta6a hawowa sama,Inaas de saida tadan gwada halin nata,domin kuwa sai kalle Kalle take sosai tabawa idonta abinci saboda abinda ba'a saba gani bane,tundaga falon sama har cikin dakin na Jawad sun kai maqurar haduwa, an tsara shi dakyau kamar baza'a mutu ba.

Kwantar dashi sukai akan gado,sannan Fu'ad yakira wayar likita,dukansu kowa yayi shiru ya nemi wajan zama sukai jugum-jugum har likita yazo ya dubashi,bayan yagama dubashi ya kalli mazan dakin yace"babu abinda yake damunsa,kawai yaji wani wani abu ne wanda yabashi tsoro,insha Allah idan yafarka zai tashi lafiya"

Daddy yace"to Alhamdulillah likita,mungode sosai, Allah ya tasheshi lafiya"

Likita ya amsa masa, sannan yayi musu sallama yatafi.

Yaya Mariya tasaki ajiyar zuciya tace"Bature! Bature!! Bature ba mutumin kirki bane,Allah ya shirye shi idan me shiryuwa ne,idan kuma bazai shiryu ba daidai nake dashi"

Mummy tayi qasa da kanta,har gobe tana nadamar abinda suka aikata abaya itada Yayan nata,yaro yana zaune dasu zuciya d'aya,yanzu gashi saboda jin cewa su din ba iyayensa bane shine yashiga wannan hali,dole ne tasake neman gafara awajan ubangiji ta kuma nutsu taja yaranta jikinta.

Yaya Mariya ta kalli mutanan dakin baki d'aya tace"to Bilkisu ku zauna tare dashi keda Zaliha,bari mu barshi yahuta"

Cikin sauri Hajiya Zaliha ma tatashi tace"A a Yaya,yau kam itace tafi cancanta ta zauna dashi,taja shi ajikinta ta lallashe shi"

Daddy yace"hakane kam,Man Sulaiman kaima matsa kusa ku zauna tare"

Man Sulaiman ya girgiza kansa ahankali yace"Haba Alhaji,ni dakai awajan Jawad duk d'aya ne,yanda zaka fita nima fita zanyi,ita Bilkisun de ta zauna, zata iya kulawa dashi,Allah yasaka muku da Alkhairi Alhaji,Allah yabiya ku da gidan aljanna"
Ya qarasa maganar yana fashewa da kuka.

Daddy yadan bubbuga gefen kafadarsa yace"ya'isa haka Man Sulaiman"

Daga nan kowa yamiqe,Bilkisu ta qarasa kan gadon Jawad din ta zauna ahankali,Inaas ta qaraso wajanta tace"Ammiy kidena kuka, murna zakiyi"

Bilkisu tayi murmushi ta kalleta tareda shafa kanta tace"to Inaas,kije ki kwanta karki manta kiyi Addu'ah kinji?zan zauna tareda Yayanki"

Inaas tace"to Ammiy"

Sannan itama ta futo tabiyo bayan su Yaya Mariya,saida tasake yiwa Ammiy bye bye da hannunta,sannan taja musu qofar tarufe.

Fu'ad ya dauki Yaya Mariya zai maida ta gida,Mummy kuma suka wuce daki itada Daddy,itama Inaas tabi bayan Abban ta da Man Sulaiman suka nufi nasu Plat din.
Tana zuwa dakinsu tamurzawa qofar key,sannan ta jingina ajikin qofar tana sakin wani irin murmushin jin dad'i,Yaya Jawad shine Yayanta? kenan shiyasa Ammiy take sonsa?
Cikin wata irin murna tayi jifa da Mayafin Abayar dake kanta tahau kan gadon nasu ta dinga tsallen murna.

****

Qarfe goma da rabi na dare Bilkisu tajuya ta kalli Jawad wanda yake bacci har yanzu,ta kalli yatsun qafarsa har yanzu de sak irin yatsun qafar Man Sulaiman ne,hawaye yazubo daga idonta tayi sauri ta goge su,sannan tasake matsawa kusa da Jawad din tadauke kansa dake kan fillo tadawo dashi kan cinyarta,ahankali ta dora hannunta akan lallausar sumar kansa ta dinga shafawa,bata cikakken minti d'aya batare data sake kallonsa ba.

Har wajan shabiyun dare Jawad bai tashi ba,har zuwa wannan lokacin kuma Bilkisu bata daina shafa sumar kansa ba,jitake kamar a mafarki wai yau itace tareda d'anta,bayan shekaru talatin da bakwai yau Allah ya bayyana mata d'anta.

Cikin wata irin murya me rauni tace"Baba na ina kashiga? ina ka shige kabar Mama tsawon wannan shekarun?"

Hawaye yacika idonta,ba tareda data goge hawayen ba taci gaba da fadin"meyasa na aikata haka? meyasa na salwantar dakai?"

Hawayen ta ya d'iso akan fuskar Jawad,tunda tafara magana yana jinta,shi kansa hawaye yake,itama tanajin yanda hawayensa yake sauka akan cinyarta.

Ahankali yasaka hannayen sa a bayanta dede qugunta,yasake rungume ta yana sakin kuka kamar ba Yalla6ai Jawad ba.
Daga ita harshi kuka suke,cikin kuka yace"Karki sake tafiya ki barni Mama...."

Bilkisu dake kuka tace"bazan sake ba Jawad,ina tare dakai bazan sake yin nesa dakai ba,Mama tana nan bazata sake barin d'anta ba"

Jawad yasake Rungume ta sukaci gaba da kuka,sun dade suna kuka sannan tayi shiru,shima ta share masa hawayen idonsa,taci gaba da fadin"ba'asan raina narabu dakai ba,lokacin da nabar jigawa state munshigo Niger ahanya yan fashi suka taremu, sun nunamin suna so suyi fasiqanci dani,nikuma na bijire musu,hakan yasa na gudu,sukabi bayana zasu kamoni,gashi sai kuka kake,duk inda sukaji kukan ka saisu biyoni,nasa hannu na na rufema baki naga kana qoqarin shid'ewa, hakan yasa danaga mota a ajiye agefe kuma duka glass din motar a rufe suke sainayi sauri nasaka ka aciki na rufe motar, ashe yan fashin sun ganni,sukazo suka Jani cikin duhu suka rufemin baki na, akan idona Alhaji yaja mota yatafi,gashi kana cikin motar, ganin Antafi min da dana hakan yasa naji wani irin qarfi naqwaci kaina a wajansu nabi bayan motar da gudu,saide tuni Alhaji yamin nisa,Nashiga matuqar damuwa alokacin dana rasaka,bansan adadin kwanakin danayi kewarka ba,har bayan wasu shekaru ban dawo daidai ba,saida Jamila matar qanina Farouq ta haifi Inaas,sannan ne Inaas taci gaba da 'DEBE MIN KEWARKA,daga qarshe Jamila mahaifiyar Inaas ta rasu,Farouq yabani Inaas Halak Malak, amma duk da haka na nunawa Inaas cewa tanada Yaya namiji,duk wahalhalun damuke sha nida ita ina fada mata cewa da yayanta yana nan bazai bari tayi aikin komai ba,kaida ita duk daya ne awajena,kaci gaba da kula da qanwar ka kaji?"

ta qare maganar cikin sigar lallashi.

Ahankali Jawad yatashi zaune,yakama fuskarta ya riqe da hannunsa biyu, yazuba mata ido yana kallonta cikin tsananin soyaiya dakuma farinciki, sai yanzu ne yagane dalilin dayasa gabansa yake faduwa duk lokacin dazai kusanci matar, sai yanzu ne yagane dalilin dayasa yake jin nutsuwa aransa duk lokacin datake kusa dashi,cikin yaqini yace"zan kula daku Mama,daga yau babu wanda ya'isa ko kallon banza yamiki bare yayi tunanin keta miki haddi,kiyi haquri, ki qara haquri ki yafewa Babanah"

Bilkisu a rungume Jawad ajikinta tace"Allah yayi maka Albarka Muhammad"

Jawad ya lumshe idonsa yanajin wata irin nutsuwa ajikinsa wadda tunda yake bai ta6a sanin cewa idan uwa ta rungume d'a haka akeji ba.

Acikin qirjinsa yasa ta,dukansu suna zaune,sun jingina da jikin gadon,ahaka wani irin bacci me dadi ya daukesu.

****

Washegari sassafe Inaas tatashi tataho wajan Ammiy,saide alokacin basu farka daga bacci ba itada Jawad,kuma babu wanda yayi yunqurin tashin su,dan haka ta wuce kitchen wajan Hajiya Zaliha tana ganin yanda suke irin nasu aikin breakfast din na yan gayu,daga nan itama tasaka hannu sukaci gaba dayi tare da masu aikin suna sake koya mata wani abun, ga Inaas da shegen surutu abu kad'an idan taga bata ganeba sai an dakata da aiki anyi mata bayanin sa.
Chapter 44 · 0% Book details