← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 63

Sashe 49

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilkisu ta girgiza kanta tana murmushi bayan tagama ganin irin kallon soyaiyar da Jawad yazubawa Inaas ko kunyarta baiji ba,to wannan agaban idonta ne suke jifan juna da irin wannan salon soyaiyar,to idan kuma bayan idonta ne yaya kenan?(🤔)

Acan Compound suka tarar da Daddy taredasu kawu Amadu,Jawad yayi sallama da iyayen nasa,guard dinsa suka bude masa mota yashiga suka tafi.

Bayan Daddy yadawo falo tunda ya zauna yaketa amsa kiran mutane masu yimasa Allah ya sanya Alkhairi.

Mummy ta kalleshi tace"Alhaji tunda ka zauna kake waya,yau mutane sun hanaka nutsuwa,tun da safe kake falon baqi daga wannan yatafi sai wannan"

Alhaji Mekudi ya kalli Hajiya Zaliha yace"ni kaina abun yana bani mamaki,kuma duka fa 'yan Allah ya sanya Alkhairi ne, sunji batun saka ranar Jawad, bansan cewa mutane suna daakon zuwan ranar auren Jawad har haka ba"

Kafin Mummy tayi magana,wata wayar tasake shigowa,yadauka cikin murmushi yana fadin"Alhaji Mudan mutanan Ghana"

Alhaji Mudan yayi murmushi irinna qosassun masu kudi sannan yace"Mekud'i da kansa..."

Gaba dayansu suka sa dariya,Alhaji Mekudi yace"to Yaya kasuwanci, ya Ghana?"

Alhaji Mudan yace"Alhamdulillah kasuwanci suna tafiya sosai,da taimakon yaronka Jawad yanzu nima yarona shima yayi nisa a nasa kasuwancin"

Daddy yace"to Alhamdulillah,Allah yayi musu Albarka"

Alhaji Mudan yace"Amin Alhaji,yauwa yanzu nake gani a labarai ansa ranar auren Jawad,shiyasa na kira da wuri in sanar dakai cewa na dauki nauyin esin d'akin dinner,da kujerun zama, tareda kyautar da za'a rabawa jama'ah"

Alhaji Mekudi yace"Alhaji Mudan ayi haka? meyasa kuke so kumin komai ne? d'azu-d'azu Alhaji Hadi yamin waya yace kada asaiwa Amarya komai na lefe kawai afada masa size dinta zai aiko komai daga Dubai,ga Alhaji Auwal yace kada nasa hannu na akan bikin nabar masa komai a hannunsa zai shigo jibi,kaima kuma yanzu kafadi haka"

Alhaji Mudan yace"Haba Alhaji Mekudi,Jawad ai yaron mu,karka manta kayimin fiye da haka abaya"

Alhaji Mekudi yayi murmushi irin nasu na manya sannan yace"to godia nake Alhaji Mudan,godia nake"

Daga nan yakashe wayar,ya kalli Hajiya Zaliha yace"sai yanzu ne nake tunanin gara da bamu fadi bikin Jawad na farko ba,domin kuwa Alhaji Bature da ba qaramin kunyatani zaiyi ba a'idon mutanan nan"

Mummy tayi ajiyar zuciya sannan tace"Alhaji,nikaina yanzu hankali na yafi kwanciya akan Inaas din,bansan me Yaya Bature yayimin harya yaudareni na dinga tura masa wannan kud'ad'en ba"
Ta qarasa maganar cikeda hawaye,tana nadamar abinda ta aikata.

Alhaji Mekudi yace"Haba Hajiya Zaliha,meyasa kike haka ne? komai fa yariga yawuce,kigodewa Allah tunda Jawad din baisan komai ba,yanzu shima Baturen ba gashi nan kudin sun qone ba? ai matsalar haram kenan,gashi shikuma Jawad din yanata Samun cigaba kina ji de yanda mutane suke tururuwar yimasa komai na hidimar bikin,dan Allah kidena kukan nan"

Ya qarasa maganar yana janta jikinsa yana lallashin ta,Hajiya Zaliha tayi shiru tasake yin luf a qirjinsa(🙊🙈)

Washegari Bilkisu tana zaune afalon Mummy dawata qawar Mummy din da tazo domin jin yanda zasuyi tsare-tsaren biki.
Hajiya Zaliha tace"yanzu de tunda bamuda isasshen lokacin,kamata yayi afara yiwa Amarya gyaran jiki kona kwana goma ne,da ina tunanin aturo mana me gyaran jiki daga Sudan,tazo ta dinga yimata har zuwa lokacin bikin"

Bilkisu tace"Hajiya dakin bar maganar gyaran jikin nan,hakan ma ai qalau take,me za'a gyara?"

Mummy tace"a a Bilkisu,yarona zanyi wa komai,bazai iyu mubarta haka kamar marar gata ba"

Hajiya Zainab tayi ajiyar zuciya tace"ni kuma inaga da anbar maganar ta Sudan dinnan,tunda suma yanzu qasar tasu zaman lafiya yayi qaranci,ya kamata abawa mutanan mu na'nan qasar dama,suma suzo ayi tafiyar nan dasu,gasunan munada masu gyaran jiki dayawa muma, a dauko me gyaran jiki daga maiduguri,adauko wata daga katsina,adauko wata daga Sokoto,su hadu su baje kolin basirarsu akan Amaryar mu,bana mantawa akwai wata me gyaran jiki da aka ta6a daukowa ta yiwa wata yarinyar Deputy govnor gyaran jiki wallahi Hajiya Zaliha bakiga yanda jikin Amarya yakoma ba,kamar ka ta6a jikinta jini yafuto,jikin yarinya yayi luwai-luwai duk inda Amarya ta gifta qamshi ne yake tashi awajan,maganar maganin mata kuwa ba magana,suna dashi ingantacce mai kyau,saboda haka itama Inaas din su za'a dauko suzo har gida su mata,alokacin nikaina saida nasai magungunan mata a wajansu,kuma na gwada sunada kyau sosai,kinga suna had'in amare kala-kala akwai (Gumbar Mallaka) ,yarinya zata mallake shi babu me shigowa sai ita kadai,haka sai abinda takeso zaiyi,akwai wata Gumba Sunanta (karya gado) ,a daren farko ango saiya karya gado,saboda yanda gumbar take, akwai (a Ciji kunne), inba sa'a akaci ba ango a daren farko saiya gama cije yarinya saboda dadi,sunada hadin
(Bita makewayi),ko toilet tashiga,yana nan biye da'ita,bazai bari tayi nesa dashi ba.
sannan akwai hadin (Bita Zai-Zai),tome zamu nema kuma awata qasa daban?"

Bilkisu tayi ajiyar zuciya ta jinjina kanta bayan tagama jin bala'in da ake shirin d'urawa 'yarta,ta kallesu tace"Hajiya Zainab karfa garin neman gira arasa ido,yarinyar nan budurwa ce,idan ya kashe min ita ince mene? Ina ganin babu buqatar wad'annan magungunan,abar batun wani Bita zai-zai wallahi yanzu ma duk inda tayi binta yake"(😂)

(jama'ah kunga laifin Ammiy? 🤔🤔😂)

Mutara zuwa yammah🙏🏻

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Amnah El Yaqoub✍🏻

[1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,idan kika karanta baki biyaba keda Allah saboda ban yafe ba.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

_____

Hajiya Zainab tayi murmushi tace"mutunci zamu kankaro mata,Bilkisu saifa kinyi haquri anbawa yarinyar nan magungunan nan,saboda shima Jawad ya d'in ya more gajiyarsa"

Hajiya Zaliha tayi murmushi tace"Hajiya Zainab,magungunan sunyi yawa gaskiya,babu batun wata mallaka,da kai da kaya duk mallakar wuya ne,da yarinyar da yaron dukansu namu,ade bata wanda ya kamata kawai,inkin duba shima fa Jawad din ya dade baiyi aure ba,bana tunanin zaiyi mata da sauqi,aji tausayin yarinya arage magani"

Hajiya Zainab tayi ajiyar zuciya tace"naji wannan,toya maganar kayan lefe"

Hajiya Zaliha tace"mungama da wannan Fannin,Abokin Alhaji zai turo su daga Dubai,amma nima anan zan qara abunda nake ganin yakamata a qara"

Hajiya Zainab tace"to ba damuwa,sai muyi maganar kayan da Amarya zatayi amfani dasu,kuma mu bincika muga wacce me makeup ya kamata mu dauko"

Sai alokacin Bilkisu tasaki wata irin ajiyar zuciya,dataji cewa za'a rage wannan kayan matan daza'a bawa Inaas,tana kuma yiwa Inaas din Fata Allah yasa Jawad din bai dauko jarabar Ubansa ba.(🤭)

****

Lokacin daya sauka a Cairo,ko minti ashirin baiyi da sauka ba,Na'im yakirashi,P.a ya meqo masa waya,ya kar6a yace"Na'im"

Na'im yace"Na'am late commer,yanzu nake gani a social media"(😂)

Jawad yayi murmushi yace"tanan ka 6ullo?"

"Emana,J. yanzu kasan cewa kana son yarinyar nan amma shine kabarni naje na kar6i number ta? da mun dedeta kanmu Yaya kenan?"

Jawad ya d'an motsa lips dinsa kad'an sannan yace"ai ban baku damar daidaita wa ba,what next?"

Murmushi Na'im yayi yace"dan kasuwa da soyaiya"

Jawad ya lumshe idonsa yabude sannan yace" Na'im,what next,if you don't have anything to say,I will...."

Kafin Jawad yagama magana Na'im yayi dariya yace"Allah ya shirye ka J,yanzu yaushe zaka dawo mufara shirye-shirye?"

Jawad yace"Na'im kana nan meyasa zan dawo da wuri? kuyi komai tareda Fu'ad kawai"

Na'im yace"ok bye"

Daga nan yakashe wayar yabawa P.a

Washegari aka saiwa masu gyaran jiki tickets, suka nufo garin Abuja,daki na musanman Mummy ta ware musu,aranar basu fara yiwa Inaas aikin komai ba,sai washegari da safe suka fara,dukansu sun samu hadin kai,kowa takawo fasaharta sun hada sun tashi abu mai kyau guda daya,Inaas de binsu take da kallo kawai,tana mamaki dama a Nigeria ma idan za'a yi biki sai anyi wadannan abubuwan?.

Da daddare misali shabiyu na dare yakira wayarta,saida yayi mata 3 missed call sannan ta dauka cikeda muryarta me bacci.

Daga nasa 6angaren wata irin wawiyar ajiyar zuciya yasaki yace"harkin kwanta bacci?"

Sai alokacin tabude idonta ta kalli fuskar wayar taga number qasar waje,sannan ta maida kanta kan fillo tace"na kwanta Yaya,ya gajiya ya hanya?"

"babu gajiya,na nemeta na rasa tunda naji muryarki"

Inaas tayi murmushi tana jinjina kanta cikin mamaki,yanda yake maganar kamar ba shiba,cikin jin dadi tace"banason sharri Yaya,tayaya daga jin voice dina zakaji babu gajiya?"

Jawad yasake shigewa cikin blanket dinsa mai laushi yace"serious fa,ina Mama?"

"Ammiy bata nan taje dakin Abba"

"ok,kenan saike kadai kenan?"

Inaas tace"um"

Yayi murmushi yace"Meyasa bazaki kirani inzo in tayaki bacci ba?"
Chapter 49 · 0% Book details