← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 63

Sashe 58

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jawad ya lumshe idonsa yabude yasaki ajiyar zuciya yace"meyake damunki ne Love? why all this? mekike fada haka?"

Cikin masifa ta juyo ta kalleshi tace"karka nunamin bakasan komai ba,ina ganinka kana qarewa jikinta kallo"

Cikin sauri ya qaraso wajanta yariqe hannayen ta yace"bahaka bane,tata6a turomin photo naga alokacin awaje suke,kuma yanzu ma naga ko kunyar su Daddy batayi shima tasake barinsu awaje"

Cikin 6acin rai tace"ohh shine kake qare musu kallo? ashe kasaba gani bansani ba,har turoma photo take"

Taqwace hannunta taci gaba da saka kayanta cikin jaka.

Jawad yace"sau daya nefa,kuma tun da dadewa tun kafin ku dawo nan,sannan ni dazu ban kalli abunta ba"

Tana saka kayanta ajaka tace"ka kalla mana,idan baka ganiba tayaya zaka San cewa a photo tana budewa a zahiri ma tana budewa,kaga kuwa ai kana gani"

Jawad ya rungume ta tabaya yadora kansa akan wuyanta,yayinda hannunsa yake kan qaton cikinta yana shafawa,cikin muryar lallashi yace"kinga....,nagani ko ban gani babu abinda zanyi da wancen yarinyar,bata gabana daga ita har mahaifinta,na d'aga musu qafa ne saboda shi d'in Yaya ne awajan Mummy amma da sojoji zansa suyi musu dukan tsiya"

Ya janye hannunsa daga kan cikinta ya dorashi akan nashanunta yana musu wata irin murza wacce yasan cewa tanaso,sannan yafara kissing wuyanta cikin wani irin salo yace"Love bayan ganaki kullum kina bani ina abinda nakeso dashi mezan yi dana wata? uhm...?"

Yafadi hakan yana sake aika mata dawani irin saqo,Inaas ta lumshe idonta cikin shagwa6a tace"to meyasa zaka kalleta...nide karabu dani"

Shima idonsa a lumshe yace"ni ban kalleta ba,please kiyi haquri,komai yariga yawuce,ni bazan aure ta ba"

Tabude baki zata masa magana yayi sauri ya sanya bakinsa cikin nata,daga nan nan mitar taqare,tanajin yanda yake sarrafa mata nashanunta cikin salon qwarewa,kafin daga qarshe ya futo dasu yafara sha ahankali,Inaas ta rungume kansa tana sosa masa cikin sumar kansa idonta a lumshe tanajin wani irin dadi.

Ganin al'amarin nasa yana sake gaba,hakan yasa tafara qoqarin tureshi,cikin wata irin murya yace"haquri zan baki fa....,please ki barni mana"

Inaas tace"Qauna ka manta inda muke ne? idan Abbana da Uncle suka dawo fa?"

Cikin damuwa yace"basa nanfa,sun san cewa ina nan,bazasu zoba, nide ki barni nabaki haquri kinji...? dan Allah kinji Love?"

Yafadi haka wani irin hawayen fitina yana sakkowa daga cikin idonsa.
Hakan data gani yasa tarabu dashi,suka Haye kan gadon daga nan komai ya sauya Salo.

Kusan awa biyu da futowar Jawad daga falon,iyayen nasu sukaci abinci acan falon Mummy,daga nan suka fice saboda ankusa fara kiran sallar magrib,hakan yasa Bilkisu ma tataho saboda tayi haramar sallah.
Tana sako qafarta falo taji kamar ana doke-doke,gabanta yafad'i taji tsoro kode Jawad biyewa Inaas yayi suke fada harda doke-doke? saboda taga futowar ta daga falon ranta a6ace,kuma tasan cewa shima Jawad din daya futo wajanta zaizo,cikin tashin hankali ta qarasa kusa da d'akin datake jin doke-doken,tasa hannu zata kama handle din d'akin adede lokacin gabanta yayi wata irin fad'uwa sakamakon muryar Jawad data jiyo yana kuka cikin fitar hayyaci yana fadin"kiyi haquri...kin haqura ko?, Wayyo Allah love dadi zai kasheni,kiyi haquri bazan sake ba....,Allah nadena kallon kowacce mace kinji....,Wayyoooo"

Yafadi Wayyo din yana dukan katifa.

Ammiy ta zaro ido tasaki handle da sauri ta matsa tabar wajan,bata shiga dakinta dayake kusa dasu ba,kai tsaye tawuce d'akin Man Sulaiman tashige toilet dinsa tafara haramar alwala.

Har aka idar da sallar isha'i tana cikin dakin bata futo ba,tana zaune tana tasbihi Man Sulaiman yashigo dakin yafara qoqarin cire babbar rigar jikinsa yana fadin"gaskiya iyayen yaran nan nan sunyi mana karamci sosai,bamu bar gidansu bafa saida aka saka rana nan da wata d'aya,abun yamana dadi sosai"

Bilkisu tace"Allah yasanya Alkhairi,ai bayan kun fita Hajiya take cewa zuwan Alhaji Bature yasa ko tambayar ku yanayin tafiyar bamu yi ba"

Man Sulaiman yace"to ya za'ai,sha'anin mutane sai haquri,yau anan kike zaune kenan? dana shigo banganki a falo ba nayi tunanin har yanzu kina can wajan Hajiya"

Bilkisu tace"A a ina nan,nabarwa yarana falon"

Man Sulaiman ya kalleta yace"kamarya? babu kowa afalon fa"

Ajiyar zuciya tayi tace"Alhaji yaron nan kuwa anya bazan zauna dashi nayi magana dashi ba? yarinya da tsohon ciki amma ace babu haquri acikin lamarin sa? wallahi nayi tunanin fada suke da doke doke,gaba daya baisan meyake fada ba,kuma wannan abun arasa inda za'a yi sai nan?"

Man Sulaiman yayi murmushi bayan yagano manufarta, yace"karki fara yimasa magana,kibar yarona yahuta,nan da can 6angaren Hajiyan duk d'aya,kibarshi yaci gaba da aiki babu batun d'aga qafa tunda hakan ba matsala yake kawowa yarinyar ba"

Bilkisu tace"amma mahaifin yarinyar nanfa yana nan,idan mu kadai ne dasauqi"

Man Sulaiman ya jinjina kansa sannan yace"eh kuma hakane,to amma nasan cewa shima Jawad din ba zaiyi abinda zai shafeshi shida Farouq din ba,sannan tare mukai sallar isha'i da Jawad din fa,magrib cede bamuyi dashi na, amma tare mukai sallah yanzu,kidena tunanin komai,nasan zasu dinga qoqarin 6oye sirrin su"

Bilkisu tayi ajiyar zuciya tace"to shikkenan,Allah yasa".

Tunda wannan d'an sabanin yafaru a tsakanin su basu sake samun wani sabanin ba,koda yaushe Jawad yana qoqarin ganin ya faranta mata,haka itama, 6angaren auratayya sun riga sun tsara abun su da daddare zata taho ta hanyar baya zai tarota su tafi dakinsa,su kwana suna abunda suke so,lokacin kiran sallar farko zai rakota tadawo ta kwanta,dasafe taita rama baccin gajiya,saida cikinta yacika wata takwas,sannan Daddy yayiwa Jawad maganar kowama aiki,saide Jawad din yayi masa bayani akan yanaso Inaas ta haihu yana gida,shiyasa ma yabar P.a dinsa acan saboda yaci gaba da kula da komai,duk abinda yake faruwa suna magana,kada yadawo sai lokacin bikin sa, shikuma zai zauna yaci gaba da kula da komai na nan Africa.

Hakan yasa Daddy ya haqura da batun tafiyar sa,saide ahakan ma baya zama,duk qasashen dasuke Africa wanda yake da huldar kasuwanci dasu kullum yana can yana ganin yanda abubuwa suke gudana,sau daya yaje Niger inda yaqara wa Ilyasu Manager babban muqami,hakan ba qaramin dadi yayiwa ilyasu ba,cikin ransa yaji dadin daukar Inaas aiki saboda yasan komai ta dalilin ta yasamu.

Bayan sati d'aya Jawad yana zaune a compound din gidan yana vedio call a Computer shida P.a ga wasu takardu dayawa agabansa da alama aiki zaiyi, daga can gefensa wasu guards ne a tsaye,suna zare ido.

Inaas ta qaraso wajansa jikinta sanye da dogon hijab ta ajiye masa lemo sannan ta zauna tana duba takardun tana jira yagama magana.

Lemon data kawo masa yadauka yasha,sannan ya sallami P.a ya kalli qaton cikin Inaas,idan lissafin su yazama gaskiya saura sati uku ta sauka,yayi mata Addu'ah acikin ransa sannan yace"madam"

Inaas tayi masa hararar wasa sannan tace"yau kuma?"

Murmushi yayi yadaga kafadarsa yace"har gobe,karki hargitsa min takardu na"

Dan qaramin bakinta taturo gaba cikin shagwa6a tace"nasanfa aikin,ko inci gaba kagani?"

Cikin rashin damuwa yayi qasa da muryarsa yace"why not? idan kika kasa kuma kika maida min aiki baya saina fanshe da daddare"

Wani kallon soyaiya tayi masa sannan taja computer gabanta tafara aikin,mamaki ya kama Jawad ya kalli computer sannan ya kalleta yace"waye ya koya miki? Idan inayi la6ewa kike yi kina kallo na ko?"

Cikin murmushi tace"satar amsa ma kenan,babu wanda ya koyamin,lokacin daka qaramin matsayi a wannan kamfanin na Niger,Manager yafara koyamin"

Lokaci d'aya ransa ya6aci yace"kamarya ya koya miki? Meyasa bazai sa wata mace ta koya miki ba?"

Cikin sauri tayi kwana tace"Bafa ni kadai bace Qauna, mu uku ne duka mata,kuma ko kallon inda nake ba yayi"

Sai alokacin Jawad yasaki ajiyar zuciya sannan yace"naji,bani aikina karki wahalar min da Baby na"

Inaas tatura masa computer sa sannan tace"Qauna yaufa sati biyu kenan da qarewar hutun mu,an koma second semester"

Cikin nutsuwa yazuba mata ido yana kallonta sannan ya jinjina kansa yace"zanyiwa P.a magana yaje makarantar, saiki dinga karatun anan gida, idan kin haihu lafiya,bayan kin haihu saimu koma,nasan zuwa lokacin ba za'a fara exam ba"

Inaas tasaki ajiyar zuciya sannan tace"i luv you Qauna,banda kamar ka wallahi,Allah yabar min kai ni kadai"

Tafadi hakan tana qoqarin tashi d'aqyar.

Jawad yayi murmushi yace"wato kalaman cin hanci ne wannan ko?"

Itade Inaas batace masa komai ba tawuce ciki.

Acikin wannan satin aka fara shirye shiryen bikin P.a da amaryar sa Fadila,sai kuma Fu'ad da amaryar sa Noor,Inaas taso ayi komai da'ita saide hakan bai samu ba,domin kuwa Jawad kafawa yayi yatsare babu abinda zatayi,duk yan biki dasukazo kowa yanayi mata Addu'ah da fatan Alkhairi.

Ranar daurin aure aka hada aka daura dana Farouq Abban Inaas,da Amarya sa Surayya yarinya 'yar shekara talatin,banda mijinta daya rasu da yanzu itama tana gidan mijinta,to kuma Yaya Mariya tana yiwa Abban Inaas din maganar Surayyan saiya amince,itama Surayya ganin bawani tsufa yayi ba kuma ga kudi ga kyau nan da nan ta amince aka wuce wajan.

Gidan yacika maqil da jama'ah Jawad yazama busy komai shi Daddy yake sakawa,Bilkisu ce take kula da 6angaren abincin baqi, babu irin naman da babu saide na mutum,anyi karamci sosai a bikin.
Acan kaduna sukai taron dinner inda yan wasan hausa sukaje suka baje kolin basirar waqoqi,daga nan aka taho da Amare.

Kai tsaye aka wuce da Amaryar P.a hadaddan gidanta, shikuma Fu'ad wani Plat din daban yakoma, haka Shima Abban Inaas shida matarsa.
Fu'ad yaso yakoma wani gidan daban, danyayi amarcinsa yanda yakeso,saide Daddy ya hanashi,acewarsa Jawad ma bai barshi yafita daga family house ba,hakan yasa Fu'ad yayi zamansa.

Cikin kwanciyar hankali aka gama biki lafiya,Surayya matar Abban Inaas tunda taga Inaas din taji tana qaunar yarinyar,lokaci daya taja Inaas din ajikinta suka hade kansu.

Satin bikinsu daya,Fu'ad yadauki matarsa suka tafi Honeymoon.

Washegari dasafe Inaas tanata bacci adaki sai wajan shadaya na safe tatashi sakamakon Yaya Jawad bai barta ta runtsa ba,tayi tunanin zuwa yanzu zai harta,saboda yanayin girman cikinta,to amma saita ga ya sauya style, yanda cikin bazai takura shi ba.

wanka tayi ta shirya,sannan tafuto falo tafara cin abinci.
Bata dade da zamaba Jawad yashigo,Bilkisu ta kalleshi tace"daga ina haka kamar an koroka?"

Jawad ya kwanta akan doguwar kujerar falon sannan yadora kansa akan cinyarta yace"Mama nagaji,wallahi daga kamfani nake tun sassafe nafita,bacci nakeji"

Bilkisu tace"to tayaya zakayi bacci bakaci abinci ba?d'aga min cinya kaje kuci abinci kaida matarka"

Jawad ya yamutsa fuskarsa cikin shagwa6a ya rungumota ta hanyar zagayo da hannunsa ta qugunta yace"Mama idan natashi zanci"
Chapter 58 · 0% Book details