Sashe 57
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.
17&18
Washegari dasafe a wajan Mummy sukai breakfast,Abban ta da Uncle Sulaiman sun fita zasu taho dawani abokin Alhaji tareda shi zasuyi tafiyar zuwa kaduna.
hakan yasa itada Ammiy suka tafi wajan Mummy,bayan Daddy yagama cin abincin sa ya kalli Mummy yace"ina Jawad ne? banganshi a masallaci ba,dana dawo ma banganshi ba,yanzu qarfe takwas,kuma su man Sulaiman suna dawowa zasu wuce,meyake ne haka bai futo ba?"
Mummy tace"jiya da daddare idonsa qyamas yake babu alamun bacci,saida nace yaje ya kwanta sannan yatafi daki,nasan baiyi bacci da wuri ba,shiyasa yake ramuwar bacci"
Daddy ya kalli Inaas datake shan tea yace"jeki taso shi kice yashirya dawuri suna dawowa daga dauko abokina bazasu jira shi ba ko baiyi wanka ba haka zai bisu su tafi"
Bilkisu tayi murmushi,yayinda Inaas tatashi tana tafiya daqyar ta nufi sama dakin Jawad.
Mummy tace"Alhaji ace ko baiyi wanka ba sai tafiya? babu maganar cin abinci?"
Daddy yace"banaso yasa iyayen nasa jirane,inaso kuma yashige gaba ayi komai dashi akan neman auren,musanman saboda P.a dinsa, kinga gara a dinga yin komai dashi, because sune manyan gobe agidan"
Mummy tace"eh hakane kuma,gara a dinga saka su acikin sabgar tun yanzu"
****
Inaas tana shiga ta ganshi a kwance cikin bargo yana matse qafafunsa,cikin sauri ta qarasa gadon tace"Qauna lafiya? meyake damunka? Daddy yace ba kaje sallar asuba ba meyafaru?"
Ahankali yad'ago kansa ya kalleta da Jan idonsa,lokaci daya tagane yanayin da mijinta yake ciki,cikin sauri tace"Subhanallah meyasa bazaka kirani ba?"
Cikin shaqaqqiyar murya yace"bansan ma ina na jefa wayar ba,yau sallar asuba adaki nayi,kinganni fa tayaya zan fita ahaka?"
Yafadi hakan yana yaye mata bargon dayake ciki,gabanta yafad'i saboda yanda taga yanayinsa babu sauqi,ta matsa kusa dashi tayi kissing goshinsa tace"sorry,kuma su Uncle idan suka dawo Daddy yace kaduna zaku tafi"
Jawad yace"bazaniba Love"
Cikin sauri tace"A a sai kaje,bani minti goma kaga"
Tana fadar haka tatashi ta kulle dakin sannan tadawo tacire rigar jikinta,Jawad duk yana kallonta,yana jinta tashige cikin bargon tana yi masa wani irin salo,daga nan al'amari ya sauya,Jawad ya dinga abu daya saida yaji ya d'an samu sassauaci,bai haqura ba daga nan yafara qoqarin sake wani round din,Inaas dataga abinda yake qoqarin sake yi tace"su Uncle fa karsu dawo"
Cikin sauri yace"bazasu zoba yanzu zan gama"
Tana jinsa yayi abinda yakeso,sannan ya qanqameta zai fara sakin ihu tayi sauri ta rufe masa baki,saida suka nutsu,taga yana hawaye,tagoge masa hawayen tace"me yafaru kuma?"
Jawad yayi kissing dinta yace" hawayen farinciki nake bisa ni'imar da Allah yamin ya mallaka min ke,Allah yayi miki Albarka,wallahi naji dad'i sosai"
Inaas tayi murmushi tatashi tace"jekayi wanka Yaya,karsuzo"
Saida yayi wata irin miqa,sannan yatashi yashige toilet.
Itama tashi tayi tagyara jikinta,sannan tamaida kayan ta tagyara gadon tsaf,yana futowa yace"kishiga kiyi wanka saimu fita tare"
Cikin sauri tace"wallahi idan nayi wanka zasu fahimci abinda yafaru,ka shirya ni zan wuce dakin Ammiy inyi wankan"
Cikin sauri ya shirya tana taimaka masa,cikin d'an qanqanin lokaci ya shirya cikin shadda light blue da babbar riga,suka futo,sai tashin qamshi yake,fuskarsa cikeda walwala.
suna saukowa Daddy ya kalli Jawad yayi ajiyar zuciya,yasan cewa duk abinda zai hana Jawad zuwa masallaci ba d'an qarami bane,saboda tun yana yaro baya wasa da lokacin sallah,hakan yasa ya fahimci Jawad din yana buqatar matarsa ne,shiyasa ya tura masa ita,kuma da alama ta warware komai,saide yaji dadin yanda suka 6oye sirrin su babu wata alama dazaka gani daga wajan Inaas din wacce zata nunama yaran sunyi wani abu.
Ko minti daya ba suyi da saukowa falon ba su man Sulaiman suka dawo,hakan yasa Inaas ta zame tabar falon ta gudu toilet din Ammiy zatayi wanka,Daddy dayaga fitar ta yayi murmushi kawai.
Cikin sauri Jawad yaci abinci daga nan suka nufi kaduna state.
Bayan sun tafi Bilkisu tatafi domin tabar Hajiya da Daddy suma su huta, tana shiga daki taga Inaas tafuto daga wanka tana busar da gashin kanta da handrayer,lokaci daya tagano su,ta riga tagama yarda Jawad gadon ubansa yayi,domin kuwa har zuwa yanzun shima uban ba yayiwa Bilkisun ta sauqi,cikin dare idan tatafi dakinsa saisu raba dare yana abu daya kamar ba tsoho ba.
Tayi ajiyar zuciya ta zauna a gadon tana qoqarin kunna kallo bata nunawa Inaas d'in tagane komai ba.
Basu koma wajan Mummy ba sai wajan yamma,farfesun jan nama ne agaban Inaas tanaci ahankali, yayinda Hajiya Zaliha take cewa" Bilkisu ni kayan Babyn nan menene ba'a siyo bane?"
Bilkisu tace"Hajiya duk yawan kayan nan ai bana tunanin akwai abinda bamu siyo ba, bayan taku siyaiyar nima awajena fa akwai wasu kayan"
Mummy tace"duk da haka sai nake ganin bazai hana mu qara wasu ba,kamar sunyi kad'an"
Bilkisu tayi dariya tace"Hajiya yanda kike yiwa yarinyar nan tanadi Allah yasa de kartazo ta qwace miki Alhaji"
Inaas tayi dariya bayan tagama jinsu.
Adede lokacin Alhaji Bature yayi sallama yashigo falon,abayansa wata yarinya ce budurwa tana biye dashi.
Hajiya Zaliha tana ganinsu gabanta yafad'i,domin kuwa ba Alkhairi a ganin Yaya Bature.
Bilkisu tana ganinsa ta sunkuyar da kanta qasa,sarai tagane shi, shine mutumin daya zo ya musu tijara,Inaas ma tana ganinsa tagane shi saboda ranar da yazo yafad'a wa Jawad maganganu suna tare,kawai de macen dasuke tare ne bata ganeta ba.
Hajiya Zaliha tace"Yaya yau kune atafe?, sannunku da zuwa,ku zauna,Amal qaraso ki zauna mana"
Gaban Inaas yayi wata irin fad'uwa,tun ranar da taji sunan Amal ta riqe sunan a kanta,itace da za'a bata Yaya Jawad,lokaci d'aya ta dauke kanta daga wajansu tamaida kan kayan kallo.
Bilkisu tace"sannunku da zuwa"
Tafadi haka tana miqewa,ko sauraren amsarsu batayi ba,bowl din gaban Inaas ta dauka tawuce kitchen taqaro mata wani farfesun,tadawo ta ajiye mata tace"ki cinye shi gaba daya"
Mummy tajuya ta kalleta tace"idan ta cinye ma ai akwai fruit dinta dana had'a mata tun dazu ba tasha ba,sai tasha ko kad'an ne, kada Babyn ta zauna da yunwa"
Bature ya jinjina kansa ganin kotasu basayi gaba daya sun maida hankalinsu akan yarinyar dayake gani da qaton ciki.
Yayinda Amal taji kamar taje ta Shaqe Inaas din kowama yahuta, sai wani nan-nan suke da'ita da yanzu fa ita za'a yiwa wannan Kulawar.
Alhaji Bature yace"zaliha munzo amma kuma baki tambayeni menene yake tafe dani ba"
Mummy ta kalleshi,tace"af Yaya kuyi haquri,kunsan sha'anin me juna biyu dole saida kulawa,menene yake faruwa?"
Alhaji Bature yagyara zamansa zaiyi magana saigasu Jawad sun dawo,tare suka shigo da Daddy fuskarsu cikeda Farinciki da alama sun samu nasarar abinda sukaje nema, mamaki ya bayyana qarara akan fuskokin su,Jawad yabashi hannu suka gaisa kamar babu abinda yata6a hadosu,Fu'ad kuwa sannu yayi musu kawai.
Amal tana ganin Jawad tafara gyare gyaren mayafi har saida Mayafin jikinta ya sauka daga gaban qirjinta,nonuwanta duk suka furfuto tanayi tana satar kallon Jawad.
Inaas da hankalin ta ke kan Amal din tana ganin duk abinda takeyi.
Daddy ya kalli Alhaji Bature yace"Bature meyafaru?"
Alhaji Bature yace"Alhaji Mekudi dama wajanku nazo,saboda maganar gaba dayanku tahada daku,maganar gobara danayi har nazo nan nace zankai kotu, na janye ta, yan'uwa sun min fada sun nunamin ni daku ai duk daya ne,hakan yasa na haqura na janye,yanzu de inaso komai yawuce,ina roqon ku garafa ku yafemin,d'an jarin nan idan da hali atemaka min,Amal kuma dama yarku ce,gatanan na kawo muku ita sai abata Jawad d'in,itama ai qanwar sa ce"
Cikin sauri Jawad yadago kansa ya kalli Uncle Bature sannan ya maida kallonsa wajan Amal,anan yayi tozali da nashanunta,yafara tunani ita bayan budeshi datakeyi acikin photo a zahiri ma haka take ashe?
Inaas ta kalli yanda Jawad din yake kallon Amal,wani irin Kishi ya kamata,ahankali tatashi tsaye sannan ta gyara mayafin rigar jikinta tafice daga falon.
Fu'ad yayi d'an qaramin murmushi ganin madam ta shaqa,yamaida kallonsa wajan Jawad,yaga shima binta yayi da kallo harta fice daga falon.
Daddy yayi dariya yace"to wannan maganar kam aiba tawa bace Bature,duk abubuwa guda biyun daka nema d'aya ne nake tunanin zan'iya yima shine nabaka Jari,Shima saika jirani naduba nagani ko zaka samu,maganar Amal kuma ga Jawad dinnan agabanka"
Bature ya kalli Jawad yayi murmushi yace"yarona Jawad kayi haquri ka manta baya kaji,nasan nayi kuskure amma ina nema daka yafemin, yanzu me kace game da qanwar ka Amal?"
Jawad ya kalleshi cikin kwanciyar hankali yace" Uncle dama ni bance ina sonta ba,zan aure tane saboda Mummy na,yanzu kuma tasake kawomin wata yarinyar gashinan kana gani kasan komai kuma,na aure ta,ina tunanin zatafi rufamin asiri tunda ita jininace"
Bilkisu tasaki ajiyar zuciya tana d'an murmushi ahankali.
Daddy ya kalli Alhaji Bature yace"to kaji,bari inje dakina in duba ma ko zaka samu jarin ko dubu dari ce"
Alhaji Bature ransa baqiqqirin yakalli Amal yace"Ke tashi mutafi,dama saida nace ko munzo bazasu amince ba kika dage sai munzo,Jawad dinnan ko dan gwal ne yakamata ki haqura dashi tunda dama can nine dalilin haduwar ki dashi, yanzu daga ganinsa a TV shida matarsa sun zo shikkenan kikabi kika rikice"
Yajuya ya kalli Daddy yace"Alhaji kabar dubu darinka,idan qari kake buqata zanyi dako na aiko ma dawata dubu darin"
Yana fadin haka ya miqe suka fice daga falon, Amal sai share hawaye take tana dana sanin biyewa mahaifinta datayi a baya saboda kudi harta bari Jawad din ya kubce mata.
Daddy ya girgiza kansa yace"bazai sauya bafa,dan in gwada shi yasa nace masa dubu dari amma ba hakan zan bashi ba,Bature bazai sauya ba"
Abban Inaas yace"Alhaji da anyi haquri inde zai iyun ayi musu auren tunda naga yarinyar kamar tana son shi"
Jawad ya kalleshi da sauri,cikin daure fuska yamiqe yabi bayan matarsa.
Daddy yayi murmushi ya nuna masa Jawad da hannu yace"kaga amsar maganar taka ko?"
Man Sulaiman yayi murmushi yace"Allah yasa mudace"
Hajiya Zaliha tasaki ajiyar zuciya tace"Allah ya shirye shi"
****
Yana shiga falon bai ganta anan ba,hakan yasa yaduba dakin Ammiy nan ma bata ciki,yaduba d'ayan dakin nakusa dana Ammiy yaganta aciki tana gyara kayanta,ya rufe dakin yasaki ajiyar zuciya hannunsa zube cikin aljihun wandon sa.
Dakin yafara qarewa kallo da alama ba'a zama aciki kawai kayan Unborn Babyn sune adakin saikuma wasu daga cikin kayanta.
Ya kalleta yace"aikin mekike haka bayan kinsan cewa likita ta hanaki aiki?"
Batare data kalleshi ba tace"qasarmu zan tafi,tunda nan d'in kasamu wacce zata dinga 'DEBE MA KEWA"