← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 63

Sashe 60

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummy tashigo itada Bilkisu suka ajiye Babyn acikin gadonta kusa dana Inaas,sannan Mummy ta shafa kan Jawad suka fice daga dakin tunda ba'a so a tasheta.
Jawad yatashi tsam yadauko Babyn ya kwantar da'ita ajikin Inaas sannan yasaka hannunsa ya rungume su gaba daya ya lumshe idonsa.
Sai bayan sallar asuba tatashi bayan gari yafara haske,ahankali tabude idonta ta saukeshi akan na Jawad,suka zubawa juna ido kamar zasu cinye kansu,hawaye yazubo daga idonta,Jawad ya matsa yayi kissing goshinta sannan yasake rungume su yace"Allah yayi muku albarka sweet,Allah yabarmu tare har gidan aljanna,kiyi haquri akan abinda yafaru ki rufamin asiri..."
Ya qarasa maganar hawaye yana zubo masa daga idonsa.

Cikin sauri tarufe masa baki,tana girgiza masa kai,yayi qasa da kansa ya dauko Babyn daga tsakiyarsu yace"kinga Babyn mu,kalla kigani tana kama dake,riqe Mamanki kisa mata Albarka"

Cikin sauri Inaas ta kar6i Babyn hawaye yana sake zuba daga fuskarta,taji dadin yanda Jawad yakira Babyn da Maman ta,taji qaunar Babyn tana ratsa ta,yanzu irin wannan wahalar Maman ta tayi akan ta? lokaci daya sabon kuka yazo mata,cikin kuka tabude bakinta tace"Allah yayi mata Albarka,Allah yaji qan Mamana"

Jawad yayi sauri ya goge mata hawaye,sannan yayi caraf yakama lips dinta na qasa yafara tsotsa,ahankali itama takama nashi nasama tanasha,saida ya tabbatar ta daina kukan sannan yazare bakinsa daga nata,yayi kissing Babyn,ya futo daga dakin yana fadawa su Mummy ta farka.

Gaba dayansu suka shigo dakin ciki harda Doctor's din dasuka kar6i haihuwar ta,saida suka dubata suka tabbatar tana lafiya sannan suka fara qoqarin ficewa daga dakin,daya daga cikin Doctor's din ta dauko waya zata dauki photon Babyn,amma qiri-qiri Jawad ya hanata,Man Sulaiman yajasu gefe ya kar6i account number su nan take sukaji alert me nauyi,Daddy ma yayi murmushi yace"idan kun tashi daga aiki kuje gida ku kar6i tawa kyautar"

Cikin farinciki suka fice daga dakin.
Sai wajan qarfe tara nasafe aka sallamesu daga asbitin,'yan Jarida kuwa sunyi cincirundo agaban asbitin Jawad yarasa yanda akai sukaji,hakan yasa yaja Mayafin Mama Bilkisu yasake rufe Baby ruf babu wanda zaice Babyn tana hannunta.

Har suka shiga mota qara da hasken camera ne yake tashi,Inaas de an dauki photon ta,amma babu wanda yaga Baby.

Kafin azahar duniyar yana gizo ta dauka matar Jawad Mekudi ta haihu,photunan uwa da uba sai yawo suke,amma babu Photon Baby,harda masu dubo date din bikin suna cewa wata daya Inaas din ta qara akan na aurensu sannan ta haihu.

Mutane sai kiran Jawad suke suna masa murna banda saqonni da'ake ta turo masa bayan sun samu labarin haihuwar awajan P.a lokacin da yayi posting ashafukan su inda yace ayiwa Babyn Addu'ah.

Babu wanda baya nunawa Inaas gata,tana dakin Mummy anayi mata wankan jego irinna mutanan da,kullum Jawad yana wajan Babyn bashida aiki sai kissing dinta ko kunyar Mummyn bayaji.
Saida ya shawarci Daddy akan sunan da zaisa wa yarinyar,sannan yayi mata hud'uba da JAMILA.

Ranar suna kuwa aka rad'awa yarinyar suna Jamila,za'a dinga kiranta da Beauty a cewar Jawad d'in.

Bilkisu tafi kowa farinciki,saboda har yanzu tana tuno irin zaman dasukai da Jamila.
sassafe P.a yasake yin posting sunan Baby,dakuma sunan da kowa zai dinga kiranta dashi.
Wannan posting na p.a saida wasu mutanan sukayi screenshot dinsa aka dinga dorawa a status ana rubuta comment aqasan screenshot din wannan yace da alama anhaifo balarabiya,wannan yace kaji wani suna wai Beauty to waye ba Beauty ba?
Yayinda wasu suke cewa da alama de yarinyar ba qaramar kyakykywa bace shiyasa iyayenta suka 6oyeta sukaqi nunawa duniya photon Babyn.

Tun safe Jawad yake jin alert yanata shigowa wayarsa wannan yace kudin Baby ne asiya mata chocolate wannan yace kudin keken koyon tafiyar Baby ne,wannan yace kudin pampers din Babyne,sosai yan'uwa da abokan arziqi sukai masa kara akan haihuwar Beauty.

Kayan Baby dana maijego tun su Mummy suna gani har suka gaji dagani,banda kyautar da Inaas tasamu daga wajan Jawad din dakuma mutane,abun har yayi yawa.
Bayan suna da kwana uku Jawad yabar qasar,kullum suna yin video call yana ganin Baby da Maman baby,Mummy tana jinsu saide ta to she kunnanta tana mamakin yaran zamani,wannan Jawad kenan shida baya magana baya shiga wasu sabgogin to idan Fu'ad ne Yaya za'a yi kenan?(🤔)

Wannan karon Bilkisu ce da kanta ta zage take gyaran 'Yarta,gyara take mata na haqiqa irinnasu na Niger,kafin wata daya kuwa sunyi shar dasu itada Baby,sai alokacin su Fu'ad suka dawo,Baby tayi wani sabon uban, domin kuwa Fu'ad ma kullum yana wajan Baby bashida aiki sai de yayi ta yimusu photo, tun yarinya bata tsaida idonta akan camera harta saba.(🤭)
Duk yanda yake daukar yarinyar a photo bai ta6a d'orawa awata kafa da za'a ce ga Babyn Jawad ba,saboda lokacin haihuwar duk yana ganin surutun da'ake tayi a yanar gizo akan rashin posting photon yarinyar.

Bayan sunyi arba'in Jawad yadawo,suka shirya gaba dayansu gidan suka hau jirgi iyasu yasu family suka tafi jigawa.
Acikin jirgin ma saida aka daukeshi photo kowa yana ganinsu yasan suna cikin kwanciyar hankali,Inaas kamar ba haihuwa tayi ba,duk wanda yaga wannan photo saiya fara dubawa ina zaiga Beauty? amma shiru kokadan babu alamar ta,hakan yasa wasu suke cewa to da alama de yarinyar wani ciwon ne da'ita shiyasa ba'a son nunawa duniya(😂)

A dutse suka fara sauka,sannan suka shiga motoci suka nufi Hadeja,ta Gujungu sukabi,suka wuce qayyuka dayawa su marke,yalo,kwanar Auyo, suka shiga cikin Hadejia sannan suka dauki hanyar garin Galadima,suka wuce garin Galadima suka qaraso cikin Garin Malam.
Ba qaramin tarba suka samu ba daga wajan mutanan gari,Bilkisu dake gefen Jawad tayi qasa da murya tace"Muhammad ga asalin garinku"

Jawad yayi murmushi yanajin qaunar garin acikin zuciyarsa,kwanan su d'aya agarin,amma saida Jawad yayi qoqarin yin wani abu amatsayin sa na d'an garin,yabada aiki aqara musu famfon ruwa,titi babu kwalbati nanma yabada aikinsa,aka janyo musu sabuwar kwalta,sannan ya kar6i takardun samari masu n.c.e dakuma degree domin taimaka musu wajan daukarsu aiki.

Wannan abubuwan da Jawad yabari ayi,ba qaramin cece-kuce ya janyo ba tsakanin Garin Galadima dakuma garin su Jawad din wato Garin Malam,suma yan Garin Galadima suna gani ai yaci ace suma anyi musu hakan suci albarkacin maqotaka,tunda sai an fara wucewa ta garin su, sannan a shiga Garin Malam din,su kuwa yan Garin Malam har wani buda hanci suke su ala dole Jawad d'in d'an garin su ne.

Saida suka sake kwana acikin masarautar Hadejia sannan Washegari suka koma Abuja cikeda KEWAR karamcin dasuka samu daga Masarautar Hadejia.

*** *** ***

Bayan shekara uku.

'Dakin taron yacika sosai da jama'ah,na gida dana qasar waje,iyaye da yan'uwa da abokan arziqi,Na'im yana zaune shida matarsa agefe wadda take d'aukeda d'an qaramin ciki,Bilkisu tasake yin qiba hutu yasake zama da kuma jin dadi,Man Sulaiman yana gefenta sunyi shar dasu babu alamun tsufa atare dasu, Yayinda Mummy da Daddy ma suke zaune agefe d'aya fuskar kowa da farinciki,Abban Inaas yana Sanye cikin Suit yasake yin kyau kamar Balarabe,suna zaune hannunsa yana cikin na Surayya, Fu'ad da Noor ma suna zaune sunyi bala'in kyau da Baby boy dinsu me kamada Noor sak d'an shekara biyu.

Kowa ya matsu afara taron hakan yasa Daddy yafara dube-dube yanaso yaga a'ina Jawad ya la6e ne kowa yanata faman jiransa?
Tawagar mutanan daya hango sun shigo hall din dakuma yanda yan Jarida suketa faman daukarsa photo kamar shugaban qasa ne yashigo hakan ne yadauki hankalin jama'ah.
Jawad ne yashigo cikin hall din yayi bala'in kyau cikin manyan kaya farare tas,Inaas tana gefen sa tasa farar laffaya me adon stone hannunta na hagu tana riqe da Babbar wayarta dawata hand bag me mutuqar kyau.
Yayinda hannunta na dama take riqeda da hannun Beauty na hagu,shima Jawad ya riqe hannun Beauty na dama,ahankali suke tafiya saboda tafiyar Beauty tafiyar yara ce,daga Jawad har Inaas hankalinsu yana kan Babyn su fuskarsu cikeda Farinciki.

Wannan shine karon farko dasuka nunawa duniya fuskar 'yarsu,saboda tsabar son labari irinna d'an jarida lokaci daya suka tsugunna dede tsowon yarinyar suka dinga yimata photo sai qaran camera wajan yake,yarinyar bata sababa,hakan yasa ta qamqame Inaas cikin tsoro,yarinyar tayi mutuqar kyau sosai cikin doguwar riga fara me adon net,net din rigar yabaje daga qasa,rigar batada hannu,sai dogon gashinta da akayi mata parking dinsa,anyi mata kwalliya harda janbaki pink,ba qaramin kyau tayi ba,sai yanzu ne mutane dayawa suka sake sanin dalilin da yasa Jawad yake 6oye yarsa,kuma sai yanzu ne sukasan cewa ashe ga dalilin dayasa yace za'a dinga kiranta da Beauty,haqiqa yarinya taci Sunanta.

Ganin yanda ake cincirundon daukar Beauty a photo yaqi qarewa hakan yasa wani guard din Jawad din ya dauketa,yakaita wajan Fu'ad,Beauty tana ganin Young Mekudi wato takwaran Daddy yaron Fu'ad sai hankalin ta ya kwanta bata sake bi takan nata iyayen ba,daga nan kuma photo yadawo wajansu Fu'ad,saida suka gaji suka daina dan kansu.

Bayan bude taro da Addu'ah Jawad yayi wa mutanan dasuka samu damar halartar wannan taro wanda dubban ma'aikatan sa suka shirya masa domin tayashi murna, kasancewar cikin wannan watan yasamu shiga jerin cikin sunayen mutum goma na masu kudin duniya.

Yayi godia,yayi godia bisa wannan taro sannan yaqara da yiwa gomnatin Nigeria godiya bisa hadin kai dayake samu daga wajanta,yakuma yiwa gomnati alqawarin zai sauke farashin wasu kayan masarufi domin talakawan Nigeria,tareda daukan matasa aiki domin a ragewa gomnati wani nauyin.
Daga qarshe yadauki duk wasu kula da harkokin kasuwancin sa na Africa ya damqashi a hannun qaninsa Fu'ad,daga rana irinta yau,Fu'ad shine yake da haqqin komai da komai na Africa,shine zaici gaba da kula musu da wannan 6angaren,shikuma Jawad zaiji da kasuwancin su na sauran qasashen duniya,wannan hukunci da Jawad ya yanke ba qaramin dadi yayiwa iyayensa ba,lokaci daya hall yadauki tafi.

Fu'ad yatashi ya rungume Yayan nasa,yan Jarida suka samu nayi,sai daukarsu ake a photo.

Daga nan suka dawo suka zauna akaci gaba da taro har aka gama taro lafiya.
Bayan sun dawo gida suna zaune suna kallon labarai babu abinda ake nunawa sai photon Beauty,dayawa daga gidan TV da Radio maganar da ake kenan,mutane dayawa suna ganin matakin da Jawad din ya dauka na 6oye yarsa hakan shine daidai.
Inaas ta sanya kayan bacci takawo wa Jawad coffee tace"yalla6ai gashi"

Jawad ya kalleta dawani irin murmushi me salo daban daban yace"anjima zaki min bayanin dalilin dayasa kika fadi sunan nan"
Chapter 60 · 0% Book details