← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 63

Sashe 62

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin jin dadi ya rungume ta,daga nan suka sauko qasa,abinci suka fara ci, yayinda Mummy take bawa Jawad abaki.

Adede lokacin su Bilkisu suka shigo,Beauty tatafi da gudu wajan Jawad tace"Dad ka warke ko?"

Jawad ya shafa fuskar Beauty sannan yace"sosai Babyna"

Yadauketa ya d'orata akan cinyarsa.

Bayan sungama cin abinci Inaas ta kalli Ammiy da Mummy tace"nafasa yin hutu Ammiy,zamu koma yanzu"

Bilkisu tace"yanzu-yanzu? ko sati biyu fa bakuyi ba"

Jawad yace"wallahi Mama anyi min kiran gaggawa ne,inada meeting anjima"

Mummy tace"to Allah dai yatsare,Allah yakare mana ku"

Atare suka amsa da "Amin"

Jawad yayi gaba yana kiran wayar Fu'ad,cikin sauri Inaas ta shirya Beauty suka futo gaba dayansu harda Noor matar Fu'ad dakuma Abban ta da Anty Surayya,Daddy yana tareda Jawad agaban motar,yayinda Inaas take gefen Bilkisu,saida taga babu kowa akusa dasu sannan tace"Ammiy akwai matsala idan mun sauka zan kiraki"

Bilkisu ta riqe hannunta tace"fadamin meyake faruwa?"

Inaas ta qaqaro murmushin dole tace"Ammiy bawani abu bane babba,ki kwantar da hankalin ki,zan kiraka idan munje"

Bilkisu tasaki ajiyar zuciya sannan tace"dazaran kun sauka ki kirani"

Inaas tace"to Ammiy"
Daga nan ta rungume ta,taqarasa wajan su Mummy ta rungume Mummy da Noor da Anty Surayya,sannan ta yiwa iyayen nata maza sallama tashige mota,Shima Jawad saida ya qaraso ya rungume Mummy,sannan ya qarasa wajan Bilkisu itama ya rungume ta tsam ajikinsa tareda lumshe idonsa yace"Mama ki mana Addu'ah,wannan lokacin ba zamu dawo da wuri ba,zamu dade sosai"

Bilkisu ta shafa bayansa tace"adduah kullum ina cikin yimuku ita kaida qanwar ka Muhammad,ka dinga haquri da'ita kaji? Inaas yarinya ce,Allah ne yabata haihuwa da girman jiki dawuri,kaja qanwar ka a jikinka karnaji wata magana"

Jawad yasaki wata irin ajiyar zuciya sannan yace"insha Allah Mama,sannan idan kina buqatar wani abu kimin waya"

Daga nan yasaketa yashige mota suka tafi,babu wanda yabar wajan saida sukaga ficewar motarsu daga gidan tukunna.

Suna sauka a Malessia yawuce wajan meeting,sun dauki lokaci sosai suna meeting sannan yadawo gida agajiye,kwanan su daya Washegari suka koma Qatar.
Saida tasake gyara gidanta tsaf,tashirya shi yatafi wajan aiki,sannan tasamu nutsuwa ta zauna ita kadai bayan tahada Beauty da kayan wasa, takira Bilkisu.

Cikin sauri Bilkisu ta dauka tace"Inaas kin sa nakasa nutsuwa,fad'amin menene yafaru? banason jin matsala a tsakanin ku kokadan"

Inaas tasaki ajiyar zuciya ta lumshe idonta sannan tace"Ammiy Yaya ne"

Cikin sauri Bilkisu tace"me Yayan naki yayi? Fad'amin"

Inaas tace"Ammiy mun samu sa6ani ne dashi tun muna gida,shine yake cemin zai iya qara aure,hankali na yatashi Ammiy,ina tsoro karya fara kula wata"

Bilkisu ta lumshe idonta tasaki ajiyar zuciya bayan taji kanun zancen sannan tace"Inaas,duk irin son da namiji yake miki karki sake kisa aranki cewa bazai qara aure ba,soyaiyar da Babansa ya nunamin ban ta6a tunanin cewa zai iya tafiya yabarni ba,saboda haka ki nutsu,ki iya takunki,idan ma auren zaiyi ai duk wacce ta'iya allonta saita wanke,fadamin menene yasa yafada miki hakan? yace miki yafara neman auren ne?"

Cikin sauri Inaas ta goge hawayen idonta sannan tace"A a Ammiy,Beauty ce bata bacci da wuri,idan yazo wajena yarinyar bata barinsa,saida mukai haka dashi lokuta da dama,har mukazo gida hakance take ta faruwa har yazo yana yiwa yarinyar fad'a,kuma bai ta6a yimata fad'a ba,shine nayi masa magana akan fad'an dayayi mata,shine yace min shiya gaji,yanada iyali kamar bashida su,ya dinga fada shine yace garama yaje yanemi aure kawai"
Taqarasa maganar tana sake fashewa da kuka harda shashsheka.

Bilkisu tayi shiru tana jinta,saida tabarta ta danyi kukan,nauyin zuciyar ta yaragu,sannan tasaki ajiyar zuciya tace"Kukan ya'isa haka,yanzu ina Jamilan take?"

Inaas ta share hawayen idonta tace"tana falo na kunna mata kallo, nabata kayan wasa"

Bilkisu tace"to ai wannan matsalar da kin fad'amin ita da tun tuni kin kawar da'ita da kanki Inaas,meyasa kuke kwana tare da'ita? shekara uku yakamata kidena kwanciya da'ita,sannan tanada bala'in wayo ga surutu,duk wani abu dazakuyi kidinga taka tsantsan da yarinyar karta ga wata alama"

Inaas tace"Ammiy tun kafin takai haka nace masa zata dinga kwanciya ita kadai shine yacemin tayi qanqanta mu barta ita kadai,wai bazan bar masa Babynsa ita kadai ba rashin tausayi ne"

Bilkisu tace"to dole yanzu ki barta ita kadai,inda baku fara fuskantar wannan matsalar ba toda sauqi,yarinyar nan da wayon ta,da surutun ta,an dade da yayeta sannan wayon ta zaisa wasu suce tafi shekara uku,idan baku dena kwana da'ita ba to duk abinda taji, kota gani kunayi kusa aranku zata fadawa wasu,saboda haka ki lalla6ashi ki nuna masa illar kwanciya tareda ita"

Inaas tasaki ajiyar zuciya me nauyi sannan tace"to Ammiy,kuma batasan yin bacci da wuri ma"

Bilkisu tace"seta mata komai zakiyi Inaas,tun yanzu ya kamata kidinga tsara mata lokacin bacci dana tashi,tana yin baccin rana ne?"

Inaas tace"eh tana dawowa daga school nake sata tayi bacci saboda qwaqwalwar ta tahuta"

Cikin sauri Bilkisu tace"toki dena, karki sake bari tayi baccin rana,sannan duk inda qarfe takwas na dare yake kije kisata ta kwanta kiyi mata Addu'ah,wannan gajiyar datayi da rana shine zaisa nan da nan bacci me nauyi zai dauketa,ki gwada wannan shawarwarin,idan sunyi shikkenan,idan ba'a dace ba saiki sake kirana"

Inaas tasaki ajiyar zuciya tace"to Ammiy insha Allah zanyi tun daga yau ma"

Bilkisu tayi murmushi tace"yawwa,kuma adena tsoron kishiya,koya sake yimiki zancen ki danne kishi ki nuna masa kinaso yayi auren,kuma duk lokacin daya zo miki da buqata ki nuna masa aike kinma fishi,dayake miki mita yana cewa mutum yanada iyali kamar bashi dasu saiki nuna masa cewa kema ai hakan kika gani,ki nuna masa ko de bayarda Beuaty din zakuyi tadawo Nigeria danki dinga sauraren sa? Idan kika nuna masa kin fishi shiga damuwa akan komai to jikinsa zaiyi sanyi,ki tabbatar kinsa ya manta da wannan furucin nasa na batun qarin aure, dole saikin koyi kissa qarfi da yaji kinji abinda nafad'a miki ko?"

Inaas tayi murmushi tace"naji Ammiy,saikin jini"

Bilkisu tace"to Allah yayi muku albarka,Allah yasake had'e min kanku"

Inaas tace"Amin Ammiy"

Sannan ta kashe wayar tayi ciki.

Bilkisu tadafe kanta a fili tace"kaii yaran zamani,wannan yaro ka gado jarabar ubanka qarfi da yaji,haba wannan abu har ina"

Man Sulaiman yana jinta yayi murmushi,baice mata komai ba.

****

Inaas tana komawa falo taga Beauty harta fara bacci,cikin sauri ta qarasa ta tasheta,yarinyar sai shagwa6a take mata amma haka ta hanata wannan bacci,qarshe ma qananun kaya tasaka musu suka futo compound d'in gidan suna wasa,har wajan yamma batabar Beauty tayi bacci ba.
Jawad bai dawo da wuri ba sai dare,kafin yadawo Inaas ta shirya cikin wasu arnan kayan bacci,tasha magungunan ta masu kyau da inganci tana lalla6a Beauty kamar yanda Ammiy tafada mata.

Yana shigowa falon alokacin Beauty har bacci yafara nisa,hakan yasa Inaas ta kalleshi tace"Zan kaita dakinta,acan zata kwana yau"

Jawad daya qura mata ido yana ganin yanda kayan baccin nata yayi mata mutuqar kyau,bai iya yimata musu ba, har takai Beauty daki tadawo falon,itada kanta tabashi abinci, sannan sukaje yayi wanka,tun kafin yasaka kayansa yana daure da towel dauketa cak,ya zauna abakin gado sannan ya d'orata akan cinyarsa,yazura hannunsa cikin rigar baccin ta yayiwa nashanunta wata irin damqa sannan yace"yau mun yaye Beauty ne?"

Inaas tayi masa wani fari da'ido sannan ta saqalo wuyansa da hannayen ta tace"Naga alama Dad dinta bazai yaye taba,nikuma ina cutuwa sosai idan tana nan, mijina bayamin service yanda nakeso"

Wani irin dad'i yakama Jawad,har ya kasa 6oye hakan akan fuskarsa,yayi sama da hannunsa dake cikin rigar ta yakama nipples dinta yana murzawa sannan yace"tunda Mom dinta tafad'i haka shikkenan,bazan shiga haqqin Mom dinta ba,za'a dinga service dinta yanda takeso,Love inaso kibani dama idan kin qare semester dinki ta qarshe,inaso in dauko Junior yaron Fu'ad,zasu dinga tafiya makaranta shida Beauty,inaso in kula da yaron ta yanda zai gajeni nida Daddy,yanda Fu'ad yasaka masa sunan Daddy inaso in tabbatar da wannan sunan,inaso sunan ALIYU MEKU'DI,yasake dawowa akaro na biyu,inaso in yiwa yaron horo irin wanda Daddy yamin,inaso yazama Babban d'an kasuwa fiye da ni da Daddy, amma idan kin bani dama"

Inaas tayi murmushi tace"Qaunah ni duk wannan maganar nariga nagama amin cewa,inaso mutane sudena kiransa da junior, nanda wasu yan shekaru su dinga kiransa da YOUNG MEKU'DI, but.... nide kaji dani yanzu,a hannu nake fa"

Cikin tsantsar jin dadi Jawad yayi mata wani irin kallo,ahankali ya matso da fuskarsa harya had'e fuskokin su,yajefa bakinsa cikin nata,Inaas tana jinsa bata fara maida masa martani ba,saide kuma tana tuno shawarar da Bilkisu ta bata,cikin sauri ta hanashi komai,taci gaba da sarrafa shi cikeda zafin nama,hakan ne yasake tabbatar wa Jawad cewa lalle da gaske take,ashe yana shiga haqqin ta batare daya sani ba,ashe itama abun yana damunta,ashe kwanciyar su tareda Beauty ba qaramin jin dadi yake ragewa kansa ba.
Lokaci d'aya yasaka hannunsa yayaga rigar jikinta,ya qwace bakinsa daga cikin nata yadora shi kan nashanunta,kasancewar sun dade basu sake kamar haka ba, hakan yasa gaba daya suka fita hayyacinsu sai nishi suke suna surutai,da tafiya tayi tafiya sai Jawad yakoma yin ihu sakamakon wani iri dad'i dayaji saboda magungunan data sha.

Sai wajan qarfe uku na dare sannan suka gama round na uku,Inaas ta gaji mutuqar gajiya amma ko kad'an bata nuna masa ba,saima kallonsa da tayi cikin qwarin gwiwa tace"Qauna bade kagaji bako? nide...uhm"
ta qarasa maganar cikin shagwa6a.

Jawad yasake rungume ta yace"Love ashe haka nake shiga haqqin ki bansaniba? kiyafemin kinji?"

Inaas tayi qoqari ta 6oye gazawarta bata bari yagano taba,tasaki wani irin murmushi sannan taja hannunsa ta d'ora akan nashanunta,babu musu Jawad yafara matsawa cikin dad'i sannan ya kalleta yace"Love yau kin fita daban,qarfi da yaji kin goge min hadda,kin shafe min batun qarin aure daga cikin qwaqwalwa da zuciya ta"

Inaas tayi murmushi tace"yaza'ai nayi wasa da kyautar da Allah yamin? Qauna banason gazawata tasa ka qara aure,saide ka qara dan niyyar kanka"

Jawad yasake matsa nashanunta sannan yace"kicire wannan batun aranki Love,6acin raine yasa nafad'a,kin riga kinzama ni,rashi na akusa da mahaifiyata yasa kece kikaci gaba da 'DEBE MATA KEWA,kika zama kamar qawarta,tayaya zan iya kawo wata matar tashiga tsakanin wannan aminan guda biyu?,bazan iya yiwa Love d'ina kishiya ba,because you're so sweet takowanne 6angare,har gida ake kawomin photunan mata amma ke kad'ai nagani a cikinsu,inaso kisani aiki nama bazai bani lokacin kallon mata ba,ke kad'ai kin isheni,wannan abun nede bansan yaushe zai isheni ba...."
Yaqarasa maganar yana shafa qasan mararta.

Inaas tasaki wata irin wawiyar ajiyar zuciya sannan tace" I'm ready ai, muje round na hud'u "
Chapter 62 · 0% Book details