← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 63

Sashe 6

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilkisu ta kalli Jamila dajan idonta tace"ina hayyacina,lafiyata kalau Jami,talauci yasa Sulaimanu yagudu yabarni da tsohon ciki,na haihu kwana tara dasuka wuce,ahanyata ta zuwa nan munhadu da 'yan fashi....."
Tsaf Bilkisu ta zayyane musu abinda yasameta har kukan da yaron yake tayi ahanya har zuwa lokacin data qwace daqyar daga hannun 'yan fashi....
Tun kafin ta qarasa basu labarin Jamila take kuka,shi kansa Farouq saida ya goge qwallar tausayi daga idonsa,cikin jajircewa irinta maza ya dubeta yace"ki kwantar da hankalin ki Yaya,insha Allahu d'anki yana cikin aminci,yanzu babu wani abu dakika riqe amatsayin shaida wanda zamuyi bincike dashi ko Allah zaisa mugane inda yaron yake? "

Cikin sauri Bilkisu ta goge qwallar idonta tazana masa number motar aqasa,batajin ko nanda shekara d'ari ne zata manta number wannan mota, bayan ta rubuta masa ta kalleshi tace"motar baqar kala ce da'ita,katemaka min Farouq"

Farouq ya girgiza kansa yace"kiyi haquri Yaya,insha Allah gobe zanje police station inyi report,za'a ga d'anki da iznin Allah"

Sai alokacin tayi wata irin ajiyar zuciya,sannan Jamila tagoge hawayen idonta tabata shayi tasha.

*** *** ***

Lagos Nigeria

Hajiya Zaliha takama jariri ta rungume sai walwala takeyi bakinta yaqi rufuwa kamar gonar audiga,Yaya Mariya ta kalleta tace"to Zaliha,Kinga de kundad'e kuna neman haihuwa Allah bai kawo ba,yanzu gashi sama taka kin samu yaro,dan Allah Zaliha, kiriqe yaron nan amana, bashida kowa saimu,idan muka riqe shi da gaskiya muma saiki ga Allah yatemakemu ta dalilin sa"

Cikin tsananin farinciki Hajiya Zaliha ta kalli mijinta Aliyu Mekud'i da yayarsa Hajiya Mariya sannan tace"Yaya insha Allahu bazan baku kunya ba,zan riqeshi irin ruqon da mahaifiyarsa zata masa"

Alhaji Mekud'i yayi wata irin ajiyar zuciya,dama Sam baya jin Zaliha, yasan bazai samu matsala da'ita ba kamar yanda yasani tana bala'in qaunar Yara.

Yaya Mariya ta kalleshi tace"to Alhamdulillah,Aliyu kar6eshi kayi masa hud'uba, sai kaje masallaci atara mutane suma su shaida sunansa"

Cikin farinciki Alhaji Mekudi ya kar6i jaririn daga hannun Zaliha wadda takeji kamar tagama samun komai a duniya tunda gashi Allah yabata yaro.

Cikin ikon Allah Alhaji Aliyu Mekudi yayiwa yaro hud'uba da suna JAWAD, yad'ago kansa ya kallesu yace"daga yau sunansa Jawad A. Mekudi"

(Muhammad d'inmu yakoma Jawad 😭)

Farinciki ya wanzu a fuskar Yaya Mariya da Hajiya Zaliha,Yaya Mariya tace"masha Allah, Allah yaraya mana Jawad"

Alhaji Mekudi yace"Amin ya Allah yaya"

Itama Hajiya Zaliha tace"Allah yarayamin Baby na"

Cikin farinciki suka amsa mata gaba dayansu,daga nan yadauki yaron yafita masallaci dashi,abunka da me kudi nan da nan aka siyo goro da alawa aka rabawa mutane a masallaci,liman ya kar6i yaro yayi masa Addu'ah yasa masa albarka,sannan Alhaji Mekudi yadawo gidan yayar tasa, basu zauna ba, kai tsaye asbiti suka wuce duka su ukun,wani qwararran doctor yaduba Jawad ciki da waje ya tabbatar musu da cewa yaron yanada cikakkiyar lafiya
babu abinda yake damunsa,daga nan likitan ya rubutawa Hajiya Zaliha magungunan da zatayi amfani dashi ruwan nono yazo domin taci gaba da shayar da Jawad.
Sai dare suka dawo gidansu shida Zaliha,kasancewar dare ne hakan ne yasa ba kowa ne yaga Jaririn dake hannun Hajiya Zaliha ba.

Saida yaraka su ciki sannan yasake futowa driver ya dauke shi suka fita da mota guda biyu,kai tsaye sayaiyar kaya yafara yiwa Jawad,hatta da d'an qaramin gadon kwantar da jarirai irinna turawa saida aka hado dashi,siyaiya aka yi masa ta hauka kamar a yarinta zai tabbata bazai girma ba,duka mota biyun dasuka fita da'ita saida suka cikota da kayan Jawad,bayan sun dawo gida yatsaya a farfajiyar gidan mutane suna sake yimasa Allah sanya Alkhairi akan sabon kamfanin dayaje qasar Nijar yabude,yayinda ma'aikata suke shigar da kayan siyaiyar tasa zuwa cikin falo.

Bayan yadawo falo yana zama guard dinsa guda daya yashigo falon cikin ladabi ya rissina yace"Yalla6ai ya za'ai da mutumin da muka kusa kadewa jiya,kace a bashi masauqi idan kadawo zaka ganshi"

Alhaji Mekudi yadafe goshinsa da hannunsa yace"subhanallah, na manta dashi wallahi, jeka shigo dashi"

Cikin sauri guard din yajuya,yayinda Alhaji Mekudi yajuya yana bawa Hajiya Zaliha datake sanyawa Jawad pampers labarin abinda yafaru jiyan.
Cikin mintuna qalilan aka gabatar masa da Malam Manu wanda kwana daya kawai harya fara sauya wa black beauty din fatarsa taji esi da naman kaji,Alhaji Mekudi yazuba wa Malam Manu ido yana kallonsa,yayinda Malam Manu ya shagala a kallon kyakykywan yaronda Hajiya Zaliha take sakawa wata hadaddiyar singlet ta jarirai,jiyake kamar ya dauwama yana kallon yaron,yaji lokaci d'aya wata matsananciyar qaunar yaron tana ratsa shi.

Alhaji Mekudi yace"bawan Allah daga ina kake? Sannan tunanin mekake kana tafiya haka akan titi har mota tazo tabigeka baka sani ba?"

Malam Manu yayi shiru cikin yanayin damuwa,bai dauki wannan bigeshin da mota tasoyi abakin komai ba face haqqin Bilkisu daya fara bibiyarsa,ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan yace"Ina tunanin aikin dazan nema nafara ne intara kudi sannan in koma wajan iyalina,ni mutumin jihar jigawa ne,nabar iyalina a halin babu,damuwa tamin yawa ganin tunda nazo cikin garin Lagos babu wata sana'ah dana samu domin in riqe kaina, tunani yamin yawa hakan yasa bansan motarku tazo kusana ba"

Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya,Hajiya Zaliha tayi kissing goshin Jawad tasakashi a qirjinta ta rungumeshi tana shashshafa masa baya tana so yayi bacci, sai lalla6ashi take saikace d'an gwal (😚).
Kallon Manu yayi bayan yagama ajiyar zuciyar yace"to zan baka aikinyi insha Allah, kaga nima asali na dan arewa ne, nema ne yakawo ni garin nan har Allah yasa nan garin yazama kamar shine tushena yanzu,zaka iyayin driving din mota?"

Cikin sauri Manu yace" zan'iya Alhaji,a dacan ai na'iya tuqin mota kafin iyayena su rasu"

Alhaji Mekudi yace"to zan baka driving,sannan akwai wajan zama, zaka dinga zama anan tare damu insha Allah"

Cikin sauri Manu yasake rissina wa duk da yana zaune, yayi godia Iya godia, Alhaji Mekudi ya kalli guard dinsa yace"aje anuna masa masauqinsa "

Guard d'in ya amsa cikin biyaiya,sannan yasaka malam Manu agaba zasu fita daga falon, saide kafin su fice saida Malan Manu yasake juyawa ya kalli Jawad dake kwance a kafad'ar Hajiya Zaliha.

Washegari tun safe har azahar ruwan nonon Hajiya Zaliha baizo ba,saboda wannan dalilin Alhaji Mekudi ko office baije ba,Hajiya Zaliha kuwa hawaye tafara ganin Jawad din yafara galabaita,dole saida aka kira doctor gida yazo yasake dubashi yafada musu yunwa yakeji,gashi nono yaqi zuwa,hakan yasa likitan ya rubuta musu Kala kalar madara ta jarirai,Alhaji Mekudi yabada umarni akawo wannan madara, aikuwa nan da nan aka kawowa Jawad madara katan katan,Hajiya Zaliha tahad'a masa tafara bashi,nan take yafara sha babu musu,sai alokacin hankalinsu ya kwanta.

*** *** ***
Niger Republic

A6angaren mutanan Niger kuwa tun safe da Farouq yafita da number motar wajan police yanaso yaji yanda za'a yi,Bilkisu taqi ci taqi sha tana jira yadawo taji Ina aka tsaya,Jamila sai kallonta take cikin tausayawa,duk da bata haihu ba taji zafin rashin wannan yaro jitake kamar d'anta ne aka tafi dashi.
Farouq yana dawowa Bilkisu me gwanjo tamiqe tsaye tanufeshi tana fadin"Farouq ya ake ciki?"

Cikin sanyin jiki Farouq yace"Yaya abun nanfa ba d'an qarami bane,naje nayi report sannan na basu number motar sun tabbatar min cewa ba motar qasar Nijar bace,motar daga Nigeria take,wai wani gari Lagos, kuma nima sai bayan nakai musu naga sunan garin sannan natuna ba motar qasar nan bace,tashin hankali ne ya hanani fahimta tun jiya dakika rubuta min,amma kiyi haquri sunce zasu tura wasiqa zuwa hukumar garin ko Allah zaisa adace...."

Tun lokacin dayace ance motar qasar Nigeria ce, daga nan tadena fahimtar komai tasan cewa a Nigeria ma taji labari ana cewa Lagos da nisa,sai an kwana ake zuwa,tasan cewa shima Muhammad shikkenan yatafi yabarta,lokaci d'aya idonta ya rufe ruf...tadena ganin haske sai duhu....

Cikin sauri Jamila tatarota tana fadin"innalillahi Farouq riqeta karta fadi tasuma fa"

Farouq yayi azamar tareta shida Jamila, suka samu suka kwantar da'ita akan tabarmar kaba wadda take shimfide a saharar tsakar gidan nasu, Jamila ta debo ruwa tashafa mata,lokaci daya taja wani irin numfashi tafarka azabure tana fadin "Muhammad!!!"

sannan tafashe dawani irin kuka,Jamila ta goge hawayen idonta, cikin muryar kuka tace"Yaya kiyi haquri,inda rabo watarana zaku had'u,kisa dangana aranki Yaya ubangiji shine yasan nufinsa akan hakan"

cikin tashin hankali da damuwa Bilkisu tafara magana tana fad'in"yanzu shikkenan na salwantar da d'ana dakaina? nasan cewa bazai soni ba, bazai yafemin ba"

Cikin sauri dakuma juriya irinta maza Farouq yace"Yaya meyasa zakice bazai soki ba? akwai yaron da uwa zata haifa sannan yazo yaqi uwarsa?"

Cikin kuka Bilkisu tace" Farouq ban shayar dashi ba tayaya zai soni? koda zai soni ba kamar yanda natsaya na shayar dashi tsawon shekara biyu ba,nasan yanzu duk inda yake bashida lafiya,baisha isasshen nono ba,ba lalle yayi basira kamar sauran yara sa'anninsa ba,ba zaiyi kuzari kamar suba,bazai tashi da qawazucin uwa ba..."

Jamila ta girgiza kanta cikin muryar kuka tace" karkice haka Yaya,jariranda uwa take mutuwa tabar su kuma su tashi da basirar sufa Yaya? ubangijin daya rabaki da d'anki zai azurtashi da wad'annan abubuwan dakika lissafa koma fiyeda haka..."

(karfa ace inason kashe Bilkisu saboda yanayin rayuwa ato nasan hali😂)

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝
('yar me gwanjo)

Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Bilkisu's name

https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu

7&8

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

___

Shima Farouq yayi ajiyar zuciya ya kalleta yace"abinda Jami tafad'a miki hakane Yaya,kiyi haquri ki kwantar da hankalin ki,ki daure ki kar6i wannan qaddarar a yanda tazo miki,Yaya kefa musulma ce,nasan ki da haquri ko a baya,yanzu ma ki daure kici gaba da haqurin"
Chapter 6 · 0% Book details