← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 63

Sashe 56

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilkisu ta lumshe idonta cikin farinciki,kasancewar babbar waya ce a wajanta yanzu,kana iya jiyo abinda ake fada, hakan yasa cikin sauri Hajiya Zaliha datake zaune agefenta ta qwace wayar tace"Jawad menake ji haka?"

Jawad ya d'an sosa kansa kad'an,sannan yace"Mummy kin kusa samun jika,nanda 3 months"

Cikin farinciki Mummy tace"Jawad tome kuke jira? kakawo ta gida ta haihu mana"

Gabansa yafad'i,cikin sauri yace"But Mummy she's fine fa"

Cikin muryar rashin wasa Mummy tace"Jawad,bazai iyu fa yanda kake shekara bakazo gida ba itama kace haka zaka mata,dole zaka bar yarinya tazo gida"

"to Mummy karatu fa take,kune kukace nasata a makaranta,idan tagama karatun nanda 4 years sai tazo gidan"

Mummy tace"dama take takenka Kenan? to karna sakejin wannan maganar,dazu da safennan Fu'ad yanuna min picture's din data turo masa sun gama first semester,tunda hutu suke yanzu kakawo min yarinya ta haihu agida kaji Nafada ma"

Cikin 6acin rai yace"ok Mummy"
Sannan yakashe wayar ya kalli Inaas yace"Kinji wata sabuwa kuma"
Yana fadar hakan yakoma cikin kujera ya runtse idonsa cikeda damuwa.

Inaas ta sauke qafafunta daga kan cinyarsa, ta matsa ta rungume ta tafara lallashin sa,daga wannan lallashi kid'an ya sauya salo,rawar ta sauya,shida yake mita yana complain baison kawo ta gida sai gashi shine yadawo yana ihun dad'i saboda yanda take tafiyar dashi cikin wani irin salo wanda baisan inda takoyi hakan ba.

Sosai yake bata kulawa tunda suka gano cewa tanada ciki,har yanzu batacin abinci sosai saide kayan qwalam,kullum sai Yaya Mariya takira su taji lafiyar Inaas din,itace take hanata yawan shan zaqi dakuma abubuwa masu sanyi kamar ice-cream,Jawad baya barin ta tayi komai idan wani abu take buqata saide yayi musu order kawai,bai sake bi takan maganar dawowar ta gida ba,haka itama Mummy ta zuba masa ido tana so taga gudun ruwansa.
6angaren aurataiyarsu babu abinda ya canza, saima naci da Jawad din yasake qarawa babu ranar dayake iya haquri ya d'aga mata qafa,kasancewar itama ta zama yar hannu hakan ba qaramin dadi yake mata ba,sai yanzu nema takejin tsantsar dadin,abaya duk haukan ta take,kullum suna manne da juna,basu da wani lokaci ke6a66e wanda basa wannan abun saide in baya gida.

Saida cikinta yacika wata bakwai sannan Daddy yayi masa waya akan yazo zaije tareda su Man Sulaiman a nemawa Fu'ad da P.a dinsa aure a Kaduna state,yasan da biyu suka shirya masa wannan tafiyar,bai Isa yaqi tafiya da'ita ba,tunda yaga alama zuba masa ido sukai akan maganar kawo ta gida haihuwa.

Hakan yasa suka shirya tafiya Nigeria,Inaas tayi mutuqar kyau cikin laffayar ta milk color,ta rataya yar qaramar hand back ta gayu a kafadarta, yayinda hannunta yake riqe da babbar wayarta tana danne danne,lokacin dasuka sauka a Nigeria sosai yan Jarida suka so kashe mata ido ta hasken camera,hannunta yana cikin na Jawad yayinda ya kama gefen laffayar ta ya riqe saboda tanada tsantsi kuma da tsawo zata iya jan qasa,sai kakkareta yake kamar wata zinariya.
Har wajan motocin dasukazo daukarsu yan Jarida suka bisu, amma Jawad bai basu damar magana dashi ba,kan kace me, labari ya watsu a media,daga masu cewa Amarya taji kudi tayi qiba abunta,sai masu cewa kamar ma ciki ne da'ita, wasu kuma suce batada cikin komai kawai qiba tayi da alama Jawad din ya'iya kiwo,saide wasu manyan mata iyaye masu bibiyar kafafen yad'a labarai kallo daya sukewa Inaas din sugano tanada ciki tsoho ma kuwa,suma daga nasu 6angaren suna ganin da alama Jawad d'in ya'iya aiki(🙈)

Acikin mota ajiyar zuciya ta saki tadora kanta akan kafadarsa,cikin kulawa yayi mata rada acikin kunanta yace"sorry"

Inaas ta gyad'a masa kanta,ya sunkuya yayi kissing kanta,sannan yadora hannunsa akan cikinta yana shafawa har sukaje gida.
Awajan adana motoci sukaga iyayen nasu a tsaye da alama jiran zuwansu suke,motar tana tsayawa Jawad yayi kissing bakinta sannan yabude mata motar tafita,shima ya futo daga d'aya 6angaren.

Cikin farinciki Inaas ta rungume Bilkisu,sannan ta rungume Mummy.
Yaya Mariya ta ruqo hannunta tana kallon yanayin jikin nata tace"sannu Inaas,Allah ya raba lafiya,muje ciki"

Gaba dayansu falon Mummy suka wuce,fuskar kowa d'aukeda farinciki,abinci sukaci saide Inaas kam nama kawai taci tasha ruwa,Jawad yana cin abincin yana satar kallonta,saida Fu'ad yayi masa rada yace"yaya Daddy fa yana kallonka"

Sannan ne yadan sosa kansa,ya daidaita kansa yamaida hankali kan cin abincin.

Shine yafara tashi,idonsa akanta yawuce sama domin ya watsa ruwa yayi sallah.
Itama Inaas adakin Mummy tayi sallah,batayi wankan ba,tadawo falo ta zauna sunata fira,har Jawad ya sauko yadawo falon suna nan,sai qarfe goma Yaya Mariya tatafi gida abokin rakiyar tata ya rakata, wato Fu'ad.

Su kuwa sai wajan goma da rabi sannan Bilkisu tayi musu saida safe,Inaas ma tamiqe taqi kallon inda Jawad din yake ma,tabi bayan Ammiy,Jawad ya dinga binta da kallon mamaki har suka 6acewa ganinsa.

Mummy ta juyo ta kalli Jawad tace"Jawad kashe kayan kallon nan kaje ka kwanta,naga alama kamar baka gaji ba, kuda kukai doguwar tafiya"

Ransa duk ba dadi yatashi yakashe kallon sannan murya ciki-ciki yace"saida safe Mummy"

Mummy tayi murmushi tace"Allah yakaimu"

Saida taga hawan sa sama sannan tayi ajiyar zuciya tawuce dakinta,tasan sarai saboda Inaas tatafi ne shiyasa yake wannan fishin,bazai iyu ta hanata tafiya ba saboda ko Yaya ne ya kamata ace anbarta da Bilkisun suyi firar yaushe Gamo.

Suna zuwa daki tacire kayanta tashiga toilet tayi wanka da ruwan d'umi,tana futowa Ammiy tabata mai ta shafa,sannan tahado mata turaren wuta irin nasu na Niger ta turara jikinta,tasaka kayan bacci tafara qoqarin daure dogon gashinta,tajuyo wajan Ammiy tace"Ammiy daure min"

Bilkisu ta kalli cikin Inaas din taga ciki da girmansa sosai,laffayar da tasa ce ta 6oye cikin,amma yanzu da tasa doguwar riga ta bacci marar nauyi gashinan ya futo zahiri.

Ta kar6i ribon din hannun Inaas din tace"Kafin kiyi aure ban huta da daure wannan gashi ba, yanzun ma bazaki barni nahuta ba? acan qasar taku waye yake daure miki?"

Inaas tace"haka nake barinsa Ammiy,idan na daure ma Yaya zaice bayaso"

Bilkisu tayi murmushi takama gashin nata ta daure mata,suka kashe wutar dakin suka kwanta,sannan tace"ai babu matsala azaman naku ko?"

Inaas tace"A a Ammiy babu komai wallahi,Yaya yanamin duk abinda nakeso,ko nan da can baya barina inje,ko aiki ne saide shi yayi,girkin ma banayi dayake likita ta hanani aiki,saide yayi mata order abinci"

Bilkisu tasaki wata irin wawiyar ajiyar zuciya,hankalin ta yasake kwanciya,duk da suna cikin duhu haka ta fuskanci Inaas din tace"to kinga wannan abun nake hango miki tun farko,shiyasa banso alaqarku keda yaron nan Is'haq ba,nafiso Kiji dad'i agidan aurenki banaso ko kad'an kiyi irin rayuwar danayi saide in Allah ne yariga ya qaddara miki,kinga ni lokacin danake d'aukeda cikin mijinki,bama samun abinda zamuci,daqyar babansa yake nemo mana garin kwaki,shi zamu jiqa muci,wani lokacin ma duk da inada tsohon ciki sainayi wankin kudi,kokuma nayi niqan Lada,sannan zan Samo mana abinda zamu dan tarkada muci,shinkafa kuwa bama ganinta,abincinmu daga qanzo sai garin kwaki..."

Taqarasa maganar tana share hawaye,Inaas ma hawayen ta share tace"Ammiy kiyi haquri,kidena tuna baya,yanzu ba gashi Yaya Jawad yana yi mana komai ba?"

Bilkisu ta share hawayen ta tace"hakane kam,kinga katin bankin daya baki lokacin bikinku yace ko zamu cire kudi dana yi masa maganar katin qin kar6a yayi,daga qarshe yacemin duk abinda ya mallaka wanda yasani da wanda bai saniba yabani shi,nace masa samunsa agareni yafiyemin dukkan wani qyale-qyalen duniya"

Inaas tace"ai Yaya yahadu,wallahi bashida matsalar komai Ammiy"

Bilkisu tayi murmushi ta dungure mata kai,suka sa dariya daga nan sukai Addu'ah suka fara bacci.

Qarfe daya na dare wayarta dake vibration tafara haskawa,Bilkisu tayi juyi taga wayar Inaas din ana kira,tad'an ta6ata tace"Inaas tashi ki dauki waya"

Inaas takai hannu ta dauki wayar cikin muryar bacci tace"Qaunah"

Jawad ya lumshe idonsa yace"Love nakasa bacci"

Idonta a lumshe tace"Meyasa?"

Jawad yace"ina gefen window ina hango falon ku,kifuto falo kibude window naganki,ko zan'iya baccin"

Ahankali tad'an bude idonta sannan tatashi tafuto daga dakin,tazo falon ta yaye labulan window ta hango shi daga can sama yana tsaye, tace"kaganni?"

"yes naganki,meyasa zakibi Mama? yanzu biyu saura,kuma a'irin wannan lokacin kin riga kin san memuke yi,kin saba min da abun dad'inki,yanzu gaba daya na a firgice nake wallahi,narasa nutsuwa, tun dazu sai juyi nake nakasa bacci"

Inaas tayi ajiyar zuciya tayi qasa muryarta cikin rad'a tace"Qaunah,yanzu fa muna gida,dole haquri zamuyi"

Cikin sauri yace"what!? mekike nufi?,kasheni zakiyi?"

Idonta ta lumshe tabude tace"bahaka nake nufi ba,Qaunah kasanfa bazai iyu ba,da kunya inbika sama mu kwanta tunda su Mummy suna nan"

Cikin sauri yace"ok,to zan dinga biyoki wajan Mama"

Cikin sauri tace"Qaunah tareda itafa nake kwana,kawai mudinga fita wani wajan idan mukai abinda zamuyi saimu dawo"

Jawad zaro idonsa waje yace"muje ina? to duk inda nasa qafata agarinnan sai yan Jarida sun sani,nide kawai kisan yanda zaki dinga yin dabara muna haduwa,wallahi zan'iya cutuwa,yanzu haka nasan cewa yau bazan fita sallar asuba ba,saboda idan nafita za'a gane halin danake ciki"

Inaas ta lumshe idonta tace"toya zamuyi? nide bazan yarda kazo nan ba,saboda dakunan mu babu space sosai tsakanin na juna,duk abinda zakayi wallahi Uncle da Mama da Abbana duk sai sun jika,kuma kaima Qauna baka iya abun sirri ba,saika dinga ihu kana dukan gado kamar wani d'an dambe"

Jawad ya motsa lips dinsa sannan yace"to waye yake sani hakan? ba kece ba? dama aina dade da sanin cewa kallon d'an dambe kikemin,kawai fada ne bakya yi, ranar dana fara ganinki abinda kika fadamin kenan"

Inaas tayi murmushi tace"siffar mijina ne hakan,shi din jarumi ne,inaji dashi fiyeda yanda nakeji dakaina,yanzu de abinda za'a yi shine duk lokacin danaga Ammiy tayi bacci zan futo,kaima idan kaduba kaga Mummy da Daddy sunyi bacci kazo mu hadu ta qofar bayan Plat dinku, sai muje dakinka,kafin asuba saina dawo"

Jawad yayi wata irin ajiyar zuciya sannan yace"i luv you so much love"

Daga nan yasakar mata kiss yakashe wayar.

Takoma daki tashiga toilet tayi fitsari,sannan ta kwanta a gadon tana tunanin mijinta.
Sai alokacin Bilkisu taci gaba da bacci,itama tashi tayi takasa komawa saida taji Inaas din tadawo daki sannan hankalin ta ya kwanta.(🙊🙆🏻‍♀️)

(kuyi haquri da wannan ba yawa, idan nace saina gama rubuta page din zan turo to zaku iya kaiwa qarfe goma kuna jirana,ku rage wannan mu hadu zuwa safe insha Allah 🙏🏻saida safenku nagode ❤️

Amnah El Yaqoub ✍🏻
[1/23, 08:05] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Chapter 56 · 0% Book details