Sashe 3
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yayinda Malam Manu yakasa runtsawa yasata agaba yana kallonta kamar bai ta6a ganinta ba,jikinsa yayi mutuqar sanyi,ahankali yasaka hannunsa ya shafa cikinta,sannan ya shafa fuskarta, wani irin hawaye yazubo daga idonsa,yadad'e yana hawaye har kusan qarfe uku nadare,ahankali yatashi yaduba takarda ad'akin,akwai wata tawada ta rubutu itama yad'aukota yayi rubutu ajikin takardar da Ajami.
kasancewar a wannan lokacin be'iya Boko ba,amma yasan yanda zaiyi rubutu da Ajami,hawayen idonsa ya share ya ninke takardar ya ajiyeta agefen fuskarta,yabude dakin yafuto, ya qarewa gidan nasu kallo, yafashe dawani irin kuka sannan yafice daga gidan cikin sauri.(😭)
Kiran sallar farko ta farka taji ana sheqa musu ruwan sama,tashafa gefenta bataji malam Manu ba,sai tayi tunanin ko yana tsakar gidane yana tattara musu 'yan tarkace,tasake juyi daqyar saboda girman cikinta, taci gaba da baccinta,bata sake farkawa ba saida gari yayi Haske,cikin fad'uwar gaba ta yunqura tatashi tana salati saboda wani irin mummunan mafarki da tayi,saita danganta hakan da rashin yin sallar asuba da batayi ba akan lokaci,tamiqe tana hamma ta tattare dogon gashin kanta daya warware saboda bacci,tafuto tsakar gida taga yanda tabar komai jiya,haka yake yana nan yanda yake,a fili tace"to malam kode shima yau ya makara ne? bai tasheni sallah ba,ga gida yana nan yanda na barshi na kwanta,kode yana band'aki ne?"
Ta d'aga murya tace"malam!!"
Taji shiru,ta d'auki buta tashiga band'aki tagama uzurinta tafuto tayi alwala tayi sallah,bayan ta idar da sallar haka nan ta tsinci kanta da rashin kwanciyar hankali,malam bai ta6a fita yaqi sanar da'ita inda yaje ba,koda tana bacci zai tasheta yafad'a mata,to ina yaje haka?
Cikin hanzari tatashi tafuto tsakar gida gabanta yana fad'uwa,mayafin da tayi sallah dashi shine ajikinta tashin hankali yasa ko takan niqab d'inta batabi ba,suba wani d'akuna ne dasu ba bare tace yashiga ciki,d'akinsu ne qwaya daya jal kuma baya nan,qofar gida tafuto tana faman kiran sunansa, sai dube-dube take tana fad'in "Malam...!!"
Amma shiru kakeji,wasu d'aid'aikun masu tafiya gona sai kallonta suke saboda sunga abun mamaki,basu ta6a tunanin akwai kyakykywar halitta kamarta acikin qaunyensu na Garin Malam ba,wani me Keke yazo wucewa shima zai tafi gona tsabar waigowar dayake yana kallonta har fad'uwa yayi sakamakon cin karo dayayi dawani tsoho.
Tana ganin abunda yafaru tasan cewa itace sila,cikin sauri taja mayafin jikinta ta6oye fuskarta,sannan tajuya takoma gida,d'akinsu tashiga tafara tattare musu kayan Shimfid'arsu,anan idonta yasaauka akan wata farar takarda,gabanta ne yafad'i da ganin takardar cikin sauri tad'auka sannan ta bud'eta,lokaci d'aya taci karo da rubutun mijinta Malam Manu inda ya rubuta mata cewa ( KIYAFEMIN ) jikinta ne yafara rawa,taji numfashinta yana sama kamar zai d'auke,hakan yana nufin kenan Manu yagudu yabarta,daqyar tasamu ta fuzgo numfashinta tareda sakin wata irin gigitacciyar qara,wanda yajawo hankalin maqotanta.
(so sad😭,sorry Mama Bilki)
Littafin ME 'DEBE KEWA na kud'i ne,300 Naira kacal👌🏻
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034
Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝
('yar me gwanjo)
Writing By Amnah El Yaqoub
Dedicated to Bilkisu's name
https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu
3&4
maqotanta sunyi tunanin naquda ce ta taso mata,hakan yasa suka shigo a fujajan,anan suka tarar da bilkisu tana kuka tad'ora hannunta akanta,d'aya daga ciki ce tafara bubbuga bayanta alamar lallashi tace"Balki me gwanjo kiyi haquri,ciwo ba mutuwa bane"
Cikin kuka da baqin cikin halin da tashiga tace"Manu ya gudu yabarni Bintu,bai duba maraicina ba yatafi yabarni da tsohon ciki"
Wadda Bilkisu takira da Bintu saita zabura taja gefe guda jikinta yana rawa,d'ayar maqociyar tata kuwa duka hannunta biyu tasa tarufe bakinta hawaye yana zuba a'idon ta,cikin kuka tafice da gudu tabar gidan taje tafad'awa mijinta halin da'ake ciki.
Kan kace me,labari yaje kunan mai Gari,Bintu tana rungume da Bilkisu tana lallashinta saide itama hawaye take zubar wa tana fad'in"kiyi haquri me gwanjo,insha Allahu muna nan tare dake bazaki tagayyara ba"
Sallama suka jiyo daga qofar gida,Bintu taje taduba,mutumin dayake tsaye yace"kece Balki me gwanjo?"
Bintu ta girgiza kai hawaye yana zarya daga idonta tace"Balki tana ciki"
"kice mata megari yana kiranta,maqocinta yakai masa labari yanzu"
Bintu batace masa komai ba tajuya,takamo hannun Bilkisu suka futo idanun nan nata yayi jajir abunka da farar mace,zama sukai agaban megari yayinda idanun fadawansa yadawo kan Bilkisu,wasu suna mata kallon qurulla wasu suna mata kallon tausayi, maigari yayi gyaran murya yace"Munsamu labarin abinda yafaru,kiyi haquri insha Allahu za'a ga mijinki,haqiqa Sulaimanu bai kyauta ba,kuma dole zai kar6i hukunci mai tsanani daga fada,maqociyarki fatsime tafad'awa mijinta Haruna gashinan a zaune,Haruna yazo fada ya sameni yafad'a min abinda yake faruwa,bamuyi qasa a gwiwa ba mun tashi matashi me hanzari akan Keke, mun turashi Garin Gandun Galadima yaje yanemo Sulaimanu,nasan duk inda Sulaimanu yake,bazai wuce garin Gandun Galadima ba"
Rufe bakin megari keda wuya,dan aikensa yadawo,lokaci d'aya idanun fada yakoma kansa,cikin ladabi matashin yadubi maigari yace"Allah yaqarama lafiya mun bincika cikin Gandun Galadima kaf....babu malam Manu babu dalilin sa,da yiyuwar yayi nisa ranka ya dad'e"
Bilkisu tanajin bayanin wannan matashi kanta yasara,cikinta yayi wata irin juyawa,lokaci daya tasaki qara tafara naquda afadar megari,nan take megari ya kalli Bintu da Fatsime maqotan Bilkisu yace"ku qarasa da'ita cikin gidana ta sauka acan har mugama binciken inda Sulaimanu yake"
Babu musu fatsime da Bintu suka kama Bilkisu datake d'aga qafa daqyar saboda naquda tazo mata gadan-gadan sukai cikin gidan megari da'ita.
Da taimakon 'Dayyaba matar maigari su Bintu da Fatsime suka had'u suka dinga tausar Bilkisu har Allah ya sauketa lafiya,ta haifi d'anta namiji kyakykywa dashi masha Allah,kallo d'aya zaka yiwa yaron kaji yashiga ranka,fari ne tas qato,babu abinda ya dauko na mahaifinsa sai yatsun qafarsa sak irinna Manu,babu rama atareda yaron 6ul6ul dashi kamar ba rainon Gaarin kwaki ba, bayan sun tsaftace su itada yaran haka ta rungume shi a qirjinta tana hawaye,gashi de abinda take fatan haifa Allah yabata,saide babu Manu,baisan me suka haifa ba,baisan awanne hali take ciki ba,baisaniba tana raye kota mutu ta dalilin haihuwar d'ansa,hawayen idonta ta share tazuba wa yaron ido tana kallonsa yayinda yafarka daga baccin dayake shima idonsa cikin nata,wani hawayen ne yasake zubo mata tana kallonsa tana murmushi ga hawaye,Fatsime ce tashigo takawo mata kunun kanwa,suka zauna agabanta suna sake bata haquri dakuma tabbacin insha Allahu za'a ga mijinta.
Sai dare aka kawo mata dahuwar Jan nama umarnin maigari kenan,haka take cin naman amma daqyar take iya had'iyeshi saboda jin wani irin abu aqarqashin wuyanta wanda takeji kamar dutsi ne awajan tsabar damuwa.
Washegari ma tasamu kulawa wajan matar maigari anyi mata wankan jego irinna mutanan da,taci dumaman tuwon dawa dakuma kunun kanwa,babu 6ata lokaci kuwa ruwan nonon ta yake zuwa yaronta yanasha yana qoshi.
Da misalin qarfe goma shad'aya na safe kira yasameta daga maigari,wannan lokacin bayan Fatsime da Bintu maqotanta harda ita kanta 'Dayyaba matar maigari suka nufi fada,yaronta yana rungume a qirjinta ta qanqameshi,bayan sun zazzauna maigari yadubeta yace"Balki saide kiyi haquri,mun tura mutanan mu Garin Galadima jiya ba'a ga Malam Manu ba,munsake tura mutane cikin garin Hadejia da Gaarin Gabas,har zuwa Birniwa,amma babu labarin Mijinki Manu,wasu daga cikin masu zaman fada sunbawa fada shawara asake bincikawa, duk da haka fada batayi qasa a gwiwa ba munsake tashin mutane sun nufi yamma har zuwa garin Gujungu,amma babu Manu, babu Labarinsa"
Lokaci d'aya Bilkisu tafashe da kuka harda shashsheka.
'Daya daga cikin masu zaman fada ya gyara zaman sa ya kalli Bilkisu sannan yakai dubansa wajan Maigari yace"Allah yaqara ma lafiya ai tunda akayi irin wannan nema ba'aga Manu ba to haqiqa yagudu yabi duniya,akwai manema aure dayawa anan,saboda haka kawai karaba wannan auren nasu,saita samu miji kamar de nid'innan sai tayi aurenta"(😲🤭)
Cikin tsawa Megari yace"Rufe mana baki Bala"
Yajuya ya kalli Bilkisu yace"Balkisu nasan danginki suna qasar Nijar,zakiyi haquri ki zauna damu har aga mijinki? Ina miki albishir zamu harhad'a miki kud'i kidinga sana'ar saida kayan gwanjo,tunda med'akina tafada min cewa duk garin nan,bayan Tabawa me saida kayan gwanjo babu wanda yakaiki samun nasibi akan saida gwanjo,zaki zauna tare damu?"
Ba tareda tunanin komai ba,Bilkisu tagoge qwallar data taru a'idon ta tace"Zan tafi qasarmu Ranka yadade"
Megari yace"to kiyi haquri kizauna damu idan anyi suna saiki tafi,kafin nan kema kin sake samun qwarin jikinki"
Bata iya amsa masaba tatashi suka koma cikin gidan maigari,domin kuwa idan tace zatayi magana haqiqa kuka ne zai biyo baya.
Zaman Bilkisu agidan maigari babu laifi,tana Samun kulawa kamar tana gidan iyayenta,matar maigari 'Dayyaba cikin kwana shida ta koya mata yanda zata dinga wankan yaronta,Bilkisu tanajin bala'in qaunar d'anta,koda yaushe idon yaron qur akan uwarsa kamar ba haihuwar kwana shida ba,haka itama Bikisun kullum idonta a kansa tanajin wani irin nishad'i idan ta tuna ko bata da kowa to tabbas tana dashi,tasan cewa koda kowa zai gujeta shikam yana tareda ita,ita kanta 'Dayyaba matar maigari jitake kamar ta qwace wannan yaro na Bilkisu,yaron abun sha'awa fari qal dashi kamar Mamansa.
Yauda safe tanayi masa wanka tana masa surutu kamar tana magana dame hankali,bayan tasakashi acikin zani ta lullu6eshi tana qoqarin shafa masa mai ajikinsa ta kalleshi cikin sanyin jiki tace"Babanka yagudu yabarmu,nasan kai bazaka gudu kabar Mama bako?Mama tana sonka,karka gudu kabarta kaji? idan kabarni bazan iya jurewa ba,nima ina tareda kai Babana,yanda Babanka yagudu yabarmu insha Allahu saimun bashi kunya,insha Allahu saika mulki mutane dayawa a duniyar nan,kaine d'ana,d'anda nafiso fiyeda komai a rayuwata...."
tana kaiwa nan ta sunkuya ta sumbaci goshin yaron.
'Dayyaba matar maigari tashare hawayen tausayin Bilkisu,sannan tajuya ahankali tafasa shigowa cikin dakin bayan tagama jin duk maganganun da Bilkisu take yiwa yaronta.
Washegari tacika kwana bakwai da haihuwa,kuma a ranar aka sanyawa yaron Bilkisu suna MUHAMMAD kamar yanda ta buqata,yaro yaci sunan mahaifinta,Megari yasa mutanan gari sukayi karo-karo aka hada mata kudad'e masu yawa aka bata,a ranar kuma aka kira me photo yayiwa yaronta photo yace zaije cikin garin Hadejia ya wanko mata photon gobe zai kawo mata,a ranar taso tafiya amma saboda photon ta tsaya tasake kwana,washegari da safe kuwa me photo yakawo mata,tashirya yaronta tagoyashi,sannan itama ta shirya suka futo.