Sashe 33
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Mekudi yayi murmushi ya kalli Hajiya Aisha matar Alhaji Auwal yace"Hajiya kice zanyi muku fashi"
Hajiya Aisha tayi murmushi tace"aiba komai Alhaji"
Duk wannan abun dasuke kan Bilkisu yana qasa,batasan dalilin da yasa Sulaimanu ya kwaso mata wannan gayyar yakawo mata ba.
Yaya Mariya ta kalli Alhaji Mekudi tace"Bissmillah Aliyu"
Alhaji Mekudi yadago kansa ya kalli Bilkisu,tun a fuskar ta yasan cewa da alama tanada haquri,tanada innocent face,yanaso ya roqeta amatsayin sa na Alhaji Mekudi,mashahurin mutum wanda babu wanda baisan dashi ba afad'in Africa da kewayanta, saide bayaso tayi masa Alfarma amatsayin kasancewar sa wani babban mutum,gara tayi masa Alfarma amatsayin sa na mutum kamar kowa,hakan yasa ya6oye mata cikakkan sunansa na Alhaji Mekudi, yadubeta yace"Bilkisu Sunana Alhaji Aliyu,ni mutumin Nigeria ne,atare dani akwai Yayata uwa daya uba daya,gakuma matata Zaliha,inada yarana guda biyu maza,sannan nazo qasar nan ne nida dangina saboda ke....,bayan mun sauka a Airport naqarasa gidan Aminina gashinan a zaune Alhaji Auwal da matarsa Hajiya Aisha,kamar yanda nace munzo qasar nan ne saboda ke,to saboda ke din mukazo amma ta dalilin Man Sulaiman..."
Bilkisu tanajin haka qwalla tacika idonta,batason mutane su shiga cikin matsalar ta itada Sulaimanu ,menene amfanin kawo mata wannan mutanan? shida ba mutumin arziqi ba tayaya ya hadu da mutanan arziqi?
Inaas tanajin wannan Alhaji yace sunzo ta dalilin Man Sulaiman tasan cewa Man Sulaiman dinnan shine Manu mijin Ammin ta,ahankali tadago kanta ta kalleshi, kansa yana qasa,cikin nutsuwa tatashi tashige daki ganin maganar tasu ta manya ce,saide daga cikin d'akin tana Iya jiyo abinda suke fada.
Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya yaci gaba da fadin"Bilkisu gaba dayan mu munzo ne domin mu taya Man Sulaiman baki haquri,dukkan mu munsan komai,munji abinda yamiki, sannan munji batun 6atan yaro muna qara baki haquri,haqiqa kinyi haquri,amma inaso ki qara haquri,ki qara haquri Bilkisu,Man Sulaiman din dakika sani abaya,yanzu bashi bane,yatuba yayi nadama Bilkisu,inaso ki yafe masa sannan keda d'an'uwanki da yarinyar ki muna so kubimu mukoma Abuja muzama ahali d'aya,domin kuwa ni Man Sulaiman kamar dan'uwana na daukeshi,shekaru talatin da bakwai dasuka wuce direba na yakadeshi,nafuto daga mota na bashi haquri,nace a kaishi gidana, bayan wasu kwanaki nazauna dashi,yayimin bayanin dalilin da yasa yabar ki,kuma ko alokacin akwai tsantsar damuwa atare dashi,kiyi haquri Bilkisu,ki yafe masa, sannan ki kar6i roqona inaso na maida aurenku kuci gaba da rayuwa kamar baya"
Tsakar gidan yayi tsit bakajin motsin kowa sai kukan Bilkisu dake tashi,sosai take kuka harda shashsheka,Yaya Mariya ta kalleta cikeda tausayi tace"kiyi haquri Bilkisu,karki duba baya,idan kikace zaki tuna baya, bazaki iya yafe masa ba"
Bilkisu dake faman kuka ta gyada kanta alamun amsawa sannan tace"nayafe masa Alhaji...,Allah ya yafe mana baki daya"
Cikin sauri Man Sulaiman ya goge hawayen idonsa yanajin wata irin nutsuwa tana kwaranya acikin zuciyarsa.
Alhaji Mekudi yayi murmushi yace"to Alhamdulillah,kin kyauta,Allah yasaka miki da Alkhairi,to Yaya batun mayarda auren ku?"
Bilkisu ta goge sauran hawayen ta idonta,fuskarta ba yabo ba fallasa tace" a a,abar wannan maganar Alhaji"
Alhaji Mekudi yasake yin murmushi,ya kalli Hajiya Zaliha,kafin yayi magana Hajiya Zaliha tace"Bilkisu mungode sosai,Allah yasaka da Alkhairi,maganar aure baza'a tilasta miki ba,zamu baki lokaci duk lokacin dakika ga yadace saiki taimaka ki koma dakin ki,amma yanzu de maganar tafiya tare daku zamu tafi,muna fatan kun yarda damu kuma zaku bimu"
Bilkisu ta kalli Farouq tace"kuyi magana dasu"
Farouq ya kalli Alhaji Mekudi yace"Alhaji bazamu dora muku nauyi ba? tayaya harmu uku zamu tashi daga wata qasa mu koma gidanku cinmu da shanmu yahau kanku?"
Alhaji Auwal yayi murmushi yace"Uncle din yara karka damu,tunda abokina ne da kansa yace ku koma, to banaso ku watsa masa qasa a'ido,ku daure kutafi tare dasu"
Farouq ya kalli Alhaji Mekudi yace"to Alhaji mungode,Allah yasaka da Alkhairi,Allah yaraya bayanka,mungode"
Alhaji Mekudi yace" a'a babu damuwa,ai mun zama daya,Man Sulaiman yawuce haka awajena"
Ya kalli Alhaji Auwal da Man Sulaiman yace"muje waje mubasu waje su shirya saimu wuce ko?"
Alhaji Auwal da Man Sulaiman da Farouq duk suka fice,a kabar iya matan agidan.
Bilkisu tashiga daki domin tarkata yan kayansu,Hajiya Zaliha tamiqe tacire Mayafin ta tace"bari naje nataya ta had'a kayan"
tafadi haka tana shigewa cikin falon nasu,Yaya Mariya ta miqe qafa a tabarma tacire mayafi tadaga murya tace"Zaliha bafa komai zaku dauko ba,kawai Iya d'an abun amfani wanda suke so zaku dauka,amma karsu dauki ko sutura,idan munje can sai ayi musu wasu"
Hajiya Zaliha tace"eh Yaya nagane"
Yaya Mariya tasake daga murya tace"ina yarinyar nan take ne,zoki bani buta nakama ruwa"
Inaas tafuto da sauri tazubo mata ruwan takawo mata,Yaya Mariya ta kalleta tace"yanmata ya sunan kine?"
Inaas tayi murmushi tace"Sunana INAAS"
Yaya Mariya tace"masha Allah,munzo zamu rabaki da samarin ki ko? karki damu zaki samu wasu samarin a Nigeria,muma munada samari guda biyu a gidan namu sai wanda kika za6a"(🤭)
Hajiya Aisha da hankalin ta yake kan waya ta dago ta kalli Yaya Mariya tace"haba Yaya,haka yayan nawa suka koma kuma?"
Yaya Mariya tace" ato tunda sunqi sukawo matar aure ai kinga sai yan matan sufara tsabar su"
Inaas tayi murmushi takoma daki sukaci gaba da hada yan kayansu,duk abinda Ammiy ta dauko sai Hajiya Zaliha tahanata dauka acewarta basa buqatar komai,zasu samu komai acan,bawani kayan kirki suka dauka ba,yawanci abubuwan su ne masu muhinmanci, musanman Bilkisu ba komai ta dauka ba sai photunan Muhammad dinta wanda aka masa tun lokacin haihuwar sa.
Agurguje suka kammala komai,Ammiy da Inaas da Hajiya Zaliha suka shiga maqota sukai musu sallama,sannan Farouq yakira me gidan hayar yayi masa bayani zasu tashi,sannan suka dunguma suka tafi gidan Alhaji Auwal,acan suka huta sukaci abinci,Inaas takira wayar manager a wayar Ammiy tayi masa cikakkan bayani akan komawarsu Nigeria, takuma bashi haquri akan rashin sanar dashi da batayi ba dawuri itama abun yazo matane baga tatan, har yamma lis suna gidan Alhaji Auwal har saida aka nema musu tickets sannan sukai bankwana da Niger suka nufi Nigeria.
*** *** ***
Lokacin dasuka sauka dare yayi,amma duk da haka daga Bilkisu har Farouq da Inaas babu wanda bai tsorata da ganin girman gidan ba,Inaas da Bilkisu suka sake qanqame hannun juna ganin yanda sojoji suke shawagi a harabar gidan kowa hannunsa daukeda bindiga.
Farouq kuwa duk da yana zuwa gidan Alhaji Auwal za'a iya cewa yasaba da ganin babban gida,saide bai ta6a ganin irin wannan gida gari guda haka ba,baisan cewa wannan shine katafaren gidan Alhaji Mekudi ba,baisan cewa wannan shine gidansu Jawad dinnan de dayace kada 'yarsa tayi amfani da kyautar sa ba.
Daga Hajiya Zaliha har Alhaji Mekudi da Yaya Mariya saida suka rakasu har part dinsu dayake kusa danasu Hajiya Zaliha,Inaas tana liqe ajikin Bilkisu hannunsu yana cikin na juna sai kalle-kallen hadaddan falon suke, wanda yaji komai da komai najin dadin rayuwa,Alhaji Mekudi yace"to Alhamdulillah,Bilkisu wannan shine masaukin ku,akwai dakuna dayawa sannan akwai abubuwan buqata aciki,Man Sulaiman zai dawo nan shima yaza6i daki daya saikuci gaba da zama tare,sannan muna sake baki haquri akan duk abubuwan dasuka faru,yanzu ma kiyi haquri ki kwantar da hankalin ki ku zauna tare damu"
Bilkisu ta gyada kanta sannan tace"Alhaji mungode,wannan dawainiyar tayi yawa Alhaji,yanzu Ina zamu kai wannan uban dakuna da wannan tangamemen falo,Alhaji dame zamu saka maka?"
Yaya Mariya tace"kuyi masa Addu'ah Bilkisu,ladansa yana wajan Allah"
Farouq yace"gaskiya Alhaji badan badanba, zan iya cewa babu irin ka a duniyar nan,bamu hada dangi dakai ba,baka sanmu ba, amma kayi mana abinda ko wani dan'uwan namu ne ba zaiyi mana haka ba, mungode Alhaji,Allah yasaka da Alkhairi "
Alhaji Mekudi yace"Haba Malam Farouq,yazakace kuba dangi na bane? ai nayi tunanin cewa tsawon shekaru talatin da bakwai danayi tareda Man Sulaiman munriga mun zama d'aya ni dashi,danhaka kuma daga yau kun zama ahalina,Allah yabamu zaman lafiya"
Gaba dayansu suka amsa da "Amin"
Daga nan Alhaji Mekudi yamiqe,Yaya Mariya da Hajiya Zaliha ma suka musu saida safe da niyyar idan sunje su aiko musu da abinci,Man Sulaiman yatashi yasaci kallon Bilkisu aikuwa karaf idonsu yahadu dana juna tayi sauri ta watsa masa wata irin harara,cikin sauri ya janye idonsa yabi bayansu Alhaji Mekudi.
Farouq da komai yafaru akan idonsa ya kalli yayar tasa yasaki murmushi.
Inaas tana ganin babu kowa tatashi tsaye cikin murna tafara warware laffayar jikinta tana duba d'akunan cikin farinciki tace"wayyo Allah Ammiy zoki gani wanne d'akin zamu za6a?"
*** *** ***
Yana tsaye acikin wani hadaddan jirgin ruwa yayi kyau sosai cikin qananun kaya nashan is'ka,wandon duka dukansa iyakar sa gwiwar sane, yayinda rigar ta kasance marar hannu,cikin ruwan yake kalla amma hankalinsa kwata-kwata baya wajan, kawai idonsa ne awajan,zuciyarsa da tunanin sa sun tafi wajan kiran waya,kowanne lokaci yana nan yana dakon ranar dazata kira wayarsa.
Yayi ajiyar zuciya ya furzar dawata irin is'ka me zafi daga bakinsa,yadawo yanemi waje ya zauna,wata baturiya taqaraso tazuba masa lemo tajuya takoma cikin jirgin,Jawad bai kalli inda lemon yake ba yahade hannunsa biyu yayi tagumi, kana ganin fuskarsa zakasan cewa yana cikin damuwa.
P.a ya kalleshi cikin girmamawa yace"yalla6ai lafiya kuwa?meyake damunka?"
Batare daya kalleshi ba yace" ina cikin damuwa P.a,please ina buqatar ke6ewa"
Yana fadin haka yatashi yakoma cikin jirgin yashige wani dan daki ya kwanta tareda lumshe idonsa.
P.a ya girgiza kansa,tabbas koma menene wannan ba qaramin abu bane yake damun Yalla6ai Jawad,duba da ko yana cikin damuwa ba kasafai ake iya gane halin dayake ciki ba.
Basu bar ga6ar ruwan ba sai yamma,kai tsaye gida suka wuce,Jawad yayi wanka yasake shiryawa cikin qananun kaya saide wannan lokacin wandon jeans yasaka amma tsawon wandon yadan wuce gwiwar sa da kad'an amma bai qarasa har can qasa irin kowanne wando ba,sai rigar me hade da hula wadda tasake qawata kyawun halittarsa.
Waya ce a maqale a kunnansa yana waya da Mummy,adede wannan lokacin Mummy ta kaiwa su Bilkisu abinci itada yan aikinta, tadawo tayi wanka ta kwanta taji kiran Jawad din, a wannan lokacin qarfe tara na dare a agogon Nigeria,bayan sungama gaisawa tana so tafara yimasa zancen zuwansu Bilkisu,P.a yakawo masa waya,cikin sauri yayi mata saida safe yakashe ya kar6i wayarda P.a yake bashi dawani irin sauri yayi tunanin Inaas ce take kiransa (🤭)
Yana dauka yaji ba'ita bace,lokaci daya 6acin rai ya bayyana a fuskarsa,tsabar baqin ciki ko magana yakasa yi,daga dayan 6angaren akace"Yalla6ai dama maganar wannan gwanjon kamfanin daka siya ne na Suleja, angama duk wani gyare-gyare nashi,an sabunta komai taron budewa kawai yarage sai batun aiki"