← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 63

Sashe 2

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani yaro ne yayi sallama da wata roba a kansa,yana zuwa yabata robar yace"Balki ME GWANJO waiga niqa inji innata"

Cikin sauri ta kar6i niqan tareda ladan niqan nata naira goma,ta dubi yaron tace"to Ashiru kadawo anjima kad'an ka d'auka mata"

Yaron Yajuya yafice da gudu,batayi qasa a gwiwa ba tatashi takoma wajan datake niqa da dutsin niqa irinna da can,tsumma tasa tagoge jikin dutsin, sannan tafara zuba geron akan dutsin, tadora wani dutsin d'an qarami Wanda ake riqe shi da hannu, sannan tafara niqa musu geron,yunwa tasa cikinta ya murd'a,lokaci d'aya wani irin hawaye yazubo mata,tasaka bayan hannunta ta share taci gaba da niqan.

Tsaf tagama yin niqan burabusko ta ajiye musu agefe, sannan ta dawo wajan Malam Manu dayayi tagumi hannu bibbiyu yayi zurfi cikin tunani tazauna sannan tabashi naira goman da Ashiru yakawo mata ladan niqan datayi, ta meqa masa kudin tace"Malam kayi haquri kadena tunani dan Allah,duk wani tsanani yana tareda sauqi,kaje ka siyo mana gari da siga ashago sai musha"

Cikin sauri ya kar6i kud'in sannan yatashi tsaye yace"to Bilkisu,ubangiji Allah yayi miki Albarka"

Cikin kulawa ta amsa masa,sannan ta kwanta tana maida numfashi tareda shafa qaton cikinta tanajin tsananin qaunar cikin tana sake ratsata.
Malam Manu bai jimaba yadawo hannunsa daukeda garin kwaki da siga,shine yajiqa musu,yadawo yazauna akusa da'ita yace"Bilkisu tashi musha gaarin"

Saida ta runtse idonta sannan tatashi daqyar,tazauna tafara sha.
Canjin hannunsa daya rage na qwandala biyu ya'ajiye agabanta yace"ki adana wannan canjin a wajanki ko zaki sai wani abu,garin nera biyar nasiyo mana,da siga na naira uku,yau nayi muku horon yunwa keda abinda ke cikinki Bilkisu kiyi haquri"

Cikin kulawa tace"Babu komai malam"

Basu sake magana ba har suka kammala cin garin, sannan yayi mata sallama yafita nema,sai alokacin tasamu nutsuwa,qarfin jikinta yadawo harta samu damar gyangyad'i anan qasan bishiyar.

Baidawo gidan ba sai yamma lis,hannunsa d'aukeda baqar leda,alokacin tana zaune tana tunanin yanda zatayi tasamu kudi taje tasaro kayan gwanjo kamar yanda tasaba siyarwa kafin jarinta ya karye.

Zama yayi kusa da'ita yace"Bilkisu ga gaarin kwaki nasake samo mana"

Wani irin farinciki ne ya wanzu a fuskarta,ta kalleshi da kulawa "Ina kasamu kudi Malam?"

Cikin farinciki yace"bakin titi naje na zauna, sai Allah yakawo wani baqo,na kar6i kayansa nayi masa dako,yad'auki naira hamsin yabani,shine naje shago nasiyo mana garin kwaki dashi,kinga ai zamu dade muna ci"

Gaarin taduba tagani sannan tamaida dubanta gareshi tace"ai kuma babu abun had'i malam,ko zaka daure kamaida masa saiya rage gaarin yasako mana siga na canjin?"

Saida malam Manu yayi jimmm...sannan yace"eh kema kuma kince wani abu,to bari naje nakai masa,duk abinda kikace ai haka za'a yi Mai gadon zinare..."

Murmushi tayi batare datace masa komai ba,har yaje yadawo tana tunanin mafita akan yanda za'a yi tasake Samun jarin kayan gwanjo amma tarasa mafita.

Bayan sunyi shirin bacci da daddare tanajin yanda yake shafe mata jikinta da Addu'ah,ta kalli kyakykywan Black Beauty d'in mijin nata tana yaba irin kulawar dayake bata duk da bashi dashi,cikin qasan zuciyarta tanajin qaunar sa tana sake ninkuwa aranta,cikin kulawa dawata irin soyaiya tace"SULAIMAN...."

Cikin sauri ya kalleta,saboda zai Iya cewa yadad'e rabon dayaji Bilkisu takira sunansa kai tsaye,saide Malam,amma yasan cewa duk yanda akayi maganar dazata fad'a masa tabbas mai muhinmanci ce,cikin kulawa yace"na'am mai gadon zinare"

"inason ganin qanina FAROUQ,inaso bayan na haihu kayimin qoqari nasamu naje naganshi,idan ba'a samu kud'in ba,to kasamu ko saqon wasiqa ne atura masa,baisan inada ciki ba,tabbas da yasan halin danake ciki,zaizo yaganni"

"Bilkisu wannan ne abun dakike buqata?"

Ahankali ta d'aga masa kanta alamun amsawa.

Ajiyar zuciya yasauke yace"nayi miki alqawari insha Allah zanyi abinda kikace Bilkisu,kina haihuwa dazaran kin zubar da wanka zamu shirya ni dake muje can nijar d'in kiga danginki,kinga nima nasake ganin FAROUQ d'in,rabona dashi tun bayan aure na dake"

Daganan yad'aga hannayesa yayi karatu yatofa acikin hannun nasa, sannan yasake bin jikinta yana shafa mata addu'ar har hannunsa yasauka akan manya-manyan nashanunta,wani irin numfashi ta sauke najin dad'i,tanajin yanda yake murza mata nashanunta ko kad'an batayi kuskuren hanashi ba,daga baya ya lalla6a ya kwanta,yanaci gaba da abinda yake har yayi nasarar futo dasu waje yad'ora bakinsa akai,wani irin numfashi taja med'an qara wanda yake nuni da cewa taji dad'in abinda yafara d'in,wannan dalilin yana d'aya daga cikin abinda yasa take qaunar Manu,kuma tayi haqurin zama dashi saboda shid'in ba baya bane ta wannan Fannin,ya'iya sarrafa mace sosai.

Tsawon lokaci yana abu d'aya kamar jariri,ahankali tasaka hannayenta tariqe fuskarsa dashi,cikin sanyin murya me cikeda kasala dajin dad'i tace"meyasa Manu na baya gajiya da shan wannan abun ne?"

Murmushi yayi yace"ajinina abun yake Bilkisu,bazan Iya daina soba,koda abunda yake cikinki yazo wannan duniyar,bazan Iya barmasa yadinga sha shi kad'ai ba"(🙈)

Murmushi tayi me sauti,bata qara cemasa komai ba,hakanne yabashi qwarin gwiwar jiyar dasu wani irin dad'i wanda yasa suka manta da hali dakuma quncin rayuwar dasuke ciki.

Washegari da safe garin kwakin daya siyo musu jiya shi suka jiqa sukasha,sannan yayi mata sallama yafita,bai dad'e da fita ba aka kawo mata wankau,babu musu ta kar6a tazauna tafara wanke musu kayan tana daga zaune,tana cikin shanya kayan wankin aka sake kawo mata surfen dawa,shima ta kar6a ta surfa ta bushe musu,tanemi waje ta zauna ta qirga kud'ad'en data samu yakama naira dari biyu da hamsin,kudin ta ajiye agefenta, sannan ta zubawa tafin hannunta ido tana kallon yanda hannunta yayi wani iri,uwa uba gefen hannunta duk yayi kanta gashi hannun yayi wani irin tauri kamar ba hannun mace ba,amma data tuna yawan kudin data samu har d'ari biyu da hamsin sai hankalinta ya kwanta ta manta da batun halin da hannun nata yake ciki,taji komai yawuce.
Hijabin ta ta d'auka tazura, sannan ta nemi niqab dinta ta d'aura,tafuto tanufi gidan Tabawa me kayan gwanjo,gaba d'aya kudin hannunta tabata,tasiyo wasu daga cikin kayan gwanjo na yara,bata koma gida ba saida tabiya wajan wata tela tarage mata fad'in kayan,sannan ta nufo gida tashiga maqotanta tana shaida musu cewa ankawo kayan gwanjo.

Bayan Malam Manu yadawo ta nuna masa,yayi farinciki sosai yayi mata Addu'ah akan Allah yasa albarka, Washegari da safe bayan malam Manu yafita itama shiryawa tayi kamar kullum tasaka niqab dinta tashiga cikin gari,tana tafiya ahankali tana shiga gida-gida tana tallar gwanjon kayanta,kasancewar yanayin damuna ake ciki hakan yasa bata dawo gida da kaya ko d'ayaba,dukansu ta saida su tas.

Cikin farinciki tadawo gida ta zauna ta qirga kud'in da ribar data samu dakuma uwar kud'in gaba d'aya kud'i suka koma naira d'ari bakwai,cikin farinciki ta d'aga hannunta tafara godewa Allah bisa ni'imar dayayi mata,dakuma nasibin datake dashi akan kayan gwanjo.

Malam Manu kuwa bai nufo gida ba sai yamma lis, yana cikin tafiya yaga mutane sunsha gabansa,cikin tashin hankali yaja yatsaya saboda ganin gaba d'ayansu babu wanda baici bashi awajansa ba,ciki harda Aminu me shago wanda yaje ya kar6i bashin alabo a wajansa tun Bilkisu tana laulayin ciki,cikin qarfin hali malam Manu yace"Aminu ya akayi kukasha gabana kuka tareni haka babu magana,aiko hannu kwabani mu gaisa ko?"

Cikin tsantsar rashin kunya Aminu yace"Malam Manu munji labarin ka saida kekenka harka samu sukunin biyan bashi amma mu dayake munyi shiru mun zubama ido shine kahanamu namu kud'in,to munga alama kud'ad'en mu kariga kaci ham,ba futowa zasuyi daga hannunka ba,danhaka gara muyi maka dukan kud'inmu ko zamu huce taqaici..."(🙆🏻‍♀️)

Cikin sauri Malam Manu yace"ku tsaya kuji,kuyi haquri nayi muku bayani wallahi suma wanda suka kar6i kudin..."

Basu bari Malam Manu yagama magana ba suka rufeshi da duka saida suka kaishi qasa,daqyar wani tsoho daya dawo daga gona ya qwaci malam Manu a hannun su,gaba d'aya sun nuna masa jiki,gefen bakinsa ya fashe saida wannan tsoho yabashi sauran ruwa irin wanda ake tafiya dashi gona ya wanke bakinsa, sannan yabashi haquri suka rabu.

Koda ya koma gida bai fad'awa Bilkisu abinda yafaru ba saboda kada hankalin ta yatashi,cikin sanyin jiki Yanemi waje yazauna jikinsa ko'ina yana masa ciwo,umarni yabata tadafa masa ruwan wanka,cikin farinciki kuwa tatashi tadora masa ruwan, yaga sai fara'ah takeyi kamar gonar auduga da alama zata bashi wani daddad'an labari ne,ido yazuba mata yana aikin kallonta,yana tuna irin baiwar da Allah yayi mata na kyau dakuma shi Karan kansa baiwar da ubangiji yamasa na Samun ta amatsayin mata, ya tabbatar da'acikin birni suke babu yanda za'a yi manyan masu kudi su barshi ya auri Bilkisu,duk wani kai kawo datake yana kallonta kamar yasamu tv.
Koda yafuto daga wanka shiru yayi yana kallonta yayi jirim...kamar wanda aka masa albishir da mutuwar sa.
Baiwar Allah Bilkisu batasan yana mata wannan kallon ba,saida ta juyo ta fuskanceshi sannan tace"Malam meyafaru?naga yanayin ka ya sauya meyake damunka?"

"Bilkisu duk lokacin danake tare dake inajina wani mutum na daban,kina 'DEBE MIN KEWA aduk lokacin dana kasance cikin qunci ko tunani,babu abinda yake damuna Ina tunanin hanyar dazanbi ne domin insamo kud'in dazan siya miki raagon suna tunda kin shiga watan haihuwar ki"

Murmushi tayi ta kalleshi tana sakin ajiyar zuciya tace"saboda wannan kake tunani? to Abishirinka,ga kud'in kayan gwanjon dana siyar d'azu naira d'ari bakwai ne,ka ajiyesu awajanka kafara tarawa insha Allahu zamu tara kud'in abun suna"

Cikin farinciki ya kar6i kud'in yana kallonta yace"Bilkisu bai kamata ki tara kud'in abinda zamu siya ayi miki yanka dashi ba,wannan haqqinane amatsayina na uba"

Cikin rashin damuwa tace"karka damu Malam,zan iya sadaukar maka da komai nawa inde zamu taru mu rufawa kanmu asiri,kasaki ranka muyi farinciki malam,ubangiji yana sane damu"

Cikin farinciki Malam Manu yace"hakane Bilkisu,Allah yayi miki Albarka,Allah yabaki abinda kikeso duniya da lahira Bilkisu"

Cikin farinciki tace"Amin Malam"

Kallon kud'in hannunsa yayi,yad'ago kansa ya kalleta lokaci d'aya jikinsa yayi sanyi,kallonta yake kamar ba gobe,saide kwata-kwata batasan yanayi ba,zuciyarta tana cikeda farinciki ta kyautatawa mijinta, tasa shi walwala,akoda yaushe fatan ta tayi sana'ah ko zasu samu su rufawa kansu asiri shiyasa kowa yasanta a unguwar inde aikin hannu ne,babu abinda batayi,itace niqan dutsi,wanki, surfe,dakuma saida kayan gwanjo idan tasamu ribar kud'i me yawa.

Da daddare shine yayi mata Addu'ar bacci kamar yanda suka saba,sama-sama take jinsa yana tofa mata Addu'ah saboda agajiye take tilis nan da nan wani irin nannauyan bacci ya kwasheta.
Chapter 2 · 0% Book details