Sashe 25
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda yaga anata shirye shiryen biki yaji hankalinsa yatashi,ga Na'im dayake ta damunsa akan abubuwan dazasu tsara,hakan yasa yabar Abuja yakoma Lagos yake harkokin sa,bai tashi shirin dawowa daga Abuja ba saida biki yarage saura kwana bakwai shima saboda Mummy tana ta kiransa ne,saide wani abu guda daya dayake bashi mamaki shine yanda yarinyar har yanzu bata sake yimasa magana ba duk da bikin yazo kusa,to saiyayi tunanin tunda auren had'i ne may be itama bataso,hakan yasa yashareta,bazai takura mata ba kokadan,idan zaman auren ma taji zata takura zai iya sauwaqe mata.
Cikin nutsuwa suke tafiya yana zaune abayan mota shi kadai, yadora computer akan cinyarsa yana danne-danne, p.a da driver suna gidan gaba, wayarsa ce tayi qara p.a yajuyo yabashi, bayan ya dauka daga can 6angaren akace"Yalla6ai dama maganar takardun nan ne dakace yau mu tuna maka idan kagama dubawa"
Cikin nutsuwa murya qasa-qasa yace"nagama dubawa zaku Iya zuwa ku kar6a,na shigo Abujan ma"
Cikin girmamawa suka kashe wayar sannan shima ya ajiye tasa agefe yaci gaba da shafa computer sa.
Suna dawowa gida yaga babu kowa afalo,yayi mamaki sosai ganin falon nasu baya rabo da mutane,cikin sauri yawuce dakinsa ya watsa ruwa a gurguje yadawo falon yazauna yana ganin labarai inda ake sanarwa cewa ga jihohin dazasu Iya samun ambaliyar ruwa idan damuna tazo,remote yadauka ya canza channel sannan yasaka hannunsa yadauki inab guda daya yasaka a bakinsa, yajuya gefensa yaji de gidan shiru har yanzu babu wanda ya futo, cikin sauri yatashi yanufi dakin Mummy yaga wayam babu kowa, yajuya yashiga dakin Fu'ad nanma baya nan, hakan yasa kai tsaye yawuce dakin Daddy, yana shiga yaga Fu'ad agefe yayi tagumi, yayinda Mummy take rusgar kuka tana share hawaye da dan kwalin ta,Daddy kuwa yana zagaya falon nasa fuskarsa cikeda damuwa.
Lokaci d'aya jikin Jawad yayi sanyi ya qaraso cikin falon yanufi Mummy yana fadin"mummy meyafaru kike kuka? waye yata6a ki?"
Daddy yajuyo ya kalli Jawad tausayin sa ya kamashi,gaba daya yaron tausayi yake bashi,nafarko har zuwa wannan lokacin baisan asalin suwaye iyayensa ba,yanzu ma gawata qaddarar tasake samunsa,ganin Hajiya Zaliha tana kuka takasa jurewa tayi magana hakan yasa Daddy yadaure yace"Jawad saide kayi haquri Allah yayiwa Amal rasuwa yanzu,gaba dayanmu mun rasa ta'ina zamu iya kiranka muyi maka wannan maganar, ga biki ya matso,ina fatan zaka kar6i qaddara da hannu biyu"
Jawad yadago ya kalli Daddy cikin sanyin jiki,lokaci daya chat dinsu yafado masa,sai yaji bai kyauta mataba datace suje susha ice-cream yanuna baida lokaci,yana qin aure ashe ashe yarinyar ma ba zataga bikin ba,toko alamun mutuwar tafara ji shiyasa bata sake nemansa ba?
Ahankali yafurta kalmar "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"
Sannan yazauna kusada Mummy ya rungume ta yana bubbuga bayanta alamun lallashi saboda yasan cewa Mummy tafi kowa qwallafa rai akan auren nan,kuma dole zataji mutuwar saboda yanda ta shaqu da Uncle Bature mahaifin Amal din, cikin sigar lallashi yace"Mummy kiyi haquri kidena kuka,muma jiran tamu mutuwar muke, kiyi haquri"
Hajiya Zaliha tasa hannu tasake rungume Jawad tana kuka tace"kaima kayi haquri Jawad,kai akaiwa rashi kayi haquri Jawad"
Jawad baice komai ba sai kansa daya jinjina kawai.
Hajiya Zaliha tadauki wayarta takira Yaya Mariya yayar Daddy, bugu daya Yaya Mariya ta dauka, Hajiya Zaliha tace"Yaya idan kingama Ina jiranki kizo muje gidan suturar nan"
Yaya Mariya tace"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un ni Mariya waye yarasu?"
Hajiya Zaliha ta share hawayen idonta tace"Amal ta rigamu gidan gaskiya Yaya"
Cikin sauri Yaya Mariya tace"ke dakata Zaliha!!,wacce Amal kike magana akai?, tarigamu gidan gaskiya kamar Yaya? ba dazu-dazu aka nunamin Amal din tana live video na tik-tok ba? kode wata Amal din kike nufi?"
Hajiya Zaliha tace"wallahi Yaya da gaske nake,Amal ta mutu,yanzun nan Yaya Bature yakirani yake sanar dani hakan"
Yaya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"shi Baturen ne yace 'yar tasa tamutu? nadade da sawa a dinga bimin diddigin yarinyar fa, kuma tunda akasa ranar aurenta da Jawad kullum saitayi video na fitsara ta dora a shafinta na tiktok,ga wasu filla-fillan motoci da yarinyar take hawa kullum da irin motar dazata sake posting tana yawo da qawaye a mota saikace yar gidan shugaban qasa,zanje har gidan Baturen yanzu inje Inga gawar Amal din da idona"
Tana fadin haka ta kashe waya.
Lokaci d'aya gaban Mummy yayi wata irjn bugawa,kanta ya Sara, amma babu wanda ya lura da hakan.
Jawad ya sunkuyar da kansa qasa bayan dukansu sungama jin komai kasancewar babbar waya babu rufin asiri, kwata-kwata yarasa meyasa Yaya Mariya take haka,mutuwa aita wuce wasa,ya za'ai mutum bemutu ba kuma mahaifinsa da kansa yace ya mutu?.
Daddy yace"Allah yarufa asiri"
Ya kallesu gaba dayansu yace"muje falo sai nayiwa Man Sulaiman magana shida maqota su shirya suzo muwuce gidan suturar gaba daya, karmu rasa jana'iza.
Babu musu dukansu suka nufo Babban falon qasa.
****
Kai tsaye Hajiya Mariya ta yiwa Sojan dayake mata aiki waya,shine tasa yake kula da duk wani shige da ficen Amal,haka yayi following nata ako wanne kafar sada zumunta datake amfani, duk wani abu datake posting yana gani, shikuma idan yagani zai turawa Yaya Mariya,tunda akasa ranar auren hankalin ta bai kwanta da yarinyar ba,saboda ko a vedio wani lokacin duk da maza takeyi tana ganin hakan kamar wayewa ce, abun yana yiwa Yaya Mariya ciwo, Jawad nutsatstse, shiba magana ba,shiba hayaniya ba,idan aka bashi yarinyar kamar da cutarwa aciki, to amma ganin yarinyar yar gidan yayan Zaliha ce kuma Daddy yabata haquri, hakan yasa ta danne komai tazuba musu ido.
Wayarsa tana shiga yadauka, Hajiya Zaliha tace"Yaya batun aikin dana baka?"
Cikin ladabi yace" Hajiya anakan yi, yanzu haka ma Ina tareda ita,taje super market"
Yaya Mariya tasaki wata irin ajiyar zuciya tace"ka tabbatar Amal din kagani da idonka?"
Yace" yes Ma"
Cikin 6acin rai tace"wanka mata mari kasakota amota kutaho gidan ubanta,nima ganinan zuwa"
Babu musu wannan soja yanufi Amal gadan-gadan,yana zuwa kawai gefen rigar sa yadaga yanuna mata wata bindiga sannan yasauke rigar sa yayi mata nuni da mota, babu musu Amal tashige mota shima yashiga yazauna ya futo da bindiga yana shafata yadaka mata tsawa yace"muje gida"
Cikin sauri Amal tata da mota jikinta yana rawa suka nufi gidansu.
Suna zuwa bakin get suka tarar da Hajiya Mariya tana tsaye tana jiran su sai kaikawo take, tana ganin su ko jira batayi sun bude motar ba tabude dakanta takamo hannun Amal tajata suka shiga gidan,babu kowa agidan sai yan tsirarun mutane da basu fi mutum goma ba, suma duk yan'uwansa ne dangin su Hajiya Zaliha babu maqota babu yan'unguwa tabbacin abun dama shiryaiye ne.
Kota kansu batabiba taja Amal sukayi ciki,saida ta dire Amal a falonsu sannan ta daga murya tace"Bature!!!"
Cikin sauri Uncle Bature da matarsa suka futo jin kiran kamar bana hankali bane,yana ganin Amal yatsaya yayi turus, yarinyar daya turata gidan abokinsa yace karta kuskura tafuto waje menene yakaita futowa har wannan masifaffiyar matar taganta?
Yaya Mariya ta nuna Uncle Bature da hannu tace"kaikam Bature anyi girman banza wallahi,karasa wacce zaka ha'inta sai qanwar ka, toka sani kanka kayiwa, dama banda Zaliha ta dage me Jawad zaiyi da wata Amal,inde Amal ce gatanan kadena d'ora mata mutuwa kwanan ta bai qare ba,gata nan saika jiqata kasha,duk kud'ad'en da'aka turo maka kuma kayi gaggawar maida su"
Alhaji Bature dayaga bashida wata mafita asirinsa yariga yagama tonuwa saiya fara kuskurin kunya da fadan qarfin hali yace"ke dakata Mariya,yazakizo har cikin gidana kina fadamin maganar da kikaga dama? ko cewa nayi Amal tamutu ta rayo babu abinda yamiki zafi yarinya de 'yata ce,kuma dakike maganar Zaliha Zaliha aida ita muka shirya komai, dan haka idan kin shirya tonamin asiri ne toki had'a da matar qaninki ki tona mana asiri gaba d'aya,Amal kuma dama banda niyyar bata DAN TSUNTUWA"
Wannan furucin na Alhaji Bature yadaki Yaya Mariya,har saida taji wani jiri-jiri yana dibarta, numfashinta yafara yin sama, amma tsabar masifar datakeji haka ta kalleshi tace"okay haka kace ko? to gaba dayanku daga kai har Zalihan na isheku riga da wando,matsiyata dangin maciya amana, kuma insha Allahu saikunga irin matarda Jawad zai aura,saiya auri wacce ta ninka Amal sau dubu"
Tana fadin haka tajuya tafice tabar gidan,Sojan daya biyo Amal suka dawo gida tabawa key din motar ta tace"kaini chemist mafi kusa"
Cikin sauri ya kar6i key din yashiga yaja motar aguje suka nemi chemist, yana tsayawa tafuto tashiga ta kar6i maganin hawan jini tasha,saboda tabar nata agida, kuma tabbas wannan mummunan labarin da taji tasan cewa zai Iya tada mata hawan jinin ta, batafi minti biyar ba tafuto tace masa yakaita gidan Aliyu Mekudi.
Ahanya kawai lumshe idonta tayi tana maimaita hailala aranta har sukazo gidan Alhaji Mekudi,anan taga ana sake goge motoci da alama gidan rasuwar qaryar zasuje.
Tana qarasawa falo kuwa taga Daddy da Fu'ad da Jawad duk sun gama shiryawa zasu tafi.
ta kalli Daddy tace"Aliyu Ina zuwa?"
Yanda yaji muryar ta tayi magana hakan ne yasake tabbatar masa da cewa ba lafiya ba, yace"gidan rasuwar zamuje Yaya"
Yaya Mariya ta girgiza kanta tace"bade gidan rasuwa ba,saide kace gidan tantirai kokuma kace gidan dangin tantirai"(🙆🏻♀️)
Fu'ad da Jawad suka hada ido kowa fuskarsa daukeda tsananin damuwa.
Yaya Mariya ta kalli Daddy tace"yarinya tana nan da ranta da lafiyar ta bata mutu ba ina tunanin ma tafika lafiya,ubanta de yace bazai bamu yarsa ba, kudi da'aka tura musu kuma sun cinye bazasu biya ba,amma maganar mutuwar yarinya babu ita, Amal tana nan araye saide tahadu da iyaye tsofaffin najadu..."(🙆🏻♀️)
Daddy yace"Subhanallah..."
Jawad da Fu'ad kuwa ganin cewa maganar ba qarama bace, hakan yasa suka tashi suka basu waje suka wuce sama,Jawad baisan dalili ba haka nan yake jin ransa sakayau kamar ancire masa wata qaya daga jikinsa.
Yaya Mariya saida ta tabbatar su Jawad basa nan sannan ta kalli Hajiya Zaliha suka hada ido,Hajiya Zaliha tayi maza ta sunkuyar da kanta qasa,Yaya Mariya tasaka hannu ta goge hawayen taqaici tace"zaliha kin bani mamaki,nayi tunanin da Jawad,da duk abinda ya mallaka naki ne...."
(yara marayu wanda basu tashi da iyayensu ba, da wanda aka tsinta Allah ya bayyana muku iyayenku idan da rabon haduwar ku da juna😭😭😭)
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.
300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.
Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.