← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 63

Sashe 28

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ilyasu manager baiyi qasa a gwiwa ba yahada meeting din gaggawa,duk wanda yashigo dakin taron cikin ransa yana mamakin cewa wanne irin taro ne haka yataso na gaggawa,zama sukai akan dogon table din dasuke zama domin meeting yayinda aka ajiyewa kowa gorar ruwan DALLOL agabansa,bayan kowa ya nutsu manager yayi gyaran murya sannan yace"nataraku anan ne domin in sanar daku cewa munsamu saqo daga mamallakin wannan kamfani wato Yalla6ai Jawad Mekudi,zaiyi taron qarin shekara a qasar Kuwait,Allah da ikonsa kamfanin mu yana cikin wanda zasuje wannan qasa domin tayashi murna..."

Gaban Inaas yayanke yafadi,tunda ya ambaci sunan Jawad takejin fad'uwar gaba, amma saita maze ta sunkuyar da kanta qasa.

Manager yaci gaba da fadin" munsamu kyautar tickets na mutum biyar,saboda haka wannan kamfanin namu yayi selecting mutum biyar din dazasu je ciki harda Inaas Omar Farouq "

Cikin sauri Inaas tadago kanta tana kallon manager,gabanta yaci gaba da faduwa hannunta yafara rawa.

Ahankali surutu yafara tashi adakin meeting din nasu kowa sai qus-qus yake dana kusa dashi suna sake tabbatar wa cewa lalle da gaske zargin da'ake ya tabbata, manager son Inaas yake (😂🤭)
duba da yanda mamallakin kamfani Jawad Mekudi yazo yakoreta aiki,amma manager yadawo da ita,kuma daya dawo da ita dinma sai wani nan-nan yake da'ita yana bata girma kamar wata 'yar wani.

Manager yaci gaba da fadin"idan akwai me magana kokuma wanda zai bada wata shawara dangane da wannan tafiya zai iya magana"

Daya daga cikin maza yadaga hannu alamun yanada abun fada,hankalin manager da sauran mutane yadawo kansa,yayi gyaran murya sannan yace"gaskiya munji dadin wannan al'amari,wannan ma wata babbar nasara ce da kamfanin mu yasamu wanda abaya bamu ta6a samun irinta ba,saide inaso nabada shawara akan yakamata kamfani ya shirya masa wata 'yar kyauta wadda za'a kai masa domin nuna jin dadinmu akan wannan gayyata"

Manager ya jinjina kansa yace"wannan hakane,zamuyi qoqarin hakan insha Allah,sannan duk wanda wannan tafiya tafad'o kansu,zasu Iya tafiya gida su shirya,idan lokacin tashinmu yayi,saisu futo mu wuce"

Yadauki wata takarda ya karanto sunayen mutum biyu maza,sai shi na uku,sai wata mace saboda yasan halin ta batada surutu kuma tanada kamun kai sosai babbar mace ce,itace ta hudu, saikuma Inaas ta biyar.

Daga nan taro yatashi,Inaas tawuce office dinta ta dauki Jakarta tafuto tarufe office din sannan ta nufi gida jikinta a sanyaye,har yanzu mamaki take to ita awa? dazata shiga cikin jerin wanda za'ai wannan tafiyar dasu? sannan manager bai ta6a nuna mata wata alama da zatayi zargin sonta yake ba,tunda tadawo bakin aikinta taga yana girmamata abun har tsoro yake bata.

Tana shigowa gida taga Abbanta yaci manyan kaya yanad'a rawani a kansa irinna buzaye da alama fita zaiyi,Bilkisu datake gefe a zaune tana ninke kayan wanki tadago ta kalleta tace"yanaga kindawo jiki a sanyaye bade korarki sukayi ba?"

Abbanta ma yanemi waje ya zauna yana jiran amsar ta.
Zama tayi agefe jikinta duk a sanyaye sannan tace" Ammiy wannan Jawad din da yazo gidannan kin tuna shi ko?"

Cikin sauri Bilkisu tace"sosai kuwa,menene ya sameshi? aiba cutar dashi akayi bako?"

Abban Inaas da ita kanta Inaas din duk sai suka kalleta da tsananin mamaki,ganin daga cewa Jawad duk tabi ta rude tana tsoro kar ace wani abu ne ya sameshi.

Inaas tace"A a babu abinda aka masa,wai shine zaiyi Birthday awata qasa,sai akace zamuje muyi masa murna muma"

Cikin sauri Abbanta yace"ban fahimta ba,yanzu dama ita taya murna harta wuce a kirashi awaya kokuma atura masa saqo dole sai anje har wata qasa? toki fada musu babu inda zakije"

Cikin ladabi Inaas tace"to Abba"

Sannan ta dauki wayar Ammiy,tabude Jakarta ta dauki wata takarda wadda number manager take ciki sannan ta kirashi, yana dauka tace"yalla6ai dama zan baka haquri ne ko za'a sa sunan wata a gurbina saboda Abbana yace inbaka haquri ba zanje ba"

Manager yanajin haka gabansa yafadi,shi ya'isa yaje wannan qasa babu wannan yarinyar?(🤔)

Cikin sauri yace"kinga Inaas,bai wuce awa biyu yarage ba jirginmu zai tashi,ki cewa Abbanki yajirani agida, gani nan zuwa"

Inaas tace"to Yalla6ai"

Sannan ta kashe wayar ta kalli Abbanta tace"Abba nafada masa,yacemin infada ma dan Allah kajira shi zaizo yanzu"

Abbanta baice komai ba,itama daga haka bata sake cewa komai ba tawuce daki.
Bilkisu tasaki ajiyar zuciya tace"Farouq dakayi haquri taje,Inaas ba zatayi wani abu ba kaide barta a surutun ta kawai,amma kasan cewa ba zatayi shashanci ba,sannan yaron nan ni sheda ce yanada hankali wallahi,kuma tafiyar nan bafa ita kadai akace mutura masa ba,da mutane zasuje,idan wani abu kake tunani me wannan yaron zaiyi da Inaas? ai munsani cewa yafi qarfinta ruwa ba sa'an kwando bane,amma bai kamata dama ta samu, sannan kaikuma kahana ba,inde ka yarda da tarbiyar dana bawa Inaas to karkaji ko d'ar aranka,zataje ko'ina kuma ta dawo lafiya,bare ma yaron nan wallahi naga a nutse yake,bashida hali marar kyau"

Farouq ya kalli Bilkisu ya girgiza kansa yace"Yaya kenan, sai yabonsa kike kamar kin zauna dashi tsawon shekaru kin karanci halinsa"

Bilkisu tayi shiru ta qyaleshi bata sake magana ba.

Inaas tafuto ta dauki buta tawuce bandaki, adede lokacin kuma manager ya Parker motarsa a qofar gidan,yadaga murya yayi sallama, Abban Inaas yatashi yafita waje yabashi hannu suka gaisa, sannan yace"Bissmillah shigo daga ciki mana"

Bilkisu tatashi tayafa mayafi sannan ta Shimfida musu tabarma suka zauna,takawo shayi me zafi ta'ajiye masa.

Abban Inaas yace"yanzu Inaas tazo min da wata magana,to ba komai ne yasa nace ba zataje ba kasan yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba,kadauki 'ya mace katura wata qasa ba tareda muharramin taba akwai matsala,shiyasa nace ba zataje ba"

Manager yayi murmushi yace"wannan haka yake,kayi gaskiya, kuma kowanne uba dole zaiyi wannan tunanin,amma inaso kabani amanar Inaas,zan riqeta amana tunda dani za'a yi tafiyar nan zamuje lafiya mudawo lafiya insha Allah,yanda nazo gida na dauketa,dakaina zan dawo da'ita gida, insha Allah nayima alqawarin babu abinda zai sameta"

Abban Inaas yayi ajiyar zuciya sannan yace"to Alhamdulillah,yanzu kaga hankali na zaifi kwanciya"

Yadaga murya yace"Ke kina ina? futo kutafi"

Inaas tafuto daga bandaki ta wanke hannunta,sannan tashiga daki ta sauya kayanta tafuto,manager yatashi shima Abban nata yatashi tsaye yace"nima wajan daurin aure zanje gidan Alhaji Auwal, yau za'a daura auren yaransa,aida har Airport din zamuje na rakaku"

Manager yace"ato muje mana tunda hanya ce saimu saukeka,nima badan wannan tafiyar tamu ba aida zan halarci daurin auren"

Abba yace"to shikkenan nagode sosai muje"

Suna fita, Bilkisu ta janyo Inaas takama kunnanta ta riqe dakyau sannan tace"kishiga hankalin ki dakyau kina jina?"

Cikin sauri Inaas tadora hannunta akan kunnanta tana runtse ido tace" to Ammiy"

Bilkisu tasaki kunnanta sannan tace"idan kunje babu ruwanki da wannan surutun naki,ki zauna awaje daya ki nutsu kiyi shiru kinji?"(😂)

Inaas tace" to Ammiy,dama ni babu ruwana da kowa"

Bilkisu ta kalli kyakykywar fuskar 'yar tata sannan tasa hannunta tana sake goge mata fuskar tana cewa"wannan fuska taki ko kwalli baki saka mataba,bare powder,kinde ji menace miki ki nutsu idan kinje,ungo wannan kudin ko zakiga abu ki siya a hanya"

tafadi haka tana zaro kudi agefen zaninta, Inaas ta kar6a tafice, Bilkisu ta taraka ta har bakin mota tana daga musu hannu, saida sukai nisa ta daina ganinsu sannan ta juyo gida ranta fes kamar ba wata qasa 'yar tata tatafi ba, musanman idan tatuna wajan Jawad tatafi haka kawai sai taji hankalin ta ya kwanta, domin kuwa kokad'an bata yiwa yaron kallon tantiri.

Har qofar gidan Alhaji Auwal manager ya ajiye Abba, sannan Abba yayi mata nasiha yashige gidan, ita kuma suka tafi itada manager idonta yana kan gidan tana kallon tsantsar kyau irinna gidan kana gani kasan ba gidan qaramin Mekudi bane.

Tayi tunanin Airport zasu wuce,sai taga sun dauki wata hanya saida sukaje wani shago yatsaya yajuyo ya kalleta yace"kishiga cikin shagon nan Hajiya Halima ma tana ciki,kuyi sauri kufuto"

Inaas kanta ya daure, tarasa me zatayi a shagon?
amma ganin yace mata Hajiya Halima tana ciki,kuma tasan Hajiya Haliman itace wacce akace zasu tafi tareda ita,hakan yasa tafuto tashiga cikin shagon, tana shiga Hajiya Halima ta nunawa masu shagon Inaas tace"yauwa gata nan ma ta qaraso"

Matar ta kalli Inaas tace"sannu da zuwa yanmata zauna mufara"

Inaas tarasa meza'a fara,taja kujera ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido.
Dogon gashinta suka kunce kasancewar a wanke yake hakan yasa suka shafa mata mayuka aka sake taje shi da hand rayer, yasake miqewa yayi kyau,akayi mata light makeup, sannan suka bata wata hadaddiyar laffaya baqa,wadda taji duwatsu sai walwali take,aka bata yar fos tariqe tareda takalmi mai kyau,bayan angama data kalli kanta a madubi ita kanta tasan cewa bata ta6a yin masifar kyau irin wannan ba.
Saide tarasa dalilin wannan gyara dasuke mata.

Suna futowa manager dayake zaune amota ya kalleta yayi saurin kawar da kansa tun kafin ma yaji aransa cewa Inama ace zata zama mallakinsa.(🤭)

Sai yanzu ne yasake yarda cewa lalle Yalla6ai Jawad baiyi za6en tumun dare ba,duk wanda ya kalleta karon farko babu qarya zaice ita din matar manya ce.

Tunda suka sauka a qasar Kuwait,Inaas taketa kalle-kalle, har wasu had'ad'd'un motoci sukazo suka dauke su,mazan sai firar su suke yayinda Hajiya Halima take ta danna waya,Inaas kuwa da batada waya hankalin ta yana kan window tana bawa idonta abinci,kai tsaye wani gida aka wuce dasu,suka yada zango a babban falon,abinci aka kawo musu da lemuka da ruwa,sukaci suka sha yayinda Inaas tafi maida hankali wajan cin nama,daga nan mazan suka fita,Hajiya Halima tahau WhatsApp tana voice note da mutanan gida,Inaas kuwa tashi tayi tai sallah sannan tadawo falon ta gyara zamanta ta lumshe idonta lokaci daya bacci ya dauketa.

Batasan tsawon lokacin data dauka tana bacci ba saiji tayi Hajiya Halima tana tashinta,cikin murmushi tace"Inaas tashi zamu tafi wajan Birthday din"

Inaas tatashi,ta dauki fos dinta zata wuce Hajiya Halima tace"haba Inaas kamar ba yanmata ba,zona gyara miki fuskar taki mana"

Kasancewar ta babbar mace, hakan yasa Inaas din ta tsaya, babu musu Hajiya Halima tasake gyara mata fuska,Inaas tafuto tai ras da'ita, sannan takamo hannunta suka futo.
Chapter 28 · 0% Book details